Addininmu Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  S Reza Category :  Love

Chapter   4 / 37

9K to 12K   out of 109.2K words

muryar tausayi ya ce "Haba hajiya aurefa kikace? Yanzu Dan Allah ina zan iya wani zaman aure yanzu!!? Jin haka yasa Lad'ifa fashewa da dariya ta ce "Haba bro sai kace wani mace wai yaushe zaka iya zaman aure. Hajiya ta ce "to in bazakiyi to wallhi aurena sainayi, da sauri Lad'ifa ta ce "No hajiya Babba mun yarda zamuyi! Da sauri salis ya kalleta ya doka mata harara sannan ya ce "Hajiya Wallhi nifa ban shir... " Kafin ya karasa hajiya Babba ta tuna da wani abu sai ta ce...

"Naji kuje zanyi tinani. Sun tashi zasu tafi hajiya ta dawo dasu had'i da cewa ina wannan yaron da kukazo gidannan dashi har ka ce abokinane? Cikin sauri Salis ya ce...

"Ok AJ?

Hajiya Babba ta ce " Eh shi. Kafin Salis ya ce wani abu ta ci gaba da cewa... "Ina son ka kiramin shi zan bashi aiki, domin naji Kuna maganar cewar shi yanzu aiki ya keso ko?

Cikin jin dad'i Salis ya ce "Good hajiya wallhi dama ina so namiki maganar yaron, amma wannan wawan bazawarin naki... Da sauri ya ri'ke baki yana cewa I'm sorry na mantane. Ya ci gaba da cewa wallhi hajiya yaron yana burgeni, gashi ba dan kowaba sai tsafta, in kika ganshi yasin zakiyi tinanin dan mai kud'i ne, amma y'ay'an talakawa ne sosai, saboda haka Hajiya muna godiya sosai, yanzuma gidan su zanje na kirashi.

Ita dai Lad'ifa tinda ta ga A.J har zuciyar ta gayan bai wani burgetaba dan ita tana jin har yabar gidan bama zata iya masa maganaba, haka dai Hajiya ta tashi ta nufi d'akin ta tana zancen zuci. haka Salis ya nufi gidan su AJ.

( *IN BAKU MANTABA A BAYA SALIS YA JE HAR GIDAN SU A.J YA KIRASHI, SHINE YAZO GURIN HAJIYA BABBA HAR TA BASHI WANNAN KUD'IN AKAN ZAI MATA AIKI, TO KUNJI DALILIN KIRAN, DAMA KUMA SALIS YA CE MASA HAJIYA CE TAKE KIRAN SA. MUJE ZUWA)*

*A.J POV*

Har ya gaji da jiranta amma shuru bata zoba, ya kira number ta amma no amsar, yana dai tsaye a gurin har a ka fara kiran sallar magariba, nann ya ganggara yayi, yana cikin sallar ne yaji wayarsa na 'kara. Bayan ya idar ya ro'ki Allah yasa Hajiya ta kirashi gobe, sannan ya ce Allah yasa kud'in da sarha ta sato masa sukai dubu hamsin (500k) cikin zuciyar sa ya ce "Ai kuwa Nana zan baiwa wannan wayar tawa, Innah kuma na siya mata 'karama nikuma naje na siyo maikyu. Yana cikin Addu'ar ne yasake jin 'karar wayar sa, hakanne yasa ya fita daga masallacin kafin ya d'aga.

*SARAH POV*

Tin tana harabar gidan su take kiran wayar sa, amma baya d'agawa har ta iso gurin da zasu had'u, tana sake kira ya d'aga, ta bud'e baki zatayi magana ta hangoshi yana isowa gurin. Kana kallon fuskarsa zakaga hasken musulunci irin wanda ke fita daga goshin duk wani musilmin da ke tseda sallharsa, hoton tabon sallahr dake goshin sa ta 'kurawa ido, dukda duhun dare ya farayi amma hasken gurin bai hanna ta hango abun da yake bata sha'awa a goshin nasaba.

Cikin sakin fuska ya 'karaso gurin dad'in da yin sallama wacce shikaidai zaiji kayarsa. Kallonta ya keyi kamar yanda Itama take kallon sa. Cikin d'an 'bata fuska ya ce "Meyasa yau baki saka hulaba kika fito da kanki a haka? SARAH ta ce "sorry I'm forgetting. Kallon ta ya sakeyi yaga kamar tayi kuka sai ya ce "lafiya kuwa naga kaman kinyi kuka?

Sarha ta ce " Samuel ne ya cuceni d'azu. take ta kwashe yanda sukayi da shi ta fad'a masa, amma bata sanar dashi akan d'aukar kud'i bane. Tin da yake bai ta'ba jin sontaba ko tausayin taba sai yazu, cikin ransa ya ce yanzu ma haka duk a kainane!!! Afili kuwa ya ce...

"Ok sorry stop crying.

Da sauri ta kalleshi jin yau shine yake bata ha'kuri, ta tsayar da kukan...

Ta ce "please AJ dan Allah kana sona?

A.J ya ce "please yanzu duk ba wannan ba, kinga dare nayi bani kud'in ki koma gidan kar Daddy ya dawo bai gabkiba.

Cikin sauri ta ce "please AJ amsar me. Kana sona?

A.J cikin jin haushi ya ce "Yes Sarah I really love you, kibani kinga dare nayi?

Da gudu ta rungumshi had'i da cewa I'm so happy to you my AJ.

Lokaci d'aya tsikar jikinsa ta tashi, in ka gansu a haka zaka rantse da Allah Sarah babu wando a jikin ta, domin kuwa wandon ruwan tokane kuma iya cinya ya tsaya, ga kuma yanda jikin su ya had'u da juna kamar irin suna cikin wani yanayi.

Da sauri AJ ya janyeta daga jikinsa had'i da cewa... "Na fad'a miki cewar Wannan abun babu kyu a *ADDININMU*, please karki... "Cikin sauri ta ce " muma babu kyu a namu addinin amma in dai da wanda zaka aurane babu laifi.

Cikin sauri ya ce "To mu koda kuwa an saka muku ranane in dai ba'a d'auraba to babu kyu, saboda haka kikiyaye, ADDININMU da naku a kwai babban ci, ta bud'e baki zata sakeyin mgn ya ce "please ina kud'in dare nayi kingama an kusa kiran sallar isha.

Cikin jakar da tazo da ita ta sa hannu ta d'auko kud'in ta mi'ka masa. AJ ya zaro ido waje Yana kallonta ya ce "Sarah sarh sarhh wannan kud'in nawaye? Ganinn yanda kud'in suka bud'e masa ido, nann fa ya rikice ya shiga tambayarta.

*ABDULLHA POV*

Tin Yana mota yake tinanin irin cin mutuncin da abokin sa ya kaishi a ka masa, cikin ransa kuwa yana kallon lokacin da take kallon sa har wani hararra take masa. Palorn Mommy ya nufa tin kafin ya 'karasa ya fara jin kamar sauti ko surutan mutane, yana isa ya tsaya chak Yana kallon abun mamaki.

Maryam ce tsaye cikin shigar 'kanana kaya ta kunna waqar Zainab Ambato ita da wasu 'kawayanta mata guda biyu, kasan cewar Mommy bata gidan, Nusaiba da Sadiya ma duk tare suka fita da Mommy. Daga ita sai nura d'an autansu, sai 'kawayan nata guda biyu. yayinda d'aya ta tashi suke bin waqar ita kuwa d'ayar tana chatting a waya.

Dukkansu basu ga shigowar saba tsabar sunshiga hadaya, Saida yayi a'kalla mt5 yana tsaye yana kallonsu, yama rasa mai zai fara musu, sannan sai mamaki ya keyi, da gaske agidan su a keyin kad'e-kad'e da rare-rare!? Kuma Maryam!

Lokaci d'aya haushin abun da Zainab d'in tamasa da kuma abun da ya tarar d'in suka had'e masa yanzu, yanufi gurin da suka jona wayar, yana zuwa ya cire wayar daga cikin abun speaker d'in, baiyi wat-wataba ya buga wayar da 'kasa.

Ita kuwa Maryam jin an katsemata yasa ta juyo da niyar zagin qawar tata, a tinaninta itace ta kashe. Ai kuwa tana juyowa sukayi ido hud'u da shi, kafin kace me ya d'auke ta damari, had'i da bin kawayen nata. Sukuwa basubi ta kan jakokinsu ba da ta'kalmin su, ita daiyar ma harda gyalenta da wayarta. Haka suka fita da gudu, shikuwa ganinn sun gudune yasa ya dawo gurin Maryam, itama ta nufi d'akin ta da gudu tana kiran sunann Mommy.

Dai-dai ta turo 'kofar zata rufe shima ya iso d'akin, kafin ta tura ya rigata, ya turo, hakane yasa ta fad'a a tsakiyar d'akin. Nann ya cire hular kansa,. Sannan ya zare wayar caja dake d'akin ya shiga lamta mata, tana ihuuu yana zabga Mata, saida ya mata shegen duka kafin ya ce "Bade ke mai taurin kaiba muje zuwa ina dai-dai da ke... tsabar kin raina mutane kizo har gida kina kunna mana wa'ka!? Ya kara d'aga wayar ya labtamata, har saida Maryam ta daina kuka tsabar azaba.

*AJ POV*

Sarah waye ya baki wannan kud'in!? Yafad'a yana 'kura mata ido?

Sarha ta ce "please 'kar'ba in kuma bakaso tom na koma dasu?. AJ ya kar'ba ya 'kirga yaga dubu d'ari dai-dai, kallonta yayi ya ce "To amma yanzu yazaa..." Zamuyi waya kar Daddy ya dawo yaga bananan. Haka ta sake rungumarshi sanna ta tafi, ta barshi tsaye yana kallon ta. Shima cikin kasala ya kama hanyar gida.....📝




*
*PAGE* 👉6️⃣

............ A.J. Duk yanda yakai da son kud'i yaukan yaji ya tsorata da wannan kud'in, shi babban tashin hankalin sama shine... kar Daddy ya kama Sahra ita kuma tace shine yake turata. Haka ya shiga gida jiki babu 'kwari. Ko sallama baiyiba ya shiga gidan nasu yana tinanin mafita, Nana ce kad'ai a tsakiyar gidan tana cin abinci, hakanne yasa ta tsaya tana kallon yanayin yayan nata. "Yaya Lafiya kuwa kake?. Shikuwa A.J baima san tanayiba. Ganin bai bata amsa ta ce "Yaya kiran sallar isha fa a keyi kuma naga kashigo gida? Cikin hanzari ya dawo daga tinanin na sa ya ce "Sorry na mantane yanzu zanje nayi. Tana kallosa ya bargidan da alama dai wani abun na damun sa.

*SALIS POV*

Kallon 'kanwar tasa ya keyi cikin soda ƙauna, tinda suke tare da ita basa ɓoyewa junann su komai domin kuwa ko saurayine yazo gurinta tofa saita sanar da shi haka shima, dukdade shi baitaɓa cewa yana sonwata yarinyar ba. Akaro na farko kenann yakejin bazai iya sanar da ita abun da ke ransaba, saninn halinta na kushe zaɓin wani.

Cikin zuciyar sa ya shiga tinann abun da yafaru yanzu minti kaɗan da suka huce. Tsaye yake a 'kofar gidan su AJ yana jiran yaga yaro ya aikeshi ya kira masa AJ, kasan cewar yakira wayar AJ ɗin bata shiga. Yana tsaye ya ga yaro yazo shiga gidan, nann take ya sanar da yaron cewar in ya shiga yace ana neman AJ. Bayan kamar minti 2 yaron yazo ya ce wai bayanann amma ga ƙanwarsa wai zataga kowaye in yazo sai a faɗa masa. Salis ya ce "ok. Sannan ya kira yaron ya masa ihisani. Cikin gidan kuwa Innah ce ta ceda Nana taje ta dubo kowaye, domin kuwa sunsan A.J da abokai kuma duk yaran masu kuɗi.

Hakanne yasa ta saka hijab ta nufo ƙofar gidan. Leƙowa tayi ta hango baƙar mota a fake a ƙofar gidan, gakuma mutum a jingine a jikin motar, hakanne yasa ta nufi gurin sa. Tana zuwa tayi sallama haɗi da gaishisa. Salis da yake danna waya, ko kallonta baiyiba ya ce "Idan A.J yazo kice masa Salis ne yazo kuma kuce yasameni a gid... Maganar tasa ce ta maƙale a bakin sa sanadiyar tozali da fuskar Nana.

Cikin rikicea ya ce "am am am kikace baya gida ko? Nana ta ce " Eh baya gida amma yanzu zai dawo.

Ai take Salis yayi mutuwar tsaye jin wata sassaiyar muryarda tamasa magana da ita. Ya ce "To kice Salis ne yazo neman sa, Kuma kice yazo gida yanzu.

Nana ta ce "to zan fad'a masa, tana faɗa ta juya ta nufi gida cikin takunta na yan mata masu natsuwa. Salis kuwa neman fad'uwa ya keyi ganinn yanda take tafiya kamar zata karye, haka ya bar ƙofargidan cikin begen Nana.

Sauke ajiyar zuciya yayi bayan ya dawo daga tinanin.

Laɗifa ta ce "bro lfy kuwa tin ɗazu kazo Kanata tinani kuma kayi shiru?

Salis ya ce "sis ina maganar da hajiya Babba tamana ɗazu?

Laɗifa ta ce "Maganar aure ko maganar yaronnan abokin ka ɗan talakawannan?

Salis kuwa cikin ranshi ya ce "Allah ya sa ban faɗa mataba da wallhi bazata goyi bayana ba. Afili kuwa ya ce " maganar aure... Na yarda zanyi domin kuwa nasamu wacce na keso. Cikin mamaki Laɗifa ta ce "Yanzu-yanzu daga kaje gidansu A.J ka dawo kace min kasamu matar aure? Salis ya ce "Yes haka Allah yake abun sa. Laɗifa ta ce "Tofa!! Lallai koma wacece ta iya kamu, tabaɗa had'i da yin dariya sannan ta ce "ya sunann ta? Salis ya ce " ban saniba, bata faɗa min ba.

Laɗifa ta ce "To yanzu dai muje mu sanarwa da hajiya Babba, kaga itama saita dena maganar aurannan nata ko ya kace? Salis ya ce hakane tashi muje?. Haka suka jera suna tafiya Laɗifa na tsokanar sa, wai wata yarinyar tayi WUFF da shi a cikin lokaci kaɗan.

*ABDALH POV*

Cikin tsananin ɓacin rai ya bargidan ya nufi gidan sa wanda ke unguwar hotoro ɗan marke, yau ransa in yayi dubu to duk sunɓaci, baisan yazaiyi da Maryam ba, a'ce wai ƙanwarsa da suke uwa ɗaya uba ɗaya itace keyin rawa, rawa da waƙar ƴan bidi'a!!?. Yanufi gidansa da niyar bazai dawo ba sai gobe domin a'san yanda za'a yi da Maryam, kawai aure za'a Mata. Wata zuciyar ta faɗa masa, ai kuwa ya aminta da hakan.

Maryam kuwa bayan Abdalh ya fi ta, ta yunƙura da niyar tashi amma Ina, take ta sake rusa ihuuu, hakanne yasa nura da tin shigowar yayan nasu yagudu,. ganinn yanda fuskarsa ta ɓaci. Dukda nura bashida ƙarfi haka ya taimaka mata ta miƙe tsaye ,ya kwantar da ita a kangado. Abin dariya amma ba damaryi, haka ya gintse dariyarsa ganinn yanda takeyi kamar wacce a ka ɗaye fatar jikin ta, ga ihuu da takeyi. Ganinn kamar nura nason yin dariyane yasa cikin kuka ta ce "Wallhi nura in kasake naji dariyarka saina kusan karkaryaka.

Shikuwa nura jin yanda tayi maganar cikin kuka da rakici ne yasa dariyarsa kufcewa, aikuwa ya saki dariyar, haɗi da sakin ta ta faɗa kangadon da ƙarfi. Aiku mai neman kukane aka jefeshi da kashin a waki, nann take kuka ya dawo sabo, tadin buɗe baki tanayi, shikuwa nura yabar ɗakin yana dariya.

*ZAINAB VOP*

Dariya takeyi wacce rabon da tayi irin ta harta manta. Kallon Isa tayi ta cigaba da bashi labari. "To bayan ya tafine mukayi wa'azi sauran abokan nasa harda wani kafeni da ido, Nikuwa ko ta kansu bambiba.

ISA ya kwashe da dariya sannan ya ce "Amma fa kin burgeni Wallhi, wani abuma saigobe in munje kusa da gidansa gabatar da walimar da zamuyi, nifa Allah har na matso naji wannan sabuwar wa'kar da kikace zakiyi mai taken bud'ad'd'iyar wasi'ka.

Zainab ta ce "Yanzuma zan je na ƙarasa aikinta, ai i'na sane da Al'kawarin da na ɗaukarwa mlm. Isa ya ce "Ɗazu Aliyu yazo wai ya kira number ki baki ɗaga ba? Zainab ta ce " Oo!! Allah sarki ban sanar dashi batun zuwana walimar bane, Kuma kasan idan i'na kan aiki bana ɗaka waya, Allah dai yasa baije gurin mlm ba?

ISA ya ce "Nima agurin mlm ɗin na ganshi, kuma nasan maganar ce ta kawoshi, kuma zakigani mlm zai miki mgn. ISA ya cigaba da cewa "To Zainab in kina sonsa kawai kiyarda ayi auran mana tindade shi yace ko yaushe kika shirya?. Zainab ta miƙe ta bargurin haɗi da cewa Yaya zamuyi mgn anjima yanzu inada aiki.

*LAƊIFA SALIS. POV*

Salis ya ce "No Sistar karmu sanarwa da hajiya tukunna, saboda ban samu mun yi magana da yarinyar ba, kibari nann da kwana biyu lokacin mun shirya da ita. Lad'ifa ta kwashe da dariya sosai kamar zata faɗi sannan ta ce "Kai bro karfa kodai kaima irin mazannanne masu tsoran Mata?

Salis ya ce "Dama a kwai mazan da suke tsoran Mata!?

"Hh mana ga ɗaya ma a gabana.

"Haba yarinya aini jarumin mazane, ke bama niba duk mai irin sunan Salis to yanmata ma shakkarsa sukeyi.

Laɗifa ta ce "Tom zade mugani

.Haka suka bari sai ya shawo kan yarinyar. ( Wanda ya kasance ranar ne A.J yaje gurin Hajiya)

*A.J POV*

Bayan ya dawo daga sallar isha ne ya shigo gida, cikin kwarin gyiwa domin kuwa zuciyar sa ta bashi tabbacin kawai yaci kuɗin domin Sarah bazata tona masa asiri ba. Kallon Nana yayi ya ce "NANA goba zan baki wayata iyah kuma zansiyo mata ƙarama, amma fa bance ki dinga tara number samari a waya ba, kuma kullum sai na Kar'bi wayar naduba, kin yarda?

Da sauri ta barcin abincin da sukeyi tare da yayan nata ta ce "Yaya wallhi na yarda, ni daga number ka sai number Innah sai kuma number kadija ƙawata shikenan. AJ ya buɗe baki zaiyi magana yaji wayarsa na ƙara, yana dubawa yaga number Hajiya wacce ta bashi akan zata kirashi, da sauri ya ɗaga yana cewa hello Hajiya?. "AJ hajiya Babba ta Kira sunann sa ta cikin wayar.

"Na'am"

Hajiya ta ce "Kazo gida misalin qarfe goma na safe, kuma banason Africa time?.

"Angama Hajiya in Sha Allah zanzo. Amma hajiya kituro Salis sai mutafi tare da shi?

Da sauri Hajiya ta ce "no banason yasan da zuwanka, Kuma karka sanarmasa da cewa kazo kuma duk aikin da na baka karka nuna masa komai kaide yardarka kawai nake buƙata.

Cikin sauri AJ ya ce "An gama ranki shidad'e, yanda kikeso haka za'a yi. Nann ya kashe wayar dai-dai lokacin inah ta fito daga bayan gida. Ta ce "Yanzu Abdul jabaru inayin magana kafini baki, kacemin kai baka sata, yanzu a ina kasamu kud'ad'an nann da kake cewa zaka siyamana waya?

AJ ya ce "Yanzu Innha fisabillhi sokike mu ƙare a wannan talaucin? Abun arzuƙi ya samemu amma kicewai... to Innah in baki son wayar ai sai kibarta, yanzu ki dubeki daga jiya zuwa yau dan Allah baki ji kinfi samun kuzariba?kinci kaza kin sha yourgot ga kaya mekyu, amma bazaki samin albarkaba.

NANA ma ta amsa da cewa, mudai innah muna son wayar please yaya kabani taka kaji?. Haka innah tayi shiru badan batada da abun cewaba sai dan anfita baki.

Washe gari, kamar yanda A.J ya ce, ya siyowa Nana layi, yabata wayarsa, itama Innah yasiyo Mata ƙarama da layinta, yayinda shima yaje shagon siyarda waya ya siyo wayarsa mai kyu. Ƙarfe goma na safe dai-dai aka tafka saɓani tsakanin Salis da A.J. yayinda Salis yake kan hanyarsa ta zuwa neman soyayyar Nana. Shikuma AJ yaje domin jin wani aiki Hajiya zata bashi.


*A.J. SALIS POV*

Kallon Hajiya babba yakeyi cikin tsanani mamaki, haɗi da kallon jakar kuɗin gaban sa. AJ ya ce "Hajiya ban fahimci abun da kikenufiba?. Cikin shawƙin abunda ta keji ta ce "Yes kamar yadda kaji na sanar dakai, aure nakeso muyi da kai amma cikin sirri, karkowa yaji, in har ka amin ta, kasanar dani duk abun da kakeso tin daga kan miliyoyin ɗari da kuma gida da kuma mota, zan mallaka maka.

Sanye take da dokuwar riga sai gyale fari. Kallon sa takeyi ganinn shima ya zuba mata ido. Cikin jin kunya ta ce "ina u'ni? Salis kuwa

4 / 37