ya rufe mata ido ta baya yana dariya ƙasa-ƙasa. Ita kuwa sara cikin masifa ta ce "Samuel I don't like it please..."Kafin ta ƙarasa Usha ya zagayo yana mai haɗe fuskarsu. Cikin murna da farin ciki SARAH ta rungumeshi cikin yaransu ta ke cewa "Usha yaushe a gari? Shine ko ka sanar dani? Ihun da Sarah tayine ya fito da Momy daga ɗaki, ai kuwa itama tana ganinn Usha tazo da gudu ta rungumeshi tana masa welcome back. Suna cikin haka Samuel ya shigo, shima yana ganinn ɗan uwan nasa kuma abokin sa, yazo da sauri yana shiga jikin sa.
Nann Sarah ta fito masa da kayan mutsawa sai dariya ta keyi. Usha ya ce "Momy tinda natafi sau ɗaya Sarah taje gidan mu, saboda taga bananan. Cikin sauri Momy ta kalli Sarah wacce gabanta ya faɗi. Momy ta ce "Da gaske? Shikuwa Usha da baisan komai ba ya ce "Yes Mommy domin kuwa haka mama tace min, shinema yasa nazo kodai ba lfy ba.
Cikin mamaki Mommy ta ce "To Sarah ina kike zuwa kullum sai kice zaki gidan su Usha? Cikin rashin sanin abunyi ta buɗe baki zatayi mgn sai wayarta ta fara rori. Ɗauko wayar tayi a kujerarr da ta zauna ɗazu. Kwallon number da ta gama zama a kanta tayi, cikin sauri ta ɗaga haɗi da fita daga palorn. Duk binta sukayi da kallo, sannan suka shiga wata hirarr. Yayinda Samuel yake neman hanyar shiga ɗakin daddy, ganinn motarsa batanan sannan sojojin da suke binsama yaga basanan sai kawai masu jiran gidan.
Nana kuwa bayan A.J ya shiga ɗakine ta ciro wayar domin duba waye zai haɗata faɗa da ƴaƴanta, kafin ta duba saiga kiran sa a karo na uku. My sweetheart, Shine sunann da tagani a kan wayar, cikin zaro ido da yazama mata ɗabi'a in abu ya bata mamaki ta ce "Kuttt!! Allah ya taimakeni, take ta goge number sannan ta kashe wayar gaba ɗaya ta ajiye ta koma gurin girkin da innah keta surfa masifa daga taga Nana ta kalleta tin ɗazu.
*SARAH* Hello my AJ.
Hi my Sarah, ya amsa cikin shwƙi da jin kansa a sama.
Sarah ta ce "I hope you buy the phone?
"Yes my Sarah, yanzuma da ita muke waya.
"Waoooo I'm very happy, wacce iri kasiya? Allah yasa de ba irin ta yara kasiyaba?
A.J yayi dariya yana jin wani girma na shigarsa sannan ya ce "Sai mun haɗu yau zan nuna miki.
Sarh ta ce "Tom mu haɗu yau?
Ya ce "Ok yau abokina yana da birthday da daddare, so zamu tafi tare, ar you ready?
Cikin jin daɗi ta ce "Yes But I don't know...sai tayi shiru. AJ ya ce "What is your problem?
Tana so tace masa batada kuɗi kuma tana jin kunya, sannan tana son tace masa in tayi dare Daddy zai karkaryata, in ba hakaba saide ta kwana a wani gurin. Cikin jan numfashi ta ce "Ok I'm or ready. A.J yayi dariya sannan ya ce "Good Allah ya kaimu lokacin, amma fa kiyi wankan shiga taro. Ya faɗa yana dariya domin kuwa yasan ta wajan ɗaukar wanka. Haka sukayi sallama Sarah tana tinanin yanda zata shiga ɗakin daddy ta ɗauki kuɗi, domin tasan AJ bashi da kuɗi. Nann ta shiga tinanin abun yi, take ta tuna cewar Usha ya dawo zataje ta tambayeshi ko dubu ashirin (200) ya bata sai ta haɗa da na gurin ta. Amma me sai ta tuna da cewar ya ce ya daina bata kuɗi in dai bazata amince da abun da ya umar ceta ba. Nann take ta shirya domin zuwa ɗakin daddy.
*ZAINAB VOP*
Zaune take a gaban MLM ya ce "Yauwa kin haɗa komai na majalisin yau ɗin ko? Zainab ta ce "Eh mlm. "To Allah yabada Sa'a. "Amin ya Allah. Zainab ta amsa tana meƙewa domin tafiya gurin majalisin da a ka gaiyaceta. Mlm ya ce Abu? Ta ce "Na'am mlm.
Mlm ya ce "Jiya Aliyu yazo, sannan ya tabbatar min da cewar zai turo iyayensa, shine nace to dama de kunyi magana dashi? Ya cemin a'a baisamekiba, sai na ce masa yaje zamuyi mgn dake, in kinyarda sai a faɗa masa ya turo, tinda ai Aliyu ɗan gidane kinsan halin sa yasan naki kinga babu wani dogon bincike da zamuyi a kan haka ko? Cikin jin kunya da abun da Aliyu yayi ta ce "Tom mlm Allah yasa hakan shene mafi alkairi.
Mlm ya ce "Amin Zainabu abu, Allah dai ya miki albarka, yasa kema naki yaran sumiki abun da kike mn. Ta amsa da amin tana barin ɗakin. Ta ce "Yanzu abun da Aliyu zaimin kenann!? Ni nace masa ina sonsane, take ta watsar da batun Aliyu ta shiga haɗa kayan da zata tafi gurin walimar tata. Ta shirya domin zuwa ɗakin mama suyi sallama kamar yanda ta saba a duk lokacin da zata wani guri da a ka gaiyaceta.
Aisha ce zaune a gabon maman nasu, wato ƴar auta a gidan su Zainab. Mama ta ce "Wa cece mahaifiyar Nana faɗima ƴar manzan Allah? S a w?
Aisha ta ce "Nana Kadija.
"A'wacce rana a ka haifeta?
Asha "Ranar juma'a, jimada sani.
Mama ta ce "good. Sannan ta ce "Waye ya aureta?
Aisha ta ce "Saiyadi Aliyu bin abu ɗalib.
"Yaranta nawa? "Yaranta biyar.
Mama ta ce "Tom faɗa min sunann su?
Aisha ta ce "I'mamu Hasan. Sai imamu Husaini. Sai Musa sai Zainab sai Ummu ƙursum. Mama ta ce "Allah hu akbar!!! Yanzu sai "kafin ta ƙarasa Zainab ta shigo da sallama. Mama ta ce "Anjima zamuyi cigaban kinji? Aisha ta ce "Tom mama.
Bayan Mama ta amsa ne Zainab ta ce "Mama ina jin karatunku keda auta, kinga itace zata gajeni in Sha Allah!. Mama ta ce "Ai in Sha Allah Humaira tama sai ta fiku daga ke har yayan naki. Zainab ta ce "Aikuwa dai ga alama, sukayi dariya sannan Aisha ta ce "To ai Anty Zainab kece kika faɗa a waƙarki kuma dama ana mana a islamiyar mu, shinefa na riƙe. Zainab ta ce "To kinji Mama ashe agurina taji.
Sukayi dariya sannan Zainab ta ce "Mama zamu tafi kimin addu'a, domin inajin gabana na faɗuwa sosai. Mama ta ce "ki yawaita ambaton azbunanlahu wa ni'imal wakil. Zainab ta ce "in Sha Allah Mama, na gode sai na dawo. Mama ta ce "Zainab nasan unguwar su Shek Abdulh kabir kabuga zakuje, saboda haka banason jin wani abun ya biyo baya. Zainab tayi dariya ta bargidan batare da ta ce komai ba. Fitowa da sabuwar waƙar da tayi, mai suna biuɗaɗɗiyar wasiƙa tayi tana sauraro, wacce jiya da yamma ta bugota, sannan a daran jiya ta gaiyaci masoyanta izuwa gurin majalisin nasu domin anann zata fara sakin waƙar kafin ta saketa a duniya. Ai kuwa masoyanta sun nuna mata cewar zasozo, kodan jin abun da wasiƙar ta ƙunsa.
Tin daran jiya take samun saƙonni daga masoyanta akan zasu halarci taron. Wasu kuma suna mata fatan alkairi domin ba a Kano suke ba, bazasu samu damar halartar ba. Haka ta shirya itada halifiyar ta da kuma wani daga cikin halifofin ta maza, suka nufi gurin taron.
*SARAH . SAMUEL POV*
Samuel ne tsaye a jikin ɗakin Daddy yana sanɗa domin yaga ƙofar a buɗe. Da sanɗa ya tura ƙofar haɗi da leƙawa, baiga kowaba, hakanne yasa ya koma palor domin rufewa koda Daddy yazo sai yayi magana kafin ya shigo.
Sarah ce zaune a bakin gadon ta, ta haɗa kaida gyiwa domin tinann shiga ɗakin Daddy, take wata zuciyar ta ce mata, ai Daddy bazai dawo da huriba kawai kije har ki dawo. Hakane yasa ta cire taƙalminta ta nufi ɗakin. Tana zuwa ta tura ɗakin sai ta jishi a buɗe, nann take ta tura kanta babu tinanin komai.
Saida ya tabbatar ya rufe palorn kafin ya dawo izuwa ɗakin Momy, ya sameta tana waya, hakanne yasa bai tsaya dubawa ko ita da waye a cikin ɗakinba kawai ya fita izuwa ɗakin Daddy.
Tana shiga ta nufi gurin da tasaba ɗaukar kuɗin, amma abin mamaki, sai taga gurin abuɗe, aikuwa ta duba toilet babu kowa ta duba ƙarƙashin gado, nann ma ba kowa. Take ta shiga jiddar kuɗin saida ta ɗiba nasu yawa zata fita taji motsin shigowar mutum.
Yana zuwa saida ya ɗan tsaya ya sake kallon ko ina na gidan (wato gefe da gefansa) kafin yasa kai cikin ɗakin, yana shiga ya nufi gurin da yasaba ɗaukar kuɗin, abun mamaki sai yaga gurin a buɗe, nann babu ko tinanin komai ya sa hannu ya ɗiba masu yawa, sannan ya sa a aljihun wandon sa, sannan ya juyo zai fita. Nann yaji takun mutum na dosar ɗakin kuma da sauri.
Tana jin motsin shigowar mutum tayi WUFF ta faɗa ƙarƙashin gado gurin da ta saba ɓoyewa, aikuwa sai taga Samuel ya nufi gurin guɗin ya sa hannu ya ɗiba zai fita. Ashe dama shima yana satar kuɗin!? Ta burta a zuciyarta.
Da sauri ya faɗa toilet Yana mai jin gabansa na dukan tara-tara, neman yin fitsari a wando ya keyi tsabar ruɗewa... Yana kallo ya shigo ɗakin cikin sauri.
Cikin tashin hankali Sarah take kallon mai shigowa ɗakin bayan Samuel ya faɗa toilet. Daddy ne cikin shigarsa na zaman gida alamar dai ya daɗe a gida. Take wani fitsari ya kufcewa Sarah ganinn ya nufo bakin gadon yana amsa waya, ihuu ne ya kufce mata haɗi da sakin fitsari...📝
?
*PAGE* 👉9️⃣
.........Cikin sauri Daddy ya zauna a bakin gadon yana amsa waya. Cikin minti kaɗan ya shirya cikin kayansa na sojoji, baiko tsaya ya kalli abun da ke faruwa a ɗakin nasaba, haka ya fita yana mai gyara rigar sa haɗi da kiran Mommy da ƙarfi! "A'lexa! "A'liza! "Da sauri Mommy tazo haɗi da cewa "Lafiya kuwa? Cikin sauri Daddy ya jefa mata kyin ɗakin haɗi da cewa ta rufe masa ɗaki zasuje Abuja yanzu sun samu kiran gaggawa sai gobe zasu dawo...sannan ya ce idan Samuel ya dawo ta ce ya kirashi. Haka Mommy ta masa fatan dawowa lfy haɗi da kissin ɗinsa sannan ya fita har yana haɗawa da gudu. Mommy kuwa komawa ɗaki tayi batare da rufe ɗakinba.
Duk abun da Daddy ke faɗa yana sauraro amma tsabar tsoro ya hana ya fahimci komai, yana cikin hakane yaji alamar zai fita, ai kuwa yazo jikin ƙofar toilet ɗin yana leƙawa har yaga fitar Daddy ɗin, sannan ya sauke a jiyar zuciya yayi hanyar fita. SARAH kuwa lokacin da ihu ya kufce mata haɗi da fitsari sai tayi saurin rufe bakinta, amma fitsarin kuwa saida ya kufce. A kan idonta Samuel ya fito daga toilet har ya bar ɗakin kafin itama ta fito cikin tsoro ta nufi ɗakinta. Tana shiga ɗaki ta faɗa toilet tayi wanka kafin ta fito tana cewa "Walhi daga yau bazan sake satarwa Daddy kuɗiba irin wannan tashin hankali da nake shiga! Haka ta ƙirga kuɗin dubu arba'in da uku (43,000) sannan ta shiga neman kayan da zata saka.
*LAƊIFA. SALIS POV*
Tana shiga palorn ta tararr da Hajiya Babba sai sakin murmushi takeyi, harda wani lissafi da hannu. Tin daga ƙofar palorn take kiran Hajiya Babba Hajiya. "Wai Hajiya wani irin aiki kika baiwa wannan wawan yaronne!? Allah Hajiya na tsani yaron Please dan Allah a koreshi akawo wani. Cikin mama Hajiya ta ce "Wai wani yaro kike magana a kaine kinzo tin daga waje kina kirana kamar namiki laifi?
Cikin tsananin jin haushin AJ Laɗifa ta ce "Hajiya wannan yaron dayafita daga gidannan mana dashi nakeyi Please wani aiki kika bashi? Kafin Hajiya tayi magana saiga Salis ya shigo yana ƙoƙarin zama laɗifa ta ce "Bro please dan Allah ka fita a harkar yaronnan, kaga abunda yamin yanzu kuwa!? Zaginafa yayi harda cewa wai wai yafi ƙarfin yayi dani! Yana ɗan aiki to Walhi sai ya bar gidannan tinda ba gidan ubansa bane. Cikin kwantar da murya Salis ya ce "Haba my sister meye na ɗaukar zafi haka, Allah yaron baida wata damuwa kece dai kike son saka abun a ranki amma karki damu A.J mutumin kirkine.
Cikin fushi Hajiya ta ce "To naji zan koreshi tundade kince bakya sonsa, amma bari kiji na faɗa miki... wallhi nima zanyi aure ko kunaso ko bakwaso, tinda na fahimci saboda ina goyan bayankune shine kuke son Sai kun kasheni da raina ko!? To na gode.
Cikin mamaki Salis da Laɗifa suke kallon Hajiya domin jin abun da take faɗa. Cikin ƙarfin hali Salis ya ce "To yanzu Hajiya ina ruwan auranki da aikin AJ? Sannan ma meyakawo zancen zakiyi aure bayan muna magana a kan ɗan aikine? Sai a lokacin Hajiya Babba ta fahimci katoɓararr da takusa ta tafka. Ai kuwa cikin sauri da rikicewa ta gyara maganar ta da cewa "To ai nasan halinkune yanzu ina faɗa muku aikin da na ɗauke shi sai kuce ku bai mukuba kumani haka nakeso.
Da sauri suka haɗa baki da cewa "Faɗa mana mun yarda? Hajiya Babba cikin farin ciki ta ce "Zai dinga tuƙani duk lokacin da naso haka. Sannan zan dinga aikansa cefane dade sauransu, shikenan fa aikin, ma'ana dai yaron gidana. Da sauri Salis ya ce "To yanzu Hajiya a kan wannan shine kike cewa wai zamuce bamaso?...ai gaskiya ma Walhi daɗima naji kinga shima yaron yanzu sai ya ɗanji daɗi ,Allah ma dai yasa ya iya mota? Hajiya Babba ta ce in bai iyaba za'a koya masa. Ita dai laɗifa bataso AJ yasamu aiki a gidan nasu indai ba aikin gadi bane, amma ya zatayi haka zata haƙura, amma tayi alƙawarin shida kansa zaibar gidan saboda cin mutuncin da zata dinga masa. ( *NI KO S REZA NA CE UMM-UMM FA🤓)* Ta ce "Bro muje nazo da labari? Salis ya ce to muje ɗakina. Haka suka tafi suka bar Hajiya Babba cikin murna ganinn ta shawo kan yaran nata cikin sauƙi.
Laɗifa ta ce Bro Inason namaka wata tambaya dan Allah ka bani amsa?
Salis ya ce "ina jinki.
Ta ce "Shin ADDINIMU ya amince mace musilma ta auri arne? ( KRISTEN)
Cikin mamaki ya ce "Ban gane ba?
Ta ce "To kaman dai ni Laɗifa zan iya auran wanda ba Musulmi ba? Ta basa maganar dalla-dalla domin taga yana son ɗaukar abun kamar wasa.
Salis ya ce "Bana son rainin hankali idan zakimin bayani yanda zangane to kimin in ba hakaba Allah zan koreki waje tinda naga bakida abun faɗa sai shirme.
Cikin serus ta ce "Bro Walhi sonsa nakeyi... tin jiya da na haɗu da shi har yanzu ban manta dashiba, kuma inajin zuciyata namin zafi duk lokacin da na aiyana cewa babu aure a tsakanin mu, ganin ba ADDINIMU ɗaya ba.
Salis ya ce "Waye... kuma yaushe kuka haɗu... kuma me ya haɗaku???
Cikin rashin tsoro da kuma saboda yayan nata wajan sanar masa da duk wani sirrinta ta fara bashi labari abun da ya haɗata da shi kamar haka... Laɗifa ta ce "Jiyane a clup munje taya zee-zee bikin birthday ɗinta. "Sai me ya faru? Salis ya sake tambayar ta.
"Farine dogo kansa yayi wani irin ɗan iskan aski, zaune muke a teburin gabammu wanda muka cika shi da kayan shaye-shaye (abu buwan sha) dade sauransu, Kasancewar gurin bawai iya mune muke gudanar da fatin ba harda wasu hakanne yasa gurin ya cika sosai. Muna cikin hakane sai mukaga ana ihuu! An zagaye wani teburi, muna zuwa sai mukaga mata da maza ne agurin yayinda ake saka gasar kuɗi...
Budurwa da saurayi ne zasu fara yiwa junann su kiss batare da kowa ya taɓa ɗan uwansaba, idan macen ta taɓa namijin to shine yaci, idan kuma namijin ne ya taɓa macen to itace ta ci. Taci gaba da cewa...ana cikin haka layi yazo kansa. Sanda tayi shiru zuwa wani lokaci kafin taci gaba da cewa...Suka saka dubu ashirin-ashiri shida wata yarinya, nann suka fara... yarinyar tsaɓar ta cika cikakkiyar yar duniya batayi komai ba amma shi sai ya ke neman ruɗewa hakane yasa ya faɗi. Sai'a ka fara ihuu!. Shikuma cikin jin kunya ya ce a sakeyi. In ta ƙaice maka zance saida sukayi sau uku duk tana cinyeshi. A'na cikin hakane akazo gurin bada kuɗi, duka-duka kuɗin dake jikinsa dubu sha ukune, kuma dubu sintin zai bata (60,000) nann fa ya rasa yanda zaiyi, shima abokin nasa da alamu dai bashi da kuɗi, amma abokin nasa musulmi ne.
Nikuma tun lokacin da nayi ido biyu dashi naji gabana na faɗuwa, take naji gayan ya kwanta min har cikin raina, shinefa na karɓi acont ɗin sa na tura masa dubu ɗari. Kuma tin lokacin bai kiraniba, Allah Bro ina sonsa kuma zan iya komai a kansa.
Salis ya saki baki da hanci yana sauraron ta. Saida ta gama sannan cikin ihuu!! Salis ya ce "Ya isaaaaa, harsaida laɗifa taji tsoro. Ya ce "Arne, ɗan iska, ɗan clup, mai bin Mata, wanda ya mayar da iskaci sana'a, shine kikeso!? Wanda kika ganshi yana shan bakin wata shine wanda zuciyarki ta gani kuma takeso ko!? Cikin ɓacin rai ya ce "Karki sakemin maganar wannan wawan yaron idan kuma kika sake to wallhi sai na lahira ya fiki jin daɗi, shin ina hankalin ki da tinanin ki, mutumin da ba ADDINIMU ɗaya ba, kuma ɗan iska!!! Tashi yayi yana nunata da hannu ya ce "Karki bari Hajiya Babba taji wannan maganar kuma kema karki sake mai-maita zance domin bazan miki ta daɗi ba a kan haka. Kibar ganin wai ina sonki ina damu da dawarki, hakan ba yana nuna cewa bazan iya hukuntaki bane. Yana faɗa ya tashi yabar ɗakin cikin mamaki haɗi da fushi.
Ita kuma Laɗifa kallon bayansa tayi harya bar ɗakin sannan ta share hawayen da suka zubo mata tun lokacin da ya fara mata faɗa. Ta ce "Kaman yanda nace akansa zan iya yin komai to tabbas hakane zanyi komai koda kuwa ADDINIMU mai yardaba domin nidai ina sonsa.
*AJ. SARAH*
Gudu-gudu sauri-sauri yakeyi domin kuwa yasan ya ɓata mata lokaci sosai. Wayarsa ce tayi ƙara sau babu adaddi amma yaƙi ɗagawa, saida ya gama shirinsa gaba ɗaya kafin ya ɗauka wayar yana mai ɓoye dariyarsa ganin tarin miss call ɗin ta har guda ashirin da uku (23) da sauri ya fito daga ɗakin nasa cikin shiga irin ta masu zuwa club. Cikin mamaki Nana take kallon yayan nata ganin yanda yayi kyu. Ta ce "yaya ina zuwa ne haka kodai kasamo