tsabar farin ciki da abun alherin da ya samesu, Innah ta kamo ƴan jikokinta guda biyu ta rungumosu tana saka musu albarka kamar ba gobe. Kallon kuɗin da mutum ya ajiye musu a cewar sa wai AJ ɗin ya kama wata sana'ar. Nana ta ce "Shekinan yaya yanzu babumu ba zama a wannan gidan. Ta faɗa tana jin wani sanyin daɗi na ratsa zuciyarta. Innah ta ce "Kai amma gaskiya wannan ogan naka ɗan arziƙine Allah ya saka masa da albarka. Dukkansu suka amsa da amin sannan AJ ya kwaso wannnan kuɗin ya ƙirga su naira dubu ɗari biyu ne dai-dai. Innah ta ce "To Abdauljabaru kaga dai yanda Allah yayi damu cikin lokaci ƙan-ƙani sai ka sake nutsuwa domin kaima yanzu Allah ya baka naka, kuma ba ruwanka da surutu domin kasan halin wannan zamanin namu ana jinka da ɗan abun harziƙi sai kaga ana neman halakaka. "AJ ya ce "Haba Innah a naira dubu ɗari biyun za'a wani damu dani, to walhi a wani gidan ma wannan shine kuɗin abincisu na rana ɗaya. Innah ta rafko salamulai tana tafa hannaye a lamar mamaki. Haka dai tai masa faɗa sosai kafin ta ce masa ba yanzu zasu koma gidan ba sai ya fara sana'a tukunna, AJ da yake son a gobe subar unguwar ya ce "No no no ai kawai tattarwa zamuyi gobe-gobe mubar wanga unguwa, sannan ya ce yanzuma zasu tafi da Nana domin ganin gidan. Innah ta ce "A wani unguwa gidan ya ke? "Innah ai ba a kusa muke ba can wajan gidan kwamna nefa. "Har kusa da gidan kwamna, to ai naga gurin yayi nisa, to amma Allah dai ya kyuta. Haka Nana da AJ sukayi wanka suka shirya izuwa sabon gidansu. A'jinkin takardun gidan ya duba yaga sunan unguwar da gidan harda Numbar gidan. Gidane ɗan dai-dai mai ɗauke da ɗakuna shida, sai toilet a kowani ɗaki kicin guda ɗaya palon biyu babba da ƙarami, sai filin gidan mai ɗan girma sai gurin da motoci kamar huɗu zasu faka. Gidan yayi asalin haɗuwa, da a lama dai sabon gidane domin babu komai a ciki. Haka suka dawo cike da shawƙin gidan. A ranar kuma suka ƙara fita da Nana domin siyan wasu kayan su fara kaiwa gidan batare da Innah ta saniba.
Dubu ɗari biyun da Hajiya Babba ta basu ya haɗa da sauran kuɗin da Hajiya babbar ta bashi tun kafin su tafi Cemeron ya haɗa suka shiga kasuwa da sabuwar motarsa. Duk gurin da yaga wanda ya sani sai ya sauƙe glas ɗin motar ya ɗaga musu hannu, masu mamaki sunayi masu tambayar junansu nayi. Burin AJ kenan a ce yau ya mallaki gida da mota ga kuma kudaɗe masu yawa, burinsa ya ganshi a cikin mota wacce kowa ya ganta sai ya ƙara kalla. Yana cikin tafiya wata zuciyar ta ce masa "Yanzu meme burinka na gaba? Yayi shiru yana tunani sai kawai yaji wata zuciyar ta ce "Sarah ce burinka na gaba, ta maka hallacci ta soka da zuciya ɗaya. Afili ya ce "No ƙaryane ba gaskiya bane ba zai taɓa faruwaba Addininmu ba ɗayaba.
*HANYAR KATUNGU*
Salis ya kalli Sarah wacce gaba ɗaya tayi nisa a cikin tunanin da takeyi, izuwa yanzu ta haɗa komai da zai tabbatar da cewar AJ aure sukayi da Hajiya Babba. To amma yaushe kuma a ina? Batasan hawaye na mata zirya afuskartaba tana jin wani sabon son AJ ɗin na shigarta, ita koma me zaiyi tana sonsa, tana haka har saida taji Salis ya kira sunanta. "Sarah! Sarah!.
Da sauri ta goge idon ta ta amsa da "Yes Bro?
Sai ya ciro wayar da ya sayo mata ya miƙa mata ba tare da yace mata komai ba, amma yana lura da ita ta gefen ido. Hanunta tasa ta karɓa tana kallonsa, domin jin ƙarin bayani. "Wayar ki ce idan muka dawo kije kiyi welcome bak.
Taji daɗin kyutar har cikin zuciyarta, amma a fili sai ta kasa nuna masa cewar taji taɗin sai kawai bata ce komai ba ta ajiye wayar a kan cinyarta ta ci gaba da kallon waje. "Sarah inason muyi magana da ke akan saurayinki, kuma banaso kimin ƙarya? Lokaci ɗaya ta ɗaga kai ta kalleshi sai kuma ta gyara zamanta da kyu tana kallonsa yana tuƙinsa kamar ba shine yayi maganar ba. "AJ saurayinki ne, ni kuma a bokinane to saboda haka inaso na miki tambaya akansa? Ya sake yin maganar yana cigaba da tuƙinsa.
"AJ abokinka ne? Itama ta tambayeshi tana kallon kyawawan i danunsa da ya zubasu a kan ƙwaltar da suka tafiya?
"Eh abokinane sannan kuma yayanane.
"Yayanka kamar ya?
Sai kuma ya waske ya ce "AJ yana turaki ki ɗaukarwa Daddy kuɗi ki kai masa ko?
Da sauri ta sake kallonsa ta ce "Eh amma waye ya sanar maka?
Ya ce "Bani labarin haɗuwarku da rabuwarku? Sarah ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Ai bamu rabuba har yanzu muna tare, amma naji Laɗifa ta ce min wai ya taɓa yin aiki a gidan ku ko?
"Eh yayi aiki amma fa aikin bai kwana ko ɗaya ba sukayi tafiya da Hajiya, to bayan ya dawo n... Sai kuma Salis yayi shiru yana tunani ya ce "Innah ta ce yaje Niger baya gida a ka kamasu, kuma lokacin yayi dai-dai da tafiyan da sukayi tare da Hajiya, kuma shi baima san ko tare suka dawoba. Ya ce "Lokacin da Daddy ya kamaki AJ yana gari? Itama ta shiga tunanin ranar rabuwarsu da AJ ta ƙarshe. Idan bata mantaba ranar har kuɗi ya bata bayan sun dawo daga club, kuma a washe garin ranar ne a ka kamata, kuma dama ya ce mata zai tafi ba laillai ta sake ganin sa ba. A yanzu kam Sarah ta gama yarda da cewar AJ aure sukayi da Hajiya Babba auranma na kuɗi.
"Ya ce min zaiyi tafiya ne, bayan haka ban sake ganin saba sai da yazo gidanmu. Nan Sarah ta bashi labarin haɗuwarsu da AJ har zuwa ranar da suka rabu. Salis ya ce "AJ yanada kirki matsala sa ɗaya shine son kuɗi, amma banda wannan gayan ya iya zama da mutane ga sakin fuska ga iya mu'a'mula da mutane, amma a kan kuɗi zai iya yin komai indai ba zai taɓa mutuncinsaba to amma ya akai yake turaki satar kuɗi!?
Sarah tayi shiru tana tunanin kodai a addininsu idan mutum ya aure mamar a bokinsa ba wani abu bane! Ko kuma Salis ɗin bai sani bane, to ko dai ta sanar masa! Haka dai ta keta saƙe-saƙe, shi kuma Salis sai yabon halin AJ yakeyi, tawani gefen kuma yana haɗawa da Nana. Kamar ta tambayeshi sauran abu guda biyun da ta riƙe a hirarr su AJ da Hajiya Babba amma tana tsoro. To me ma zan tabaya bayan komai ya baiyana kansa.
Ɓangaren su Samuel da laɗifa kuwa sukam soyayya suke zubawa babu kunyar kowa, domin izuwa yanzu Samuel ya zubar da makaman yaƙinsa yana son laɗifa ta shiga daga cikin zuciyarsa tukunna. Hajiya Babba kuwa dukda irin damuwoyin dake cunkushe a zuciyarta hakan bai hana sarkin ɓarayin duniya barci yayi wuff da itaba. Tafiyar a'wa ɗaya da wasu ƴan mutuna sukayi sai gasu a bakin titin da zai sadasu da cikin ƙwayan katunku.
Babu laifi yanzu ƙauyan sun samu burji har cikin gari. Usman da Umar da Muhammad tun daga nan suka fafa kalle-kalke domin kuwa garin ya koma musu kamar ba shiba. Titi ce da yake ita tazo tin bayan samun wannan burjin sai ta dinga nuna musu hanya har suka shigo cikin garin. A tsarin dokar garin Katungu duk wani musulmi idan ya sake ya shiga cikin garinnan tofa ya zama gawa, tun labarin da ya riskesu na cewar Solomon ya mayar da yaransu masu yin Sallah kuma an kashesu.
Duk wanda ya ɗaga kai ya kalli jerin motocin to fa ko mai ya keyi sai ajiye ya biyo bayansu. Kafin su ƙarasa cikin tsakiyar garin har sama da mutane ɗari maza da mata sun biyosu, wasu da abun duka wasu kuma domin ganewa idanunsu. Lokacin da motarsu ta tsaya a tsakiyar garin kuwa mutanene suka zagayesu kaman dai a'na wani taron. Garin ko kaɗan basa son baƙo, shi yasa duk wanda zai shigo sai an sani domin tsaro. Titi da Usha ne suka fara fitowa ai kuwa ana ganin su kowa bakinsa ya washe domin idan har tazo tana musu wani ɗan isaninn, amma ita idan zatazo to a mota ɗaya take zuwa, ko shi Daniyel lokacin da yazo mota ɗayace. Ganin haka yasa kowa ya fara komawa gurin aikinsa. Saida a ka watse saura ƴan kaɗan kafin Titi ta kalli Uncle ɗinsu ta sanar masa da halin da a ke ciki.
Da sauri ya ce "Ina suke? Kafin Titi ta fara magana har ya fara ihuuu yana sanar musu da cewar Tena da Gumma sun dawo. Kafin kace me, saiga mutanen da suka tafi sun dawo domin jin abunda Uncle ɗin ke cewa. Tena da Gumma irin mutanennene da ko sun mutu ba'a saurin mancewa dasu saboda sunan da sukayi a garin.
Ganin haka yasa Titi cewa su fito. Ai kuwa dukkansu suka fito harda Hajiya Babba da sai yanzu ta farka daga barcinta, gaba ɗaya tayi lakwas. Tena wato Usman shine ya fara fitowa sai kuma Gumma wato Umar. Sai Solomon Muhammad. Kafin kace me, an'hau koke-koke, ma haifin Usman yazo ya rungumi sa yana fashewa da kuka, shi dai Usman jira yake yaga ma haifiyarsa da ƙanwarsa guda ɗaya da suke tare. Cikin yaransu na tibi ya ce "Baba ina mamana da ƙanwata? Baban ya sake fashewa da kuka ya sanar masa da cewar a ciwon zuciyane ya kasheta, kuma ta mutu da burin idan har ta sake ganinn Solomon sai ta kasheshi. Usman yayi kuka sosai ya ce ƙanwarsa fa? ita ma a ka sanar masa cewar tayi aure gurin aihuwa ta mutu. Nan take Usman ya fita a haiyacinsa yana kuka kamar ƙaramin yaro.
Umar kuwa duk gaba ɗaya uwa da uban sun mutu, sa ƙaninsa guda ɗaya wanda ya rage masa, shi ɗinma cikin rashin lafiya yake. Haka ya huce gidan nasu ya tarar da ƙanin nasa a kwace cikin ciwo. Ai kuwa ƙaninn ganin sa ya ganeshi, yayi kuka haɗida murna da farin cikin sake ganin ɗan uwan nasa. Su kuwa su Muhammad ganin haka sai suka nufi gidan Uncle ɗinsu. Samuel da Sarah harma da Usha ba wani sanin su a kayi sosai a garinba domin basa zuwa, hakanne yasa suka zama baƙi, amma hakan bai hana matar Uncle ɗin nasu ganesuba.
Tini jama'ar gari suka gama shirya yanda zasubi Muhammad har gida su kasheshi domin sun san da cewar shine ya sace su Gumma. Shigarsu gidan bada daɗewa ba aka fara dukan gidan wai sai an fito da duk wasu masu yin Sallah an kashe. Shi kuma Uncle ɗin nasu lokacin ya fita izuwa gidan Sarkin garin ya sanar masa da abun da Titi ta sanar masa a kan cewar duk wannan abun Daniyel ne ya haɗa. Matar Uncle ce da Titi suka fito suna bada haƙuri amma ina suka ce Walhi sai an kashesu. Ana cikin haka sarkin garin ya iso gurin cikin bada umarni ya ce kowa ya tsaya, aikuwa kowa yayi tsait. Ya ce "Duk a tattara a je fadarsa harda su Muhammad ɗin da su Gumma da Tena.
*Elliza*
Koda ta iso gidan ta tarar da shi a rufe sai ta fara dukun gidan tana zagi. Jin haka yasa mai gadi fitowa yana tambayar waye? "Cikin English da yaransu ta fara maga wanda har tagama mai gadi bai gane ko abu ɗayaba. Ganin tana kiran sunan Sarah da Samuel ya sa mai gatin da bai san ko suwayeba ya ce "Hajiya ba nan gidan bane. Yana faɗa ya koma ciki ya rufe gidan yana jin haushin ta zu ta tasheshi daga barcinsa. Haka ta bar gurin cike da tunanin ina kuma suka tafi. Ɓangaren Daniyel kuwa. Tinda a ka rufeshi a wani ɗaki babu wanda ya ƙara bi ta kansa. Ba'a hanashi ci ko sha ba. amma bai isa ya leƙa ko nan da wajeba ko kuma yayi amfani da waya ba har sai ogan nasu yazo. Haka yake rayuwa shi ɗaya cikin wannan ɗakin ga ac ga fanka ga abinci mai rai da lafiya ga ruwan wanka ga kayan sawa amma a hakan yana jin kansa a taƙure. Yana cikin wannan halin ya tuno irin halinda su Solomon suka shiga, suda ba kullum suke samun abinciba ga babu wanka sai kusan watannani biyu za'a sakar musu da ruwan toilet. Azuciyarsa ya ce "Ooo my GOD! Why why why!.
Zaune suke a fadar sarkin garin dukkansu. Bayan Muhammad ya gama basu labarin komai ne sannan a ka tambayi su Umar suma suka tabbatar da cewa hakane. Kowa dake gurin mamaki ya kamashi harda shi kansa Uncle ɗin nasu. Dama kowa yasan halin Muhammad tin lokacin yana ƙwayan yanada haƙuri ga kawar da kai a abun da babu ruwansa, ga kuma baya ƙarya, idan har ya faɗi magana to ana tabbatar da gaskiyasa. Su Usman suka ƙara da yabon halin Muhammad ɗin harda irin halayyar sa na gaskiya. Daga ƙarshe suka gabatar da Salis da laɗifa a matsayin yaransa sai Hajiya Babba a matsayin matarsa. Sai kuma su Sarah da Samuel matsayin yaran Daniyel. Nan fa sarki ya tambayi dalilin zaman yaran Daniyel a gurinsa. Nan suka sanar musu da ƙoƙarin kashesu da yayi kuma ya gudu.
Gaba ɗaya garin kowa ya tausaya musu, kowa na tsinewa Daniyel, badan shiɗin soja bane da shi sarkin da kansa zai sa a yanke masa hukumci. Koda suke ba musulmai ba amma suma addidinsu bai amince da zalunciba. Sunyi niyar su dawo a ranar amma dole saida suka kwana. Hajiya Babba kam ba haka tasoba shima kansa Salis yaso ace sun koma, ita kuwa Laɗifa a fili take nuna bata son garin. Muhammad kuwa farin ciki ba'a musaltawa suma su Usman da Umar haka kana ganin su kasan suna cikin farinciki duk da cewar rashin iyaye ba ƙaramin abu bane . Nan fa a ka fara raba abubuwan da a ka kawo, kusan kowani gida saida suka samu nasu tsarabar. Dama kuma haka yakeyi duk lokacin da yazo garin to kusan kowani gida sai sun samu kasonsu.
Washe gari da safe suka shirya zasu tafi. Salis ya bawa Sarkin garin kuɗi masu yawa, Uncle ɗin suma haka, sai su Umar da Usman suma Salis ya ce idan suka huta sai suzo har gida su sameshi, haka suma ya musu kyauta , kowa dake ƙauyan saida ya yabawa Salis da irin kyutar da yayi, itama Hajiya Babba ta ɗan rabawa mata cikin juriya da halin da take ciki. Haka suka tattara suka kamo hanya cikin jin daɗin yanda abun yazo da sauƙ. A hanya ya ke sanarwa da Daddy Muhammad cewar ya lura kamar fa Hajiya bata lafiya, hakanne yasa yace to su huce aasbiti batare da ta saniba.....📝
*hammmm garin daɗi a kusa*
*Comments ɗinku shine ƙwarin guiwata*
*By S REZA ✍️*
[10/21 22:06] Aliyu Makko: *ADDININMU*
*S REZA...✍️*
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
*PAGE3️⃣9️⃣*
.......Kamar Hajiya Babba tasan maganar da sukeyi sai ta ɗauki wayarta ta kira Dr Lurwan a kan yazo gida ya sameta bata jin daɗi. Ganin sun ɗauki hanyar asbitine ya sa ta sanar musu sewar ai ta kira Dr yana zuwa gida yanzu. Gidan Anty Titi a ka fara zuwa saida suka tsaya mijinta yazo suka gaisa da Muhammad da Hajiya Babba. Shima dai ya jinjina wannan lamarin na Daniyel. Samuel da Sarah sukace zasu bi su Hajiya Babba hakan ne yasa suka tafi tare. Koda suka isa gida kowa ya nufi ɗakinsa cike da gajiya da yunwa. Shi kuma Salis ya kira Numbar Nana har kiran ya tsinke bata ɗaga ba sai ya sake kira a karo na biyu, saida ta kusa tsinkewa ta ɗaga ta na sallama. Sarah da Samuel suka shirya domin zuwa yin welcome bak, Laɗifa ta ce zata rakasu. Salis ya basu mota ɗaya ya ce su tafi da ita. Haka Samuel ya tuƙasu suka bar gidan. Suna fita Dr ya shigo ya tarar da Muhammad shi kaɗai a zaune a palo ya na tunani. Ganinn Dr yasa ya haura sama domin kira Hajiya Babba.
Cikin mamaki yake jin kuka na tashi daga cikin ɗakin na ta. Tsayawa ya yi yana saurara da kyu ya tabbatar da kukantane sai kuma ya tura ƙofar ɗakin ya shiga kamar mai tsoron shiga ɗakin. A sunkuye ya sameta a bakin gadon ta na rusar kuka kamar ba gobe. Cikin mamaki ya ce "Aisha" Da sauri ta ɗago haɗi da share hawaye ta tana kallonsa cikin tsoro. "Lafiya ku wa? "Cikin rashin sanin abun cewa ta ce "Kaina ne kemin ciwo kuma ya kusa dainawa, ta faɗa tana miƙewa daga durƙushen da take. Kallonta ya ke yi da mamaki ya ce "Dr yazo ya na palo ya na jirranki. Ya na faɗa ta bar gurin da sauri ta na ɓoye wayar dake hannunta. Muhammad ya bi bayanta yana gir-giza kai. Dr ya tambayeta abun da ke damunta ta sanar masa shi kuma ya sanar mata da cewar kawai damuwa ta saka a ranta da tunani saboda haka idan ma wani abunne ke damunta to tayi ƙoƙarin magance shi. Hajiya Babba ta ce "Kai Dr to maganar abincifa? Kwata-kwata fa bana son cin komai a cikin ƴan kwanakinnan, ga saurin tashin zuciya wanda ni duk ban saba da suba, ga shegen barci. Da Hajiya Babba tasan maganar da Dr zai faɗa mata kenan da bata sanar da shi waɗannan abubuwan ba.
Cikin wasa Dr ya kalli Muhammad da Hajiya Babba a tare ya ce "To ko ƙaruwa a ka samu ne Alhaji? Ya faɗa yana sosa kai cikin jin kunya. Lokaci ɗaya gabanta ya faɗi ta furta ƙaruwa?! Me ne ne ƙaruwa? Ta yi maganar a zuciya fatar da ta san ta fito filiba. "Ina