Addininmu Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  S Reza Category :  Love

Chapter   22 / 37

63K to 66K   out of 109.2K words

ne? Dan Allah karku bari wannan ɗinbin alkairi ya huce mu, dan Allah ku taimaki musulman da ke ƙanƙashinku suna koyi daku, ku dinga fassara aya dai-dai da faɗin Allah, ku daina raba kawunan musulmai, Walhi kullum sai na zubar da hawaye idan na ji yanda musulmi ɗan uwansa yake cin mutuncin musulmi...

Har ta kai ta kawo wai wani musulmin baya cin yankan wani saboda kawai ba aƙidarsu ɗaya ba, wasu kuma basa Sallah a masallacin da ba na ƴan aƙidarsu ba, wasu kuma basa aura taiya tsakanin juna mutuƙar ba aƙida ɗaya sukeba, hatta makaranta wai idan har ba makarantar ƴan aƙidar su bane to bazasu kai yaransuba bare kuma su kansu, a hakan kuma wai dukkkanmu musulmai ne. Dukkan musulmi ɗan uwan musulmi ne, amma yanzu abun yazama ba haka ba, domin kawai son zuciya irin na malamammu. To ina kira a garemu walhi muji tsoran Allah mu san cewar komai da mukayi yana kallonmu kuma zamuje garesa. Yanzu dukkanku kumin alƙawarin amincewa da zaku yi magana da iyayenku cikin gaskiya da biyayya? Duka suka amsa mata da cewar sunyi alƙawari, Isa da Abdalha suka gaisa kowa ya baiwa kowa haƙuri. Yayinda Abdalh ya jinjinawa Mama yana jin cewar idan suka haɗe da Momy aguri ɗaya to tabbas ADDINIMU zai ƙara samun jajir-tatun masa acikin sa.

Mama ta ce "To yanzu dai Isa ku tashi ku tafi kunga dare nayi? Suka miƙe zasu tafi Mama ta ce "Kije ki rakasu mn? Ai kuwa Zainab ta miƙe cike da farincin yanda Mama ta dawo dasu hanya. A tsaye bakin motar Abdalha suka tsaya ganin Zainab ta fito yasa Isa cewa bari ya ɗauko wayarsa a ɗakinsa. Yana tafiya, dukkansu sukayi shiru Zainab ta ɗaga kai ta kalleshi taga shima ita yake kallo, ai da sauri ta kawar da kanta gabanta na ƙara faɗuwa. Sai ta tsinkawo muryarsa na cewa "Kin san wa cece Maryam? Da sauri ta ɗago tana kallonsa wanda har yanzu kallonta ya keyi, shiru tayi tana tuno a inama ta taɓa jin wannan sunan. Ganin ta kasa tunowa ne yasa ya ce "Maryam Kabir kabuga ƙawarki?

Sai yanzu ta tuno da ita, sai kawai ta saki murmishi ta ce "Ban santaba sai a wannan ranar. Yana son ya ce mata wani abu amma ya kasa sai kawai ya ce "Dama ba kwayin waya da ita ne? "No bamayi. Ta bashi amsa tana kallon Isa da yake isowa gurin.

Isa na zuwa Abdalha ya ce "Kice da Mama na gode? Itama ta ce "na gode. Tana tsaye a gurin har suka tafi, dai-dai za asu fita daga gidan shikuma ya shigo gidan shima cikin motarsa. Ganin motar Aliyu yasa Isa ya ce da Abdalha ya ɗan tsaya dan Allah.

Abdalha na zaune har ya dawo ya ce muje. Abdalha ya ce "Ko dai shima yayanku ne baga kamar zai girmeka ko? Isa ya ce "Eh ya girmeni, amma a bokinane, kuma ba ɗan gidannan bane amma dai yanzu ya zama ɗan gida. Abdalha ya ce "Ya maka faɗa da yagammu tare ko? Isa ya ce "No ai baima ganeniba. Abdalha sake cewa "to me ya zoyi a darannan tunda kace ba ɗan gidan bane? Isa ya ce "Inaga dawowar Zainab ne ya riskeshi kasan shine wanda zai aureta, angama magana yanzu rana kawai a ke jira a sa. Da sauri Abdalha ya kalli Isa sai kuma ya sun kuyar da kansa, bai ƙara jin me isa ya kecewa ba har saida isa ya taɓashi a lamar ina zai kaisu, domin kuwa wata hanyar ya ɗauka. Cikin suɓutar baki Abdalha ya ce "Kuma za'ayi auran da ita? Da mamaki Isa ya kalli shi domin shi harga Allah harma ya manta da sunyi wata maganar aure, kuma yanzuma bai fa himci me yake nufiba sai kawai ya ce "Aura da wace? Abdalha ya waske da cewar "Aure da yarinyar da kake so mn?. A haka suka iso ƙofar gidan su Abdalha ɗin.

*NANA POV*

Tinda suka dawo Innah batayi maganar AJ ba, hakanne yasa Nana ce wa "Wai Innah bakiji maganar da na ce miki cewar nazo naga kaya a gidannan bane, kuma ina tunanin yaya ne ya kawo ba? Innah bata tamka mata ba. Ta ci gaba da cewa "Wai dan Allah Innah haka zamu zauna mu biyu bazamu tafi neman yaya ba, nifa harga Allah jikina yana bani cewar wani abune ya sameshi, kuma wannan abunda a ka mana nasan ba laifin sa ba ne, dan Allah Innah mn uje nemansa!? Ta ƙasa maganar cikin sha ƙwaɓa. Innah ta kalleta cikin nuna cewar ko a jikina ta ce "Idan zaki tafi nemansa ga hanya nann, sannan kuma mutuƙar Abdauljabaru ya dawo gidannan to tabbas zama a gidan ya ƙare kenan, koda kuwa shi ba zai bar gidan ba, to tabbas ni zan bar masa gidan domin kuwa gidan ubanku ne. Innah ta fashe da irin kukannan da a ke cewa kukan baƙin ciki, tabbas bazan manta da abunda yaronnane yasa a kamin ba, kuma Allah sai ya saka min, dukma inda ya shiga to in sha Allah sai ya ɗan-ɗani irin abunda ya sa a ka mana. Nana ta faɗa jikin Innah tana kuka itama ta cewa "Dan Allah inna karki wa yaya baki, Walhi bakin ki zai kamashi domin kuwa matsayin u'wa kike a garemu, kuma dan Allah idan yaya ya dawo ki tsaya ki fahimceshi na san halinsa walhi zai fahimtar da ke, karki yanke hukunci cikin fushi dan Allah Innah!

Cikin tsan-tsar ɓaƙin cikin abun da wasu gin-gima gin-giman arna suka mata ta ce "Arne kuma soja wanda baisan Allah ya ce Annabi ya ce ba shine ya shigo har gidana ya ɗaya hannu ya mareni bai duba tsufana ba, Arne!.. Arne!.. Arne!.. Arne!... Wanda bai sai mutunci ba shine ya mareni duk saboda Abduljabaru, kuma tunda abun ya faru bai zo ba, badan wannan yaron da ya dinga taimaka mana da abinci ba da basu san yanzu a wani hali muke ciki ba. Innah tayi magar tana tuna lokacin da sojan ya mareta. Nana ta ƙara cewa "Dan Allah dai kiyi haƙuri bari na je gidan su Kadija na tambayeta ko da gaske yaya ɗin ya dawo. Innah dai bata ce mata komai ba har ta fita reƙe da wayar ta, tana kuma tuno Salis ko ina ya shiga, gashi ita ta manta da numbar sa da sai ta kirashi kodai shima ba lfy ya ke ba!

Kallon Kadija takeyi har ta gama sanar mata da komai abunda ya samu AJ ɗin lokacin da ya dawo. "Lokacin da yaki labarin kuka ya dingayi har yana faɗuwa, kuma duk u'nguwarnan anrasa wanda zai tai maka masa koda da maganar aiziƙi ne, to ana cikin hakane wani ɗan shaye-shaye mai suna Bala ya zo gurin ya sanar masa da cewar wai wannan sojan babban wannan yarinyar da nake ganin ku tare ne yazo tare da yarinyar tana kuka ta nuna gidanku wai...wai...wai...Kadija ta kasa ƙaras sauran maganar da Bala ɗin ya ce tsabar kunya da nauyin maganar, wacce itama tunda taji maganar har kwanciya rashin lafiya tayi tsabar kishin da tayi da yarinyar. "Kadija faɗa min koma meye dan Allah karkiji komai? Kadija ta ce "Wai ci ci ci ki ciki ya mata shine babban yarinyar ya ke nemansa....📝






[10/21 22:06] Aliyu Makko: *ADDININMU*




*S REZA... ✍️*


*First Class writer's asso...*


*PAGE3️⃣1️⃣*

.....Da gudu ta bar gidan bata tsaya sauraron kiran da Kadija ke mata ba har tana cin karo da mamar Kadijan zata shigo ɗakin bata ko bi ta kan ta ba ta kwasa da gudu sai gida. Ta na shiga gida ta tarar da Innah a gurin da ta barta, da sauri ta faɗa jikin innar ta na kuka ta na toshe bakinta. Cikin tsorata da halinda Nana ta shigo gidan Innah ta ce "Nana me ke faruwa? Waye ya taɓaki? Me a ka miki? Cikin kuka Nana ta ce "Innah wallhi walhi yaya ya dawo kuma kuma kuma! Sai ta kasa ƙarasawa ta sake fashewa da wani kukan. Cikin jin haushen abubda take cewa Innah ta ce "Saboda ya dawo shine kika shigo min gida da kuka kamar wacce a ka daka? To saime idan ya dawo, ai dama ni nasan babu inda yaje yana cikin garinnan, kuma in sha Allah sai Allah ya saka mana akan abinda ya sa aka ai kata mana. Cikin rashin sanin abunyi Nana ke kuka tana tsoran sanar wa da Innah abunda taji kuma kar taje abun ya ɓata mata rai! Sai kawai ta ce "Wannan sojan ne ya zo ya kamashi, wai saboda ya dawone yasa aka sakemu. Innah ta ce "To wai dan ƙundun ubansa me ya ha ɗashi da arne? Ina ruwansa da marasa sallah da har zaije ya jawo mana irrin wannan azabar? Nana ta ce "Yanzu dai Innah zanje nemansa Kadija ta ce min tasan unguwarsu harma gidan sojan, saboda haka zamuje tare kinji? "To walhi idan kikasa ƙafa kika bar gidannan da niyar zuwa neman Abduljabaru to ina tabbatar miki cewar bazaki dawo ki sameni a gidannan ba, zan tattara kayana na barmuku gida na shiga duniya ƙila a cikin duniyar na samu waɗanda zasu iya zama dani, dama ai nasan ba gidana bane gidan ubanku ne saboda hk zan bar muku gidan. Da sauri Nana ta rugomo Innah ta na kuka tana bata haƙuri a kan cewar ta fasa zuwa, "Pls Innah ki daina irin wannan zancen bai da ceba samm! Cewar Nana ta na kuka. Innah ta tashi ta bar gurin izuwa ɗakinta tana tunano ma haifin su Nana ɗin. Ganin haka yasa itama Nana bin bayanta ta na kuka, ai kuwa ta na shiga sai ga kiran Dr. Tana ɗagawa ya ce "Ina wa je! Nana ta ce "Innah Dr ne yazo wai yana wa je? Innah ta ce "Tashi kije amma karki daɗe, kuma ban yarda da zuwa ko ina ba. Dr kuwa yau dai ya zo da ƙarfin sa domin baiyana abunda ke cikin zuciyarsa a gurin hasken rayuwarsa.

*GIDAN SOJA*

Addu'a suka duƙufa yi dukkansu domin Allah ya kuɓutar dasu daga hannun wannan ƙaton arnan, ko wa ya manta da komai sai addu'a, wasu kuma suna karatun qur'ani. Muhammad da sauran ƴan uwan nasa wanda suma kaɗan daga cikin ƴan cikin ƙauyan Katungu ne da suka musulunta shine fa Daniyel ɗin ya haɗa dasu, sannan yaje ƙauyan ya sanar wa da iyayensu cewar ai dama idan ka ƙarɓi musulimci kuɗi a ke yi da mutum, saboda haka Solo yaje yayi kuɗi da yaransu. Hakanne yasa suka ƙara ƙiyayyar Addinin Musulunci, wanda har wasu da ɗan dama sun fara nuna buƙatarsu ta shiga addinin saboda yawan zuwan da Muhammad ɗin keyi cikin ƙauyan Katungun, amma yanzu duk sun ƙara jin sun tsani addinin da ma mutanan cikin ta. Hakanne yasa suka fara kashe duk wani ko wata Musulmi da ya shiga yankin nasu. Yanzu dai cikin ƙauyan Katungu babu dama wani musulmi ya shiga.

Muhammad, Umar, Usman, Salis, Hajiya Babba, Laɗifa, AJ. Sune a cikin ɗakin rai bakwai(7) kuma dukkansu musulmai. Ko wa ƙoƙarin karanto duk addu'ar da tazo bakinsa ya keyi, banda Laɗifa wacce tun da ta shiga jikin mahaifin ta take ta kuka har yanzu, Hajiya Babba ma kam izuwa yanzu ta saddaƙar domin bata manta abunda ya ce mata ba, ga kuma ƙarar tashin motocin su da sukaji alamar sun tafi. *(Tofa!)*

Gudu sukeyi sosai wanda yasa suka isa cikin garin Bokon da wuri, dubada yanda jiniyar motocin nasu ke tashi a dukkan hanyar da suka biyo, kowani mai abun ha wa ƙoƙari yake ya basu hanya kar a halakashi. Abun da ya ɗaure wa kowa kai ku wa shine...suna shigowa unguwar da yake ɗin suka ga al'umma a tsaye a bakin gidan, ga kuma hayaƙi da ke tashi. Ko da suka ƙarasa sai sukayi gamo da abun mamaki. Gidan wani ɗan kasuwa ne ya kama da wuta hakan yasa ya laso na kusa dashi, shima ya kamo na kusa dashi, wanda kuma gidan Comandar Daniyel ne a tsakiyar su. Ko kafin ƴan agajin suzo har kowani gida ya gama cinye wa tass. Ganin sojoji yasa sauran al'ummar dake tsaye a gurin suna kallo kowa ya ɗau na kare. Cikin tashin hankali Elixa ta fara rusa ihu har ta manta da ita ɗin wacece, ihu ta kayi tana faɗin irin dukiyar da ta ajiye a cikin gidan, su kansu sojojin mamakin wannan abun sukeyi, domin ai ba wannan gidan bane ya ka ma ta a ce ya ƙone. Shi kuwa Comandar tsabar ruɗewa bai san lokacin da ya tun kari wutar ba, duda cewar wutar ta gama cinye komai amma har yanzu tanada zafi.

Kamo shi a keyi yana ƙwacewa ana ruƙoshi yana shiga. Da sauri ya ya tsaya cak yana wani tunani. Waya ya ciro ya kira ɗaya daga cikin sojojin da ya bari a wancen gidan, ai kuwa tana shiga suka ɗaga. Da sauri ya tambaye su cewar sun ƙona gidan ne? Cikin tabbatar da cika umarnin su sukace "Yess sir. Ai da ƙar fi Daniyel ya ce "Nooooooo a kashe wutar yanzu-yanzu kafin ta cinye gidan?. Cikin rawar baki suka cce "Ai muna saka wutar muka bar gidan domin kar a kamamu. Ta ke Daniyel ya sulale agurin a sume ya na sakin wayar tasa. Elixa kuwa sai ihu takeyi tana kiran sunan mijin nata. Da sauri sojojin suka saka Ogan nasu a mota suka kama hanyar asibiti, shi kuwa Samuel zafin bulet ya hanashi gane a wani hali suke ciki ne yanzu. Suna cikin tafiyane wayar dake cikin motar tayi ƙara a lamar kira daga Captain. Wato Captain ɗin dukka sojojin Benue sts, domin shi dama Comandar ne na iya barikin da yake.

Da sauri na hannun damansa ya ɗaga. Cikin umarni aka buƙaci Daniyel a cikin garin Benue sts yanzu-yanzu. Ai kuwa bai tsaya jin me zai ce masaba ya kashe wayar. Cikin sauri sojan ya sanarwa da Elixa abunda ke faruwa. Cikin tashin hankali ta ce "An ƙona wancan gidanne? "Sojan ya ce ""eh an ƙona. Ai ta ke ta sake sakin wani sabon kukan, sai yanzu taga wawtarsu na sawa a ƙona gidan. Sojan ya ce "Yanzu fa dole saide muje offece ɗin Captain idan kuma ba haka a kwai matsala. Da sauri Elixa ta kalli mijin nata cikin jin haushin shawarar da ya basu ta ɗauki ruwa mai sanyi ta watsa masa, ai kuwa ya saki wata ajiyar zuciya yana far kawa da da wani ihuu! "No Pls don't se Yes Please Elixa don't . Cikin ruɗewa ya fara faɗin (ƙaryane karkice min gaskene dan Allah Elixa karkice hakane)

Cikin tashin hankali ta ce "Pls dan Allah ka nutsu kaji halin da muke ciki. Nan fa Daniyel ya rikice, ganin haka yasa Elixa sanar masa da umarnin Coptaing. Chk ya tsaya da kukan yana kallon dreban nasa, sai kuma ya kai kallonsa izuwa hanyar da suke bi, ta ke cikinsa ya bada wani sauti. Bai ƙara cewa komaiba har suka shiga cikin Makurdi. Saboda tabbatarwa Elixa ta ce da dreban yabi ta ƙofar gidan nasu sugani. Ai kuwa suna shiga unguwar suka tarar da ƙofar gidan cike damutane, ga ƴan kwana-kwana har sun isa gurin sun fara aikinsu, sannan kuma kamar motar sojoji suka hango a gurin harda police, nan fa hankalinsu ya ƙara tashi. Ta ke Elixa ta shiga tunanin idan Sarah tana cikin gidan fa! Shikuwa Daniyel gabansa ne ya shiga faɗuwa yana tinanin Allah dai yasa dukkansu kowa ya ƙone, domin kuwa idan har ba hakaba to tasa ta ƙare, lokacin da ya hango motar police da sojoji kuwa take yasa suka juya da mutarsu suka koma hanyar da zata sadasu da office ɗin Captain.

*SARAH POV*

Da gudu ta fita ta ƙaramar ƙofar gidan kasan cewar dama tasaba bi ta gurin idan zata fita, kuma duk gidan babu wanda yasan tana da makullin ƙofar. Gidan su Usha ta nufa babu ko taƙalmi a ƙafarta, dukda cewar tsakanin gidan su Usha ɗin da gidansu a kwai ta zara hakan baisa ta hau abin hawaba. Sai da tayi tafiya sosai kafin ta isa gidan. Mai gadin gidan na ganin ta a cikin wannan halin ya buɗe mata get yana mai cewa sannu. Bata ko tsaya bi ta kansa ba ta shiga gidan da gudu. Tana shiga palorn gidan sai ga mamar Usha ɗin wato Titi cikin shigar ta zata fita unguwa. Da gudu ta faɗa jikinta tana kuka tana nuna mata hanyar waje. Jin kukan ta ne yasa Usha dake ɗakinsa shima ya gama shiryawa kenan da alamar dai tare zasu fita. Da gudu-gudu ya sauƙo yana ƙarasowa gurin yana mai jawo fuskar Sarah ya ce "Menene? Me a ka miki? Itama Titi cikin tsoron kodai wani abune ya samu ƴan gidan nasu ta ce "Sarah meke faruwa ne? Ki nutsu kiyi magana mn? Da sauri Usha ya ɗau ko ruwa ya bata, ai kuwa take ta sha kusan rabi, wanda dama tana buƙatar ruwan. Sai a lokacin suka kula da yanayin ta, tayi baƙi ta rame ta koma kamar wata ƴar almajira.

Alokacin Titi ta ƙara shiga tashin hankali. Usha kuwa ya jawota jikinsa yana kwantar mata da hankali. Sai da ta ɗan samu nutsuwa sannan ta ce "Anty Titi kinsan Solomon? Zumbur Titi ta miƙe tana nuna Sarah cikin tashin hankali ta ce "Me ya faru? Sarah ta ce "Yana raye bai mutu b"...Ai kafin ta rufe baki Titi ta ruƙota jikinta tana neman ƙaryata ta ce "Me kikesone kicemin? Ta ke Sarah ta kwashe dukan abunda ya faru ta sanar wa da Titi da Usha. Cikin tashin hankali Titi ta ce "Solomon bai mutuba? Yana gidan ku? No ƙaryane wannan ban yarda ba. Cikin mamaki Usha ya ce "Dama bayan ke da Daddy kuna da wani ɗan u'wa ne? Da sauri Titi ta ce "Yes mu ukune amma ɗayan ya mutu, wanda shine mafi hankali da tausayi a cikinmu, duk lokacin da na tuno da Solomon sai nayi kuka, idan na tuna da abunda ya faru a tsakanin na da shi kullum

22 / 37