Addininmu Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  S Reza Category :  Love

Chapter   16 / 37

45K to 48K   out of 109.2K words

a haiyacinta, har wani ƙara tsofewa tayi. Buɗe ƙofar gurin akayi da sauri Nana ta ɗago kai ta kalli ɗan sanda da ke ɗauke da sanda a hannu. Shima kansa ganin irin halinda suke cikine yasa ya kasa dukansu ya shiga lallaɓasu kar wannan tsohuwar ta mutu a hannunsu. "Kutashi ku fit. shine abunda ya ce yana kallon Nana. Haka Nana ta ɗago Innah wacce ko buɗe ido batayi. Ita kanta nanar ba kwari garetaba, sai kawai ta shiga jan innar yayinda ƙadafunta ke jan ƙas. Saida suka fito waje tukun idon Nana ya raina fata domin kuwa ganin gurin da suke. Da kyar ta samu mai keke ya ɗauketa izuwa asibiti. Da sauri likitoci suka amshi Innah, yayinda ta ce da mai mashin ɗin bari ta bitu ya kaita gida ya dawo da ita sai ta bashi kuɗin.

Saida taga ɗakin da aka ajiye Inna kafin ta fito izuwa gurin mai keken. Unguwarsu ta faɗa masa ta ce ya kaita. Aƙofar gida ya ajiyeta ita kuwa tana sauƙa ta shige gida domin bataso wanda ya santa ya ganta a yanda take. Gurin da ta ajiye kuɗe taje ta ɗauko dubu ɗaya ta fito ta tsaya daga ciki ta meƙawa mai mashin ɗin, bata ko tsaya ba ta koma ciki da sauri. Tana shiga ɗakinta ta faɗi a ƙasa ta fashe da kuka tana kiran sunan yaya yaya yaya! Wani ɗaci takeji tanajin ta tsani soja da ɗansada domin kuwa tasan basuyi komaiba yayantama tasan baiyi komaiba, tunowa da tayi da Innah sai ta miƙe ta rasa nema zatayi yanzu.

Tashi tayi ta ɗibi ruwa aranda ta shiga bayan gida tayi wanka, sosai ta wanke jikinta da har wani wari-wari takeyi, ta fito daga bayan gida ta zaɓi ɗaya daga cikin dogayan rigunann da Aj ya sayo musa ta saka, sannan ta shiga ɗan ƙaramin kicing ɗinsu ta ɗora ruwa domin samar musu abinci.......✍️







*PAGE.* 2️⃣3️⃣

.........Bayan ta kammala komaine ta zauna taci abincin sosai sannan ta shiga neman wayarta ganin lokaci na tafiyane yasa tabar neman wayar ta fito da kuɗin da AJ ya bata gaba ɗaya. Gaba ɗaya tasaka kuɗin ajaka sannan ta shiga ɗakin Innah itama ta ɗaukar mata doguwar riga guda ɗaya da kuma atamba da zani. Saida ta haɗa komai kafin ta tsaya ta ɗan gyara gidan sama-sama. Haka taci gaba dayin komai cikin juriya da jajircewa domin kuwa ita kanta tana buƙatar hutu. Kasan cewar basuda wani ɗan abunda zata zuba gaba ɗaya kayan nasu harda abincin ne yasa ta ɗauki ledar da AJ ya kawo musu kaya aciki tun wancan lokacin, gaba ɗaya ta zuba kayan aciki kafin ta koma ɗakin Innah domin ɗaukar wayar Innah. Dai-dai jikin ƙofar ɗakin Innah taga leda, tinda tashigo taga ledar amma batabi ta kantaba. Ɗauka tayi da sauri tana buɗewa, da sauri ta zuba kayan aƙasa cikin mamaki ta ce "Waye ya kawo! Sai kuma ta gyaɗa kai domin abinda zuciyarta tace mata.

Abubuwa ne aciki wanda ke nunida cewar kayan tsaraba ne aciki kala-kala...irinsu lemo ayaba biskit madaran ƙwankwani da dai sauran abubuwa harda kayan shayi. Cikin sauri ta ce "Kode yaya yana garine kokuma ya dawo! Kodai yasan abunda ke faruwa damune amma ya share! Kodai da gaske kuɗin yasata ya gudu yabarmu!?. Ta ce "No Yaya bazai iya ba. Take hawaye ya shiga zubo mata, ta miƙe tabar kayan a haka ta fita daga gidan tana kuka.

Farin hijjab ne ajikinta wanda ya rufe mata dukkan jikinta, tana tafiya kamar wacce bata son taka ƙasar. Kowa dake unguwar kallonta yakeyi cikin mamakin ganinta a unguwar, gashi anason yin gulma babu dama, domin kuwa Nana Bama kowane yasanta a unguwarba, ita kuwa batasan sunan kowa a unguwarba saide Kadija da ƴan gidansu. Haka dai takai har bakin titi ta tare me kike izuwa asibitin da Innah take.

*SALIS* *POV*

Koda ƴan sandan suka sakeshi sai yazo gurinsu ya amshi wayarsa, yana dubawa yaga tarin miss call. Cikin mamaki yakebin numbar Hajiya dake nuni da cewar daga 9j take kiransa. Take ya danna numbar Hajiya Babba yana jin wani farincikin. Dai-dai lokacin da sojan yazo yace dasu Hajiya Babba sushoigo dai-dai wannan lokacin kiran Salis na shigowa wayar Hajiya Babba. Bayan ta ɗaga ya ce "Hajiya yaushe kika dawo? Yayi tambayar cikin farin ciki, domin kuwa harga Allah yana son hajiya ta dawo domin asan abinyi. "Kana ina yanzu? Yaji muryar ta acikin kunnuwansa? "Gani a hanyar gida yanzu zan shigo. Hajiya ta ce "Ban gane ba? Salis da baisan cewar Hajiya taji labarinba ya ce "Yes Hajiya na ɗan je wani gurine amma ganinan yanzu. Yana faɗa ya jashe waya yanufi gida cikin sauri. Ita kuwa Hajiya Babba tayi tunanin ko Salis ɗin yana gudan Daniyel, amma hakan bazai hanata shigaba domin yau tanaso ayi komai a gaban yaransu, kowaji abunda yakesonji.

Bayan Hajiya Babba taji ya kashe wayar sai ta kalli laɗifa ta ce "Yau zan ƙarasa baku labarin tsakanin Daddinku da wannan mutumin. Laɗifa ta ce "to Hajiya mu koma gida mn sai muyi labarin agida? Hajiya ta ce "no a gaban sa za'ayi domin kusan asalinsa. Ɗan gajeran message ta turawa Salis kafin suka shiga gidan bayan manya-manyan sojojin sun wangale musu ƙaton get ɗin gidan.

Saida yaje ƙofar get ɗin gidan nasu kafin ya ji shigowar message, yana dubawa ya tsaya yaci gaba da karan tawa, afili ya ce "Gidansa kuma! Why? Hajiya. Ya ɗauki a ƙalla awa ɗaya acikin gidan kafin ya shirya yafito cikin shigarsa ta mlm bahaushe. Ɗanyar shadda ce wacce taji aki ga hular kalar kayan, kana kallon Salis sai ka ƙara tsabar yanda shiga tayi dai-dai da surar da Allah ya bashi. Wata motar ya ɗauka yana sauri domin yasan ya makara tundade minty talatin ta bashi.

Saida yabi ta police station ɗin da aka kulleshi akan ko wani zai sanar dashi inane a ka kai su Nana, amma kowa na tsoro. Sai kawai yabi ta unguwar su Nana ɗin, yana zuwa yaga gidan a ƙulle, da mamaki ya ce "To kodai shima aj ɗin ya dawone, aikuwa ya shiga kiran numbar Aj amma no amsa, numbar Nana kuma har yanzu bata shiga, haka yanufi gidan da zaije batare da yayiwa kowa magana a'unguwar ba.

Dai-dai Hajiya Babba ta saka ƙafarta gidan Comanda Daniyel sai taji wani mugun faɗuwar gaba haɗida jin ƙirjinta nayin wani zafi. Kallon gidan tayi sama da ƙasa kafin ta fara karanto duk addu'ar da tazo bakinta, amma tafi ambaton hazbinalhu wa'ni'imal wakil. Tabbas wannan faɗuwar gaban nata da wani abu da ya shafe ta a cikin gidannan.

*GIDAN SOJA*

Wanka yayi cikin sauri-sauri

, Haka yayi shigarƙananana kaya rigar adides, kallon kansa yayi da kyu yaga yanda ya rame, sai ya ɗauki ledan kuɗin da abokan nasa suka kawo ya fito da kuɗin ya ce "Waoo i love this baby girl so much. Cikin yaran su ya ce "Thanks laɗifa bari komai ya dai-daita zan huta dake kin haɗu sosai, yana kaiwa nann ya bar ɗakin izuwa kicing yana tunanin ƙanwar tasa ko ya zata kaya tsakanin Daddy da kuma aj ɗin.

Kallon gidan takeyi ta ko ta ina. Tabbas gidan yafi nasu gyrma amma bai kai nasu haɗuwa ba. Cikin dakiyar fuska suka tura ƙofar palorn itada ɗiyar tata, ai kuwa sukayi ido huɗu da Comandar Daniyel da kuma matarsa wato Elixa. Cikin mama Momy wato Elixa ta miƙe cikin mugun mmk ta ce "Fatima!? Hajiya Babba ta ce "Na'am Elixa!? Comandar ya ce "Fatima!? Dai-dai wannan lokacin Samuel ya nufo gurin, aikuwa sukayi ido huɗdu da laɗifa.

Cikin mamaki ya ce "laɗifa! Itama ta kalleshi batare da tace komai ba. Cikin sauri Daddy ya ce "SAMUEL...."kafin yayi mgn Hajiya Babba ta ce "Shima ɗan naka kasheshi zakayi saboda yabi addinin da ba nakaba? Cikin zafin rai mommy ta ce "Fatima karkiyi tunanin ko yanzuma kinfi ƙarfin ƙara ƙarɓar wani hukuncin ne irin na baya. Dai-dai Lokacin Salis ya shigo palorn ɗauke da sallama. Laɗifa ce ta amsa yayinda Elixa ta daja masa wata tsawar da tasa Sarah dake cikin ɗakin da aka mayarta tsorata. "Ƙarka ƙara mana wannan abun a gidan idan ba hakaba Walhi sai kayi ladama. Idon Salis ne ya sauƙa akan wani ƙaton hoto dake cikin palorn wanda iri ɗayane da nacikin palornsu. Baiyi mgn ba dukkda kuwa ya tsaorata da tsawar da mommy tayi. Ɗaukar hoton yayi yana shfa hoton cikin sakin mura. Wata tsohuwa ce manne a jikin hoton wanda duk iri ɗaya ne da na palornsu. Ganin haka yasa itama laɗifa nufar gurin cikin sauri. Daddy ya ce "Kifita kibarmin gida yanzu kokuma nasa ayi miki abinda bakiyi tunaniba kinsan irin matakin da nake ɗauka akan duk wani musulmin daya shiga sabgata? Jin haka Hajiya Babba ta samu guri ta zauna ta ce "Ok tom Ina jiranka?

*(Akwai batu a'cikin wannan labarin)*

*WASU SHEKARU DA SUKA SHUƊ ABAYA* .

Wani ɗan ƙaramin ƙauyene dake cikin local Government ɗin *BOKON* ta cikin Benue st. Ƙauyan mai suna...katunku. kamar yanda kowa ya sani garin garine na tibabe, haka zaluka bakowane kejin wani yareba bayan yaransu na tibi. Akwai ƴan kaɗan da suka samu shiga cikin gari wato *BOKON* kokuma cikin Benue MKD domin samun ilimin zamani. Garin dukkansu ƙabila ɗayane haka zaluka addininsu ɗayane, wato addinin Cirstand. Garin ɗan ƙaramine saide kallo ɗaya zaka musu kasan suna cikin tsanani na rashin wayewa da kuma rashin abubuwan zamani.

Zaune suke su huɗu yayinda ɗaya daga cikin take kwance alamar dai batada lafiya, sukuma sauran ukun sun zagayeta suna mgn cikin neman mafita daga ciwon ma haifiyar tasu. Mace ɗaya sai maza biyu wanda kana kallonsu kasan jini ɗaya ne.

Cikin kuka macen ta kalli yayun nata guda biyu cikin harshen da shikaɗai ta iya ta ce "Yaya dan Allah koda shagon nakane ka siyar sai mu kaita asibitin cikin gari dan Allah kar mama ta mutu? Wanda a kewa wannan maganar ya sunguyar da kansa ƙasa yana zubar da hawaye cikin tsananin tausayin halinda suke ciki, kafin yayi mgn babban yayan nasu ya ce "Yanzu da mama nada lafiya komai shi zatace, idan anyi magana tace shine mai tausayinta idan kuma anyi laifi saide ta ɗora min koda kuwa shine yayi laifi, Amma yanzu bata da lafiya ance kasiyar da shagonka a kaita asibiti kaƙi.

Cikin kuka da takai ci wanda akewa wannan maganar ya ce "Haba Daniyel yakakeso nayi da rayuwata, shagon da kuke ta magana akai menene acikin sa komai ya ƙare, kai kanka lokacin da zakaje zana jarabawarka acikin kuɗin shagonne, sannan kuma tun lokacin da mama take wannan rashin lafiya duk acikin kuɗin shagonne. Yanzu haka babu komai a cikin shagon, komai ya ƙara. Ya faɗa yana kamo hannun mamar tasu yana sake fashewa da kuka.

Cikin faɗa yayan nasa ya ce "Ƙarya kakeyi Solomon yanzu da ka siyar da shagon ƙwara mama tamutu!? Cikin sauri Solomon ya ce "Shikenan aje a nemo mai siya, idan ya siya sai mu kaita asibitin. Cikin sauri Daniyel ya fita sai gashi da mai siyan shagon. Aikuwa aka yiwa shagon guɗi naira dubu ashirin da ɗaya, kasan cewar babu komai a'cikin shagon. Haka Daniyel ya karɓi kuɗin, batare da yayi wa ɗan uwan nasa bayanin komaiba, saide yace washe gari zasu tafi cikin garin Bokon domin kaita asibiti.

Washe gari tun safe Solomon da ƙanwarsa wato titi suka nemi ɗan uwans Daniyel sama da ƙasa an rasashi, tun safe har yamma babu shi babu alamunsa. Cikin wani sabon tashin hankalin Solomon yake kuka yana kallon mahaifiyar tasu da duk abunda sukeyi tana kallonsu amma babu damar magana. Daniyel da Solomon da titi...yarane ga Ushe wato mahaifinsu, ya daɗe da rasuwa tin lokacin titi tana ƙaramar. Sai mahaifiyarsu suna cemata maman Daniyel. Acikin yaran nasu kuda ɗayane yayi karatu wato Daniyel, domin lokacin ubansu na raye,har yagama Secondary school. Ɗan uwansa kuma yana son karatu amma basuda dama kasan cewar noman doya sukeyi.

Haka dai ya dage har ya ɗan buɗe ƙaramin shago agarin wanda shagon yake ƙofar gidansu, kuma a hakan shagon babu kamarsa duk cikin ƙwayan dukda ɗan ƙaramine. Tin da aka kafa wannan shagon Shikenan yayansa wato Daniyel ya ce tofa shine zai ɗauki nauyin karatunsa ga nauyin gida. Haka kuwa a kayi yana noma yana kasuwanci sai Allah ya dafa masa, yake ɗan samun riba dai-dai kwarkwado.

Yana son yin karatu amma saboda na yayansa shikuma ya haƙura da nasa. Ana cikin haka shago ya fara jabaya domin kuwa anfi ƙarfin shagon. Ana cikin haka rashin lafiya ya kama mamarsu shine zaije gurin wannan mai magani suje gurin wannan har komai na shigone ya ƙarasa ƙarewa sai kuma ga shi yanzu yayansa yasa an sigar da shagon kuma ya gudu da kuɗin.

Kwana ɗaya kwana biyu, babu Daniyel babu alamarsa. Haka Solomon da ƙanwarsa suka cigaba da jinyar mamarsu. Cikin kwana na biyarne, cikin wani dare sai ji sukayi tana musu mgn bayan ta kai wata huɗu batayi magana ba. "Solomon Solomon! Ina kuke ina titi? Haka take ta cewa cikin dare. Da sauri sukazo gareta suna kamo hannuta. Ta ce "Solomon ga ƙanwarka ka kula da ita kuma duk rintsi duk wuya karkubar Addiniku kuzauna acikin ƴan uwanku, sannan shima ɗan uwanka ka sanar dashi akan muhimmancin addinimu Pls dan Allah karku bar addinimu da al'adar mu, kuma kukula da ƙanwarku karka bari ƙiyayar dan uwanka ya shigeka haka yake sai kayi haƙuri dashi.

Cikin sauri Solomon ya ce "Mama kin samu lafiya ne? Walhi namiki alƙawarin bazan taɓa barin ADDINIMU ba, namiki alƙawari, itama titi tafaɗa hk. Haka dai Solomon ya ce "Dan Allah Mama ki daina faɗa haka bazakimutu ba muna tare gashi kin warke kin samu lfy. Titi sai murna takeyi tana ganin yanda mamarsu ta samu lfy lokaci ɗaya.

Haka sukaci gaba da hira tana basu labari akan muhimmancin addininnasu. Cikin mamaki sukayi barci cikin farinci tati na manne ajikin mamar tasu. Washe gari kamar yanda ya saba da safe yaje gona ya ciro musu doya. Tindaga bakin layin unguwarsu yake jin koke-koke, da sauri yazo ƙofar gidannasu ganin anɗan fara taruwa. Yana shiga yaga titi a gaban mama sai kuka takeyi. Haka shima ya shiga rusar kuka kamar wanda kukan zai dawo musu da ita.

Suna cikin wannan hali,wani kawunsu yazo ya ce "Ga mota ankawo wacce zata ɗauki gawar daga nann ƙauyan zuwa cikin gari wato BOKON domin a kaita mutuware kuma kuɗin motar sai an bashi dubu ɗari harda ashirin. ..sannan ga kuɗin wata allura da ake siya domin miƙar da gawar karta sanƙare, ita kuma dubu goma kuma guda biyu akeyi, sannan duk a yau akeso kuma ayanzu.. Sannan idan ankai gawar mutuware duk kwana ɗaya idan gawar tayi dubu ɗaya ne za'a biya, bayan nann kuma idan an karɓo gawar ranar da za'a binneta sai sunyi biki an yanka abubuwa kamar akuyoyi alade da abubuwan shaye-shaye irinsu giya burkutu dadai sauran abubuwan da al'adar su ta tanadar. wannan duk al'adar su ce kokuma na ce Addininsu. Idan wannan gawar takai shekara tofa sai kabiya kuɗin shekara, idan wata ɗaya ne ko biyu kai komai dai nawane. Cikin sauri Solomon ya ɗago kai ya kalli kawun nasa cikin hawaye idanuwansa sunyi jajawur...📝





*Tofa masu karatu kunji wani addinin fa!? Shin yaya Solomon zaiyi? Shin kokunsan waye wannan solomon ɗin?*




*PAGE2⃣4⃣*

............Tabbas solomon yasan wannan abubuwan da Uncle ya lissafo duk cikin al'adarsune, tabbas yasan wannan duk al'ada ce ba addininsu bane, amma shi bai taɓa tunanin cewar abun zai zagayo ta kansa ba! Kallon kawun nasu yayi(Uncle) cikin muryar kuka ya ce "Banida kuɗi banida komai bansan ya zanyi ba, yana kuka yana riƙe da hannun titi wacce itama kukan takeyi. (duk wannan maganar cikin yaransu yakeyi wato yaren tibi) Kafin kowa ya sake mgn sai sukaji anshigo gida cikin ihuu! haɗi da ƙara. Suna juyawa sukayi ido biyu da Daniyel wandake rusar kuka ko ganin gabansa bayayi. Da sauri titi ta 'karaso gurinsa ta rike 'kafarsa tana kuka tana cewa "Yaya Daniel mama ta mutu please and please ka ce mata karta tafi ta barni!?. Cikin kuka shima Daniel ya kamota tsam ajikinsa yana rarrashinta,shima Solomon sai kawai ya fad'a jikinsu yana kuku abun tausayi. Suna cikin hk kawun su ya sake cewar "kunsan fa tin cikin dare ta mutu saboda hk dolene ayi wannan alluwar domin karta fara wari agari, kuma kar ta san'kare. Daniye da baisan zancen me a keba ya kalli uncle din nasu ya ce "Kawu meya faru?

Tsaf uncle din nasu yasanar masa da duk abunda ake bu'kata kamar yanda ya sanarwa da Solomon. Cikin sayri Daniel ya ce "Uncl a samo mai siyan gonar mu sai kawai a siyar masa kaga ai sai musamu na kaita mutuware? Da sauri Solomon ya d'ago kai ya kalli yayan nasa cikin mmk amma bai ce komai. Tabbas kam indai har ba gonar zasu siyarba to basu da wannan ku'din da zasu iya biya, to amma gonar fa guda biyuce kawai, ɗayama daga ciki ta solo d'in ce da ya siya da kansa tunda sad'ewa.

Haka kuwa akayi suka samo wanda zaisiya, akayi cinikin gonar amma solo ya ce banda kayan ciki wato doyarsa, domin kuwa doyar ta nuna harma an fara cira ana ci.

Bayan ansiyar ne solo ya samu yayansa ya ce "Yaya ina kuɗin shagon da aka siyar kace zamu kai ma..."kafin ya 'karasa ya ce "Ninasan dama baku damu daniba, wato na ɓata amma kai damuwar ka kud'iko? To 'barayine suka bini abaya, Ina tunanin sunga lokacin da kabani kuɗinne shine suka bini, amma dai basumin komaiba kud'in kawai suka 'kar'ba. Solo ya ce "kayi ha'kuri Allah ya kiyaye gaba. Ya amsa da amin sannan ya ce yanzu zanje na nemo mai motar da zai d'aukemu zuwa cikin gari. Yana fad'a ya bar gurin yayinda solo ya bishi da kallo.

Sai wajan ƙarpe sha biyu na rana kafin Daniel ya dawo da wani mai moto har cikin garin nasu. Wanda har gawar ta Bara wari, ƴan gari sun fara surutu, dan gin ubansu kuma babu wanda ya taimaka da komai. Aikuwa solo da Daniel ne kad'ai suka d'auketa

16 / 37