Addininmu Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  S Reza Category :  Love

Chapter   1 / 37

1 to 3K   out of 109.2K words

[5/7, 10:31 AM] S REZA ✍️: 🤷‍♂️ *ADDININMU* 🤷‍♀️

( *By S REZA* )



☀️ *

*BISMILLAHI RAHAMANUN RAHIM*


*ADDININMU*
*PAGE* 👉0️⃣1️⃣

(Labarin ya fara kamar haka) Kai gaskiya innah wallhi masu kud'i suna hutawa suna jin dad'in su, kinga gidan da mukaje jiya kuws? Wallhi nidai idan na mallaki wannan gidan to nida talauci guma har a bada, yayi can nikuma nayi nann. Innah ta kalleshi cike da gajiya da wannan surutun nasa Ta ce "To dame zakayi kud'in ance kanemi aikin gomnati kace kai badomin aikin gomnati kayi karatuba, to a haka zakayi kud'in? Kuma ance kafara zuwa kasuwa ka ce kai bayanzu ba, kazama daga wancan gidan sai wannan anya kuwa rayu zata yu a haka Abdul jabari?

Abdul jabar wanda ya komar da sunan sa izuwa A J ya ce "Innah aikin gomnatin ne babu wani samu, nikuma da nakeso na zama shahararran mai kud'i a cikin garinnan sai kawai naje na kama aikin gomnati!! Ya ci gaba da cewa, yanzu fa a cikin wannan 'kasar tamu idan ana lissafin masu kud'i bazaki ta'ba jin sunann ma'ai kacin gomnati ba saide Yan kasuwa sabo da haka ni kasuwanci zanyi, kuma ki jira lokaci... Kinga yanzu innah bari na miki misali, yanzu a ce nasamu ai kin gomnati ace ana biyane dubu hamsin, to acikin wata d'aya menene dubu hamsin zata mana, mu uku?

Kinga ga kud'in makarantar Nana ga kayan sawa ga abin da zamuci. Sannan ba lallai bane bafa a biyani dubu hamsin d'in, amma in kasuwancine a rana d'aya ma Sai na samu dubu d'ari uku wallhi, to kinga Mai a keyi da wani aikin gomnati, Innah ta kalleshi cikin mamaki ta ce "yanzu Abdul jabaru kana ba d'an kowaba kake irin wannan lissafin wallhi kaji tsoron duni da mutan cikinta, ka rage son gud'i dayawa, yanzu abokankama da kuka taso duk ka zubar dasu saboda tsabar alfaharin ka na banza, kaje kana abota da Yayan manya, yau kaje gidan su wannan gobe gidan su wannan, anya Abdul kana tsoran wula'kancin mutane kuwa?

AJ ya ce "To innah in banda abinki yaza'ayi ina talaka kuma nayi abota da y'ay'an talakawa haba ai abumma sam baiyi dai-dai ba...kinga in Nana ta dawo kice ta shanyamin kayannan ana kirana. Kafin inna tayi magana har ya tashi daga zaunan da yake ya nufi d'akin sa ya ciro wayar sa daga caji yana mai ciro wata jallabiya ya d'ora a kan kayan da suke jikinsa kafin ya kalli in na ya ce "Inna watarana sai labari amma dai tabbas zanyi kud'i in Sha Allah. Innah ta ce "Nidai bazan dena maka addu'a ba Allah ya shiryamin kai domin ni harga Allah ina tsoron wannan shegen son kud'in naka ya jefaka a damuwa.

A J kuwa yana fita ya hangota a gefen gidan su tana tsaye tana waige-waige kamar mara gaskiya, yana hangota yaji wani sanyin dad'i domin kuwa yasan an dace. da sauri ya 'karaso gurin ta yana mai washe baki, kafin yayi magana ta kamo hannun sa suka shiga cikin wani lungu, ta ce "A J I don't get the money.

Kallon yayi da kyu ganinn irin shigar da ke jikinta daga ita sai riga mai siririnhannu sai wando jins wanda ya tsaya mata iya cinya, kana kallon shigarta kasan ba musilma ba ce, cikin jin haushi ya ce "what are you saying? "ai see idont have the money, jin haka yasa AJ juyawa zai bar gurin tayi saurin sake kamoshi ta ce please AJ listing to me? Kallon ta yayi cikin muryar Hausa domin kuwa yasan baji takeyi ba ya ce "in bandama ina son kud'i Mai zaisa na dinga tsayawa da ke kidubi irin shigarki in wani yazo hucewa ya gammu a haka ai shikenan, baride na samu abun da nakeso a gareki wallhi bazaki sake ganinaba.

Zarah ta ce "What are you saying? Ya ce "no is not you. Nann take suka fara magana cikin turanci domin kuwa ita bata jin Hausa ko zo in kashaka bata saniba. Zahrah ta ce "AJ saura kad'an Daddy ya kamani kuma nasan yanzu yasan nice nake sata masa kud'i, kuma duk kaine kake sakani. A J cikin rashin tsoro ya ce "kinga ni in bazan samu ba kawai a bar maganar kuma daga yau bani babu ke, na ce miki waya zan sake tawa tayi 'karama mutane suna rainani, yanzu a ce ina da ke amma ina ri'ke irin wannan wayar!

Ganinn ransa ya b'aci ne yasa zahrah ta ce "please I'm so sorry I well bring the money for you tomorrow, tafad'a kamar tayi kuka. Tabbas zahrah tana son A J sosai hakanne yasa bata son 'bacin ransa, yayinda shi kuma domin kud'in iyayenta ya keson ta yana amfani da itane kawai domin samun kud'i. da sauri ya ce "Yawwa ko kefa, ta ce "To kayi dariya? Ai kuwa nann yayi dariya tazo da gudu ta rungumshi tana cewa I love you so much my A J, shikuwa bai amsaba sai son ganinn ya cireta daga jikin sa ya keyi.

Zahrah kuwa tana zuwa gida ta shiga tinanin yaza'ayi ta samu gud'in nann ta kai masa gashi Daddy na gida. Haka ta tashi ta nufi d'akin Mommy cikin sand'a amma tana zuwa taga Mommy na zaune tana cin uban 'kwalliya kamar wata amarya, komawa tayi da baya ta shiga d'akin Daddy ai kuwa ta samu yana barci. Gurin da tasaba d'aukar kud'in ta nufa cikin sand'a kana ganinn ta kaga mara gaskiy. Wani 'karamin kurido ne a kasan drowan kayan sa, nann take Zarah ta fara jawoshi a hankali ai kuwa tana zarowa taga kud'ad'e masu uban yawa wanda sun ci uban wanda take gani a baya...

Ai kuwa saida ta tsorata tsabar yawan kud'in tana cikin hakane wayar daddy tafara ringtone alamar kira, ai kuwa da sauri ta tura abun kud'in ciki ta rufe ta fad'a 'kar'kashin gado wanda yayi dai-dai da shigowar Mommy d'akin sannan Kuma Daddy ma ya farka.

Bayan ya amsa wayar ne ya kalli Mommy ya ce Eliza we are you going In this time? Cikin yaransu na tibi ta ce "Sorry sar yanzu I'm coming back now...ta ci gaba da cewa wai dama kana gidane baka fitaba? Daddy ya ce "okay bari nima nashirya mufita munada mitin on this time, da sauri ya shirya Mommy na tsaye har suka fita a d'akin Daddy ya kalli Mommy ya ce "Bari na 'kulle d'akin nann domin kuwa na daina yarda da kowa a gidannan kullum sai an d'auka min kud'i kuma arasa waye ya ke d'auka. Mommy ta ce "Ni kaina ana d'aukar min kud'i Kuma na tabbayi Zahrah ta ce ita ba itaba ce shima Samuel ya ce bashi bane to kaga wazamu zarga acikin su?

Daddy ya ce "Samuel ne yake d'aukar kud'in in bashiba to ita zahrah me zatayi da kud'i masu yawa? Mommy ta ce komade waye zamu kamashi. Haka Daddy ya rufe gofar ta waje ya murza ki har sau uku kafin ya saka kin a aljihun...ya d'ago kai ya kalli Mommy ya ce "We zahrah? Mommy ta ce "taje gidan su Usha, ta bashi amsa tana mai rufe gidan gaba d'aya.

Zahrah kuwa bayan daddy ya fitane ta zaro abun kud'in sannan ta fara d'iba Saida ta kwasa da yawa domin kuwa sunfi Wanda ta saba d'iba a baya, sannan cikin sassafar tayi hanyar fita daga d'akin, tana zuwa taji 'kofar a 'kulle, ta buga amma taji ko motsi batayi, nann fa ta zubar da kud'in a gurin ta fara rusar kuka.

*KANO STETA*

*ZAINAB AMBATO*

Shahararriyar mawa'kiyar Annabi Muhammad sallalahu a w s, wacce tayi fice sosai a harka yabon Annabi Muhammad sallalahu a w s, wacce kowa yasan da zamanta a wannan 'kasar tamu domin kuwa tana lokacin ta. Kallon wani video da abokin takun sa'karta yayi nayau Wanda yake caccakar bidi'a da kuma masu yinta takeyi, kallon sa takeyi ganinn yanda ya dage yana bayani akan wa'kar da ta sake jiya, cikin tsananin b'acin rai da jin d'acin abun da yake furtawa ta ce "Yau kuma wanann mutumi harda cikin mutunci a cikin baton nasa!! Kafin tayi magana taji ya sake cewa...

"Al'umma wallhi ku guji ai kata bidi'a kuma ku guji masu ai katata, jiya naji wata daga cikin su ta saki wata sabuwar wa'ka, tana cewa...(bagudu baja dabaya kan 'kwanar shehu maulansu). Ya rera wa'kar cikin bar kwaci, ai kuwa nann take Jamar gurin suka kwashe da dariya sannan ya ce "kutsaya kuji, dan Allah wannan begen annabine kodai begen wani? Nann take suka amsa da cewa begen wanine... Kafin ya sake magana Zainab ta kashe wayar cikin tsananin b'acin rai tayi hurgi da wayar tana maijin d'acin abun da yake mata. Tashi tayi ta bar d'akin ta nufi d'akin mahai fiyar ta kamar zata kamar zata tashi sama.

Da sallama ta shiga d'akin kamar yanda ta saba, amma taji ba'a amsa mata ba, hakanne ya bata damar shiga cikin d'akin, tana shiga ta tarar da ita tana sallha sai kawai ta juya izuwa d'akin yayan ta, ai kuwa tana shiga ta tararr dashi shima yana kallon wannan video d'in, cikin sauri ta isa gareshi ta ce, "Isa kaga abun da wannan gayan ya sake min ko? Ni bansan mai na tare masa ba, ni bana shiga har karsa amma shi kullam yana bibiyata, in anyi magana ya ce shi Wai mau ilimine, cikin 'bacin rai ISA ya ce "to Ina ilimin yake a nann mutum kullum saide ya tara mutane yana cin zarafin wasu saboda basa bin gungiyar su, in anyi magana kuma suce wai su sunnha sukeyi haka sunna take?

Isa ya ci gaba da cewa "wallhi wannan yaron haushi ya ke bani, mutum Dan Allah ya baka ilimi sai kuma ka dinga kallon kowa a banza! in ilimin nanne yasan mun sha kansa domin yaje yayi bin cike a kan wannan gidannamu. Zainab ta ce "Sai su dinga fakewa da cewa mu yan bidi'a ne sukuma yan sunah, Kuma sune suke ai kata bidi'a d'in a bayan 'kasa. Isa ya ce "yanzu to yaza'ayi? Ta ce "Nima zan fara mayar masa da martanine domin in ba hakaba bazai san cewa nima niceba.

Cikin jin dad'i ISA ya ce "toma wai meye wannan yaron zai nuna miki in banda dogon gemu kamar bunsuru, Zainab ta ce "Toma wai yaushe a ka san dashi? Shifa albarkacin mahaifin sanema yasa jama'a suka san dashi amma har zaizo yana min habaici to wallhi ina dai-dai da ubansama ba shiba. Haka dai ISA da Zainab suka dinga zagin sa saboda abun da ya musu.

*ABDALHA*

Cikin tsananin b'acin rai yake kallon 'kanwar tasa cikeda jin aushin abun da tayi ya ce "Waye wannan? Itama cikin dubur-burcewa ta ce "Shine wanda nake fad'a maka zai zo gurinka tin..."tin kafin ta 'Karasa ya katseta da cewa... "Wannan d'an bidi'ar zaki kawo mana gida kice wai shine zaki aura!? Bakiji abun da nace mukuba ko Maryam ta ce "Yaya wallhi bad'an bidi'a ban... "Zakimin shiru ko saina fasa miki baki yanzunnan?

Abdullha ya kalli Maryam ya ce "Dabansan ko shid'in wayeba da saiki min 'karya, to bari kiji wannan yaron har ubansa na sani saboda haka daga yau bake bashi karna sake ganinn ku tare kinji na fad'a miki ko?. Ta gyad'a masa kai sannan ya bar d'akin cikin 'bacin rai.

Maryam kuwa cikin kuka ta nufi d'akin mahaifiyar su domin sanar da ita komai, tana zuwa ta tararr da sauran Yan uwan nata dukkansu a gaban maman nasu suna d'aukar karatu hakanne yasa ta share hawayenta itama tabi layi domin kuwa tasan babu wanda zai kulata har sai in sun kammala karatun.

Abdullha kuwa part 'dinsa ya nufa yana jin mamakin taurin kai irin na Maryam, duk cikin 'kanyansa tafi kowa taurin kai ga rawar 'kafa ba kamar Sadiya da Nusaiba ba. Cikin zuciyar sa ya ce "ni na had'a jini da yan bidi'a a'a bata isaba akan wannan maganar zan iya mugun 'bata mata rai sosai.

*ZAINAB VOP*

Da sauri ta shiga gurin Mama lokacin ta idar da sallah hakane yasa ta kwashe komai ta sanar Mata abun da abdullha ya sake mata, Mama ta kalleta ta ce "Zainab ke mace ne shikuwa na mijine kinga in kina biye masa zaku zubar da girmanku a gurin al'ummar garine dukkanku, gashi kuma dukkanin ku jagororine a gurin al'ummar ku saboda haka kibarshi karki biyewa wance yayan naki mai zigaki.....📝



_
*PAGE* 👉0️⃣2️⃣

......... Zainab ta ce "To yanzu Mama haka zan barshi ya cigaba da cin mutuncin mu al'halin kuma duk abun da yake fad'a 'karyane!? Mama ta ce "Zainab karki bari malam yaji zancennan domin kinsan Shima baya 'kaunar su, saboda haka kibar komai a gurina, kinga yanzu in kika biye masa al'ummar gari zasu samu abun fad'a dukda dama batin yanzu akasaba jin kanku dashiba, dukda ke ba beye masa kikeyiba, yanzuma kiyi haguri karkice komai kiyi abun dake gabanki... yabon Annabi Muhammad sallalahu a w s ne kuma babu Wanda ya isa ya hanaki domin kuwa da albarkar uwa da uba a kanki, kuma ga soyayyar Nana batula 'Yar manzan Allah wanda shine silar saninn ki da al'umma sukaye, kinga ko iya haka ai kinci riba sosai ko?

Cikin jin dad'i Zainab ta ce "Sallahu a'lahi wasallam, tana mai shafa wa a fuskarta, sannan ta shiga rera wata 'kasida da tayiwa Nana fad'ima Yar ma'aikin Allah Mai taken *(NANA YAR MA AIKI UWAR GIDAN ALIYU SADAUKIN DA FAYA TSORO.* )

*A J.* VOP

Yana shigowa gidan ya tarrar har nana ta gama shanya masa kayan sannan ta 'dora musu girki, Yana shiga ciki inah ta ce "Wai Abdul jabaru meya had'a ka da wasu mutane yanzu suka turo wai ana neman ka? shine na tura Nana kadija akan ta dubo, tazo tacemin Wai wani saurayi ne a cikin mota! Kafin Innah ta rufe baki Nana ta ce "Yaya wanine yazo Wai yace min in kazo nace maka sunan sa salis yazo bai gankaba ka sameshi a gida.

Da sauri AJ ya ce "Wa kikace? Nana ta sake cewa "Wai Salis. Ai da sauri AJ ya rungumeta yana cewa "Innah in Sha Allah arzi'ki ne yake kirana, ina wannan gidan da nake baki labarin cewa in na mallaki gidan nahuta, tofa yaron gidanne ranar juma'ar da ta huce muka had'u dashi to shekaran jiya ya gaiyaceni gidansu har mukaci abinci, shima baban sa ya rasu daga shi sai 'kanwar sa sai mamarsu agidan Wallhi Innah in kiga ga gidan sai kin godew Allah!.

Innah ta ce "Auda bana gode masa har sai naga gida? Ta cigaba da cewa "wallhi Abdul jabaru kari'ke maraicin ka karka dinga saka kanka a gurin da Allah bai sakakaba, i'na kai i'na abota da d'an masu kud'i har kana fad'a.

AJ ya ce "Yanzu Innha dan Allah kallemufa? yana ri'ko hannun Nana yana cewa... Yanzu dan Allah Innah munyi Kama da y'ay'an talakawa, ai wallhi ko daga gani kinsan huce nann, Koda mud'in bamu da kud'i amma ai Muna Kyu ko, saboda haka mude ki dinga mana addu'a kawai. Innah tayi salati ta sanarwa da uban giji kafin ta ce "To dan gidan ku kyu d'in da kake alfahari dashi ai duk nawane shima uban naku ai ni ya gado kukuma kuka gajeshi, Kai Allah dai ya ji 'kan Rabu'u!! Tafad'a kamar tayi kuka.

Duk suka amsa da amin. Sannan Nana ta ce "Yaya sabulun wankanafa ya 'kare ga kuma a islamiya ance a kawo kud'in wata? AJ Ya kalli Innah ya ce "To kingani yanzu da bana tare dasu a Ina Zan samu wannan kud'ad'an. Nifa wallhi Inna duk wata sana'ar da zata kawomin kud'i Zan iyayi domin Naga na inganta rayuwar Nana da kuma taki...

Sannan kuma akan kud'i zan iyayin duk wani Abu in dai ADDINIMU bai haramtaba. Kede inna kinsan bana sata bana shaye-shaye bana neman mata, duk abun da kukaga inayi to nasan menakeyi. Karatunnan fa nayi, nasan dai-dai da kuma a kasin hakan, shima wannan d'in da yake kirana aiki zan samu a gurinsa shine yasa.

Innah tayi shiru tana tinani tabbas abun da yafad'a hakane, baya sata sannan Kuma komai na rayuwa shine yake musu daga ita har Nana d'in, Yana yin duk wata sana'a in dai zata rufa masa asiri. Bata mantawa, yayi san'ar okada, yayi yaron mota, yayi jiran shago ya iya d'in ki, ga ya ta'ba zama Dreban wani mutumi Kuma duk saboda su, to amma abun tambayar ba kullum yake zuwa aikiba kuma kullum baya rabuwa da kud'i, in na tambayeshi yace sana a yayi.

Tana cikin tinani taji Yana cewa, yanzu in naje gurin sa zan samu aiki wanda daga yau mun daina cin tuwo a gidanan , ya kalli Nana ya ce "kilissafa min duk abun da kikeso in nadawo zan siyo miki, cikin murna Nana ta sake rungumshi tana ji kwanar yayan nata sosai, ta ce "Allah ya dawo da Kai lafiya Yaya. Itama Innah ta ce "dan Allah kadinga tinawa damu tik inda kashiga karkabarmu. AJ yace karki damu Innata abar alfahari na.

Yana fita ya tuno da Zahrah sai yayi dariya ya ce "In banda mahaukaciya ina ta ta'ba jin ana aure tsakanin musilmi da arne! Wai ita aure takeso muyi, baride na gama samun Yan canjina na barki da nemana. Yanzufa wannan yarinyar ta satomin kud'ad'e sunfi dubu d'ari shida, anya kuwa in baban ta ya kamata bazan shiga damuwa ba!? Sai kuma yace kodan ai tana sona bazata ce nine nake sakataba, kumafa babanta soja ne! Ta'b gaskiya rabuwa zanyi da yarinyar nann Yasin kafin ta sakani a matsala, haka ya tare me mashin zuwa gidan su Salis, yana tinanin tayaya zai rabu da ita.

*ZAHRAH* *VOP*

Take ta zubar da kud'in a gurin ta shiga dukan 'kofar amma bata ko motsi, tin tana d'aukar lamarin wasa har abun yazama gaske, wasa wasa zahrah takai a'wa uku acikin d'akin amma ba wanda ya shigo gidan, nann take tafara rusar kuka domin kuwa ta tsorata

1 / 37