Addininmu Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  S Reza Category :  Love

Chapter   3 / 37

6K to 9K   out of 109.2K words

zuci da baki, sanda nakemassa masoyin sa ma'aiki)*.

Nann take abdullha ya tsaya agurin ya kalli angon ya ce "Salim kace min walima za'a yi agurinnan? Salim ya ce "Sorry Shek wallhi nima bansan za'a gaiyato mawa'kiya ba, "Amma ai kasan yarinyar da ganima yar bidi'a ceko? Inji abdullha cikin tsananin b'acin rai. Salim ya ce "Kaga mutane na Kallon mu dan Allah muje muzauna sai muyi magana.

Abdullha ya ce nine zanje na zauna Ina kallon kad'e-kad'e da rare-rare? Salim ya ce "a'a za'a tsaya da shi yanzu please dan Allah? Saida abdalh yaga mutane sun fara kallon su kafin yabar maganar ya nufi gurin da a ka ware musu wato an kwaye.

D'aya daga cikin abokin angon me suna Yusuf ya ce "Wai ita wannan yarin yar ahaka zata 'kare rayuwarta da kad'e-kad'e da rare-rare bazatayi aureba? Abdalh ya ce "To waye zai auri wannan ai rashin wanda zai aurane yasa kaganta haryanzu. Salim ya ce "Haba kau wallhi wannan da kuke gani ba matar yara bace, ai ba kowane zai iya tin karar ta da batum aureba sai de manya malamai wallhi. dai-dai lokacin da abdallha ya bud'e baki zaiyi magana ita kuma Zainab Ambato ta kai idonta gurin take idinsu ya had'u a guri d'aya, Saida sukaiwa juna kallon minti d'aya kafin suka kawar da idonsu.

Yayin da abdullha yakejin mugun tsanar abun da takeyi kana take Mata kallon rashin kamunkai. Ita kuwa Zainab idonsu na had'uwa tamai kallon 'kiyayya kafin ta kalli halifiyarta ta ce "Jeki sakamin wa'kar bagudu bajadabaya, wato wa'kar da abdullha ya musu Randi a kanta jiya.

Ai kuwa dama wa'kar sabuwace kowa soyake a zo kan wa'kar domin kuwa WAQAR tayiwa mabiya shehu dad'i. Ai kuwa ana sawa al'umma suka d'auka, nann take suka fara fitowa da hoton shehu Mata damaza samari da 'yan mata, ko ganinn Zainab d'in ma bakayi. Saide kaji ana cewa... ( *BAGUDU BA JADABAYA KAN 'KWANAR SHEHU MAULANA).* 📝


*PAGE* 👉4️⃣

______________Muryoyin al'umma ne kawai ketashi agurin ana bin wa'kar kamar sune suka rerata, ita kuwa Zainab sai kallon gurinda Abdalh yake takeyi tana son ganin wani irin yanayi zai shiga. Abdullha kuwa yana ji tasaki wannan wa'kar ya kalli abokin nasa cikin tsananin b'acin rai ya ce "Nagode da abun da kamin sannan kuma in harkana so na cigaba da zama anann to sai an kori wannan mawa'kiyar. Angon ya kalli Abdalh sannan ya ce "Haba Shek abdullha kasanfa banine na gaiyatotaba uwar amaryar ce, kuma tana gurinnan kaga kuwa banida ikon korarr ta.

Abdullha najin haka ya mi'ke tsaye ya bar gurin cikin tsananin jin haushin abokin nasa. Tin da yake ba'a ta'ba cimasa fuska irin wannan ba, wato saboda ta ganshi agurin shena tasa a ka sake Mata wannan wa'kar ko!!? Haka Abdalh ya dawo gida cikin tsananin jin haushi, dama mukullen mutar na hannun sa, sai kawai ya tafi yabar su. Duk abun dake faruwa a kan idon Zainab, dama tasan bazai zaunaba hakanne yasa tayi amfaninn da wannan damar ta kore shi. Bayan ta gama rera 'kasidar ne kuma ta koma wa'a zi a kan zaman aure tsakanin ango da amarya. Tana musu tini da irin zan auran Nana fad'ima Yar ma'aikin Allah .s a w. Yanda tayi ha'kuri agidan mijin ta, sannan tamusu tinida da, rayuwar manzan Allah da yayi da iyalan sa, haka dai Zainab ta dinga kawo musu abubuwa da manzan Allah yayiwa matansa.

Daga 'karshe ta rufe da salatul fati. Abokin ango da ango sai mamaki sukeyi ganinn yanda ta dinga fad'ar irin abubuwan da ma'aurata ya dace da suyi domin koyi da sunnonin Annabi Muhammad sallalahu a w s azaman aure. Haka mutane suka dinga mata ihisani harda ango da kansa saida ya mata, haka uwar amarya ta rasa inda zata sakata tsabar murna.

*A.J POV*

Da sallama ya shigo gidan baki har kunne, ba kowa a tsakar gidan hakanne yasa ya sake doka wata sallamar, dai-dai lokacin Nana ta fito daga wanka, ta amsa sannan ta tsaya da bokiti a hannu tana kallon ledodin da suke hannun sa, cikin mama ta ce "Yaya wannan kumafa daga Ina? "Kafin ya bata amsa Innah ta fito daga cikin d'aki tana cewa "lafiya kuw... "Lafiya lau Innah kawai taga abun da bata saba gani bane shine ta tsaya sai tayi surutun nata da tasaba.

D'akin Innah ya huce yabarsu tsaye suna kallon sa. Ya ce "Innah wallhi mugodewa Allah domin ni mai sa'a ne! Ya shiga fito da abubuwan da ya siyo , dai-dai lokacin Nana ta iso gurin bayan ta d'aura hijjabi a kan tahul d'in da tafito dashi daga wanka. Ganinn doguwar riga Amaya ne yasa ta d'auka tana cewa yayana amma wannan tawace ko?

A.J ya ce "Ai Nana daga yanzu mun fi 'karfin irin kayan da muke sawa a baya duk kyatar dasu zakiyi kifarasa na zamani. Cikin tsananin mamaki Innah ta ce "Yanzu Abdul jabaru bazakamin bayaninn yanda kasamu kud'ad'an nannba, har sai na tambayeka? Cikin farin ciki A.J ya ce "Innah amma ai tinkafin na tafi na miki bayani ko? Kuma kinsande A.J baya sata, saboda haka kawai kimanta da komai Allah ne ya dubemu.

Haka dai Innah tayi shiru domin kuwa tasan tinda yace to hakane, nann fa Innah ta shiga cin kaza ba kwa-kwatawa, haka suka kasance cikin farin ciki wannan ranar. Bayan komai ya kammala ne ya d'auki wayarsa yaga kiran Zarah, saida yaja tsaki sannan ya kirata yana cewa, yarinya yanzu kuma ai nahuce ajinki, nasan yanzuma zakicemin ba'a samu bane, kuma ke ya dama.

*LA'DIFA. SALIS. POV*

Da gudu ta fito daga cikin palorn gidan nasu tana mai kirin sunann mai gadin nasu tamkar ita ta rad'a masa. IRO!... IRO!... IRO!... Wanda shikuwa iro tin kiran farko ya taso daga sallamar sallha da yayi ya fito da gudu yana cewa "hajiya karama Dan Allah kiyi haguri wallhi yanzu na idar da sall... Cikin tsananin b'acin rai ta ce "Wai Kai wani irin wawane Kai baka da hankali ne? Shin saunawa zan cemaka karka sake barin wani ba'ko in dai magidanci ne ya shigo cikin gidannan? Cikin sabawa da irin abun da Lad'ifa ta kema dukda kuwa yakai ya haufeta, bata duba wannan domin kuwa wani lokaci ma harda mari ta had'a masa. Ya ce "Allah ya huci zuciyar ki wallhi saideko ina sallha ne ya hajiya Babba ta shigar dashi amma Dan Allah a gafarceni bazan sakeba in Sha Allah.

Cikin masifa ta ce "Kama sake mana wallhi in har ka sake barin wani mutumi ya shigo wannan gidan koda kuwa Hajiya Babba ce ta saka to abakin akin ka, ya bud'e baki zaiyi magana ta ce "bana son jin komai kadai ji me nace maka, nonsense. Tana fad'a ta bargurin ta nufi cikin gidan domin cin mutuncin mutumin da yazo neman auran mahaifiyar tasu. IRO Maigadi kuwa wani hawayene suka zubo masa daga fuskarsa, tabbas ya gaji da cin zarafin da wannan yarinyar take masa, badan bashi da abinyiba in yabar gidannan da tin ba yanzuba ya bar aikinnan.

SALIS tasamu yana zazzagayawa acikin palorn da alamar ita yake jira, aikuwa tana zuwa ta ce "Brother muje wallhi yau sai mutumin nann ya san bamuda mutunci. Suna cikin hirarrsu cikin nutsuwa dimin kuwa tasan yarannan nata bazasu dawo yanzuba, saboda zuwan wannan bakon natane yasa ta aikeso gurin da bazasu dawoba har ya tafi.

HAJIYA Babba kenannn, mace mai tarin dukiya wacce mijin ta ya rasu ya barta da yara biyu mace da namiji, Salis da Lad'ifa. Ita kuma tana son kara aure amma sukuma sun hana ta, saita gama boye musu komai daga 'karshe sai sun gano, dayawa wasu mazan domin dukiyarta suke son auranta wasu Kuma domin Allah, yanzu haka yaranta sun koremata manema sama da goma. Wasuma sai ana gobe aure wasu tin zuwa d'aya wasu sai abu yayi nisa, wasu ma sai sun dakesu wasu kuma suyi ikirarin kasheshi in har ya aureta, ita kuma tana bu'katar yin auran. Yanzy haka wannan ma magar da akeyi an saka rana, suna cikin haka taji shigowar yaran nata.

Cikin mamaki ta me'ke tsaya tana kallon fusko-kinsu ganinn yanda suka murtuke fuska, ta ce "Salis ina aiken da namuku? Bai ko bata amsaba yayi gurin da mutumin ke tsaye ya ce "Wallhi kafin na irga uku karna kara ganinn wannan fuskar taka a nann! Cikin tsananin b'acin rai Hajiya ta ce "Salis ba dakai nake mgn bane? Lad'ifa ta ce "Malam badakai akeyi bane? Ko sai ka ruga a guje? Hajiya Babba ta fashe da wani irin kuka tana cewa Wallhi in har kuka korishi to saina tsine muku dukkanku. Dai-dai lokacin da Salis ya kai uku a irgen da yakeyi.

Ai kotakan maganar Hajiya baibiba yayi kan bazawarin da gudu, itama Lad'ifa tabi bayansa. Ai kuwa gogan naku yana ganinn haka ya dau nakare. Hajiya Babba sai ihun kiran sunann su takeyi.

Shikuma bazawari tsabar gudu ya manta da cewa yazo da mota, domin kuwa ya huce bakin get da kudu, ai kuwa IRO Maigadi Yana ganin sa ya kibud'ewa, harsai da suka iso gurin. Salis da Lad'ifa suka kalleshi cikin tsananin b'acin rai suka ce "Wallhi daga yau in ya sake zuwa gurin Hajiya Allah sai sun halakashi, haka ya ce wallhi bazai ma sake nuna yasantaba, haka dai suka razana shi har ya d'auki motarsa ya bargidan cikin fargaba. Salis da Lad'ifa suka juyo gurin IRO Maigadi suka sake cemasa karya sake barin kowa ya shigo in ba hakaba hmmm!!. Iro ya ce "To yalla'bai wannan yaron da kace in yazo a barshi ya shigofa? Salis ya ce "banda wannan abokinane.

Haka suka shiga cikin gidan Lad'ifa ta cemasa "Wallhi brother bana son ka da wannan yaro, nifa Allah ban yarda da shiba, kana ganinn sa kaga d'an matsiyata, kafin Salis ya bata amsa sun iso d'akin Hajiya. Suna tura kofar d'akina suna iskota a gefen gadon ta kifa kanta sai kuka yakeyi, Salis ya ce sorry Hajiya bamasu..."Bana son jin komai a gareku kutashi kubarmin d'akin tin kafin ku 'Karasa kasheni!! "Lad'ifa ta ce "Hajiya kiyi hagur..."Kufita daga d'akina na ce!!! Ta fad'a cikin kuka had'e da ihuu!. Haka suka fita suna jin kukan nata harcikin zuciyarsu.

Bayan sunfitane hajiya ta sake fashewa da wani sabon kukan tana cewa "Bakusan abun da nakejibane, duk abun da yafaru dani bazan yafe mukuba, tana kuka tana fad'a, ai kuwa take ta tino da yaron da yazo jiya, da har tafasa abun da tayi niya amma tinda suka sake mata wannan abun to dele sai ta aikata sede ran kowa ya b'aci.

Take ta sheye hawayenta ta shiga kiran Salis tana nemo murmishii ta ya'ba a kan fuskarta duk domin ta nuna musu cewar ta ha'kura. Ai kuwa da kudu suka karasu har suna ture junann su. Ganinn Hajiya na murmishii ne yasa suka kalli juna cikin tsananin mamaki. Lad'ifa ta je da gudu ta fad'a jikin ta tana cewa kokefa Hajiya Allah yasa dai kin huce? Shedai Salis baice komaiba sai kallon ta ya keyi. Hajiya bata bata amsaba sai ta ce "Inaso muyi mgn daku ta nutsuwa? Hakanne yasa suka nutsu ta ce...

"Shin meyasa bakwa son nayi aure? Duk sukayi shiru, sai Hajiya taci gaba da cewa...yanzu abun da zanyi haramne ko mekyu? Namma sukayi shuru, hajiya Babba ta ce, aure aure aurefa nace zanyi amma kuka hanna!! Shin kunaso na jefa kaina a cikin masifane? Shin kunaso nafad'a cikin tsinuwar Allah ne? Shin abun da zanyi ADDININMU yayi hani da aikata hakanne?. To tunda de bakwaso nayi aure, naha'kura Amma da sharad'i. Cikin tsananin farin cikin jin cewar ta ha'kura suka kalleta suka ce kokefa Hajiya, sannan ki fad'i sharad'in ki komenene zamuyi? Hajiya ta ce "Kin Tabbatar? Suka had'a baki cikin zumud'i sukace "Eh mun yarda.

*SARAH POV*

Saida tama kira yakai talatin (30) Amma bai amsaba hakanne yasa ta saki wani tsaki mtsiiiiiiii sannan ta bud'e Data ta hau online, tana cikin chatting ne misalin qarfe 6 na yamma taga kiransa, saida tayi kamar bazata d'aga ba amma taga ita zata cutu sai kawai ta d'aga hadi da cewa "A.J kodai namaka laifi ne? Cikin 'kosawa ya ce "Naga kiranki Allah dai yasa an samo?

Saida ta share hawayan ta sannan ta ce "Eh ansamo.

Jin haka yasa AJ ya me'ke daga zaunan da yake ya ce "Ar you serious?

Jin ya saki fuska yasa ta d'anyi dariya sannan ta ce "eh yanzuma suna gurina aina zamu had'u sai na baka? Amma daga shi bazan sakebako? Domin wannan ma fa saura kad'an Daddy ya ganni?

Cikin tsananin farin ciki A.J Yace "No-no dagashi baza'a sakeba, amma yanzu kibari zuwa safe sai mu bud'e in kinje school ko?

Ta ce "no gobe bazanje school ba kawai muhad'u yanzu inason ganinn ka?

"Ok amma kinsan bazan iya zowa kofar gidankubako, saboda wad'annan sojojin masu Kama da suci babu?

Sarha ta yi dariya sannan ta ce "Kadaina tsoransu baruwansu da kai aikin su kawai sukeyi.

"Tom yanzu de muhad'u a WADATA makert sai ki bani. Sahra ta ce "ok bari na shirya. Haka suka kashe wayar yayinda sarha ta shirya irin shigarta wato riga da wando, yau ko hularma da tasaba sawa bata sakaba gashin kanta yasha wanji ya kwanta har kafadiun ta sannan ta nufi kofar d'akin nata zata fita.

Dai-dai ta tura shima yaturo, kana ganinn irin turowar da yayi kasan ransa a mugun'bace yake, cikin tsananin tsoro ta kalleshi ta ce "Samuel Lafiya? Kafin ta rufe baki ya d'auketa da wani wawan mari, kasan cewar babu wani girma da sukebaiwa juna, sai kawai itama ta zabga masa mari, cikin yaransu ta ce "Bakada hankali ne zaka mareni, ko Daddy bai ta'ba marinaba... "Ai bata an karaba ya sake d'auketa da mari har biyu, sannan ya nunata yana cewa.......📝




*PAGE👉5️⃣*

..................Cikin tsananin b'acin rai Sameul ya nunata da hannu cikin yaran su na tibi ya ce "Oya tell me waye ya shiga room d'in Daddy? Jin tayi shiru ne yasa ya sake zare mata ido ya ce "Tell me waye ya bud'e d'akin Daddy? Cikin rashin kunyar da tasaba Sarah ta ce "Waye zai shiga in bakaiba... 'barawo kawai kuma in kasake ta'bani Allah sai na had'aka da Daddy tif. Ganinn yayo kantane yasa ta fita dagudu izuwa d'akin Mommy ai kuwa shina sameul d'in yabi bayanta.

Tana zuwa ta fad'a jikin Mommy tana kukan karya had'i da cewa... "Mommy Kinga Samuel wai meyasa na tona masa asiri a kan ya d'auka ma Daddy kud'i, kuma nace masa banice na fad'a ba shine yabini hard'aki yana dukana. Mommy ta kalleshi ta ce "Sameul get out in my room? Ya bud'e baki zaiyi magana ta sake cewa ai se get out in my room? Had'i da nuna masa hanyar fita, tana cewa... Kasan dai tinda aka kamaka to dole sai ka fito da kud'in... Yaro baya jin magana kaine daga wancan clop sai wancan ba dole ka koma sataba, kana biyewa yaran banza a unguwa. Haka mommy tacigaba da masa fad'a har ya bardakin yana tafiya yana aiyana abun da yafaru kamar an shirya Masa.

Mommy ta kali Sarah tace "Kema nace kidaina shiga harkarsa bakiji ko? Duk ranar da bama gida ya kamaki ya kark-aryaki babu ruwanmu don kinsan ba han kali yakeda shib... Ai kafin Mommy ta rufe baki saiga Daddy re'ke da hannun Saumel ya na ihun kiran sunann mommy cewa...

Eliza!!... Eliza!!... Eliza!!...cikin tsananin mamaki Mommy da Sahra suke kallun sa. Mommy ta bud'e baki daniyar tambayar ba'asi ya katseta da cewa... "Eliza luck at this sameul Ashe bai fita harkar wannan yaron masu yin sallhanananba!? Na fad'a masa babu shi babu duk wani yaron Hausa domin basa da hakali, yanzu haka ma shine yakesa yake sato mana kud'i?

Cikin kuka da ba'kin ciki Samuel ya ce "waini Daddy yaushe na d'auka maka kud'i, nazo zan shiga d'akin ka naganshi abud'e shinafa nashiga kuma i suwet to God ina shiga kaima kana fitowa. Daddy ya ce "Sameul karna sake ganinn ka da yaran Hausa masu sallah bana so? Sameul ya ce "Allah Daddy his my class ment kuma... " I see is okay bana son ganin ka dasu. Ok sameul ya Yana hararr SARAH wacce tayi mutuwar tsaye tana jin abun da Daddy kecewa.

Mommy ta ce "I don't like all Muslims... Samuel kafita hanyarsu, mutanan babu abun da kuka had'a dasu, mutanen da suke zagin Addininmu, babu ruwanku dasu, in ba so kuke raina ya 'baciba karnaji karna gani. Tana kaiwa nann ta bar d'akin cikin 'bacin rai. Shikuwa Daddy saida ya tabbatar musu da cewar zai cigaba da tarkon mai d'auka masa kud'i kuma zai Kama, sannan ya cigaba da fad'a musu cewar Hausa masuyin sallha ba abokan zama bane.

Ita kuwa sarha duk abun da suke fad'a yana shigane ya fita, domin kuwa ita bataji bata gani a kan A J. Tashi tayi dai-dai lokacin kiran sallha yayi ita kuma ta nufi wadata market gurin AJ. Sameul kuwa yana fita ya tarrar da abokin sa Umar wanda Daddy ya ce karya sake ganinn sa tare da d'ansa.

Yana fitowa suka kama hanyar su tazuwa gurin da suka Saba. Yayin da Sameul yake mamaki ya a kayi haka, shida bai d'auki kud'i ba yau amma an kamashi, nann ya shiga tinanin kodai Sahra ma tana d'aukar kud'in me!!? To amma anya ita zata saci kud'in Daddy kuwa!? Nannn tai ya keta tinani, daga 'karshe dai yace zai bibiyeta yaga ina take zuwa.

*LAD'IFA. SALIS POV*

Hajiya Babba ta ce "Nayarda bazan yi surenba Amma sai kun cikamin wannan sharud'an? "Muna jinki Hajiya cewar Lad'ifa tana murmishii.

Ta ce "Abun da nakeso daku shine... Salis kafito da matar aure, kekuma Lad'ifa zaki koma waje ki 'karasa karatun ki. In dai kun amin ce to nima na Amin ce, in kuma ba hakaba wallhi watarana saide ku nemeni kuga bananan agari, zan tafi nabar muku gidan naje can wani guri nayi aurena, tinda ADDININMU bai haramta ba, ta 'Karasa tana hawaye.

Cikin tashin hankali Salis da Lad'ifa suka juyo suna kallon juna, ita dai Lad'ifa nata da sau'ki domin kuwa zata iya, shikuwa Salis cikin

3 / 37