Addininmu Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  S Reza Category :  Love

Chapter   31 / 37

90K to 93K   out of 109.2K words

Sunyi siyayya sosai kafin suka kamo hanyar gida.

Hira sukayi a daran sosai har Innah tana basu labarin auran iyayensu wato auran mamarsu da babansu, sunyi dariya sosai. Sunci nama sunci abinci sunsha komai dake gurin anaci ana dariya ita dai Innah komai baya mata daɗi. Inna ta kalli AJ ta ce "Abdul yanzu gaba ɗaya ka daina zuwa gidan kawunka kwata-kwata mai yasa? Ɗan
Mama-dama ma Nana tana ɗanzuwa.

Aj ya ce "Ai Innah kinsan halinsu idan mutum yaje gidan sai kowa ya dinga kawo maka wani ƙablu da ba'adinsa, amma yanzu zan je gobe insha Allah kafin mu tafi! "To Allah dai yasa, kasan shi zuminci yanada daɗi.

Nana ta ce "Aini Innah tin ranar da na karanta miki wannan littafi har kikayi kuka to tinda ga ranar na ƙara gyar mama zuminci. "Innah ta ce "Eh wannan littafin da kika karanta mini a kwanakin baya ko?, ni har yanzu baki bani labarin yanda littafin ya kasanceba. Nana ta ce "To ai haryanzu ban gama karantawa ba, ina cikin karantawa ne a ka kamamuba kuma bayan mun dawo sai banga wayarba, dama Kadija ce ta turamin itama wai yanzu bata dashi.

Innah ta ce "Kai naso jin yanda zata kasance ko idan ƙanin mahaifin nata ya gano cewar ƴar gidan ƙaninsa ce ya zaiyi? AJ ya ce "Ya sunan littafin? Da kuma sunan marubuciyar? Da sauri Nana ta ce "Sunann littafin *UWATA CE SILA.* Marubucin kuma na mijine sunansa S REZA. Dan Allah yaya ka nemomin Pls kaji? Kafin yayi magana Innah ta ce "Walhi marubucin yayi labin cikin hikima da basira, idan har ka karanta littafin to zaka riƙe zuminci da kyu. AJ ya ce "Ikon Allah! Ai kuwa zan nemeshi kodan na ƙaru. Nana ta ce "A kwai wani mai suna Allaji muɗi acikin littafin wallhi mutuminnan da zan ganshi a fili saina zabga masa mari domin mugune, harda mai sunana Nana. Innah ta ce "Ni kuma uwar yarinyar da kuma wannan shegen Uncle ɗin mai koya mata karatunne sukafi ɓata min rai walhi!, ace kina matsayin uwa amma kiyi sakaci da ƴarki akan wani banzan karatun boko. AJ ya kwashe da dariya ganin yanda inna take ta zabga masifa da fushi har hawaye sun fara taruwa a idonta. Ya ce "Innah!!! littafine fa ba gaskebane har kike kuka? Ya ƙara sa yana tashi izuwa ɗakinsa. Nana ta ce "Yaya a'a wallahi true life store ne wannan domin a farkon labarin ma an faɗa.

AJ ya ce "To zan nemo muku saida safe, amma kice Innah ta daina kuka. Ya fita ya barsu suna cigaba da labarin littafin ita da Nana. Shikuma ya fita yana mamakin jin cewar wai labarin na gaskene. Cikin dare Innah ta ke ta faman tari harsaida tasha maganin da Dr ya bata.

Da a suba AJ ya tashi yayi wanka ya shiga tunanin rayuwarsa, haka kawai yaji gabansa na faɗuwa idan ya tuno da mahaifinsa , sai kuma ya kama hawaye yana jin cewar akan Nana da Innah zai iya aikata komai, domin yanzu sune komai nasa, yana jin ba zai barsu a cikin wani hali ba mutuƙar yana raye, zai zauna dasu har gaba da abada, yana son ƙanwarsa da kakasarsa sannan ba zai taɓa yarda susan auran da yayi ba insha Allahu! Yana cikin haka a ka kira sallah , saida yabi ta dakin su Innah ya tashesu sannan ya fita Masallaci. Bai dawoba saida gari yayi haske, yana shigowa ya tarar Nana tana haɗa musu abin kari a gindin murhu. Kallon ta ya kayi cikin dariya ya ce "Daga yanzu dai kin huta da wannan banzan itacen mai sakaki hawaye ko?

"Da murmushi ta ɗago ta kalleshi ta ce "Wallhi yaya kamar kasan na gaji da shi Allah. Ya ce "Ai amma gama daga yau sai dai muma mu koma ɓangaren gass Allah yasa dai kin iya amfani dashi domin nasan Innah ba iyawa tayi ba? "Kai yaya gass ɗinne kuma kake cewa ban iya amfani da shiba?

Ya ce "Idan kin gama ki taso inna zanyi wanka kafin lokacin? Ganin har ta gama Innah bata tashi bane yasa itama ta je tayi wanka sannan ta je ɗakin AJ ta tasoshi wanda shima barcin ya ɗauke shi.

Bayan yazo gurin da suke cin abuncinne baiga Innah ba ya ce "Innah fa? "Tana barci bari na tasota. Tana faɗa tabar gurin daidai shikuma kiran ya shigo wayarsa.

"Ganin sunan Sarah ne yasa gabansa faɗuwa, har ya fara tunani sai kuma ya tuna ai yayi Welcome back.

"Salamu'alaikum" ya faɗa gabansa na cigaba da faɗuwa. "A a a Aj? Sarah ta faɗa cikin kuka. "Cikin rainin hankali ya ce "Please waye a layi?

"Sarah ce" Ta faɗa tana danne kukanta.

"Wa cece Sarah? Kuma daga ina?

"AJ nicefa Sarah zaka ce ka manta da nu n"....kafin ta ƙarasa ya ya ce "Please is ron Number . Yana faɗa ya katse wayar yana sakin dariya. Kafin ya ajiye wayar yaji muryar Nana ta kwala wani uban ihuuu! Tana kiran sunan sa.

Da gudu ya shiga ɗakin innar ya ganta a kan daddumar da tayi Sallah a kwance idanunta sun ƙafe ga carbin hannunta shima ya sake ya faɗi. Kallonta ya keyi yana kallon Nana da take ta ihuuu tana jijjiga innar. Da ƙarfi ya ce "Innah!!! Ya faɗa yana juyata sai ta sake jiki alamar ba rai a tare da ita. Lokaci ɗaya ya gane cewar Innah tayi tafiyar da ba dawowa. Nana ta ce "Yaya maiya faru? "Innah ta ra ta ta ta rasu! Ya ƙarasa yana fashewa da wani irin kuka yana dukan kasan ......📝







*Hammm* *to fa!*


*Comments ɗinku shine abun alfaharina*


*S REZA ✍️*
[10/21 22:06] Aliyu Makko: *ADDININMU*




*S REZA...✍️*

*First Class writer's asso...*


*PAGE4️⃣2️⃣*
........"No Yaya a'a Innah bata mutuba ka daina faɗa dan Allah bana son ji...Innah ki tashi dan Allah ki tashi bana son wannan wasan Innah taaaaaa!!!. Nana ta ƙarasa tana ƙara ruƙo hijabin Innar. Kuka take yi sosai AJ ma kuka yake yi yana riƙe da Nana wacce har yanzu kiran sunan Innah take yi. Cikin kuka shima ya fara cewa "Wallahi Innah na daina aikata komai kuma zan sanar miki da gaskiya bana son kuɗin da gidan dan Allah ki tashi. Tabbas dukkan wani mairai mamaci ne, haƙiƙa duk wata rai zata ɗan-ɗani zafin mutuwa, ka na taka Allah na nasa kuma na Allah shine daidai, haƙiƙa rayuwa babu tabbas duk yanda ka kai da lafiya ko ƙarfi ko arziƙi ko mulki ko... ko... ko... ko... ko...koma mai nene to tabbas sai ka tafi, da lafiya ko babu, kana zaune cikin iyalanka ko kana kan hanyar tafiya, kana aikata alfasha ko kana aikata abun kirki, ita dai mutuwa bata jira.(Allah kasa mucika da kalmar La'i'la'ha'illala Muhammadur Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallama.)

Haka suna kallo a ka sallaci Innah a ka ɗauke ta izuwa gidanta na gaskiya. Ba shakka Innah tayi jama'a, ƙofar gidannasu cike yake dam da bayin Allah, cikin gida kuwa matan Anguwa da sauran da suka samu labarin mutuwar duk sune aciki. Nana kuwa har lokacin kuka take yi, babu irin rarrashin da Kadija batayiba amma sai kiran sunan Innah takeyi tana kuka. AJ ma kana kallonsa saika tausaya masa, domin ya dawo kamar wani kurma sai kallo da ido. Matar kawunsu da yaranta da ya gujesu a baya yanzu sune a zaune a gidan , kawun nasa ma shine mai riƙe hannunsa izuwa mƙabarta.

Saida kowa ya watse a ka barshi shi kaɗai a maƙabartar sannan ya fara addu'o'i yana yi yana zubar da hawaye yana faɗar laifukan da ya aikata Mata. Ya kai a'wa guda a gurin kafin ya miƙe zai tafi sai sukayi ido biyu da Salis a tsaye a gurin yana kallonsa shima idonsa ya ciko da ruwan hawaye. Kallo ɗaya AJ ya masa ya kawar da kansa ya kama hanyar tafiya yana jin zuciyarsa na masa zafi. Shima Salis bai ce masa komaiba yabi bayansa. Suna isowa suka tarar har wasu sun fara tafiya, Kawu ne yake karɓar gaisuwa. Gurin da kawon yake suka zauna har yanzu babu wanda ya tam kawa juna. AJ ya sunkuyar da kansa ƙasa yana kuka yana tuno maganganun da sukayi da Innah a daran jiya, a she wasiya take musu. Shi sai yanzu yake jin dama bai samu wannan kuɗin ba sun zauna a talaucinsu, inama lokacin da suke faɗa da Salis da tamai magana yaji, da ba'a kaita asbiti ba da yanzu haka suna cikin sabon gidansu! Inama inama inama.

Haka har akayi kwana bakwai AJ bai ce da kowa komaiba harda kawunsu da Salis da Muhammad wanda kullum sai sunzo gurin, abincin da a ke ci a zaman makoki ma duk Salis ne ya ɗauki nauyi, shi dai AJ baisan waye mai bada abincin ba. Kawu da matarsa da yaransa biyu duk Mata suma sun dawo gidan kafin komai ya kammala. Kasancewar ba komai a gidan ne yasa kawun yasa matarsa ta ɗebo wasu kayan nasu irin tukunya da dai duk abin buƙata, haka a kaci gaba da zaman makokin Innah har a Kayi ba kwai. Daga nan ne a ka fara watsewa kowa na komawa mahallinsa.

*BAYAN KWANA GOMA SHA BIYU DA RASUWAR INNAH*

What!!! Ban gane ba? Mai kake nufi da haka? Cewar Kawu yana kallon AJ cikin tashin hankali da ruɗani. Itama Nana kallonsa tayi tana girgiza kai batare da ta iya magana ba. AJ yace "Eh Kawu da gaske nake na yi aure kuma auran ma na jari ko nace auran kuɗi, auran da Addinimu bai yarda da irinsaba, auran da yanzu haka shine ya sani a cikin da na sani auran ta kaici auran kwaɗayi auran nadama. Ya ƙara sa yana sakin kukan da ki ta damun zuciyarsa.

"Wai Abdul duk mutuwar Innar ce tasa ka koma mahaukaci ko dai yaya? Kazo kanata wasu zantukan da ba kan gado. "Lafiya ta lau Kawu, inada hankalina nasan mai nakeyi. "Cikin dashesshiyar muryarta ta ce "Yaya mai kake cewa ne? Ban fahimtaba Please?

Kuka ya keyi sosai ya fara magana yace ""Nayi aure nayi aure saboda kuɗi saboda Innah da Nana su ji daɗin rayuwa, wallahi badan kaina nayiba amma yanzu na gwammaci da banyi wannan auranba, sannan na rasa wazan aura sai sa'ar mahaifiyata, uwar abokina wanda shine ya sa na fara ganinn kaina a haka, yamin rana nikuma na masa dare daran ma mai mugun duhu. Nan take ya kwashe komai ya sanar musu bai ɓoye komai ba. Cikin sabon tashin hankali Nana ta ce "Whay wahy whay Yaya? Mahaifiyar Salis mai yasa kayi haka! Ka gama da rayuwarmu Yaya. Kawun ne ya kalli yanda suke kuka duk sun fita a cikin haiyacinsu ya ce "Yanzu ba kuka zakuyiba, ai kace kun rabu ko? AJ ya girgiza kai. Ya ce "To yanzu ku tashi muje gidan nasu domin sanin abunyi, dole ne sai mijinta yasan da wannan zancen saboda kar a je a aikata haramci.

Da sauri AJ ya ce "No bazan iya magana dashiba kunyar Salis nake ji na , ga babansa ga Sarah no bazan iya ba wallahi bazan iyaba. Saida sukayi da gaske kafin AJ ya bisu.

Ta kardun gidan da Hajiya Babba ta bashi da makullin motar ya haɗo ya tafi dasu. Saida sukazo bank ya tsayar da motarsa ya ce su jirashi. Duk kuɗin dake cikin account ɗinsa ya kwashe ganin kuɗaɗan sunyi yawane yasa ma'aikatan bank kin sukace saidai yazo da jaka, ya ce bashi da jaka. Dole a tasu suka zuba masa ya fito dasu yasa a matar suka kama hanya.

A gidan Malam Muhammad kuwa washe garin abunda ya faru dasu ne Salis da Muhammad sun shirya domin zuwa gidan su AJ a sanar da innarsa komai sai kuma suka riski rasuwar Innahr. Hakanne yasa suka fasa yin wannan maganar suka bari har sai yaran sun dawo haiyacin su. Shi kansa Salis da ya tsaya ya kalli lamarin sai ya godewa Allah da yasa aure sukayi ba abun kunya ba. Lokacin da suka dawo gida suka sanar wa da Hajiya Babba itama ta tausaya masa domin tasan yanda yakeson kakkar tasa da ƙan warsa. Sarah ko kuka takeyi wai a dole sai an kaita gurin AJ. Dama kuma ita da Samuel sunzo da batun suna son komawa Addininsu Muhammad. A ranar Muhammad da Salis harda Hajiya Babba sunyi godiya ga Allah, sannan sunce gurin shek Kabir kabuga zasu tafi dasu domin ƙarɓar Musuluncin. Dama ga batun auran yaran sa, sai kawai a yi komai a garin, yayi kewar malamin dama kuma yanaso yaje gurinsa, domin ba zai iya mantawa da shiba.

Muhammad da Hajiya Babba sun bari a kan sai sun dawo daga gurin Shek Kabir kafin su tun kari batun AJ. Yanzu dai ana gobe zasu tafi kenan.

Salis ne zaune a polo shida Samuel yana ɗan masa bayani game da Addini kafin ya karɓi kalmar sha'hada. "Da farko dai zaka ajiye shan kiya da neman mata, sannan girmama iyaye koda ba musulmai bane...Zaka daina zuwa coci, salloli guda biyar a kowacce rana.... A kwai A'zumi da a keyi a cikin watan Ramadan wanda yanzu haka ya kusa kamawa...sannan ya zama dole ka daina"...."Bai ƙara saba sukaji sallama daga bakin palon gidan. "Yes Samuel ya ce sai suka zubawa ƙofar shigowar ido. Kawu da AJ ne sai kuma Nana da ta ce lallai sai tazo.

Mi ƙewa sukayi tsaye suna kallon juna tsakanin AJ da Salis harda Samuel. Kawune ya fara maga "Ko Mahaifinka yana ciki? Salis ya kai kallonsa izuwa ga Kawu ya ce "Eh yana ciki" Nana da take bayan AJ har yanzu bai gantaba sai zuciyarsa da ta ke ta harbawa a lamar dai da mosoyi...?

Kawu da Muhammad Hajiya Babba Salis AJ laɗifa Samuel Sarah ne duk acikin palon a zaune kowa ya nutsu yana jiran abun cewa. SAMUEL dai sai yanzu ya ƙara gane waye AJ ɗin. Laɗifa kam idonta kar a kan AJ da Nana, tana jin tamkar ta tashi ta harbe su kowa ma ya huta.

Muhammad ya fara magana bayan sun gama sauraron abunda kawun ya ce kamar haka..."To muna mai sake miƙa godiya ga Allah da ya sa komai yazo cikin ruwan san yi da fahimtar juna...sannan muna ƙara miƙa ta'aziyar marigayi ya Innah, Allah yasa ta huta, mukuma idan tamu tazo yasa mucika da imani. Duk palon suka amsa da amin. To sai kuma abu na gaba... Kowa ya ɗaga kai yana kallon Muhammad. Ya ce "Aisha tana ɗauke da cikin sa a jikinta har tsawon sati huɗu yanzu haka.

Zumbur AJ ya miƙe yana kallon Hajiya Babba wacce ta kifa kanta a kan cinyoyinta. Da sauri itama Nana ta wrufe bakinta tana ƙoƙarin fashewa da kuka. Salis kam wata iriyar kunyace ta rufeshi. Laɗifa kam tsaki taja ta miƙe ta nuna AJ dake tsaye ta ce "Wallahi saina ga bayanka kuma saika tozarta kamar yanda ka tozartamu, ba dai kai mayen kuɗi ba, to wallahi Allah saiya saka mana , mugu maci amana wawa mara tinani dabba jahili ɗan a kuy"..."Kyeeeee!!! Laɗifa ya isa ya isa! Cewar Salis yana miƙewa tsaye. Da sauri Laɗifa ta bar gurin tana kuka. AJ ya ce "Ta faɗi gaskiya cewar banida tunani bani da hankali jajili maci amana tabbas duk wannan suffofinane, naci amanar Salis, bai cancanci haka daga gareniba. Yana faɗa yana kuka. Sannan ya ɗauko takardar gidan da a ka bashi ya ajiye a gaban Salis , ya ɗauko jakar kuɗin ya haɗa da makullin motar ya ajiye ya ce....

"Ga kayanku nan, basu da amfani a gareni, dama saboda Innah ta nayi gashi ta tafi batare da tamoresu ba. Tabbas Allah yasan irin halin da zata shiga idan har taji labarin na yi aure harda ciki ba tare da ta saniba, Allha ne kaɗai yasan halin da zata shiga. Tabbas Innah kin huta da ta kaicina. Sai kuma ya dawo gurin Nana itama ya fara cewa "Ki yafemin ƙanwata na lalata komai na zubar da mutuncin kanmu a kan kuɗi. Haka dai AJ ya dinga sambatu har saida ya ba kowa tausayi. Kawu ya rasa mai zaice tsabar ruɗewa.

Muhammad ya ce "Karka ɗorawa kanka laifi kai ɗaya, ni dai a ganina ai wannan ma abun farincikine , sannan wannan kuɗaɗan sun zama naka harda gidan da motar, wannan hakkin kane har a gurin uban Giji. Nan fa a kayi a kayi da AJ ya ce sam bazai ɗaukaba, Salis ya bashi baki ya ce shifa wallhi saide ya ƙare a talauci, haka ya tashi ya bar gidan cikin kuka, yana cewa "Na karɓi cikina kuma zanyi komai da uba yakeyiwa yaronsa ban yarda a tayani da komaiba, zan nemi nawa na kaina insha Allah! Yana faɗa ya fita batare da yajira komai ba. Nana ta tashi zata bishi Kawu ya tareta.

Salis ne ya kaisu gida yana rarrashin Nana. Koda sukaje gidan AJ bayanan ga gidan nasu ba kwamai domin sun kwashe komai sun kai sabon gidan. Salis bai shiga gidan ba dan haka baisan da cewar ba komai a gidan ba. A mota suka tsaya bayan kawu ya fita ya kalleta ya ce "Nana ina sonki karkiyi tunanin wannan abun zaisa na gujeki, ina tare dake har ƙarshin numfashina, sannan ga wannan ki ajiye a gurinki ko zaki buƙaci wani abun? Ya faɗa yana miƙa mata kuɗin da ya ciro. Yana jin kukan da takeyi kaman ya rungumota jikinsa ya rarrasheta, amma ba dana. Ba ta ce komaiba ta buɗe motar ta bar shi yana binta da kallon mamaki har ta shiga gida. Haka ya zauna a cikin motar yana tunanin abunyi.







*Comments ɗinku shine abun da*


*S REZA*
[10/21 22:06] Aliyu Makko: *S REZA...✍️*


*ADM*



*First Class writer's asso...*


*PAGE4️⃣3️⃣*
........Haka Salis ya bar ƙofar gidan cike da damu wa a ransa, baya son ya taƙura Mata, zai bata dan lokaci kafin komai yayi daidai. Haka rayuwa taci gaba da tafiya ta ko wani ɓangarori. AJ ya koma aikin sa na tuƙa motar bredi wanda suɗinma da

31 / 37