tare da waso mutane da suma suka musulunta. Domin tin bayan zuwansu garin KATUNGU. Muhammad ya raba musu jari mai ƙarfi wanda yasa suma suke kyautatawa wasu daga cikin ƴan garin har suka fara musulunta. Yanzu haka kowa yayi aure a cikinsu, haka suka tattaro suda iyalansu. Ranar suna yarinya taci sunan Hajara Innah amma zasu dinga kiranta da *ILHAM.* Wasu da yawa da suka halarci sunan basu san cewar ba Muhammad bane uban yarinyarba domin kuwa yanda yakeyi zaka rantse da Allah ɗansa ne na cikinsa, Salis da su Abdalh kowa ka gani farinciki yakeyi, sai yau Abdalha ya taɓa zuwa Benue Makurdi, yayi mamakin ganin musulmai da yawa a garin, don zai iya cewa ma musulmai sunfi yawa a garin, ba kamar yanda yaji a ke cewa garin arnane ba, tabbas yayi mamakin ganin yanda Musuluncin yayi ƙarfi a gari. Bai ƙara mamaki a saida yaga ko ina ya shiga ana kiran sunansa a na girmamashi, tabbas yayi mamaki sosai, manya da yara sai kiran Abdalh Kabir kabuga a keyi. Haka ɓangaren Zainab itama zuwa ta na farko krenan, bata taɓa zaton tanada masoya a garin ba sai yau, Zainab Ambato Zainab Ambato duk inda ta shiga, ganinsu tare da Abdul yasa yan garin yandar da zancen da sukaji a na cewa wai soyayya ce tsakanin Abdalha da Zainab.
Lokacin da kowa ke cikin farinciki lokacin ne kuma mutum biyu suke cikin tsananin damuwa da wannan rana. Wato AJ da Laɗifa. Ita laɗifa baƙin cikin abunda akeyine ya dameta wai AJ ne ya auri uwar ta har suka aihu kuma a ke taron suna harda murna. AJ kuwa damuwar rashin kuɗin abunyanka, dukda har yanzu babu wanda ya tambayeshi amma yayi alwashin saiyayiwa ƴarsa abun yanka kuma yanzu haka ko sisi babu a aljuhunsa.....📝
**ADDININMU*
*S REZA...✍️*
*First Class writer's asso...*
*PAGE4️⃣6️⃣*
........ Zama ya yi a gurin yana faman nazari a kan komai dake faruwa a cikin rayuwarsu shida ƙanwar tasa, haƙiƙa suɗin marayune gaba da baya basu da kowa a cikin wannan duniyar, daga shi sai ƙanwarsa sai kuma wannan yarinyar da a ka haifa masa, tabbas sau a irin wannan ranar ya ƙara jin cewar Innah bango ce makingina a cikin rayuwarsu yasan da tana raye zata yi fishi da shi amma daga baya komai zai huce, da yanzu kan cenyarta zai kwantar da kansa ya sanar mata da damuwarsa. Yana zaune a gurin Nana ta fito daga wanka cikin mamaki take kallon ta ƙaraso kusa dashi ta ce "Yaya har kadawo? Yanzu nake shirin tafiya ni da Kadija fa. Ɗago kansa yayi ya kalleta sai kukan nasa ya ƙaru yana tausayin Nana sosai domin duk shine ya jefasu a cikin wannan halin. "Haba yaya yau ai ranar farinciki ce a garemu amma kana zubar da hawayenka for noting Please yaya ka ka ka daiiii na! Itama ta ƙara sa tana kuka domin ta gano dalilin kukan nasa.
Rungumota jikinsa yayi suna sakin kuka a tare. Sai da suka yi mai isarsi kafin AJ ya sanar mata da matsalar sa. Ta ce "Yanzu yaya kaman nawane zai siya maka Ragon? Ya ɗan yi murmushin ƙarfin hali ya ce "Ai ni Nana ko na dubu sha biyar na samu na saiya ai na fita kunya. Nana tayi shiri tana tunani sai ta ce "Yaya bari na shirya Allah zai kawo mana mafita da yardar sa. Aj ya ce "To Amin ya
Rabbil Alamin.
Yarinya fa taga gata domin kuwa iyayen nata da yawa ga yayu suma ba'a barsu a baya ba. Dangin Hajiya Babba da basu san uban yarinyarba sai tambayar dangin mijin sukayi, ai kuwa matar Kawu ta ce gamu nan, matar Kawu da yaranta biyu sai mamar Kadija da wasu ƴan uwan Matar kawun sune a matsayin dangin AJ. Hajiya Babba ce da kanta ta hana kowa ya sanar dasu waye uban yarinyar. Ai kuwa Laɗifa ta fasa kwai kowa yasan waye mijin Hajiya Babba ɗin.
"Wani ɗan yarone wanda koni na girmeshi sannan ɗan matsiyata ne hasali ma yaron gidan Salis ne, daga zarar Salis yazo dashi gidannan shikenan Hajiya ta ɗauke shi suka bar ƙasarnan sukayi aure, yanzu haka yaron ko Naira baya magani, idan kuka ganshi wlhi sai kunyi tir da wannan abun. Laɗifa ta faɗa tana kuka, yayinda Hajiya Babba ta sun kuyar da kai ƙasa tana jin kunyar maganganun da Laɗifa tayi. Take ɗakin ya kaure da salati, kowa na mamaki. Wata daga ciki ta yi ƙarfin halin yin magana, domin kuwa gaba ɗaya danginsu suna mutuƙar girmamata dalilin arziƙin ta. "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Yanzu wannan wani irin abun kunyane? Shine tsabar rashin ta ido harda gaiyato dangi, mukuma muka ɗauko ƙafa mukazo wannan wani irin abun kunyane, auran abokin ɗanki harda ciki!!! An shiga uku wai namiji da cikin haihuwa. Nan fa suka mata tatatass wanda har suka gama bata ce komai.
A na cikin wannan biki bidurin ne kuma saiga AJ ya shigo gidan riƙe da ɗan ƙaramin ragonsa, ƙafarsa ko taƙalmi babu, dagashi sai wata baƙar riga waice ta kawo masa har idon sau, rigar dai kamar jallabiya, sai fuskarsa da ko gyaran fuska babu, gashi yayi tumu-tumu da lilin kokuwar da sukeyi da ragon. A wannan lokacin gaba ɗaya labarin ya karaɗe cikin domin kuwa kowa yayi tunan daga dawowar Muhammad ne ta samu juna biyu. Duda cewar wasu sun fara tafiya amma dai gidan cike yake da matan manyan mutane da dangin Hajiya Babba ɗin harda su Mama da Momy.
Da farko Laɗufa bata ganeshiba domin kallo ɗaya zaka masa ka gane cewar yana cikin tsananin rashi.
*ADM*
*S REZA...✍️*
*First Class writer's asso...*
*PAGE4️⃣7️⃣*
........Kuka ya kuffce mata batare da ta iya furta komai ba ta bar polon zuciyarta na mata zafi da abunda Ibrahim ya ce. Bayan tabar gurin ne Muhammd ya dawo da kallon sa gurin AJ ya ce "To kaji abunda Kawu ya ce ko kanada wacce kake so? Kafin AJ ya ce wani abu har Kawu ya magantu "Ai a kwai ƙanwarsa ƴar wajena ita nakeso na haɗasu kodan zumunci yayi ƙarfi. Muhammad da su Shek suka ce "Masha Allah ai abu yayi daɗi haka a keso! Allah ya sanya albarka ya sa a yi muna raye. A ranar mutanan Kano suka tattara suka tafi, shi kuma Aj a ks mayar masa da dukkan wasu kadarorinsa ko sisi ba'a taɓa ba, saima ƙari da Muhammd ya masa a kan nada. A cikin kwana uku AJ ya koma sabon gidansa bayan yasa an masa sauƙar alqur'ani mai girma. Bayan tarewar sa ne Kawu ya tura babbar ƴarsa gidan su AJ ɗin wai su zauna tare su ƙara fahimtar juna kafin lokacin bikin. Yarinyar mai suna Safarau itama tanada wanda takeso amma tana ganin irin gidan da AJ ɗin ya mallaka sai ta share wancen saurayin nata ta fara neman hanyar da zata samu fada a gurin AJ. Tare suke kwana da Nana kuma Nana ta sakar mata fuska sosai, ko dama suna ɗan shiri da ita amma ba sosai ba, ba kamar ƙanwae Safara'un ba da basa shiri da Nana kwata-kwata. Ɓangaren Kadija kuwa itama kullum tana ziryar zuwa gidan domin neman fada, hakanne yasa Nana ta rasa ya zatayi da Aj ɗin wanda shi ko a jikinsa kuma yasan da cewar duk domin shi sukeyi, lokacin da Safarau ta gane cewar Kadija ma tana zuwa gidanne domin AJ sai ta sake taku, itama kuma kadijar sai ta sake nata takun.
Ɓangaren Laɗifa kuwa har ɗakin Ibrahim ta shiga lokacin yana kwance yana waya da Hadiza, wayarma shine ya saya mata, sannan yanzu ta rage wannan rawar kan nata, ta nutsu sosai soyayar Ibrahim ta gama ɗaureta ta ko ta ina, har mamakin wasu abubuwan idan tayi takeyi,, idan tana waya dashi har wani lumshe ido takeyi kamar yana kusa da ita. "Cek ta tsaya tana kallonsa ganin yanda yake murmushi yana juyi a kan gado alamar dai hira tayi daɗi. "Ibrahim! Ta kira sunansa cikin wata muryar da bata san tanada itaba. Ibrahim najinta ya ce "My lovelly i'm Coming now. Yana faɗa ya kashe wayar ya kalli Laɗifa cikin sakin fuska ya ce "My Sister zo ki zauna mana kin tsaya a tsaye?
"Shin dama da gaske kake nufin kanada wacce kakeso? Dama ba sona kakeyiba yauda ta kayi kenan? Ibarahim ya ce "Please zo ki zauna muyi magana dan Allha. Yayi maganar yana binta da kallon tausayi. Ba dan tasoba ta zauna kusa dashi tana jiran taji yace duk wasa yakeyi itace zaɓinsa. ya ce "Laɗifa bazan ɓoye mikiba tunda nake dake ban taɓa sonkiba, da farko dai nayi sha'awar ki har na ƙudirta a raina saina sameki kota yaya, amma da naji cewar keɗin yar uwata ce ta jini sai naji hakan ba zai taɓa faruwa tsakanin nina da keba, hakanne yasa na yaƙi zuciyata har na samu nacire abun da nakeji a kanki, yanzu ina miki kallon Fatima ne, inasonki so irin wanda yaya yakewa ƙanwarsa wallhi Laɗifa bansa haka so yakeba saida na haɗu da Hadiza, kallo ɗaya na mata yarinyar ta tafi da imanina ina sonta sosai Please dan Allah ki fahimceni ba yaudarar ki nayi ba.
Ladifa ta kalleshi da kyu cikin kukanda ta ke yi ta ce "Dan Allah karka min haka wallhi ban taɓa son wani ɗan namijii a duniya ba in banda kai! Shin kasan tun yaushe nake sonka? Tana kuka ta na ce wa "Tun lokacin da na ganka a club kuna wannan wasan game ɗin kiss tun alokacin na fara sonka kuma har yanzu yi nakeyi amma yanzu lokaci ɗaya kace wata ka keso! Yanzo kodan dangantakar da ke tsakanin mu bazaka iya daurewa ka aurenuba haba Ibrahim!
Ibrahim ya matso kusa da ita kamar zai shiga jikinta ya ce "Laɗifa bakisan so ba, haƙiƙa da farko naso na cuci kaina da cewar inason ki, kuma duk sha'awa ce sai yanzu da na haɗu da wacce nake so sannan na banbance so da sha'awa, shi so ba'a masa alfarma ko tilastawa shi ɗin gaban kansa yakeyi a kan abun da yake so, baya shawara da kowa yake shiga zuciya, saboda haka ki daure ki fahimci me cece s"...."Cikin fitar haiyaci da rufewar ido ta ƙatse shi da cewa "Ya isa haka!² bana son jin komai naji kaje ka aureta ba sai kana faɗa min irin abunda kake jima, dama ai haka ɗan Adam yake barinma wanda tun farko zuciyarsa ta fara tashi a cikin duhun jahilcin kafirci, ai dama idan bakayi hakan ba ai baka cika jinin wannan ƙaton arnan ba wanda bai son komai ba sai cuta da zalunci, to ai kai abumma biyu ya haɗa maka uwar da uban duk haka su"...Bata ƙarasa ba taji sauƙar wasu lafiyanyun mari a kuncinta wanda yasa ta saki wani ihuuu mai ƙarfin gaske. Hajiya Babba ce da Muhammd suka shigo ɗakin domin jin laɗifa tana faɗin irin wannan magan-ganun.
A wannan ranar Laɗifa tayi na damar wannan furcin nata domin kuwa ba ƙaramin duka tasha a hannun Hajiya Babba ba, dama kuma itama tanada cikinta so take wata tara ya cika kafin ta haifeta, ai kuwa sai gashi yau wata taran ya cika. Shi kansa Muhammd maganar ta taɓa masa zuciya domin kuwa wannan maganar har dashi takeyi ba iya Ibrahim bane, ganin dukan yayi yawa yasa ya hana Hajiya Babba. Hajiya Babba ta ba Ibrahim hakuri a kan karya bi takan zancenta. Ibrahim kuwa a lokacin tunanin iyayensa ya zomasa ko yanzu a wani hali suke ohoo! Ai kuwa dole ya nemo su ko ma a wani hali suke, iyaye ba abun wasa bane, sannan yayi mamakin jin wannan furcin daga bakin Laɗifa, ita batasan cewar abunda yayi daddynta shine yayi naduba, sai kuma ya mata uzuri domin yasan ba'a cikin haiyacinta takeba.
Muhammad ya tambayeshi abun da ya haɗasu. Bayan Muhammd yajine ya ce ya sanar masa gidan su yarinyar da yakeso gobe zaiyi magana da Titi za'a je nemomasa auranta shida Salis. Ibrahim yayi murna sosai, sannan Daddy ya ce "kar Salis da Fatima suji abunda ya faru tsakanin ka da laɗifa, itama zan mata faɗa bazata ƙaraba, kuma kar abun ya dameka a cikin fushi ya take. Shi kam Ibrahim zuciyarsa cike da murnar za'a je zancen auransa ya ce babu wanda zaiji ni harna manta ma.
*AJ POV*
Da sallama ya shigo palon yana raba idanunsa ko zai ganta amma sai yaci karo da Ibrahim zai fita. Gaisawa sukayi yana tambayar ss Sarah. Ibrahim yayi murmushi ya ce "AJ yanzu ta bar Sarah ta koma Fatima, Allah ya nufa mun gane hanyar gaskiya dagani har ita saboda haka ka ajiye sunan Sarah ka koma ce mata Fatima. AJ ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Alhamdulillh Masha Allah! Ina tayaku murnar komawa Addininmu Addinin gaskiya da gaskiya addinin Allah maɗaukakin sarki!. Ibrahim ya ce "Muna godiya sosai. "To kai ya sunan ka? Ya ce "Ibrahim Khalil. AJ yace "Masha Allah sunan kakan fiyeyyan halittu kenan Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama! Dukkansu suka shafa harda Muhammad dake bayansu yana jinsu.
"Fatima nakeson gani na kirata bata amsaba shine yasa nazo gidan ko lafiy"..."kafin ya rufe baki sai gata ta fito daga ɗakin riƙe da waya a hannu. A zuciyarsa ya ce "Kenan duk kiran da nake mata tana gani ɗaukane bazatayi ba! Kafin kowa yayi magana Muhammd ya ce "Fatima je ki karɓo masa Hajara ya ganta ko? Ya faɗa ne domin yasan abinda ya kawo AJ ɗin kenan wato ganin Hajara da kuma Fatima. Domin kuwa tun ranar da a ka tambayeta wanda takeso ta ji kunya shine Muhammd ya tambayi Ibrahim ko tanada wanda takeso . Shikuma ya kwashe komai ya sanar da Muhammd tsakanina AJ da fatima. Muhammad yayi mamaki sosai jin cewar a she dalilin zuwan AJ gurin su kenan a gidan Comanda Daniyel. "Ok Daddy. Fatima ta amsa tana shiga gurin Hajiya Babba domin ɗauko Hajara. Saida AJ ya sunkuya har ƙasa ya gaisa da Daddy yana mai jin kunyarsa a dun lokacin da suka haɗu. Yana mamakin irin halin sa domin kuwa shiɗin na dabanne
Zaune ta sameshi ya ɗora hannayensa a kansa kamar dai kanne ke masa ciwo. Da sallama ta iso cikin palon har gurin da ya ke ta miƙe masa yarinyar tana jiran ya karɓeta ta bar gurin. Ganin bashi da niyar karɓa ne yasa ta ɗaga kai ta kalleshi sai idanunsu ya harɗe a na juna, ai da sauri ta kawar da kanta tana tsaye a gabansa. "Fatima" Ya kira sunanta da muryar da tasa tsikar jikin tashi, taji yanayin sunan kamar shi kaɗai ya iya kira. "Mai yasa bakya amsa kirana ko kin daina sonane? Ko kinaso zuciyata ta buga ne? Shiru tayi tana jin anya zata iya abunda tayi niya kuwa a kan AJ! Son da take masa a jinin jikinta yake, da shi kaɗai ta saba kuma ita son gaskiya take masa. "Kujerar dake kusa dasu ta ajiye Hajara zata fita sai ji tayi ya kamo hannunta ta baya.
Chak ta tsaya ta juyo tana masa wani irin kallo, hakan yasa ya saketa batare da ya shiryaba. "Karka kuskura hannunka ya ƙara taɓani a karo na biyu, tana faɗa tabar palon da sauri tana tare kukan da ya zo mata. AJ ya tsaya a gurin yana dukan kansa yana tunanin kodai ramawa takeson yi! Haka ya ɗauki Hajara yana kallonta cikin so da soyayya har ya gama wasa da ita ya kira mai akin gidan ta karɓeta. Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un ya dinga furtawa har ya bargidan.
Haka kullum AJ zai kirata amma bazata ɗaga ba, zai tura mata message zata karanta amma no amsa. Kullum kuma zaizo gidan domin ganinta amma abun ya fi ƙarfin sa, a gida kuwa kullum Safarau da Kadija sai sunyi rikici a kansa, Nana har ta fara gajiya da abun da sukeyi, hakanne yasa taje gidan kawu ta sanar masa shi kuma ya kira AJ yace "Idan yanada wacce yakeso ya fitar yayi aure idan kuma babu to ya shirya da ƴar uwarsa Safarau. AJ yace yanada wacce yakeso, Kawu ya ce "To gobe za'a zo maganar auran Nana sai kaima ka fitar a saka ranar gaba ɗaya. Hakane yasa AJ saida ya sa Salis a cikin lamarin domin baisan ya zaiyi Fatima ta dawo garesa. Salis ya bashi shawara wacce tasa ya yarda da ita ɗari bisa ɗari, kuma yaje yayi amfani da shawar kuma tayi masa aiki yanda yakeso. A washe gari Muhammad da Shek Kabir wanda yazo domin zuwa neman auran Salis ɗin da kuma a bokinsa Malam suka tafi gidan kawu. A ranar a kasa ranar auran Salis da Nana wata shida sai Abduljabaru da Fatima zara suna wata shida. Daga nan a ka wuce gidan su Hadiza, farko ma haifin Hadiza yaso yaƙi yarda jin cewar ɗan gidan Comanda Daniyel ne, domin bazai manta irin cin mutuncin da yakewa ɗansa ba, amma ganin shek Kabir awajan yasa ya amshi abun hannun bibbiyu. Suma dai wata shida a ka saka. A washe gari ne kuma Titi tazo da bayanin halinda su Comanda Daniyel da Eliza suke ci. Dama Muhammad ya naimi indan a ka kai shari'ar tasu amma an rufe duk wata hanya da zaka iya gane komai game da labarin, hakanne yasa ya haƙura domin dai yasan dole yayan nasa ya karɓi hukunci domin yaci amanar aikinsa, shi kuwa yafi duk wani guri domin ya sanar dasu cewar ya yafe masa amma ba ƙofa, sai kawai yaci gaba da masa addu'a. Bayan ta gama basu labarin komai ne sai kowa dake cikin palon ya fara kuka domin tausaya masu. Zara kuwa harda ihuu tana cewa ita sai taga Momy. Muhammad ya ce Yanzu suna inaa? Ta ce "Suna gidana nace suzo muje gidanka wai a'a bazasu iyaba yaransuma da kuma riƙe sun gode! HAJIYA BABBA ita kanta da take mugun jin haushi su saida ta zubar