Addininmu Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  S Reza Category :  Love

Chapter   13 / 37

36K to 39K   out of 109.2K words

su kawo min kuɗaɗena kokuma namu hukuncin da babu wanda zai yarda cewar nune ubansu, barinma wacce muna fukar da ta ɗauki kuɗinan tana kaiwa musulmi wanda nakejin da nayi ido biyu da su ƙwara a ce bani da idon, bazan taɓa ƙwanar mutanananba na tsanesu , Walhi inajin idan na kama wannan yaron AJ to tabbas zan iya kasheshi. Cikin tsananin ƙiyayar da sukewa musulmai itama mommy ta ce "Ni sonake ka kaini police station ɗin da kakai ƴan uwansa na fara zuwa naci mutuncinsu tukunna Amma kace wai ba hakaba.

Daddy ya ce "Yanzu haka daga chan nake, nasa an ci ubansu sannan ance wai ana kawo musu abinci, nasa an kori police ɗin da yabada umarnin shiga da abincin, yanzu haka nasa wani mai kula dasu ɗin kuma nace masa duk wanda yazo gurinsu ya barshi ya shiga amma ya kirani. Cikin jin daɗi Mommy ta ce "God! Idan ma yaronnane yake kai musu abincin ai zamu ganeshi. Daddy ya ce "Nima hk nake tunani kodai yaronne?.

Samuel da Sarah kuwa duk abunda akeyi suna ji. Kuka Sarah takeyi tana cewar Pls Samuel call AJ please. Shima kansa Samuel ɗin yana son yaga waye wannan AJ ɗin, sannan shima yana kiran numbar Umar amma no amsar.

*HAJIYA BABBA AJ POB*

Tafiya sukeyi a bakin wani ƙaton hotel ɗin da suka kama a ƙasar morocco mai ɗauke da sunan *HALIDYS HOTEL* Kusan duk wanda ya gansu saiya ƙara kallonsu domin kuwa kana ganin su kaga uwa da ɗanta, amma yanda suke a manne da junane zaisa ka ƙara kallonsu domin kuwa sunyi kama da masoya, bakin ƙofar hotel ɗin suka tsaya kafin Hajiya Babba ta kalleshi cike da tsananin sha'awar sa da kullum take zamar mata sabuwa da kuma yanda yake iya jure buƙatarta fiye da sauran mazan da ta zauna dasu. Kallon fuskarsa tayi wacce kana gani kasan yana cikin damuwa sosai ta ce "Aj angon Hajiya Babba inji yaranta! Yanzu idan muka koma Nijeriya yazamuyi da su Salis da laɗifa? Domin fa ni gaskiya ko mun koma 9j to Muna tare dan bazan iya nisa dakaiba.

Idan bai mantaba yau suke kwana huɗu kenan da zuwa Morocco sannan kuma yana jin cewar daga wannan kwana baƙwaɗin tofa komai zaifaru bazai ƙara kwana batare da yaga Nana da Innah ba harma da Sarah waccce yanzu yake yawan mafarkin tana cikin wani hali na taimakonta. Ya ce "Ai bamuyi cewa zamu zauna a gidankiba idan mukakoma Naiger, kodan saboda yaranki, saboda haka a gidanmu zan zauna.

Hajiya ta ce "Yanzu idan na ce muyi sati biyu a matsayin shekara ɗan da nace maka idan yaso tun. A nann na baka kuɗinka muna zuwa Najerya sai kawai ka ci kuɗin shin zaka yarda? Ka daiyi tunani miliyon 50 a sati biyu ba wasaba....📝










*INA KUKE S REZA FAN'S?⁉️⁉️⁉️*

A kwai wani tsohon littafi na da na rubuta, mai suna so ne. Tom na sake dawo muku dashi domin wanda basu karantaba su karanta. Littafin soyayya ne. Soyayya mai taɓa zuciya, littafin da masoyana suka dameni akan na sake dawo musu dashi. Tom in Sha Allah zan dinga haɗa muku da wannan na ADDINIMU zai dinga zuwar muku a tare, domin farin cikin ku. Littafin *SO NE* Littafine da ya ƙunshi soyayya mai tarin abubuwan allajabi, mai rama tsakanin masoya. Ku kasance da littafin domin suna tare da littafin *ADDINIMU* kuma dukkansu free ne, domin jin daɗin ku🥰🥰 *ADDINIMU*.da. *SO NE?* ❤️






*

*PAGE* 1️⃣9️⃣

........Kallonta yayi da kyu cikin wani sabon mamakin da tun da suka haɗu take bashi ya ce "Hajiya ban gane me kike nufiba? Hajiya Babba ta kalleshi cikeda maradin sa ta ce "Inaso muyi sati biyu a nan in yaso muna komawa 9j shikenan kaci kuɗinka? "Kina nufin daga haka mun gama auran kenann? Hajiya ta ce " Eh haka nake nufi. Cikin tsananin mamaki da farin ciki AJ ya shiga tinanin abubuwan da zaiyi idan ya mallaki wannan kuɗin fayan kwana goma. Hajiya ta ce "Bakace komai ba? Ya ce "Na amin ce, saura kwana goma kenan ko? Hajiya ta ce "Eh hakane. Tinda sukazo ƙasar Morocco Hajiya Babba bata ga farin ciki a fuskar angon nataba sai yanzu, domin kuwa ya dawo kamar ba AJ mai surutu da abun dariya da fara'a ba, tashi tayi ta kama hannun sa tana masa alama da ido. Kaman yanda suka saba kullum Hajiya saita buƙaci mijin nata sau huɗu a rana, wani lokaci ma har fiye da haka, shikuwa gogan naku tun bai saki jiki da itaba har ya ware shima ya ɓarzi abarsa domin kuwa da yana tsoro kar wani abu ya faru, idan yaran ta sun gane, amma da yaga ita ko a jikinta sai kawai ya fara abubuwan da takeso, dukda kuwa yana shan wahala domin kuwa wani lokacin har fita yakeyi a haiyacin sa.

Yauma abun da ya faru kenann domin AJ ya nunamata cewar yau fa yana cikin farincin, warewa yayi suka sha love da ƴar tsohuwar abokin nasa, amma fa saida ya gaji ya barta, saida yaji ta gamsu kafin ta yayyafa masa ruwa ya farka.

*SALISU*

Yakira numbar AJ ya kai sau goma amma bata shiga, sai kawai ya nufi police station ɗin cikin sauri domin kuwa gabansa na faɗuwa. Da sauri ya shiga gurin yana kallon sabon ɗan sanda da ke tsaye a gurin ba wanda ya saba ganiba, kasan cewar police station ɗin tsohone babu wasu ma'aikata a guri sai ƴan kaɗan hakanne yasa gurin ko mai gadi babu. Ɗan sandan ne ya tareshi yana cewa "Lfy daga ina me kake ne? Salis ya ce "Wasu mata da suke cikin gurinnan ɗazu sunake nema Pls?.

Cikin mamaki ɗan sandan ya ce "Kaine AJ? Salis ya mai-maita suna kafin ya ce "Pls ina police ɗin da ke gurin ɗazu? Cikin ɓacin rai police ɗin ya ciro waya yana dannawa kafin a ɗaga ya ce "Police ɗin dage gurin nann kuma an koreshi a aiki, sukuma wanda kazo nema an sake musu guri.

Cak Salis ya tsaya yana kallon police ɗin cikin mamaki, Salis ya buɗe baki zaiyi magana ya ji ɗan sandan na cewa "Yes sir ga wanda yake kawo musu abincin yazo, ina tsammanin ma shine AJ ɗin. Police ɗin yayi shiru yana ƙamewa a gurin kamar wani gunki yana sauraron abunda a ke cewa daga cikin wayan. Saida ya gama jin abunda a kace sannan cikin tsan-tsar girmamawa ya ce "Yes sir an gama. Salis dai sai kallonsa yake cikin mmk. Yana gama wayar ya kira wasu ƴansan dan ai kuwa nan take suka maƙala masa onka, suka turashi a cikin sel ɗin da su Innah suka fita. Yana tambayarsu lfy lfy amma ina saida suka turashi.

*LAƊIFA POV*

Salis na fita daga gida itama ta shiga ɗaki ta shirya ta ɗauki ATM card ɗinta ta shiga kiran numbar Umar. Bayan Umar ya ɗaukane ta sanar dashi cewar yazo ya karɓi kuɗin ya kai. Cikin murna Umaru ya amsa kafin ta sanar masa da gurin da zasu haɗu. Shuru tayi tana tunani. Shin meyasa Salis yafi damuwa da matsalar su yarinyar da zai aura! Bayan ga matsalar da nakeciki, kuma yasan cewar ina sonsa. Wata zuciyar ta ce "Shima saboda yana sontane, kamar wacce take zance da wani ta ce "Ok hakane shima sonta yakeyi ko, shine yasa ya manda da tawa matsalar ki, to Walhi nima saide duk abunda zaifaru yafaru, badai abunda yafaru a faya bane zai ƙara faruwa muda Daniyel to walhi muje zuwa. Tana kaiwa nann ta nufi gurinda zasu haɗu da Umar.

Jiniyar motocin sojojine ya karaɗe ilahirin unguwar da mamu wasu mutane a cikinta sai ƴan ƙalilan kasan cewar a bayan garin gurin yake. Babu mota ko ɗaya da ta sabu damar shigowa gurin kasan cewar gurin baida girma kuma ga wata tsohuwar mota a gurin ita kadai ma ta ciki gurin. Parking sukayi sannan sojoji suka fara durgowa daga cikin kowacce mota. Babban sojojin barinki garin wanda a wannan watan yake cika shekaru biyu da samun ƙarin girma daga wani muƙamin zuwa wani, wanda a Yanzu haka shine Comandar ɗin duk wani sojo dake wannan state. Kama yanda kowa yasani mutumne mara imani ga tsan-tsar kishin addinindu wato addinin Christian, mutumne mai ƙiyayya da duk wani wanda ba ɗan addinisuba, hakanne yasa ya samu matsala da manyan ƴan kasuwar dake garin Benue sts.

Baya samun yabo daga sauran addinan dake garin amma kuma duk wani ɗan addininsa yana jin daɗin abunda yakeyi, domin kuwa baya barin a takasu koda kuwa sune basu da gaskiya. Ƙiyayar sa tafi ƙarfi a kan masu bin addinin musulunci domin kuwa sune yake ganin sunfi yawa, bugu da ƙari matemakinsa ma Musulmi ne, mai suna Faruƙ. Comandar Daniyel kenan wanda ke zaune a ɗaya daga cikin gidan da kwamnati ta mallakamasa yanada mata guda ɗaya mai suna Eliza wacce sukecewa Momy, sai yara guda biyu mace da Namiji. Samuel da Sarah. SAMUEL ne babba yabata shekara huɗu. Yayinda dukkanninsu sukayi kama da Eliza sosai domin kuwa Elixa fara ce sosai ga iya cin uban wanka kamar matar shugaban ƙasa. Yanda mijinta ke ƙin musulunci sai ita ta damashi ta shanye domin kuwa ita ƴar gidan wani babban fasto ce wanda duk faɗin garin babu kamarsa.

Daniyel yana son yaransa sosai, itama Mommy hk, amma yafi son ƴar autar su, wato SARAH. Lokacin aihuwa Sarah Saida a ka findda rai da mommy domin kuwa ta wahala, hakanne yasa bayan ta aihu yasa a ka cire mata ma haifar gaba ɗaya a kan ya daina ai huwa. Eh tabbas yana son yaran sa amma hakan baya hana idan suka taɓa masa martaba tofa sai sun gane shiɗin rainun ɗajine. Shine ya fara sakar ma yaransa kuɗi daga baya kuma ya daina sukuma suka shiga satar masa batare da yasabi. a kan kuɗi zai iya komai haka a kan addinmsa ma zai iya yin komai. Wannan kenan.

Bai ko tsaya an buɗe masa ƙofar motar kamar yanda a kasaba, da sauri ya fito daga cikin motar yana nufar cikin ɗan ƙaramin Police station ɗin. Tin lokacin da da ƴan sanda sukaji jiniyar motocin suka miƙe tsaye suna ƙamewa a gurin kamar wasu gunkuna. Shikuwa Salis cikin tsananin tashin hankali yake abin wajan da ido ko zai gano waye zai shigo kodai Daniyel ne, ai kuwa kafin ya rufe baki sai gashi yana shigowa cikin takunsa na mazajen da suka shiga in da rakwaye basu iya shiba, cikin takunsa wanda ke gigita masu da sun hangoshi.

Bai tsaya tambayar kowaba ya nufi gurin da Salis yake a ƙulle, cikin umarnin na shugaba a gurinsu yasa a ka fito da Salis. Tin kafin a durƙusar da shi a gaban sa ya ɗaga ƙafarsa ya buga masa wannan shegen ta ƙalmin nasu, kafin Salis ya ɗago ya ɗauke shi da mari, ya ƙara masa ya ɗagashi ya kwasheshi ya faɗi a rufa ciki, tsabar a zaba yasa Salis kasa yin ko da ihuma. Cikin zafin rai ya ɗago Salis da niyar sake kwasheshi. Chak ya tsaya yana binsa da kallo kafin sakeshi yana nuna shi da hannu cikin mamaki. Ya ce Salisu? Kafin Salis yayi mgn ya sake cewa "na You again?

*ABDLLAH POV*

Eh tabbas baiji daɗin sace Zainab da a kayiba, amma kuma baiji hakan ya bashi wani haushiba. Yana zaune yana jin yanda abubuwan suke ƙara rikicewa a yanar gizo-gizo. Yana cikin haka yaga kirin shek Kabir a karo na babu a dadi, tuno abunda yafaru tsakanin su yayi jiya a gidan su. Yana ɗagawa Daddy ya ce "Kazo gidan yanzu ina son ganin ka? Bai tsaya jin komaiba ya kashe wayar.

Zaune suke dukkanin su a gaban Shrk Kabir kabuga. Abdllah Sadiya Nusaiba Maryam Nura sai Mommy. Cikin yanayin da yake nuni da cewa babu wasa ya kallesu ya ce "Abdalha kabani mamaki! Dama ashe a kwai wani abu tsaka ka da wannan ƴar iskar yarinyar wacce bata samu tarbiyaba, wacce bata san girman manyaba! Waccce ke rwwa da waƙa a gaban maza! Wacce take aikata saɓo ta sigar isgilanci, har ina kiranka kana katsemin waya a kan karna maka maganar ta ko? To naji kuma ka saurareni da kunnab basirar ka. Kaman yanda kasani ni dai bana amfani da duk wani abunda Allah da manzan sa basuceba, kuma duk inda ka je ka kaimusu yarinya to ina mai sanar dake yan ɗinnan kaje ka dawo musu da yarinya? Kuma nagaji da zagin da mutane suke maka akan zaman ka haka, idan kai abun bai damunka kaida ma haifiyar taka to ni yana damuna, saboda haka kaje gidan mlm Aliyu ka ga ƴarsa idan tayi ko batama mun gama mgn da mahaifinta mun tsayar da rana, idan kaga dama kaje ka ganta idan ma bakaga damaba ruwanka. Kowa shiru yayi yana sauraron Daddy domin kuwa abun ya basu mamaki, kenan daddy ma ya yarda cewar mommy da Sadiya suna bin Daddy da kallo ganin zai bar ɗakin.

Tinda take Tare da mai gidan nata bata taɓa tsayawa tayi masa magana cikin zafiba, dukda bata son wannan ƙiyayar da yake nunawa ga abokan takun saƙar dasu. ta ce "Kabiru? ba daddy ba, ba kuma Maryam ba ba kuma Abdalha ba hatta Nura dake ɗan yaro saida ya kalli Mommy jin yanda ta kira sunan Daddy. Taci gaba da cewa...

"Na gaji! Walhi na gaji da wannan baƙin ƙiyayar da kunewa junanku. Muna Musulmai ƴan uwa ɗaya Amma duk kun raba kahunanku, wasu suna yiwa wasu kallon kafurai, har takai ta kawo yanzu kana nema kayiwa yaronka aure da ƴar gidan mutumin da kowa yasan halin matarsa a garinnin. ADDININMU ɗaya al'adar mu ɗaya yaranmu ɗaya Allah mu ɗaya, annabinmu ɗaya, shin me mukeso muzama!?...

Yanzu kazo ka hau kan maganar da kaji anayi a gari a kan shine ya saceta, baka tsaya kaji daga gareshiba ka yanke hukunci, shin hakan..."Ya isa haka ya isa . Cewar Daddy Yana ɗaga mata hannu ransa a mugun ɓace.

Ya ce "Badai kince kin gajiba, to ga hanya nann daga ke har ɗan naki ai ban ɗaurekuba, kunada damar da zakuje duk inda kukikeso a cikin ƙasar nann. Yana kaiwa nann ya ce "Indai a kan su kike zance to damar kice. Ya juya yabar gidan gaba ɗaya.

Gaban Mommy ne ya faɗi, yayinda Abdalh ya ɗago ya kalli Mommy ya kalli daddy, Sadiya ma kallon daddy tayi tana riƙe ƙurji. Abdalha ya ce "Dan Allah Mommy kibar wannan zance kar a je wani abu ya faru, ina dai nune zanyi duk abunda yakeso, badai aure bane zanyi. Kuma zan fito da Zainab. Cikin mamaki suka kalleshi har suna haɗa baki gurin cewar dama kaine ka saceta ɗin? Mommy da sauran yaranta suka haɗa baki. Abdalha ya ce "Eh nine kuma kamar yanda ya ce yau zan fito da ita, amma dan Allah Mommy ku fahimcen... "Kafin ya ƙarasa Mommy ta fashe da kuka....📝





*
*PAGE.* 2️⃣0️⃣

.........Cikin mamaki suke kallon juna yayin da Comandar Daniyel ke bin Salis da wani irin kallon tsana yana nunashi da hannu. Cikin tsoro da fargaba Salis ke kallon sa yana jin tamkar a ce mafarki yakeyi ba gaske bane. Da sauri Comandar Daniyel ya kamo hannun Salis cikin tsanin ɓacin rai da ƙiyayar da ke fitowa daga fuskarsa cikin harshin English ya ce "Waye kai? Yayi tambar cikin rashin mutunci kai ka rantse da Allah baisan waye Salis ɗinba. Cikin mamaki Salis ya ɗago kansa ya kalleshi sai kuma ya sun kuyar da kansa ƙasa bai iya magana ba. Ganin haka yasa Comandar Daniyel cewa "Wato bayan duk abunda ya faru tsakanin mu daku saida kuka sake shigowa rayuwarmu ko? Wai ku meyasa musilman nan bakuda tunanine, Walhi na tsaneku bazan taɓa sonkuba, bana kwanarku. Sai kuma yayi shiru ya kalli Salis ɗin ya ce...

"Waye AJ? Kuma me nene haɗinku da shi? Cikin tsananin ɓacin rai Salis ya ce "Abokinane kuma bansan ina yake ba a halin yanzu. Cikin jin haushi ya ce "To idan har kuna son fita daga Hannuna to sai kun kawo min shi kuma yau ɗin nan ya faɗa yana karewa Salis ɗin ido. Salis ya ce "Pls wai me Aj ɗin yayi? "Wani wawan mari yaji ya sauƙa daga gefen daman sa wanda kafin ya an kara an sake ƙara masa.

Cikin tsananin ɓacin rai ya ce "Ina AJ na tambayeka ba wai nace kaima ka tam bayeniba, kasan waye Ni kuma kasan abunda zan iya akan duk wani musulmi... Waima ba ubanku yayi muku iyaka da niba!? Bashi da kansa yace babuni babukuba? Akan wannan addinin naku addinin da yace yafi masa wanda ya tashi yaganshi a cikiba. To Walhi na tsaneku daga ku har duk zuri'ar ku, kuma Walhi in dai baku fito da wannan yaron ba kaima sai na ɓatar dakai baza'a sake ganin kaba har gaba da abada. Yana gamawa ya bar gurin ya shiga motarsa sauran sojojin suka take masa baya suka bar Salis a gurin. Daniyel yana zuwa gida ya tararr da wani sabon tashin hankalin.

**HAJIYA BABBA*AJ*

Zaune take tana rangaɗa kwalliya yayinda shi kuwa uban gaiyar ke tsaye yana bata amsar ta bayar da ta ke masa. "Nima yau gaba ɗaya bana jin daɗin jikina sosai sai naji gabana na faɗuwa wani lokaci. AJ ya ce "Nima har zuwa yanzu ban dai jin hakaba amma in Sha Allah komai lafiya. Ta ce "To amin Allah yasa hakanne, amma dai yau inason muyi waya da su Salis ko hankalina zai kwanta. AJ ya ce "Eh to hakanma dai-dai ne. Take ta ciro waya ta kira laɗifa, ai kuwa kira ɗaya ta ɗaga haɗi da cewa "laɗifa lafiya...kafin ta ƙara da laɗifa ta ce "Hajiya ina kika je ne, ta faɗa kamar tayi kuka. Saida hajiya Babba ta sauke a jiyar zuciya kafin ta ce "Laɗifa fatan dai kuna lfy ko?

13 / 37