Addininmu Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  S Reza Category :  Love

Chapter   18 / 37

51K to 54K   out of 109.2K words

Rasulullah. Shima Solo ya mai-maita sannan mlm ya fassaramasa cikin turanci wato...

(ka sheda babu anin bautawa da gaskiya sai Allah, sannan ka yarda cewa Annabi Muhammad manzan sane kuma bawansane)

solo ya ce eh na sheda. Take kuwa gurin kowa ya ɗau ƙabbara cikin farin cikin cewar yau addinin Musulunci ya samu ƙaruwa. Nann aka tambayeshi wani suna ya keso? Babu wata-wata ya ce "Muhammad! Nan fa al'umma suka ƙara yin kabbara.

Bayan an gama komaine anyi wankan shiga musulunci da dai sauran abun da shari'a ta hukunta, saikuma aka fara sanar masa da komai na cikin Addinin. Alhaji Salisu ya ce "Shi indai wannanne zai koya masa komai cikin ƙanƙanin lokaci cikin yardar Allah. Masu masa kyuta nayi masu masa addu'a nayi, haka dai ranar solo wato Muhammad da Alhaji Salisu da iyalan gidan Alhaji Salisu suka kasance cikin farinci da walwala jin cewar ta sanadiyarsu Addinimu ya samu ƙaruwa. Wanda shikuwa Daniyel ranar Lahadi mai zuwane auransa, kuma baisan bidirin da akeyiba itama titi bata saniba.

Haka dai Alhaji Salisu ya dinga sanarwa da Muhammad komai nacikin musulunci haɗida koya masa karatun alƙur'ani mai girma, da kuma yanda zaiyi salla da lokutanta da sauran abubuwan da ya kamata ace yayi kafin sallah, irin su Tsarki alaula. Sannan ya sanar masa abubuwan da addinin musulunci yayi gani dasu irinsu....shan giya cin, mushe, zina, cha-cha, zuwa gidan rawa, da dai sauransu. Tabbas Addinin Musulunci addinin gaskiyane, sannan addinine wanda idan ka reƙeshi kuma kayi aiki da hukuncin dake cikinsa to tabbas zaka zauna cikin farin ciki da kwanciyar hankali. Tabbas Muhammad shine ya faɗi haka lokacin da ya kawo ƙarin karatun da Alhaji Salisu ya masa jiya, kuma dai-dai babu ɓata, saide rashin daidaituwar harshi wanda sai a hankali harshensa zaisaba. Yau kwana biyu da musuluntar solo Muhammad, wanda yayi dai-dai da ranar bikin daniye da amaryarsa. Anyi aure lfy kuma an tashi lfy bayan anyi duk wani abu da za'ayi. Har zuwa wannan lokacin Daniyel baiyiwa solo maganar uban gidansaba kuma bai ƙara masa maganar buɗe masa shagonba.

*Bayan wata uku* Eh tabbas titi da Anty wato matar daniye harma da Daniyel ɗin sunga sauyin rayuwar solo amma basu kawo komai ba, idan zasuje coci sai yace bashi da lfy kokuma ya bar gidan cikin wayo. Izuwa yanzu kuwa Muhammad ya fara nisa sosai wajan karatun addini, sannan yana cigaba da zuwa shagon nasu. Sannan kuma ƴar gidan Alhaji Salisu ansaketa har ta sake yin wani auran, amma babu wanda yasan dalilin sakin nata. Saide wani abu dake faruwa tsakanin sa da matar yayan nasa wanda abun ya fara bashi tsoro.

Da sauri Muhammad ya fito daga ɗakinsa zai fita izuwa masallacin dake kusada shagonsu domin kuwa baya son rasa jam'i, tin acikin ɗakinsa yayi alaula ya nufo waje. Yazo zai fita yaci karo da titi zaune itada saurarinta wanda dama ya daɗe yana zuwa gurinta. Saida ya kai bakin get sai
kuma ya dawo da baya domin ya makara ƙwara kawai yayi a gida cikin ɗakinsa.

Saida ya shiga yayi raka'a biyu yana zaman tashiya saiga Anty tazo kiransa domin kuwa Daniyel ne zaune palorn cikin ɓacin rai domin yau ya keso ya raba solo da wannan uban gidan nasa karyaje ya cutar masa da ɗan'uwa. Kuma yayi alwasin idan ya sake ganinsa dashi Walhi sai ransa yayi mugun ɓaci, sannan zasuyi maganar auran titi da wannan saurayin da yake zuwa gurinta. Kasan cewar titi na waje gurin saurayin batane yasa Daniyel tura Anty ta kira masa solo ɗin. Ai kuwa dama basa jituwa domin ita Anty tana son sai sun aikata alfasha tsakanin ta dashi amma shi yaƙi bata goyan baya, a cewarsa lokacin da yake da baiyiba saida ya karɓi musulumci.

Tasha binsa ɗakinsa cikin dare amma cikin addu'ar da Alhaji Salisu ya koyar dashi wajan tsare kansa daga sharrin mutum da aljan yasa bata taɓa samun nasaraba. Yanzuma dukda kuwa da ranar aallh ne amma tana fatan ko ɗan wani abu yamata. Babu ko noking ta tura ƙofar ɗakin tashiga aikuwa tsayawa tayi chak tana kallonsa daidai ya ɗago daga zaman tashiya, ya ce Allahu Akbar!!! Cikin mmk firgici haɗida faɗuwar gaba ta buɗe baki zatayi ihuuu domin harga Allah ta tsorata. Amma sai wata zuciyar ta raya mata cewar ai wannan babbar damace kika samu, domin ta gane solo musumta yayi, to bari tayi amfani da wannan damar tinda ance idan suna Sallah ai basa mgn ko cewa komai. Dukda har yanzu a tsorace take Amma ta dage ta shiga cire kayan jikinta, saida tayi tsirara aihuwar uwarta kafin ta nufi gabansa kan daddumarsa shikuma dai-dai zai kai sunjada aikuwa sai gata agabansa.....✍️



[10/21 22:05] Aliyu Makko: *ADDININMU*



*S REZA....* ✍️


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*



*PAGE* 2️⃣6️⃣

............Yana ɗagowa daga ruku'u ita kuma tana ƙarasawa gabansa, kafin ya kai ga yin sunjjada har ta zo gabansa. Hannu ɗaya yasa ya tureta sannan ya kai sunjadar. Kallonsa takeyi ta na so su haɗa ido amma ko kallon gurin da take baya yi, da sauri ta kamo hannusa ta ɗora a kan ƙirjin ta dai-dai ya ɗago. Kafin hannunsa ya kai ya sake fisge hannusa. Ai kuwa ganin haka ya sa ta rungumeshi ta baya ta na cewa "Pls Solo for only today i realy love yo"...kafin ta ƙarasa taji an banko ƙofar ɗakin an shigo, dai-dai shi kuma Solo ya ƙwace jikinsa ya kai raka'ar ƙarshe. Kallon ƙofar ɗakin ta yi cikin tsoro da firgici, ido biyu sukayi da Titi wacce ta ƙame agurin tsabar ruɗewa domin ita bata ma kula da abun da Solo keyi ba, ita dai ganin Anty da tayi tsirarane ya firgitata. Kafin Anty tayi magana Titi ta kurma wani uban ihuun da yasa Daniyel shigowa cikin ɗakin.

Da sauri ya ture Titi ya tura idonsa cikin ɗakin dai-dai lokacin Solo ya sallame sallar tasa. Idonsa bai fara sauƙa a ko'ina ba sai kan Solo da ke zaune a kan wa ta sabuwar dadduma ga wani farin carbi a gabansa, sannan kuma ga shigar farar jallabiya haɗi da ɗan ƙaramin hularta. Kafin yayi magana idonsa ya ƙara sauƙa a kan matarsa dake kakkare jikinta cikin tsoro da fargaba. Da sauri yayi kan Solo ya fara dukan sa yana cewa "Solomon What aryu doying!? Itama Titi sai kuka takeyi tana tsarlle da ihu! Yayinda Anty ta fara magana cikin kuka.

Tabbas doka ne *(DOKA)* ga duk sojan da ya daki matarsa amma jin magar da Anty takeyi ne yasa ran Daniyel ƙara tashi domin a yanayin magar ta na nuna cewar solo ne ya nemeta. Shi kuwa zuciyarsa ce ta raya masa cewar ai sun aikata. Ai kuwa a take allurar tasu ta sojojin ta motsa kafin kace me ya kamo Anty cikin fitar haiyaci ya fara dukun ta ita da Solo wanda shi tun-tuni ya suma domin kuwa ya daku. Tabbas Daniyel ya manta da cewar baban antyfa sojane kuma ogansane a gurin aiki domin kuwa ya fishi matsayi.

Saida ya tabbatar da cewa dukkansu sun jigata kafin ya barsu ya kamo hannun Titi suka bar ɗakin. Waya ya ɗauka ya kira abokinsa daga cikin susoji akan suzo gidansa. Bayan sunzone ya sa aka tafi da Solo wanda ko farfaɗowa baiyiba, bayan ya sanar musu cewar ya kamashi da matarsa ne. Ita kuma Anty ma haifinta ya kira ya sanar masa da komai akan ya kamata da ƙaninsa kuma zuciya tasa ya dakeso. Kwana biyar da abun solo ya farka kasan cewar an kaishi asibiti. Ita kuwa Anty dama babanta ba a Benue yake aikiba, jin haka yasa akazo aka tafi da ita, domin kuwa yasan halin ƴartasa, hakanne ma yasa bai bari kowa yaji zancen ba. Cikin kwana na shida Daniyel yazo asibitin ya sa aka bashi Solo ɗin. Bayan sunzo gidane ya kama wuyan rigarsa cikin ɓacin rai ya ce "Solo karka cemin wannan mutumin ne yasa ka kwanta da matata? Kar ka ce shine yasa ka koma yin Sallha? Ya faɗi maganar cikin ihuuu!!! Wanda yasa solo fashewa da kuka ya kasa Magana. Daniyel ya girgizashi ya ci gaba da cewar "Kamanta wasiyar mama kafin ta mutu! Shin ka manta da cewar suna kashe mutane! Shin kamanta da cewar sune suka kashe Daddy? Ka faɗamin da gaske ka koma Addininsu? Cikin kuka solo ya ɗaga kai alamar eh.

Lokaci ɗaya Daniyel ya dinga sakin hannunsa daga wuyansa yana ja baya a hankali. Saida yayi nisa kafin ya ce "Solo ka haɗa kayanka ka bar min gida idan ba hakaba Walhi saina kashena!! Ya faɗa yana nuna masa hanyar waje. Solo ya buɗe baki zaiyi magana ya sake cewa "Get aut!! Da ƙer Solo ya ce "Pld Daniyel ka tsaya ka sauraren"..."Cikin sauri Daniyel ya fito waje riƙe da wuƙa a hannu ya nufo gurin da yake cikin rifewar ido. Ai kuwa solo yayi waje da gudu babu ko taƙalmi. Titi kuwa mai zatayi banda kuka domin tafi son Solo fiye da Daniyel, amma itama jin cewar ya koma wani addininne yasa taji ya fita mata a rai.

Waje ya fita yana kuka yana kiran sunan tati da Daniyel, yanaso su saurareshi amma sunƙi bashi dama. Rabonsa da zuwa shago harya manta, hakanne yasa ya tashi ya nufi shagon nasu. Tsaf ya tsarawa ogansa komai bai ɓoye masaba. Alhaji Salisu bashi haƙuri kuma yace masa in sha Allah zai tayashi domin shawo kan yayan nasa, kar ya damu yanzu yana cikin fushine. Shi dai Solo kawai yana jin sane. A nanne Alhaji Salisu ya sake sanarwa da Solo (Muhammad) cewar an sake sakin Aisha (Ƴar gidan Alhaji Salisu) cikin mmk Solo ya ce "Wai shi sakinnan babu wa hala ne? Alhaji Salisu ya ce "Ai ba daga mazan bane daga itane. Muhammad ya ce "To me take musu? "Babu komai Allah ya kawo mata dai-dai da ita. Muhammad bai ƙara cewa komaiba sai Amin.

Bayan wasu lokuta. Alhaji Salisu da Muhammad sunje gidan Daniyel har sau uku, amma ya musu korarr kare azu na ukunma saida ya daki Muhammad, ganin hakane yasa Alhaji Salisu yace ya sake rabuwa dashi harna tsahun wani lokaci. Ɓangaren Daniyel kuwa ya cire solo daga cikin danginsa, sannan ya ƙara yin wani auran ya samu wata ƴar gidan pasto ya sura mai suna Elixa. Titi ma tayi aure da wannan saurayin nata, kuma duk auran basu gaiyaci Muhammad ba amma saida yaje. A auran titi saida yasan yanda yayi suka haɗu da ita amma cikin mamaki ta zazzage shi tace ita bata sansaba, kuma yasan duk Daniyel ne zai zugata, yayi kuka ranar har ya godewa Allah. A kwai ranar da daniye ya je har ƙauyansu ya ɗauko kawunsu shina yaci mutuncin Muhammad, sannan yace babu su babu shi sun barwa masu yin Sallah shi.

Ana cikin haka Daniyel ya tattara shida matarsa wacce yanzu itace take sake shiga tsakaninsa da ɗan uwanasa, domin idan Muhammad yazo gidan lokacin da Daniyel baya nan sai ta cimasa mutunci sosai. Suka tattara suka bar cikin garin Bokon suka koma cikin Benue MKD (Makurdi) sannan ga kuma ƙarin girma da Daniyel ɗin ya samu daga gurin aikin nasu. Yayinda Daniyel har yanzu abunda solo da matarsa wato Anty sukayi yake tsaya masa a rai.

Bayan susu lokuta Alhaji Salisu da Muhammad aminci ya ƙara ƙarfi sosai, yayinda yanzu haka Alhaji Salisu ya aurawa Muhammad ƴarsa wato Aisha. Cikin yardar Allah komai ke tafiya dai-dai da yanda Allah ya tsara musu. Lokacin da dangin matar Alhaji Salisu sukaji cewar zaibaiwa tubabbbe auran Aisha saida kowa ya ce bai yarda ba, amma abinda Alhaji Salisu ya faɗa musu gameda ƴar tasa ne yasa kowa yaja baki yayi tsit. Bayan ɗaura auran saida Alhaji Salisu da Aisha da Muhammad suka tattara sukaje Beby mkd domin nunawa Daniyel matar ɗan uwan nasa, amma ya ƙara cimusu mutunci harda tsarabar duka domin wannan lokacin ana bashi masu gadinsa domin ya ƙara samun girma sosai. Alokacin ne Elixa ta kama gashin kan Aisha ta na ja domin cin mutuncin, haka dai suka korosu korarr kare korarr wulaƙanci. Hatta gidan Titi itama ta nuna cewa ta manta dashi. Ananne ma yake samun labarin Titi ta aihu ta samu ɗa Namiji.

Muhammad yayi kuka Sosai domin kuwa yanzu hk ya yi sauƙar Alqur'ani maigirma, kuma yasan littatafan addini da dama, yasan cewa addinin musulunci bai yarda da ƙin zuminci ba, koda kuwa ƴan uwan naka ba addininku ɗayaba, sannan bai yarda cin mutuncin kowa ba, sannan baice kaima kabari aci na ka mutuncin ba. Hakanne yasa bai watsar da ƴan uwan nasa, dukda suɗin basa ƙaunarsa. Izuwa yanzu Muhammad aizikin sa sai ƙaruwa yakeyi, domin kuwa yanzu komai na Alhaji Salisu yana hannun sa, ya mallaki abubuwa da dama hakan ne yasa yaje ƙauyansu wato Katungu. Yayi alheri sosai, dukda kuwa suce basa ƙaunarsa amma hakan baisa sun ƙi karɓaba.

Ga kuma ya samu mata mai sonsa da gaskiya wacce itama ta ke taya shi a kan shirya wa da ƴan u'wansa. Daniyel da matarsa Elixa sunce idan Muhammad ya sake zuwar masa gida Walhi sai sun kasheshi. Domin sunji haushin abunda yamusu. Lokacin da suke cemasa Solomon sai ya ce "Yanzu na bar Solomon na koma Muhammad"...."Ai tin kafin ya ƙara sa shine suka fara zagin sa da cin mutuncin sa, sannan sukayi wannan ikirarin.

Kwanansu biyar da dawowa, suka tattara sukaje ƙasa mai tsarki domin bautar Allah. Yayinda Muhammad bai manta da ƴan uwansa ba wajan addu'a, sannan bai manta da Alhaji Salisu ba wajan masa addu'a domin kuwa ya masa komai a rayuwa.

Bayan sun dawo gida 9j ne Muhammad da Aisha suka koma Katungu wato ƙauyansu, yayinda suma Alhaji Salisu da matarsa suka ji ƙauyansu cikin garin kano domin dama Asalinsa ɗan canne shida matarsa. A hanyarsu ta tafiya ne suka kunna wa'azin malam shek Kabiru kabuga wanda yayi akan ruƙon abana da muhimmancin har. Aisha ta ce "Walhi ina son wa'azin bawan Allannan "Nima ina sonsa sosai kuma in sha Allah idan kika aihu shene zai zo garinnan domin shan wa'azi. Itama ta ce "Wooo ai kuwa da ka burgeni sosai! Suna cikin hakane wayar Muhammad ta ɗau ƙara, yana dubawa yaga numbar Daddy wato Alhaji Salisu. Da murmushi ya ɗauka yana cewa Aisha "Kinga su Daddy sun riƙamu ƙarasawa"..."kaine Muhammad? Yan wata murya ta fito daga cikin wayar wacce bata Daddy ba ce.

"E, h,h,hhe ni ne. Ya faɗa cikin rawar murya. "To ga mota ta yi hatsari mutum biyu ne aciki kuma da alamar rai yayi halinsa sabo da haka yanzu kuzo"..." Ya isa ya faɗa yana tambayar sa a ina sukayi hatsarin? Aisha dake kusa dashi sai tambayarsa takeyi lfy kuwa? Take ya sanar mata komai, aikuwa ta rafka wani uban ihuu kafin ta sume agurin ko mosti bata yi.

Kamar da wasa haka Alhaji Salisu da matarsa rai ya yi halinsa, mutuwar da ta gir-giza Muhammad da Aisha kenan. Sai da a ka'sha fama kafin Aisha ta farka. Tayi kuka har saida ta fita a haiyacinta. Tin daga lokacin komai ya dawo hannunta, dama kuma su ba ƴan Benue bane, sannan kuma ita kaɗai ce a gurin babanta. Haka har komai ya huce suka ci gaba da zamansu a gidan da suke ciki.

Cikin tsokana da agon na ta ya saba mata ne ya ke ce ma ta "Hajiya Babba, domin kuwa yanzu ta zama Hajiya Babba, saboda dukiyar da ta mallaka, itama dai da ba ta son sunan har ta fara ƙaunar sunan sosai. She karar Alhaji Salisu biyu da rasuwa ne Aishe ta haifi ɗanta na miji, wanda yaci sunan ma haifinta wato Salisu. Daga nan ne Muhammed ya ce su tattara su koma cikin mkd. Ai kuwa haka a kayi suka tattara suka koma gidan su da suka siya a cikin gari. Bayan suna da kwana huɗu, suka shirya domin komawa gidan Daniyel gaisuwa wanda shima yanzu haka ya sake samun wani girmar. A wannan zuwanne fa basu samu Daniyel ba sai matarsa Elixa. Aikuwa take ta hau Aisha da duka har saida ta kasa tashi dukda cikin da ke jikin Elixa ɗin. Shi kuma Muhammad ya na tsoran karya taɓa ta a samu wata matsalar. Amma ganin ta na neman kashe ma sa mata ya sa ya fusgota ai kuwa ta faɗi a kan kujerar dake cikin ɗakin, take jini ya hau zuba, ganin haka ya sa ya ɗauki matarsa sai gida. Washe gari da sassafe ko karyawa basuyi domin kuwa jikin Aisha da baya mata daɗi, dukda sunje asibiti jiya, kuma a jiyan ta farka shine aka sallamesu. Bata liyan sojojine mota har huɗu suka shigo unguwar tasu, ai kuwa babu wata-wata suka kama Muhammad suka tafi dashi. Sai da yayi wata huɗu babu wanda ya san inda yake kafin suka sako shi, shi ka ɗai yasan abin ya ga ni a gurin da suka kai shi.

Bayan shekaru da dama lokacin Muhammad ya ƙara samun aihuwa ita kuma ya saka sunan maman Aisha amma suna ce ma ta Laɗifa. Yayinda ita kuma Elixa saida tayi she ƙara shida da aihuwa kafin ta ƙara samun cikin ƴa mace. Yanzu dai itama yaranta biyu Samuel da mai sunan mamar su wato Sarah. Ita kuwa Titi yaranta huɗu uku maza ɗaya mace, amma duk sun koma ga Allah sai ɗan au'tanta shene Usha, wanda shine sa'an Samuel.

Har wannan lokacin Muhammad bai dai na neman ya fiyar ɗan uwansa ba, yayin da shi kuma ya yan ke sha warar kashe shi. Kafin wannan lokacin ma ansha rikici sosai da Aisha da Elixa, yayinda kowa yasan yaran kowa amma ba bu wanda ya taɓa faɗa wa yaransa dan gan takar dake tsakanin su. Sunyi iyaka da juna a kan kowa yaje yayi addinin sa, kuma kowa ya ce ya yarda. Ganin yanda Muhammad ya kwaso wasu daga cikin ƴan uwansu na ƙauyan Katungu ne sai musuluntar da su ya keyi ne, shine ran Daniyel ya ɓaci ya ce sai ya kashe shi, domin kuwa a ƙalla mutane sama da goma duk sun musulumta kuma a hakan ma suna ƙara musulunci.

*RANAR WATA JUMA'A*

Tafe yake shida yaronsa Salis a cikin motarsa

18 / 37