Addininmu Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  S Reza Category :  Love

Chapter   25 / 37

72K to 75K   out of 109.2K words

naga shegen da zai shiga gidan? Ta faɗa tana wani girgiza kamar wata barbar mace. Umar ya ce "Haba diza ta bakya ganin irin halin da yake ne, walhi bashi da lafiya kuma gobe zai tafi kinji? "Walhi saide ya mutu indai sai ya shiga gidannanne, caf ɗi jam arne ɗin na bari ya shiga mana gida ai walhi ƙarama kare ya shiga , arnafa waɗanda basu yarda da Allah da manzansa ba, a'a walhi a ƙara gaba. Haɗiza ta ƙara sa tana kawar da idonta daga na Samuel ganin irin wani kallo da yake mata. Ta ce "Shege mai idon mayu wallhi Hadiza taci dubu sai ceto. Ganin haka yasa Umar cewa su tafi gidan su wani abokinsa. Ai kuwa Hadiza ta biyosu tana ce wa "Wooo atafi can ba dai nan ba dangin marasa salla dangin masu cin kara da alade andai yi a sara maye jikan mayu. Hakanne yasa ƴan unguwa suka fara taruwa a gurin domin an san halin Hadiza. Ganin haka yasa Umar saurin jan hannun Samuel suka bar unguwar. Samuel kam gaba ɗaya ya shiga sosai da lamarin yarinyar, shi baima san Umar nada ƙanwaba sai yau gata mara kunya , ai kuwa irinsu akeso masu irin wannan wayon, lallai kam ta kwana gidan sauƙi, dole nema ya ɗan-ɗana zumar wannan yarinyar. Yana tunani har suka ƙaraso gidan bai saniba. Ai kuwa suna zuwa shima gayan yana dawowa akan mashin ɗin sa. Shima yasan Samuel ɗin hakanne yasa ya ƙarɓesu hannu bibbiyu. Samuel ya sanar da Umar abunda ya faru, kuma ya ce yanaso gobe su tafi gidan su Laɗifa domin Sarah ta na can. Lokaci ɗaya Umar ya ranƙaɗa wani salati yana sanarwa da Ubangiji jin irin abunda iyayen Samuel ɗin suka aikata akan ɗan uwansu ya bar Addininsu. lokacin ɗaya Umar ya ƙara tsorata da halin Daniyel game da ƙiyayyar Addinin Musulunci. Ta wani ɓangaren kuma yana jin ta kaicin zamowar laɗifa da Samuel ƴan uwa, gashi bai aiwatar da nufinsaba. Haka dai Samuel ya dinga bugar cikin Umar akan Hadiza har ya gano komai game da tsoranta da yakeyi. Shi kuwa Umar ganin irin halin da Samuel ɗin keciki sai bai kawo komai ba dukda yasan halinsa na tabbatar da abunda ya gani yana son. Washegari suka hau mashin ɗin abokin Umar ɗin ya kawosu har gidan su Laɗafa.

*AJ .POV*

Tafiya yake cike da ɗinmun dana sani a cikin rayuwarsa, yanzu shi babban damuwarsa ta ya ya kuɗaɗensa zasu fito. Babu komai a hannunsa da ga shi sai kayan jikinsa wanda su ɗinma Usha ne ya ɗauko masa daga cikin kayansa, fuskarsa anyi bandeji ga gefen bakinsa shima a rufe, gaba ɗaya fuskarsa a gumbure take. Kana kallon AJ kasan baya cikin haiya cinsa tsabar wahalar da yasha a hannun Sojoji. Tsakanin asbintin da unguwarsu a kwai nisa amma haka ya tako a ƙasa yana tafiya yana tanƙaɗi kamar ɗan ƙwaya. Ya daɗe yana tafiya kafin ya iso layin unguwarsu. Tsayawa ya yi a bakin wani gida yana kallo gidansu daga gurin. Lokaci ɗaya ya tuno da abunda wannan gayan ya sanar masa cewar an kama su Innah da Nana. Tunaninsa izuwa yanzu an sakesu ne kodai har yanzu suna a ƙulle? Kafin ya kaiga yin tunanisa ya hango wata baƙar mota ta tsaya a ƙofar gidan...

Gaban sa ne ya ƙara bugawa kamar zuciyarsa zata fito. Ya ƙurawa motar ido yana son ganin wanda zai fito daga ciki. An ɗauki tsawon minti goma sha biyar kafin ya ga Nana ta fito, sai kuma yaga wani saurayi shima ya fito daga motar. Lokaci ɗaya yaji wani sanyi a ransa ganin Nana. Sai kawai ya nufi gurin cikin ƙwarin guiwa.

Tin kafin ya ƙaraso yake ganin yanda Nana ke dariya da a lamar dai koma waye wannan to sun saba dashi sosai, amma a ransa yana jin baya son haka. Kafin Nana ta baiwa Dr amsar tambayarsa idonta ya sauƙa a kan yayanta, shima ya sauke fararan idanunsa a kan na ta. "Ya ya!!! Ta faɗa da ƙarfi ta na nufar gurin da yake. Kasa rungumar sa ta yi ganin fuskarsa duk ciwuka, sai tazo gabansa ta tsaya tana kallonsa kuka na son kufce mata, sai tasa hannu biyu ta rufe bakinta dai-dai kukan ya kufce. Juyawa tayi ta shiga gida da gudu tana kuka tana zuwa ta faɗa jikin Innah ta na cewa "Innha ya ya ya ya ya dawo gashi a waje. Lokaci ɗaya gaban Innah ya faɗi amma ta kawar da kai ba tare da ta ce komai ba saina wani dogon tsaki da taja.

A waje kuwa AJ da Dr ne a ka fara kallon-kallo, AJ na son tuno a ina yasan shi, shi kuma Dr yana mamakin ganinsa a nan. "Dama shine yayan Nana! Ganin AJ ya kasa tuno inda ya sanshi ne sai Dr ya miƙa masa hannu ya ce Dr Lurwan likitanku. Lokaci ɗaya ya gano shi, bayan sun gaisa Dr ya ce "Zaka iya shiga gida ka huta saboda jikinka, idan ka samu nutsuwa sai muyi maga babban yaya.

Babu sallama ya shiga gidan jiki a sanyaye. Yana shiga Innah ta meƙe tsaye kamar dama jiransa ta ke. "Walhi idan har ka kuskura ka shigo gidannan ni kuna zan bar maka gidan ka? Ta na faɗa ta shiga ɗakinta ta fara haɗo ƴan tsummokaranta. AJ na tsaye a gurin har ta fito da kayanta a ɗaure a ɗankwali. "ka fita ka je duk inda kaga dama mu zamu iya rayuwa a matsayin da Allah ya ajiyemu ba sai mun kai kanmu inda Allah bai nufemu zuwaba. AJ ya buɗe baki zaiyi magana Innah ta katseshi da cewar "Idan har ka sake ka furta maga ta shiga kunnuwana to Allah ya isa ban yafeba, kuma mutuƙar kana gidannan to ni ya haramta a gareni, ba dai kai kace a kan kuɗi zaka iya yin komai ba, to kaje ka nemi kuɗinka mukuma ka barmu a inda ka ganmu, zamu rayu cikin talaucin da muke ciki. Innah tana maganar hawaye sun wanke mata ido, aduk lokacin da zata furta wata kalma to tana tuno irin cin mutuncin da wannan arnan ya musu , da kuma zaman da sukayi a ƙulle, ga zaman asbiti duk a kansa. AJ da Nana suma kuka sukeyi duk sun kasa cewa komai tsabar tausayin kakar tasu...

"Idan kuma har so kake sai kaga bayana to Abduljabaru gani dan Allah ka zo ka kasheni sai ka ci gaba da abunda kake ai katawa, a ce ka rasa da wa zakayi a bora sai ƴaƴan arna, to ni dai na fa ɗa walhi bazan taɓa yafewa ba. Ta ƙara sa tana dur ƙushewa a gurin nunfashinta na fita kaɗan kaɗan. Da sauri Nana tazo ta rungumeta ta zaunar da ita tana bata baki akan ta manta abunda Dr ya ce ne. AJ kuwa na tsaye a gurin duk ya fita a haiyacinsa yana jin tausayin Innah ji yake inama ana dawo da hannun agogo baya da baiyi wannan kasadar ba, Allah ya isan da ta masa yake ji na masa yawo a kai, lokaci ɗaya kansa ya fara juyawa, take shima ya sulale a gurin tamkar macacce. Ai da sauri Nana tazo gareshi ta rungumoshi tana kiran asalin sunansa " Abduljabaru" "Abdul". "Abdul dan Allah ka tashi karka tafi ka barni Pls yaya. Tana cikin haka ita kuma Innah ta ɗauki ƙullin kayanta ta bi ta bayansu ta bar gidan ba tare da sun saniba......📝




*Da yardar Allah zan koma yin posting kullum har mu kammala, domin an dameni a kan a gama wannan labarin to in sha Allah zamu kama shi yanzu. Amma fa yin hakan dole saida gudun mawar na ƙaramin ƙwarin guiwa ta hanyar comments da addu'o'in ku. Ina alfarari da ku S REZA na kune*


*ADDININMU is a Normal* *book*



*By S REZA ✍️*
[10/21 22:06] Aliyu Makko: *ADDININMU*




*S REZA...✍️*

*First Class writer's asso...*


*PAGE3️⃣5️⃣*

..........Kuka Nana takeyi ta na mai gir-giza AJ wanda har zuwa yanzu bai motsa ba, Tashi ta yi cikin sauri ta ɗebo ruwa ta watsay masa ta na binsa da ido kamar wacce bata taɓa ganinsa ba, ganin bai motsa bane ya sa ta ƙara watsay masa ruwan a karo na biyu. Wata doguwar ajiyar zuciya ya sauke ya na mai buɗe idonsa a kan Nana, sai kuma ya riƙe kansa ya na jin yanda kan ke juya masa, hannunsa ta kama ta na masa sannu cikin kuka. Ya buɗe baki ya ce "I'na Innah? Sai a lokacin Nana ta kai kallonta gurin da ta bar Innah ta na ce wa "Ga ta ce"...."Tsaya wa ta yi da hannun na ta a yanda yake ta na bin gurin da kallon mamaki. Da sauri ta miƙe da gudu ta shiga kiran innar ta ko ta ina. Da gadu ta ƙara fitowa ta na ce wa "Yaya Innah ta gudu walhi bata gidannan ta taffi. Ta na magar ta na kuka. Da sauri AJ ya miƙe tsaye yana nufar waje da sauri riƙe da kansa dake mugun sara masa. Itama Nana tabiyo bayansa ta na kuka. Ya na fita ya ci karo da Innah a ƙofar gidan a duƙe tana kuka tana sharar hawaye.

Da sauri ya faɗa jikinta yana fashewa da kuka ya kasa magana, itama Nana ta na zuwa ta faɗa jikinsu ta na mai sakin nata kukan. Kuka sukeye duk su ukun babu mai rarrashin wani a cikinsu, inna ta shiga shafa kan AJ tana mai jin tausayin sa a ranta. Cikin kuka ta fara magana "Tabbas bazan iya tafiya na barkuba domin bakuda kowa sai ni, kaman yanda nima bani da kowa saiku, amma tabbas Abduljabaru ka ɓata min rai wanda bazai musaltuba, amma na maka uzuri kaman yanda mahaifinka ya ce min a kanka, tabbas kai ɗin ɗan arziƙine, ka ɗauki nauyinmu alhalin kai kanka kana buƙatar mai tallafa maka, cinmu shmmu suturarmu gurin kwanan mu duk kaine, amma ka ƙi ka tsaya ka faɗa min gaskiyar sana'ar da kakeyi, sannan meye ya haɗa ka da wannan ar'nan? Allah dai yasa ba da gaskene sata kamasa ba? Shin Abduljabaru me kake ɓoye mana a tattare da kai? Muna son sanin gaskiya amma dan Allah kar ka ƙara mana ƙarya?

Cikin kuka AJ ya ce "Tabbas Innah nayi muku ƙarya wanda yanzu haka ta sakani a halin da na sani, kuma tabbas yau zan sanar muku da komai a kan kuɗin da nasamu, amma dan Allah Innah karki gujeni kisan cewar duk abun da na ai kata danku nayi pls innah? Innah ta ce "Innalillahi wa inna i'laihim raji'un, Allah dai yasa ba wani abun kaje ka ai kataba, shin ka manta lokacin da kake cemin AJ baya sata? AJ baya neman mata? AJ ba zai aikata duk wani abun da Addininmu ya yi hani da shiba? To Allah dai yasa baka ai kata ko ɗaya daga cikiba? AJ ya ƙara jin cewar lallai ya aikata kuskure, ita kuwa Nana ta ke ta tuno da zancen Kadija na cewar ya yi wa yarinyar cikine, sai kukanta ya ƙaru domin izuwa yanzu ta fara yarda da hakan.
AJ ya ce "Innah mushiga gida sai muyi zancen a ciki.

Bayan sun shiga gida Nana ta ɗora ruwa saida yayi zafi sannan ta juye a bokiti ta ɗauka izuwa banɗaki. Saida AJ yayi wanka sannan ya ɗauki kayan adides riga da wando ya saka sannan Innah ta ce yaci abinci tukunna. Itama innar wanka tayi tazo ta zauna kusa da angon na ta ta ce "Abduljabaru kaji tsoran Allah karka sake ɓoye mana damuwarka, kasani duk abunda ya sameka muma ya samemu, duba fuskarka tunda ka shigo na ganka a haka saida gabana ya faɗi, yana daga cikin abunda yasa kaga na kasa tafiya na barku, kullum addu'a'ta Allah yasa kana lafiya ya kuma dawo mana da kai gida lafiya a duk inda kake, haƙiƙa kullum cikin dare sai na tashi na roƙi Allah a kanka, amma a fili ina nunawa Nana cewar bazan yafe makaba domin ta gane cewar abunda kayi ɗin ba dai-dai bane. Inna ta ƙara sa ta na ruƙo hannunsa tana mai kallon fuskarsa dake a kumbure. Inna ta ce "Bari kaji halin da muka shiga a dalilinka?

Take Innah ta kwashe komai abunda a ka musu ita da Nana, tun daga marin da a ka fara mata a cikin gida izuwa gidan ƴan sanda da a ka kaisu, ga cin mutuncin da ƴan sandan suka musu, da taimakon da Salis ya musu shida abokin AJ ɗin, har sallamosu da a kayi, sannan ta ɗora da zamansu a asbiti da kuɗin da Dr ya kashe a kansu da irin kulawar da ya basu, aikuwa dai inna labarin ne ya ƙara dawo mata da komai sabo ta ci gaba da kuka ta ce "Tabbas Allah yayi i'nada sauran numfashi a duniya badan haka ba saide ka dawo kaga bana duniya, bansan lokacin da Nana ta kaini asbiti ba ban sani ba!

"innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! AJ ya dinga furtawa yana mai sakin kuka da jin tausayin inar ya ƙara rushewa da kuka ya na ce wa "Walhi duk nine sila, ba haka nasoba dan Allah Innah ki hukuntani na cutar daku a kan son abun duniya, waiyo ni Abdul na kusa kashe ahalina da kaina. Ganin irin sambatun da yake ne yasa Innah fara bashi haƙuri a kan cewar haka Allah ya tsara zai faru ya bar kuka. Da kyar ya tsaya yana kallon Nana wacce duk sai yaji wani irin rauni a zuciyarsa jin irin halin da ta shiga, ya kafeta da ido yana jin kamar ya ɗauketa ya sakata a cikin sa ko zata huta da wannan kukan da yake sakata, rungumeta yayi yana shafa kanta da bayanta yana saka mata albarka ita kuma tayi luf a jikinsa tana jan hanci. Innah ta yi shiru tana tunanin me AJ zai ai kata ya sa shi irin wannan halin. Sai da suka nutsu kafin AJ ya fara magana kamar haka...

"Kuskure na farko da nafara yi a yanzu shine wannan mutumin da ya sa a ka kaiku gidan ƴan sanda to yarinyarsa ita ɗin budurwata ce. Gaban Nana ya bada wani darammm tana jin shikenan ta tabbata. "Amma ni ina sontane badan komaiba sai dan dukiyar iyayenta duk da kuwa suɗin ba musulmai bane. Ita kuma ta na sona tsakani da Allah, sai nayi amfani da son da takemin nake turata ta sato min kuɗi a gidan su. AJ ya sanar dasu komai dake tsakanin sa da Sarah, duk yawan kuɗin da ta bashi saida ya faɗa musu har zuwa lokacin da a ka kamata. Ya sanar musu irin ƙiyayyar da mahaifinta ke yiwa Musulmai, saida ya gama komai Innah ta ce ...

"To saboda baka son ya kamaka ne yasa ka gudu shi kuma ya zo ya tafi damu ko kuma kana cikin garinnan kaiwai dai ka ɓoyene? AJ yayi shiru yana tsoron sanar dasu asalin abunda ya jawo wannan tashin hankalin. Shin to aure zaice yayi ko kuma me? Shin da wani ido zai kalli inna ya ce yayi aure, auranma mahaifiyar Salis, kai no bazan iya ba, kawai na je na saketa sai ta auri tsohon mijinta ni kuma ta bani kuɗina amma dai ba zan tona wannan sirrin ba.

"Abduljabaru kayi shiru kuma muna sauraron ka. Firgigitin ya dawo da ga tunaninsa yana kallon Nana da ta ƙura masa ido da a lamar dai a kwai magana a bakinta. AJ ya ce "kaman yanda na sanar da ke cewar aiki aka ɗaukemu izuwa ƙasar Niger kuma duk mun dawo lafiya. Ya faɗi maganar wacce daga ji kasan ƙarya yayi. Ya ci gaba da cewar bayan na dawo na samu labarin abunda a ka muku shinefa na je gidansa, to a can ya sa a ka rufeni muda wasu mutane. Haka dai AJ ya sanar dasu abin da ya faru a gidan Daniyel a kan ƙonesu da zaiyi, har zuwa asibitin da a ka kaisu da kuma shigowarsa yanzu. Amma bai sanar musu da cewar shida baban su Salis bane kawai dai ya haɗa ne domin wanke kansa, ya haɗa da dukan da yasha a hannun sojoji.

Nann ma dai wani kukan suka sha jin wai ƙonesu a kaso yi, suma sun tausaya masa sosai,, kafin Innah ta ce "To Allah dai ya kiyaye gaba, yanzu sai ka keyaye, babu ruwanka da yarinyarsa, ka fita a harkarta, AJ ya ce "In sha Allah Innah.

Innha ta ce "To aikin me kukaje yi a Niger ɗin? Cikin ruɗewa ya ce "Amma am dama fa wani uban gidanmune ya ce muje tonun zinare wai ana samu sosai, shinefa ya fara bamu kuɗi wai kowa ya sallami iyalansa kafin mu dawo. "To yanzu kun samo zinaren ne? "Eh mun samo amma babu yawa saboda bamu daɗe ba. "To Allah yayi albarka, yanzu sai ka tsaya ka nutsu kasan me kakeyi. Nana da AJ sukayi dariya jin wai kasan mekakeyi.

*HAJIYA BABBA POV*

Numbar AJ ta shiga kira amma ana sanar mata cewar a kashe ta ke, ta ma rasa wani irin tunani zatayi yanzu, kawai ta samashe ya saketa ta bashi kuɗin sa kowa ya kama hanyar gabansa, to ya zatayi da Muhammad. A fili ta ce "Kai co na! Rashin haƙuri baiyiba kwata-ƙwata ma sati nawa da yin auran! Shekara nawa nayi ba tare da namij ba, amma na kasa jure wannan lokacin, a'she dai Salis da Laɗifa taimakona suke sonyi amma na ƙi yarda, na shiga uku ina zan sa kaina.

Ɓangaren su Muhammad kuwa Salis ne ke bashi labarin irin cigaban da suka samu a harkar kasuwancinsu da irin nasarorin da suka ƙara samu. Shima Muhammad ya jin-jinawa matar tasa. Haka sai suka dinga hira sosai a kan rayuwa, Titi da su Samuel ma duk sun saki jikin su Umar da Usman duk an kaisu ɓangaren da zasu zauna kafin su huta zuwa wani lokaci a shiga Katungu. Titi ma a gidan ta kwana ita da Usha. Nann fa Laɗifa da SAMUEL suka fara zama a

25 / 37