Addininmu Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  S Reza Category :  Love

Chapter   33 / 37

96K to 99K   out of 109.2K words

ƴan uwan dangin mijin da zasu auri ƙanyan nasane, a tunansa gurin auran sukazo. Saida Maryam da Laɗifa suka sha dariya kafin Maryam ta ce "To ai zaku iya sanin yarinyar da zai aura domin ba ɓoyayya bace? Salis ya ce "Tofa kenan sele ce yarinyae?! Wacece? Ta ce "Zainab Adam ambata wannan mai yin ƙasidun.

Da ƙarfi Salis da laɗifa suka haɗa baki da cewa "Zainab Adam? Maryam ta ce "Ƙunsan ta ne? Abdalha kowa da sauri ya kamo hannun Salis ya ce "Kasanta ne? Salis da mamiki da ruɗani ya saki wata dariya yana kallon laɗifa wacce itama dariyar ta keyi.

Ɓangaren iyayen kuwa cikin mamaki Muhammd yake tambayar Shek dalilin hana Abdalh auran yariyar. Shek ya faɗa masa dalili Hajiya Babba ta ce "To Wai ita yarinyar ƴar waye? Kuma meye aibunta? indai anyi bincike a kanta komai daidai ai kawai sai ku amince. "Shek ya ce "Yar bidi'a ce, sannan tana mace tana yawon zuwa gurin taro tana kaɗae kaɗe da raye raye, saboda haka nace bana sonta a zuriata. Cikin mamaki Hajiya take kallon Shek domin ta gano shi, ita kanta family ɗin su a kwai masu yin ƙasida, har yanzu gidansu a nayi, kuma a haka mahaifinta ya auro mamarta dukda ba aƙida ɗaya sukeba. Shek ya ci gaba da cewa..."Ga mahaifin yarinyar ba mutumin kirki bane baya ƙaunar cigaban addinin Allah. Cikin gajiya da zancen Hajiya ta ce "Waye uban nata? Da sauri shek ya ce "Wannan mutumin wai malam Adamu? "Da mamaki Hajiya Babba ta ce "Ya sunan yarinyar? "Wannan dai mai waƙar Zainab Adam Ambato. Tsabar mamaki saida Hajiya Babba ta ƙware, shi kansa Muhammad a mugun mamaki yake kallon Shek domin harga Allah ya mutuƙar bashi mamaki.

Da sauri Momy ta ɗauko ruwa ta bata, sannan ta ce "Lafiya dai ko? Hajiya ta kalli Shek ta ce "Idan har kanada matsala da mahaifin yarinyar to bai kamata abun ya shafi yaranku ba, saboda haka ga shawara zan baka Malam...Yaranka na cikin matsanancin hali, sannan kuma ita yarinyar da kuke magana a kai yanzu haka rana irin ita yau za'a ɗaura mata aure, kuma ita ɗin ƙanwata ce, malam Adamu kuma mahaifinane, domin shine yayan mahaifina uwa ɗaya uba ɗaya. Kafin shek da Momy su dawo daga duniyar mamaki Muhammd ya tabbatar musa da cewar hakane, wannan zuwan da sukayi ma a family House ɗinsu suka sauƙa, kuma daga nan gidan gidansa zasu nufa. Kafin su sake cewa komai saiga Abdalh da Salis da sauran suma sun fito daga ɗakin Abdalh ɗin, suma Salis ya sanar musu alaƙarsu da Zainab.

A wannan ranar Shek Kabir kabuga yaji kunyar da bai taɓa jiba, ya zaki mahaifin matar abokinsa a gaban sa. Muhammad ya bashi haƙuri a kan idan har ya amince da Abdalha ya auri Zainab to kamar anyi an gamane domin Malam Adamu baida matsala. Cikin jin kunya ya amince yana jin cewar hakan ne zaisa Muhammd yaji sauƙin abun da yama matarsa, sannan ya ce "Shida kansa zaije gidan Malam Adamu su samu jituwa. Kowa yaji daɗi yayinda Abdalh ya zo ya rungumi Muhammad yans ta faman godiya. Nan Shek ya gabatar da Muhammad a gareshi da iyalansa, jin cewar Salis abokinsa ne yasa shi cewa "A she niɗin ɗan biyune shene Momy baki taɓa faɗa min ba ko? Ya faɗa yana ƙarasowa gurin Salis. Kowa dariya yayi sosai harda Nura da yake zaune a kusa da Nusaiba.

A wannan ranar da yamma Momy da Hajiya Babba da Muhammd da shek Kabir kabuga suka nufi gidan Malam Adamu. Lokacin da Mama taji abunda ke tafe dasu tayi murna sosai, Malam kuwa ganin idon Muhammad yasa ya kasa cewa komai domin kunyar sa da kuma yar tasa wato Hajiya Babba. Dukda bata zuwa Kano Amma hakan baisa ta manta dasuba, yana jin kunyarta sosai. Sai ya saki fuska ya ce ya haƙura a kan duk abunda ya faru. A kayi sabuwar gaisuwa kowa murna da farinciki. Saida a ka nutsu sannan Muhammad ya shigo da batun auran Abdalha da Zainab.

Nan nefa Malam Adamu ya ce "To a gaskiya dai yanzu haka saura kwana kaɗan auranta, kuma yaron da zai aureta kamar ɗa yake a gurina idan nace na fasa ai sai duniya tamin kallon mutumin banza. Muhammad ya ce "Hakane to amma Malam ita yarinyar tana sonsa? Lokacin Malam yayi shiru yana kallo Mama.

Haka dai mama ta sanar musu da cewar ai dama auran biyayya zatayi, bata son Aliyu kawai dai tabi maganar iyayenta ne. Malam yasa a ka kira Zainab a gaban sa, a ka tambayeta "Shin kina son Aliyu ko kinada wanda kikeso? Nan take gabanta ya faɗi dukda kuwa tasan da zuwan su, domin Isa ya tura mata da saƙo. yanzuma kafin ta ce komai saƙo ya ƙara shigowa wayarta, tana dubawa taga numbar sa ce. Anyi gajeran saƙo kamar haka... Wannan itace kaɗai damar mu, kawai ki gyaɗa kanki a lamar Eh, nikuma zance musu kince kinada wanda kikesone. Bayan ta gama karan tawane ta ɗaga kai sai tayi ido biyu da isa yana mayar da wayarsa aljihu ya sakar mata murmushi. Maganar da Malam yayi ce ta dawo da ita daga abinda ta keyi.

"Zainabu karkiji kunya ki sanar danu komai in sha Allah zan baki wanda kikeso. Zainab cikin jin kunya ta ɗaga kai batare da ta ce komaiba. Mama ta ce "Kin ɗaga mana kai mai hakan ke nufi kenan? Hajiya Babba ta ce "Zee Ambato ki buɗe baki kiyi magana? Zainab ta ɗago kai ta kalli Hajiya Babba sai sake sun kuyar da kanta. Ai kuwa caraf Isa ya ce "Wai tanada wanda take so. Isa Malam ya ce sai ta faɗa da kanta. Haka dai akayi da ita ta kasa cewa komai. Daga haka Zainab tabar palon cikin farin cikin jin iyayen nasu sun shirya, tun a wajan ta fara tunanin yin sabuwar ƙasida a cikin satin nan......📝





*Masha Alhamdulillh A shekaran jiya lahaɗi ƙanwata abar alfaharina tayi sauƙar al-ƙurani maigirma. Allah yasa tayi mai amfanar ta da ma al'ummar musulmai baki ɗaya, Allah yasa albarka a ciki, Allah ya ƙara mata basira da juriya. Allah ka haɗa kan al'ummar musulmi baki ɗaya.* *Wannan dalili ne yasa kukaga jiya da shekaran jiya ban muku posting ba. Wannan ma ba yawa sai kuyi haƙuri.*

*Zan shiga wata gasa ta manyan marubuta ina barar addu'arku, Allah ya bamu Sa'a, domin ba iya war mubace tsan-tsar addu'o'in kune.🤲*


*Comments ɗinku shine abun alfaharina*


*S REZA ✍️*
[10/21 22:07] Aliyu Makko: *ADM*




*S REZA...✍️*

*First Class writer's asso...*


*PAGE4️⃣5️⃣*
........Hakan da Zainab ta yi ne ya ƙara tabbatar musu da cewar tanada wanda takeso. Cikin hukuncin Allah komai ya tafi daidai da yanda Allah yaso ya kasance. Malam Adamu da kansa ya zaunar da Aliyu ya tsara masa komai yanda zai fahimcesa, ya tabbatar masa da cewar ya yi haƙuri domin ba zaiwa ƴarsa auran dole ba, da farkoma rashin fahimta ne yasa naso na aikata kuskure. Da mamaki yaga Aliyu na murmushi Malam ya tambayeshi dalili. Ya ce "Ai tun ba yauba na gano Zainab tana son Abdalha, kuma nasan da cewar auran biyayya zatayi...koda hakan bai faruba to babu shekka ni da kaina inada niyar samunka muyi magana a kai...sai dai ina tsoron abunda zai biyo baya domin nasa ba kwajituwa da yaron da takeso din...sannan kuma Abdalh da kansa ya turo Isa a kan ya roƙeni na janye batun Aurena da Zainab kuma na yarda Allah ya basu zaman lafiya sannan nima naji naɗin wannan haɗin kan naku. Allah ya ƙara haɗa kan al'ummar musulmai baki ɗaya, Allah ya ƙarya duk wani abun da zai tarwatsa kan al'ummar musulmai. Malam Adamu ya kamo Aliyu yana hamdala yana amsawa da Amin amin. Haka Malam ya ce duk yarinyar da yaga ta masa a cikin dangi do yaje ya naimi soyayyarta shi kuma zai masa komai na aure. Aliyu yayi murna sosai a haka ya bar gidan yana jin son Zainab amma zai daurewa zuciyarsa kamar yanda ya ce.

Kwana biyu da faruwar haka soyayya ta ɓarƙe tsakanin Zainab da Abdalha, duk wata kafar sadarwa labarinne ke kai wa da komowa, al'ummar gari kowa mamakin wannan abun ya keyi, ai jama'a basu ƙara shiga mamaki ba saida sukaji soyayyar Maryam da Isa, nan fa kowa ya fara tofa albarkacin bakinsa. Masu cewa dama ai tun farko rashin fahimta ce tasa kowa baya ganin kowa da ƙima. Wasu kuma suce ai dama ai Malamai sune masu jefa al'umma a cikin ruɗani domin sunsan gaskiya sai su taketa domin son zuciyarsu. Wasu kuma sai suyi addu'ar Allah ya ƙara haɗa kan al'ummar musulmai mu zama addini kuda ɗaya, koda ma nawane to a zauna lafiya babu cinmutuncin juna da wulaƙanta jna da aibata juna.

Ranar juma'a a ka ɗaura auran Sadiya da angonta. Sai Nusaiba itama da nata angon. Sannan a ranar ne Sarah da Samuel suka karɓi kalmar shahada. Kowa ya zaɓi sunan da yakeso. Samuel ya koma Ibrahim Sarah kuma ta ce tana son sunan da taji Momynta tana kiran Hajiya Babba dashi wato Fatima. Manyan Malamaine suka halarci taron hakanne yasa Fatima da Ibarahim suka samu kyaututtukan bam'mamaki. Tabbas sunga yanda a ke karamci sannan sunsha wa'azi mai ratsa zuciya, har saida suka zubar da hawaye. A wannan lokacin ne kuma Fatima ta fara tinanin iyayenta tabbas tayi kewarsu tana son ganinsu.

Soyyaya ce mai tsafta da birgewa irin ta malamai Abdalh da Zainab sukeyi. Shima Isa ba'a barshi a baya ba domin soyewa sukeyi da Maryam sosai. Duk inda kaga Abdalha to suna tare su huɗu. Salis Abdalh Ibrahim Isa. Suma haka matan Laɗifa da Fatima da Maryam haka zasu tafi gurin Zainab a zauna a ta hira, a nanne Maryam ta ke sanar wa Fatima cewar ai duk wata Fatima to zara sunanta to kawai yanzu sai a koma cemata Zara, kunga an cire S na Sarah an sa Z na Zara. Cikin farinciki Zainab ta tabbatar mu da hakane, ai kuwa a ka koma cemata Zara. Tabbas Zara da Ibrahim sun tabbatar da cewar suna tare da malamai, domin a ɗan kwana goma sha huɗun da sukayi sun san abubuwa sosai. Ibrahim kam ɗan gata ya zama domin kuwa dukkansu ukun ne suke ƙara masa a bubuwa game da addini. Abdalha ya dage da koya masa karatu cikin muryarsa mai tashin daɗi, wani lokacin idan Abdalh na zubawa Ibarahim karatu sai ya ta kallonsa yana jin Allah yasa shima ya iya karatun Alqur'ani maigirma kamar haka. Isa ma haka yake koya masa wasu littattafai na addini Salis ma ba'a barshi a baya ba. Itama Zara haka Maryam wacce dama ita duk cikin yaran shek Kabir babu kamar ta a mata indai ɓangaren karatun ne, haka take rerewa Zara karatu sosai. Haka Malam Zainab zasu kwashe lokaci suna koya mata karatu ga Mama ga Momy dukkansu suna koya mata, domin suɗin sunzama wasu taurari a cikin al'umma. Shek Kabir kabuga da Malam Adamu kam komai ya huce, yanzu lokacin auran yaran nasu kawai suke jira. Mama da Momy da Hajiya Babba suma sun zama ƙawaye sosai suke zama su sha hira. A nanne Hajiya Babba take sanar musu da abunda ya faru da ita na auran AJ da tayi.

Mama da Momy matan manyan malamai wanda kowacce kanta ke ceke da sanin hukunce-hukunce da tsan-tsar sanin ilimin rayuwa. Bayanin da suka mata ne yasa hankalinta ya kwanta, ta ɗaga hannu ta godewa Allah da yasa bata aikata abun kunyaba, tabbas zama da Malamai ma wani Makaranta ce. Shima Muhammd ya naimi ƙarin bayani game da auran Hajiya Babba. Shima dai haka Shek Kabir da Malam Adamu suka tabbatar masa da cewar yanzu tana aihuwa to zai iya auratan sannan kuma kuɗin da ta bashi to kuɗin yazama halak ɗinsa. Daga haka suka tattara izuwa gida cikin kewar junansu.

*AJ POV*

Haka rayuwa taci gaba da tafiya musu cikin haƙuri da irin rayuwar da sukeyi, har yanzu Kadija bata daina nuna masa cewar tana tare dashiba, amma shi ko ta kanta baya bi, yanzu bashi da wani burin da ya huce ya ga ɗansa ko ƴarsa. Haka Allah ya ɗorawa AJ ƙaunar yaron da za'a haifa masa tun kafin yazo duniya. Sosai yake ƙoƙarin sayan komai da za'a buƙata dukda kuwa baidashi amma haka yake hana kansu ya tara. Ita kanta Nana yanzu addu'a takeyi Allah ya sauƙi ajiyar lafiya.

Ɓangaren gidan Muhammd kuwa shine ya hana Salis zuwa gurin Nana ya ce ya barta har komai yayi daidai kafin yaje mata da maganar aure. Wani sabon tashin hankali kuma shine... Ibrahim fa gaba ɗaya hankalinsa yayi ga Hadiza domin tun lokacin da ya ƙarɓi Muslunci sai abotarsu ta ƙaru da Umar. Shi kansa Umar yaji daɗin jin abokinsa ya musulunta. Yanzu sun daina zuwa club sannan sun daina zuwa wannan gurin wasan kiss ɗin. Sosai ya mai da hankalinsa a kan karatun Addini. Yanzu haka har gidan su Umar ɗin yake zuwa domin kawai ya ga Hadiza, ita kuwa Hadiza sam bata ganeshiba domin yanzu kullum cikin shigar kamala yake, haka zaluka har yanzu bata daina wannan yawon nata da kuma faɗa da koma waye ba. Shikuwa dukda hakan yaji yana ƙara sonta. Yanzu haka ya shirya idan har Hajiya ta aihu lafiya a ka ɗaura auranta da Daddy to zai gabatar da soyayyarsa ga Hadiza. Yanzu haka Ibrahim da Zara sun mallaki abubuwa sosai da a ka basu lokacin da suka Musulunta, su kansu har mamaki sukeyi.

Ɓangaren Laɗifa ma dai yanzu burinta iyayen nasu su shiga magar ta da Ibrahim, saidai yanzu taga yana ɗan ja baya da ita, amma ta bar hakan a kan yanzu baida lokaci ne. Haka shima Umar a kullum soyayyar Laɗifa ke masa baƙe-baƙe a ransa, amma yanzu dole ya haƙura kodan Musuluntar da abokinsa yayi zai bar masa ita. A da yayi alwashin ba zai taɓa bari Samuel ya auri Laɗifa ba, amma yanzu tunda ya koma Ibrahim to an zama ɗaya, zai taushi zuciyarsa ya danne komai ya barmasa, bugu da ƙari ma ƙanwarsace.

Haka ɓangaren Zara kewar Elixa da mahaifinta ne ya dameta amma taƙi sanarwa kowa, haka zata shiga ɗaki tasha kuka har ta godewa Allah. Ɓangare ɗaya kuma ga soyayar aj da ta tabbatar da cewar a jinin jikinta take, bazata daina son AJ ba koda kuwa shiɗin ya ce baya sonta bare kuma tana da tabbacin yana sonta. Duk lokacin da zaizo gidannan bata yarda su haɗu, haka ta hana kowa ya sanar masa da cewar ta Musulunta, shi kansa idan yazu sai zuciyarsa ta raya masa cewar yana son ganinta amma ya musu hakan.

Allah buwayi gagara misali, Allah mai yanda yaso a lokacin da yaso babu wanda ya isa ya ce ya haka. Ranar Litinin Hajiya Babba ta haifi ƴarta a gida ba tare da zuwa asbitiba, yarinya fara sol mai kama da ubanta. Tabbas a kwai abubuwa masu yawa da mutane da yawa suka shirya aiwatarwar bayan ai'hwar Hajiya Babba. To yau dai Allah ya sauketa lafiya sai mai zai faru?

A daran Muhammd ya kira Kawu ya sanar masa shi kuma kawu sai da gari ya waye yazo har gida ya sanarwa da AJ. Daidai lokacin Aj ko karyawa basuyi ba, abunda zasu karya dashi ma babu gashi lokacin tafiya aikinsa ya kusa. Yana tsaye a gaban Nana yana tausayinta itama tana tausaya masa, yana bata haƙurun cewar idan ya fita zai dawo da bredi in Allah ya yarda, kasan cewar yau kwana uku da biyan sa albashi kuma duk kayan jariri ya siya kasan cewar an sanar dashi aihuwa yau ko gobe, kuma bayaso a ce ya gaza. Da mamaki kawun yake kallon gidan ganin babu komai a gidan ga kuma dukkansu suna tsaye suna kuka. Kawar da wannan yayi ya sanar musu da abunda ya kawo shi. Lokaci ɗaya AJ ya daina jin yunwar, da ƙarfi ya ce "Alhamdulillh! Alhamdulillh!! Allah na gode maka. Take ya zube a gurin yayi sujjada itama Nana ta fara tata hamdalar. Gaba ɗaya suka naimi yunwar suka rasa. Nana taso binsa amma ya ce a'a ta zauna a gida, haka badan tasoba ta zauna cike da ɗokin son ganin jininn nasu.

AJ ya tattara komai na bybe ya biya ta gidan matar Kawu suka tafi. Koda sukaje babu kunya AJ ya karɓi yarinyar ya ƙura mata ido yana jin sonta na shiga duk wata jijiya dake jikinsa, lokaci ɗaya hawaye suka wanke masa ido ya ƙara jin tsoran Allah a zuciyarsa, tabbas wannan yarinyar Allah yayi ta hanyar aure za'a sameta! Haka ya faɗa a zuciyarsa. Lokacin da Hajiya Babba taji cewar AJ zai shigo sai ta bar jinjirar a gurin ta koma cikin ɗakinta. Aj yaji kaman kar ya ajiye yarinyar tsabar murna, saida matar Kawu ta masa maga sannan ya ajiye yarinyar zai fita. Ta ce "Kunjimu da ɗan ƙaramin uba! To waye zaima yarinyar huɗubar? Ai kunji matsalar ɗan yaro da aihuwa kenan ai dole a samu rashin hankali. Kasan cewar matar kawun ta fara manyanta, yana jin kunyarta hakanne yasa AJ ya sunkuyar da kai yana jin kunyar maganar ya ce "Daddy ne zai Mata? Yana faɗa yabar palon badan ya gaji da ganin yarinyar ba, sai dan kawai karya wuce gona da iri. Koda Muhammad ya zo yaji abunda AJ ya ce yaji daɗi amma hakan baisa ya yanke mata sunan da zaisaba saida ya kira AJ ɗin a ka tambayeshi ya ce "Daddy duk sunan da kaga dama ka saka mata. Daddy ya ce "A'a ba haka za'ayiba. Ganin Daddy yaƙi yarda yasa AJ ya ce "To a sa sunan Innah! Yana faɗa ya kama hawaye domin tunuwa da innar tasa. Haka kuwa a kayi Muhammad ya ma yarinya huɗuba da sunan Innah wato *HAJARA*. Haka a ka shiga sanarwa da ƴan uwa ta ko ta ina. Gaba ɗaya family Shek Kabir kabuga sunzo, harda Nusaiba da Sadiya. Haka suma gidan Malam Adamu suka tattaro gaba ɗaya. A can ɓangaren su Umar da Usman suma sunzo

33 / 37