Addininmu Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  S Reza Category :  Love

Chapter   29 / 37

84K to 87K   out of 109.2K words

nufin ko dai juna biyu k"...."Ya isa haka Dr mun gode tashi ka fita munji sai anjima. Hajiya Babba ta faɗa cikin tsananin ɓacin rai da tsoro. Da mamaki Dr ya meke zai fita daga dakin ganin yanda lokaci daya hajiyar tasa ta koma kamar mara lafiya.

"Dawo ka zauna. Yaji muryar Muhammad babu a lamar wasa. Muhammad ya kalli hajiya ya ce "Kin sanar masa da damuwar ki amma kuma tun kafin ya gama sanar miki da damuwar kin koreshi mai hakan ke nufi? "Daga kawai na ce masa bani da lafiya sai ya fara haɗani da ciki! Bashi da hankali ne? Ko an faɗa masa aikin likita haukane? To walhi sai ya barmin gida yanzunnan dan uwarsa. Hajiya Babba ta inda take shiga bata nan take fita ba, hakan ne ya sa Muhammad nazarin ta sannan ya kalli Dr ya ce "Wannan abubuwan da ka lissafo ma ta, shin da gaske alamune na masu ciki?

Dr ya kalli Hajiya da ta tsaya da zage-zagen ta na kallonsu ya ce "Eh Alhaji wannan alamunne na shigar sabon ciki. Cikin rashin wa sa Muhammad ya ce "Inaso yanzu ka gwada min ita domin tabbatarwa? "Da sauri ta fara surutai marasa kan gado domin kuwa ita kanta sai yanzu ta ke gano wasu alamu da Dr ya ce. "Alhaji ai dole sai tayi fitsari tukun zamu auna da shi? Muhammad ya kalleta alamar ta je tayi fitsari. Da sauri ta ce "To. Ta na haurawa Muhammad ya bita a baya domin shima yanzu ya gama yarda da cewar ta na ɓoye masa wani abunne. Ko da ya shiga ɗakin ya tarar har ta ɗebo ruwa a kwalbar turare zata juya. Sai kawai ta ganshi a gurin a tsaye ya na kallonta. Tsabar tsoro ta saki kalbar ta na kallonsa.

"Aisha mai ke ke ɓiyemin? Sanar dani komai kafin mukai ga aikata haramcin? Ya ƙara cikin wata muryar da tasa kukkan gaɓoɓin jikinta yin sanyi. Kukane ya kufce mata ta na kallon sa cikin so sa ƙaunarsa. Ya sake cewa "ki sanar dani komai ni mai tsaya mikene da yarda Allah karkiji komai, ko kin mata alƙawarin da na ɗaukarwa ogana kuma babana Salisu ne? Ganin ta yi sanyne yasa ya ce "Sanar sani komai karki damu nasan ki kuma nasan abunda zaki iya aikatawa da wanda bazaki iyaba.

"Hajiya cikin kuka ta ce "Babu komai walhi ban aikata konaiba pls. "To shikenan yanzu tinda har bazaki sanar min ba to kiyi fitsarin Dr na jiranki? Ta ce "No pls karka min haka dan Allah? "Ok to idan har kin yarda da ni kuma kinsan zan iya rufa miki asiri to ki sanar min da komai. Cikin kuka ta fara cewa... "Nayi Aure! Kuma kuma ku ku ma mun rabu da mijin shekaran jiiya, amma babu wanda yasan da auran. Ta ƙarasa ta na fashewa da wani irin kuka mai tafiya da imanin mai sauraronsa. Lokaci ɗaya Muhammad ya ji ɗakin na juya masa, sai kawai ya ƙura mata ido yana kallon yanda ta ke kuka kamar an zare mata nufashi.

"Saboda kinyi wani auren ne kike kuka ko saboda kin samu ciki? Ko saboda rabuwar da kukayi, kuma wani irin aurene wannan wanda kowa bai saniba? Sanar min da gaskiya Aisha? "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Wannan wani irin abun kunya ta kwasowa zuri'ar ta? Ta ma rasa ta ina zata fara masa bayani tsabar kunyarsa da ta keji. Ya ce "Aure kikace kinyi ba wani abun kunyarba, to menene abun tsoro a ciki? Idan ma nine kike tunanin zan damu to karma kisa komai a ranki domin da ma a tsarin Addinin Musulunci shekara huɗu ya bayar ga macen da mijinta ya tafi bai dawoba ta yi aure mutuƙar bazata iya jurewa ba, to bare kuma ke da nasan kin fita daban a cikin sauran mata. Hajiya Babba ta ce "Dan Allah banaso su Salis susan da wannan zancen? Muhammad dai badan zai iya hakan ba ya ce ya yarda.

Hajiya Babba ta kwashe komai da ya faru tsakanin ta da AJ har zuwa ranar da ya saketa da kuma kuɗin da ta bashi. Sannan ta ɗora da cewar...."Walhi abokin Salis ne sun shaƙu sosai domin shinema ya ka woshi gida har na ganshi walhi ina kunyar su san da wannan zancen. Muhammad sarkin haƙuri ya ce "Yanzu dai kema baki saniba ko kina da ciki ko a kasin sa ko? Ta gyaɗa kai. Sai ya ce "Je kiyi fitsarin ki kawo masa ya na palo. Ya na faɗa ya fita ya bar ɗakin cikin wani yanayi.

Dr Lurwan ya ce "Zuwa gobe zan kawo muku da sakamakon in Allah ya kaimu. "No yanzunnan zaka kawo mana. Dr ya ce "Ok an gama in sha Allah kuwa. Ya na tashi zai fita saiga Salis ya fito daga ɗakibnsa bayan ya gama waya da Nana. Suna haɗuwa Dr ya bashi hannu ya na tambayarsa ƙarfin jiki. Ya amsa da lafiya Alhamdu lillh. Sannan Dr ya bar gidan cikin sauri.

Salis ya zauna a kujerar da ke kallon Hajiya Babba zaiyi magana Muhammad ya ce "Dama ba tare kuka tafi da su Sarah ba ne? Kallon fuskokinsu ya yi yaga a lamar damuwa sai ya haɗiye maganar da yazo da ita ya ce "Daddy me Dr ya ce yana damun Hajiya ? Ta ke cikin Hajiya ya murɗa ai kuwa da sauri ta riƙe cikinta ta haura sama tana jin kashin na ƙoƙarin fitowa. Cikin dauriya Muhammad ya ce "Kawai zazzaɓi ne ba komai ba, kuma ya tafi ya kawo ma ta magani. Salis ya ce "To Allah ya sawaƙe. Daga haka ya tashi ya fita daga gidan dama a shirye ya fito. Muhammad ya yi shiru ya na tunanin abun yi yanzu! Ya zama dole yarannan suji, ai ba zina suka aikataba, saboda haka dole suji, kuma asan abinyi wannan ba maganar ɓoyewa ba ce, domin tabbas a kwai kura-kurai a cikin auran da ma sakin da a kayi.

Salis na fita gidan su Nana ya nufa cikin rashin kuzari domin yaso a ce yau ya yi magana da iyayensa a kan yarinyar da zai aura. Zaune ya ke a cikin motar bayan ya kirata ya sanar ma ma da cewar ya na ƙofar gida. Kallo Innah ta yi sai kuma ta fashe da dariya ganin yanda unnar ke kallonta tin ɗazu. "Innah ko dai kina koyan kwalliya irin wannan kallo haka? "Innah ta yi tsaki ta kawar da kai ge fe ba tare da ta ce komaiba. ""Innah dole nefa sai kin koyi kwalliya domin idan muka koma sabon gidanmu to fa wanka zakici irin ta hajiyoyinnan. Sai a lokacin Innah ta magantu ta ce "Wai ni a cikin raya guda biyunnan da suke zuwa gurinki wannane ne ya keyi da gaske? Domin ya kamata a ce izuwa yanzu munsan wanda ke zuwa da gaskiya?

Nana ta tsaya da ɗaurin kwalin ta ce "To da an faɗa miki da wasa suke zuwa? Kuma ai diukansu ina so. Ta yi maganar cikin tsokana. Inna ta ce "Au to sai ki haɗa su ga ba ɗaya ki aura rasa kunya. Yanzu waye yazo a cikin su? Dr ne ko Salisu ne? Nana ta ce "Wai Innah ina ruwankine? Ko kina son ɗaya daga cikinsu ne? To Salis ne, ta faɗa tayi hanyar fita da ga ɗakin. Innah ta dawo da ita da cewar "Idan kin fita ki toromin shi yanzu zamuyi magana.

Kallonta ya keyi har ta ƙaraso bakin motar bai ɗauke kansaba. Har ga Allah bai san irin don da ya kewa Nana ba, a koda yaushe cikin tinaninta ya ke, dik lokacin da ya ɗaga kai ya kalleta sai yaji wani sanyi na daban a cikin ransa. Da sauri ya buɗe murfin motar haɗi da sakin murmushi mai sanyi.

"Kinyi kyu sosai kamar na saceki na gudu. Ya faɗa ba tare da ya amsa gaisuwar da ta ke masa ba.

"Na gode sosai . Kaima kayi kyu fiye da nawa. Itama ta maryar masa da amsa ta na jin daɗin kasan cewa da shi. "Ni ne nayi kyu kallenifa ko wanka banyiba? "Ni dai kamin kyu sosai. "To nagode.

Sai ya kafe dara-daran idanunta da kallo batare da ya sake cewa komaiba. Itama ta tsinci kanta da kallonsa ta na jin shwƙin da bata taɓaji ba. Sun ɗauki lokaci a haka kafin motar babban yaya ta nufo gurin cikin gudan sa da yasa ba a duk lokacin da zai shigo unguwar ta su. Daga nesa ya ke binsu da kallo har baisan lokacin da ya daki motar Salis ɗin dake pake a gurin ba. Zuciyarsa ce ta hau tsalle ganin Salis da Nana a irin wannan yaninnda ba sai ka tambayaba kasan masoyansa.

A ranar da yamma Dr ya kawo musu saka mako, kuma ya nu na tana ɗauke da ciki na tsawon sati uku. Hajiya Babba ta yi kuka har saida Muhammad ya ja mata kunne akan cewar ai hakanne zaisa yaran su gano cewar a kwai matsala. "Dan Allah a zubar da wannan cikin? Cewar Hajiya Babba cikin kuka?

"Karki sa ke kice zaki fara ai kata kuskuren zubar da ɗan sunna, Idan har haka ta faru to walhi zakiyi mamaki. Wannan yaron walhi sai kin haifeshi domin da ubansa kuma kike zancen kar su Salis su sani to tayaya zaki raini cikin a gidan da suke? Kuma ya zama dole a sanar da uban ya ron. Cikin sauri da tsoro ido ta ce "To dan Allah ka ɗauki cikin a matsayin naka sai kawai muce bayan dawowarka muka samu, idan na ai'hu sai mu riƙe yaron ba tare da kowa ya saniba, Pls dan Allah kamin wannan alfarmar dan darajar Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama. Hajiya ta ƙarasa ta na kamo ƙaffun Muhammad. "Dan Allah kamin rai ka rufamin a sari walhi kunya zanji bazan iya kallon Salis da Laɗifa na ce na auri yaronnan har ya min cikiba, dan darajar Allah ka taimakamin? Ta na kuka kanta a sun kuye a ƙasa tana na damar wannan auran da tayi, wanda take jinsa tamkar a ce ciki shige ta je tayi. Ganin Muhammad ya yi shirune ya sa ta ƙara cewar "Dan Allah ko a zubar da cikin ko kuma mu karɓi yaron a matsayin namu? Dan Allah ka zaɓi ɗaya, walhi nayi na da ma, na tuba....📝





*Tofa! Muhammad sarkin tausayi da yafiya, shin wanne kuke ganin zai zaɓa a cikin alfarmar da Matarsa ta nema?*

*GA AJ GA SALIS*

*Comments ɗinku shine abun alfaharina*


*S REZA....*
[10/21 22:06] Aliyu Makko: *ADDININMU*




*S REZA...✍️*

*First Class writer's asso...*


*PAGE4️⃣0️⃣🔕*
....."Shin Aisha i'na hankalin ki da tunanin ki suka ta fi? Wannan abun da kika ai kata ba haramun ba ne, Addininmu bai yi hani ba amma gaba ɗaya kin hana kan ki sukuni haba Aisha!? "Eh na san ba haramun ba ne, am'ma wallhi na kwam'maci da na ai kata haramun ɗin da wann! "Subhana lillahi! A'uzu billahi! Aisha ba ki da hankali ne? Kinsan mai kike faɗa kuwa? Ko kinyi hauka ne? "Ban yi haukaba am'ma na tabbatar zan yi hauka idan har Salis da Laɗifa suka samu wannan labarin. Hajiya Babba ta ƙara sa ta na sake fashewa da wani sabon kukan. Muhammad ya na so ya rarrashinta amma ya rasa mai zai ce ma ta sai kawai ya fita da ga ɗakin cikin damuwa. Ya na jin yan da take ihun kiran sunan sa am'ma ya fita da ga ɗakin.

Kuka take yi sosai kai ka rantse da Allah dukanta a ke yi. "AJ ka cuceni ka tuna min asiri ci ki! Ni ni ni Aisha ɗauke da cikin abokin ɗana? Allah ka sa na mutu kafin ganinn ranar tonun wannan asirin! Muhammad da ke tsaye a bakin ƙofar ɗakin ya shigo cikin ɗakin cikin wa ni sabon salon tashin hankalin ya ce...

"Ya zama dole uban cikin da ke jikin ki ya san da wannan zancen, sannan dole yaranki suma susan da wannan abun arziƙin, bazan bi ye miki ki sake ai kata wa ni kuskuren ba, wanda kika yi a bayama ya isa haka, ki gode wa Allah ba cikin shege ba ne, walhi i'na ta ya ki murna da Allah ya tsareki da ga aikata alfasha. "Sannan ki sa ni wannan kukan da saɓon da ki ke yi ba shine ma futa ba. Ya na faɗa ya ƙara barin ɗakin jin a lamar da wowar su Sarah.

*AJ POV*

Idon sa a kan su ya fito da ga motar ta sa ya na bin Salis da wani irin kallon tsoron kar abin da zuciyarsa ta aiyana masa ya tabbata. Salis da Nana da suka ji ƙarar dukan mutar da AJ ɗin ya yi ne ya dawo da su daga duniyar soyayar da saku ta fi. Suna ganin AJ Salis ya saki murmishi ya na kallon fitowarsa da ga cikin motar da ya ke mamakin ganin sa cikin sabuwar mota. Ita ko Nana kunya ta ji domin ba ta so ya ganta a halin da ya same su ba.

"Lafiya Malam? Mai ya kawo ka gidan mu? Kuma gurin ƙanwata? AJ ya faɗa ya na haɗe fuska tamkar bai san wa ye Salis ba. Ci ke da mamaki Nana da Salis suke kallon sa ganin babu a lamar wasa a fuskarsa. Cikin tsawa ya ce da Nana "Ɓace min a nan kafin na fasa miki baki yanzu! Ai kafin ya ƙara sa har ta shige gida cikin kuka. Ya dawo da kallonsa izuwa ga Salis wanda ya yi mutuwar tsaye ya na kallon ikon Allah. "AJ Ka na cikin haiyacinka ku"..."Salis ka bar ƙofar gidannan yanzu Please? Ya faɗa ya na ƙoƙarin kawar da abun da ya zo masa zuciya.

"Wani abu ya faru ne da Hajiya ta zo gidannan? Ko dai Laɗifa ta zo ta ce wani abu a kan soyayyar mu da Nana? Salis ya yi wannnan tambayar ne domin yasan Hajiya Babba ta ce zata zo gidan su AJ. Kuma yasan Laɗifa ce ka ɗai tasan ya na son Nana. Cikin sauri AJ ya ka tsaye shi da ce wa "Ka yi haƙuri Nana ta na da Miji dan Allah kar ka ƙara zuwa ƙofar gidannan. Cikin tsananin ɓacin rai shima Salis ya ce "Ƙarya kakeyi AJ walhi Nana ta wa ce babu wanda ya isa ya rabamu da ita!

Cikin fitar haiyaci AJ ya kamo kwalar rigar Salis ya ce "Kai ɗin banza wa ye kai Nana ba sa'ar ka bace, kuma walhi sai ka bar mana ƙofar gida wawa kawai. Ganin da gaske AJ ya ke yi yasa Salis shima kamo rigarsa ya fara turashi. A na cikin ha ka Nana da Innah su ka fito. Dai-dai AJ ya sa ƙarfi ya ture Salis, ai kuwa ya yi baya-baya sai ya faɗa jikin motarsa. Da ƙarfi Innah ta ce "Abduljabaru"...."Abduljabaru"? Amma AJ ko kallonta bai yi ba. Ganin ha ka ya sa Innah ta je ta kamo hannun Salis ta na jansa cikin gidan. Da sauri AJ ya sha gabanta ya na ce wa "Walhi ba zai shiga gidannan ba, kawai ya bar an'guwar nan ga ba ɗaya. Cikin kuka Innah ta ce "Yanzu Abdul ban isa da kai ba kenan ko? Yanzu bazan maka magana ka ji ba ko? AJ ya kawar da kai gefe ya ce "Innah wai Nana ya keso kuma babu aure a tsakaninsu domin ita ɗin ba sa'ar sa ba ce, kai ga ba ɗaya ma an mata miji. "To ƙarya ka ke yi , sai na bashi ita, kai ɗin banza, Abdul ka ba ni hanya? Amma ko gizau AJ baiyi ba.

Cak Nana ta tsaya da kukanta ta na kallon AJ wanda ya ke ta zuba kamar ya zauce. "Babu aure tsakanin mu! An min miji! Wannan maganar ita ce Salis da Nana ke ta nazari. Ganin mutane har sun fara taruwa ne ya sa "Innah fashewa da kuka ta na dukan AJ wanda gaba ɗaya ya fita a haiyacinsa. Shi dai kawai ba ya son ganin salin a gabansa tsabar kunya da tsoro .

Ganin ha ka ya sa Salis cire hannunsa da ga na Innah ya na kallon Nana da itama shi ta ke kallo. Kallonta ya ke yi har ya buɗe motarsa ya shiga ya ta da ta ya bar an'guwar ci ke da ɓacin rai da tunani. Ganin ya tafi ya sa Nana sakin wani kuka ta na jin ta rabu da Salis kenan har a bada, AJ ya rabata da masoyinta na gaskiya. Da sauri AJ ya yi kan Innah da sauri ganin ta sume a gurin tammkar ba numfashi. "Innah! "Innah! Ha ka ya ke ta kiranta amma ko motsin ba ta yi. Da sauri ya ɗauke ta izuwa cikin motarsa, itama Nana ta bi yo bayan sa cikin ihun kiran sunan Innah har suka bar an'guwar.

Da sauri a ka karɓesu da umarnin Dr Lurwan wanda fituwarsa kenan da ga cikin asibitin zai tafi gida. Sun ɗauki a ƙalla a'wa guda kafin Dr ya fito ya na kallonsu da zuba masa Ido. "Dr Innar mu ta na lafiya dai ko? Dr ya ce "Ku biyoni? Ba musu suka rufa masa baya zuciyoyinsu na dukan tara-tara. "Dr ya kalli Nana ita kuma ta sunkuyar da kanta ƙasa ta na jin tsoron abunda zai fito da ga bakinsa a kan innar ta su. "Kin manta bayanin da na miki a kan ciwonta a wancan lokacin ne? Nana ta kalli AJ shima ya kalleta. "Dr ta sanar da ni, amma yanzu dai ai ta na lafiya ko? Dr ya ce "zuciyarta ta ƙara samun matsala fi ye da na baya saboda haka dole sai"...."Ya isa haka Dr idan kuɗi ne ko nawa ka ke so za'a baka Please dan Allah karka ce komai. AJ ya katse shi cikin tashin hankali. Ganin kamar baza su fahimci shine ba ne ya sa ya ce "To shikenan karka damu za'a kula da komai. Ha ka suka fito daga gunsa jiki a sanyaye.

"Laɗifa" Laɗifa" Salis ke zabga ma ta kira

29 / 37