Addininmu Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  S Reza Category :  Love

Chapter   11 / 37

30K to 33K   out of 109.2K words

da Sarah ranar da yakusa keta mata haddi. Afili ya ce. Kenan itama da nayi haka zanji wannan a zabar!? "Allah sarki Sarah ko yanzu tana wani hali na rashini!? gashi ko kiranta banyiba...ooo!! Allah sarki innah ta da Nana, kwana guda ban jikuba, ku kwantar da hankalin ku na kusa yin kuɗi, duk zaku huta, gida zan siya mana babba wanda komai sainasaka mana.

Haka dai yayi wankan tsarki kafin yayi a laula, sai kuma ya rasa kayan da zaisa, domin kuwa tsirara ya shiga toilet ɗin kuma gashi ba komai a toilet ɗin. Haka ya keta bin jikinsa da kallo, kafin ya buɗe baki ya ce "Amiƙomin kayana. Hajiya Babba dake zaune ta idar da Sallah tana jiran fitiwarsa. Ai kuwa ta saki dariya jin abunda yace. Tashi tayi ta ɗauki sabbin kayan da ta siyo musu jiya shida ita, domin kuwa ta shirya da safe zasu bar ƙasar. Ɗauka tayi ta nufi toilet ɗin, baiji tafiyartaba sai ji yayi an buɗe ƙofar an shigo.

*ABDALHA POV*

Shek Kabir kabuga ya ce "Maryam wato kin rainamu ko? Kina son mayar damu mutanan banza a idon al'ummar ko? Muna hani da ai kata bidi'a amma a dinga samunsa a gidanmu, me kike tunanin za'a ɗaukemu!? To daga yau kaman yanda yayanku ya ce...babu ke ba zuwa ko nann da bakin get, sannan wayar ma ai dama shine ya siya muku, to bani wayar? Ya miƙa mata hannu babu a lamar wasa, ai kuwa ta bashi har izuwa lokacin kuka takeyi. Sannan ya kalli Sadiya da Nusaiba ya ce "idan har naga wayar wata a hannuta to kuma waya ta haramta a hannuku. Yana kaiwa nann ya miƙe yabar ƙurin cikin ɓacin rai.

Yana fita Maryam ta faɗa cinyar Mommy tana kuka. Mommy ta tureta haɗi da cewa "Ai maganin wacce bata jin maganar uwarta, ai saida na ce karkije tunda yayanku baya so, amma kikace sai kinje. Abdalha ya miƙe ya kalli sauran ƙanyan nashi ya ce "Kunji abunda Daddy ya ce ba saina ƙara muku wani ƙarin bayaniba. Bai jira cewarsu ba yabar palorn Mommy na binsa da harara.

Yana fita Maryam ta sake fashewa da kuka tana cewa "Wannan ai san kaine me ya hana a karɓe wayoyin su Sadiya idan ba ni kaɗai a ka tsanab..."Kafin ta ƙarasa Mommy ta bige mata baki haɗi da cewa "Mune muka tsaneki ɗin?

Nusaiba harda Nura suka kwashe da dariya suna barin ƙurin , yayinda Sadiya ta zauna tana mata faɗa da kuma sanar da ita illar aikata bidi'a, dukda tasan Maryam ɗin tafita sanin komai abinda ya shafi addinmu, domin kuwa duk gidan bayan Daddy da Abdalha. To tafi kowa ilimi harda Mommy kuwa, saide Mommy ta faɗa mata saninn littafin addini wanda itama tayi amma ba kamar Momy ɗinba, domin kuwa har yanzu suna ɗaukar karatun litattafai a gurin Mommy ɗin, wanda sukeyi kowani dare, ranar asabar da Lahadi kuma harda rana, kasan cewar ba su kaɗai take koyarwar ba harda wasu daga cikin matan unguwar su. Ita kuma Maryam tana koyar da matan aure da ƴan mata karatun Alkur'ani mai girma kullum da daddare. Cikin ɓacin rai ta ce da yayar tata "Ya isa haka mlm saidinawa masu jiran ganin an min wani abu suyi dariya, to wallhi duk baƙin cikinku dani saide ku barni amma wallhi nida Zainab sai mun zama ƙawaye, kuma ku zuba ido kugani, abu kamar mutum yana gidan kaso. Taja wani dogon tsakiii mtsiiii sannan ta bar gurin. Mommy da yayar tata Sadiya suka bita da kallon mamaki.

Abdalha kuwa yana fita ya tararr da Daddy na jiransa a waje, take ya sanar dashi cewar yaje masallacin da shek ɗin yakeyin wa'azi duk ranar juma'a da yamma kafin ayi sallar magariba. Akan yaje yayi shi zaiyi tafiya zuwa Zariya sai kwana biyu zasu dawo. "Ok Abbalha ya masa sannan ya masa fatan dawowa lfy.

*ZAINAB. VOP*

Mama ce tare da Aisha da kuma Isa da malam tareda halifiyar Zainab ɗin da kuma namijin halifan nata. Mama ce ta ce "Mlm ku sake kiran numbar nata. "Mama wallhi numbar bata shiga kingani? Isa ya faɗa yana nunawa mama wayar. Malam ya ce "kumata uzuri baku saniba ko ta tsaya yin wani abunne. Hakanne yasa duk suka tsaya a wajan suna jiran ta. Wasa-wasa har ƙarfe shida da rabi, babu Zainab babu dalilinta. Nann fa hankalin su ya tashi. Gefe ɗaya kuma ga masoyanta mazauna unguwar au ( wato waɗanda suke unguwa ɗaya da ita) suna jiran dawowarta, domin kuwa sunji daɗin waƙar da ta sake ɗin. Hakafa har aka idar da sallar isha.

Take Isa ya shiga tunanin abunda ta ce masa ɗazu. Ai kuwa cikin yarda da abunda zuciyarsa ta ɗarsa masa ya ɗauko wayar sa, dama a recording take, take ya ce "Mlm inada tabbacin Abdalha Kabir kabuga ne ya sa ceta, kokuma ya sa aka kamata, kode ɗaya daga cikin su, domin kuwa tace ya turo ƙanwarsa ɗazu. Ai kuwa ya kunna musu yanda sukayi da ita.ai kuwa take suka yarda, amma Mama ta ce "Isa karkaje kayi abunda bakada tabbaci a kai, kaga baka da tabbacin abunda kake son ai katawa.

Take Isa ya fita bai tsaya ya saurari mama ba. Yana fita ya tararr da masoyan nata a ƙofar gidan su sai ɗaga hotunan Shehu nannsu haɗi da na Zainab ɗin, sannan sun kunna sabuwar waƙar sunayi domin kuwa har wasu sun riƙe waƙar. Baiyi wata-wata ba ya sanar musu da cewar Abdalh Kabir kabuga ya sace Zainab dalilin waƙar da tayi. Aikuwa nann take suka fara zaginsa, domin kuwa maganganun da tayi a cikin waƙar tamkar dashi takeyi, dama kowa yasan takun saƙar dake tsakanin su. Ai kuwa cikin daran labari ya bazu ko ina akan Abdllah Kabir kabuga ya sace Zainab saboda waƙar buɗɗiyar wasiƙa.haka dai duk inda ka shiga, dama abune na sanannun mutane, ɓangaren sada zuminta talabijin zancen a kayi.

Yayinda rikici ya ɓarke tsakanin ƙungiyoyi guda biyun, garin kono ko ina zancen akayi, wasu na cewa ai dama batada kunya, meyasa zata zageshi a cikin waƙarta, ai ƙwara haka. Yayinda wasu suke cewa ai dama ita bata taɓa masa martaniba shikuwa indai zaiyi wa'azi saiya saka da ita, to mezaisa dan tamasa ɗaya ya tsargu. Rikici dai mara dalili da tushe, abunda yaƙara raba kan sauran ɗan abunda ya rage daga ƙungiyoyi guda biyon. Wasu mazauna kabuga yan ƙungiyar Zainab ɗin suka haɗa kai domin zuwa gidan Shek Kabir kabuga ƙwato Zainab...✍️.📝
PAGE* 1️⃣6️⃣

.......Haka samari majiya ƙarfi ƴan ƙungiyar Zainab suka doshi gidan Shek Kabir kabuga, bakajin komai sai zage-zage da ikkirarin cewar sai an fito musu da Saiyadar su kokuma kowa yaji a jikinsa. Ɓangaran Isa kuwa, gaba ɗaya hankalin sa ya tashi, tun yana kiran numbar ta tana shiga har yakoma kira yaji ance tana kashe, nan fa ya shiga kiran duk wani babba da yake a ƙungiyar tasu, dama manyan malamansu yana sanar dasu cewar Abdalha Kabir kabuga ya sace Zainab saboda waƙar buɗɗiyar wasiƙa, kowa hankalinsa ya tashi, haka dai kowa ya kasance cikin mamakin lamarin har zuwa washegari.

*ABDALHA POV*

Yana barin gurin Daddy ya koma gidansa ya shirya ya tafi gurin da zai gabatar da wa'azin. Haka ya gabatar da wa'azi sosai wanda yasa al'ummar dake gurin kowa ya jinjina masa domin kuwa wa'azin a kan iyaye matane yanda suke sakaci da yaransu, harda mazan ma. Yayinda wasu daga ciki suke mamakin sa ganin komai idan zaiyi irinna mahsifinsa ya keyi harta muryar su, idan kana sauraron karatun su, bazaka taɓa babbace muryar Shek Kabir kabuga da kuma ta ɗansa Abdalha Kabir kabuga ba. Saide ko idan kana kallonsu. Kaman dai yanda yasaba yauma bayan ya gama wa'azin saida yayi tsokaci a kan ƴan waccer ƙungiyar, musammamma waƙar da sukayi ɗazu, domin kuwa tsaf yaji waƙar har ƙarshenta. Saida ya caccakesu sosai kafin ya yi addu'a ya rufe karatun.

Gidan su ya nufo daniyar zuwa suyi magana da mommy. Kaman yanda yayi tsakanin, hakane kuwa ya faru, domin kuwa yazo ya samu Sadiya ce ke koyawamatan da Maryam ke koyawa karatu. Cikin faɗa ya ce "Ina Maryam?

"Wallhi yaya anyi-anyi tazo ta koya musu karatu amma tace wai bazatayi ba.

Abdllah ya ce "Ina take? Yayi maganar cikin tsananin ɓacin rai.

"Tana cikin ɗakinta ko abinci taƙici, ko fitowama taƙiyi. Cewar Sadiya tana kallon yanayin yayan nasu. Da sauri Abdllah yayi ɗakin Maryam cikin zafin rai!. Ya kai hannu zai buɗe ɗakin yaji Nusaiba ta kwalla masa wani uban kira har bakinta narawa, ita kanta Maryam da take cikin ɗaki tana karatu saida ta tsorata domin kuwa da ƙarfi takira sunan nasa. "Yaya Abdalha!!!!!!!!!.

"Cak ya tsaya cikin ruɗewa domin kuwa yasan babu lafiya, itama Mommy da take ɗaki tana koyawa Nura karatu saida ta fito. Hakama Sadiya da ita da ɗalinbanta saida suka tsorata. "Da sauri ta ƙaraso gurin da yayan nata yake hannunta na rawa ta nuna masa abin da tagani yanzu ana yayatawa.

Karɓa yayi yana dubawa, dai-dai mommy da Maryam duk sun iso gurin. Suma kallon wayar sukeyi suna duba abinda ke cikin wayar. A kiɗime Mommy ta kalli Abdalha wanda ya kafama wayar ido yana kallo. Tabbas bazaka gane halin da yake cikiba, domin kuwa babu alamar yaji tsoro ko mamaki, ko firgici.

Mommy ta ce "Abdalha me nake gani? Shin da gaske kaine ka sace ta!? Mommy tayi maganar bakinta na rawa kamar zatayi kuka ba. Cikin zuciyarta ta ce "ya Allah karka nunamin wannan ranar. Maryam kuwa wani irin dariya ta bushe dashi tana cewa "To ai basai an tambayaba, ninasan yaya son Zainab yakeyi kuma bazai iya faɗa mataba shine ya sace ta, ai kuwa abun zaibada citta, kunga kafin ya dawo da ita soyayya tayi nisa. Ta ƙarasa maganar tana mayarwa da Nusaiba wayar sannan ta juya zata koma ɗakinta.

*NANA* *POV*

Cikin mamaki ƴansanda suke kallonta jin yanda tayi maganar cikin ihuuu. Wannan ɗan sanda da ta kira da wannan ihune ya nufo gurinsu cikin ɓacin rai, yana zuwa ya wanke mata fuska da mari, kafin ta ankara ya ƙara mata, wanda yasa Nana faɗawa jikin Innah ta saki wani kuka mai ƙarfi, itama Innah kuka takeyi. Cikin muryarsa da suke tsananin tsoro ya ce "Dan uwarki ko ance miki nann gidan ubankine da zaki dinga magana yanda kikeso, yana maganar yana buɗe gurin da makullin hannusa ya tura ya shiga, ya ɗago Nana daga jikin Innah ya ce "Wato ke mara kunyar ko? Banace karna ƙara jin muryarku anann ba? Duk abunda ya ke cewa inna bataji domin bada Hausa ya keyiba. "Kunci sa'a ku matane amma Walhi da sai kunsan kun shigo nann. Yana kaiwa nann ya turata ta faɗi kafin ya harari Innah yana ficewa daga gurin.

Haka Nana taci kuka har tana ciwonkai, sannan ga yunwar da ta ƙara rikice mata ciki. Haka suka zauna a gurin har, bayan sallar la'asar. Izuwa wannan lokacin kuwa har Nana ta daina kuka tsabar azabar yunwa, ita kuwa Innah kwanciya tayi tana jin kamar kayan cikinta zasu zubo, idonta a kafi tana kallon sama. Suna cikin haka sukaji ana kiran sunan Nana.

"Nana... "Nana... Nana? Dukda cikin rawar baki yake maganar da kuma sauri, amma hakan bai hana Nana gane muryar waye ba. Tana ji amma ta kasa magana jitakeyi kamar tana magana amai ne zai zibo, ita kuwa Innah batasan ma me a ke cikiba. Da sauri Salis ya ce da ɗan sanda ya buɗe masa gurin da sauri, amma police ɗin ya ce "Ai ba haka sukayiba, sunyi a kan kawai zai gansune ya tafi, da sauri Kamal ya ce da ɗan sanda Please dan Allah ka taimaka baka ganin halin da suke cikine? Police ɗin zaiyi magana SALIS ya ƙara zaro kuɗi ya miƙa masa haɗi da cewa Please ya buɗe.

Ai kuwa take ya buɗe musu, Salis ya yi kan Nana yana kiran sunanta, yayinda Kamal kuma yake ɗaga Innah. Ganin suna ƙoƙarin fita dasune yasa police ɗin cewa "Lfy kuwa ban gane ba? "Asibiti zamu kaisu baka ganin yanayin sune? Cewar kamal yana kallon police ɗin. Wani irin zaro ido police ɗin yayi yana cewa "Kai! Kai! Kasan kuwa me kake cewa? To wallhi idan har nabari kuka fita dasu to nabar aikina kenann, yanzu ma lokacin ku ya ƙara kuzo ku fita karku jamin masifa, yana faɗa yana jawo ƙofar zai rufe.

SALIS da Kamal sunyi yin duniya amma ya ce bazasu tafi dasuba, mutanan da sukayi sata, cikin mamaki suka ce "sata!! Police ɗin yaga alamar fa suna son jawo masa masifa ne, nan danann ya rufe gurin yana cewa idan baku bar gurin ba kuma za'a haɗa daku. Da kyar dai police ɗin ya barsu a kan zasu dinga kawo musu abinci, safe rana dare, shima a kan zasu dinga biyan sa. Haka Salis suka yarda, take sukaje suka siyo musu abinci da magani suka kawao musu.

*A.J .HAJIYA BABBA* *POV*

Aruɗe ya kalleta domin kuwa ta tsorata shi, da sauri ya karɓi kayan da take miƙomasa ya juya baya yana sakawa ransa a ɓace. Saida ya gama sosai kafin ya buɗe ƙofar toilet ɗin ya fito yana wani haɗe fuska. Kan abar sallar da yaka tayi shima yaje ya tada sallah ko kallon inda take bayayi. Bayan i idar ne ya ɗaga hannu yana addu'a wanda ni (S REZA bansan me yake roƙaba)

Bayan ya idar da addu'ar ne ya kalli Hajiya Babba cikin haɗe fuska ya ce "ina wayata?

Hajiya Babba ta tasu tazo har gabansa sannan ta ce "Good morning angona, da fatan ka tashi lfy.tana faɗa tana ƙoƙarin zama a kusa dashi.

Cikin sauri ya miƙe tsaye haɗi da cewa "Please dan Allah kibani waya wallhi Innah ta zan kira ban saba kwana ba tare da suna kusa daniba, Please dan Allah kiyi haƙuri karki ce wannan ma yana cikin kwangilar mu Please? Aj ya ƙarasa Maganar kamar zai sa kuka.

Hajiya Babba kuwa wannan abun da yayi sai yamata kyu, domin kuwa tana son ganin namiji na shaƙwaɓa, abun burgeta ya keyi. Cikin kwantar da muryar, kamar wata budurwa kai ka rantse da Allah cewa ba itace ta haifi laɗifa da Salis ba ta ce "Haba mijina acikin wannan asubar zaka kirasu ai sai kasa suyi tunanin ko ba lafiyaba, kabari zuwa safiya sai ku gaisa kafin mu tafi, Please yanzu kaje ka huta nasan a gajiye kake, Please, ta ƙarasa tana kawar da hannusa da ya miƙo mata tin ɗazu a kan ta bashi wayar.

Tabbas da alamar dai AJ bai gane me hajiya take nufi da cewar kafin su tafiba, shi yayi tunanin ko kafin su tafi gidane. Hakanne yasa ya kasa cewa komai domin kuwa kewar su Nana ce ke damunsa, gakuma sabon al'amari da yakeji a tare dashi yanzu tsakanin sa da Hajiya Babba.

Anann kan daddumar ya kwanta yana tunanin abuwa masu yawa wanda zaiyi idan ya gama cinye wannan kuɗin. Sai gani yayi itama tazo kusa dashi ta kwanta tana haɗe fuskokinsu, ai da sauri ya miƙe zaiyi magana ta ce "A cikin sharuɗanmu babu raba shin fiɗa mutuƙar zamu kwanta tare.

AJ ya ce "Amma ai baki faɗa hakaba, kuma ai yanzu ba barci zanyiba, kawai zan hutane. Ya faɗa yana tuno suman da yayi ɗazu. Ta ce "Ai na faɗa maka cewar zamu kwana duk lokacin da naso, sannan kuma ai koda ba barci zakayi ai ni matar kace ADDINIMU bai haramtaba, ladama fa zaka samu.

Ya ce "Walhi kaina kemin ciwo. Ta ce "Aiya sorry muje mu kwanta babu abunda zai faru. Haka yana ji yana kallo ta ɗiorashi a kan gado sannan itama ta hau ta ja musu bargo, suka faɗa barci mai daɗi irin na miji da mata. AJ gaba ɗaya a takure yake domin kuwa duk ta manne a jikinsa, shikuwa duk sai yaji ya kasa cigaba da barcin.

Misalin ƙarfe bakwai da wasu ƴan mintina yaji alamar tana ƙoƙarin tashi, sai ya rufe idon sa domin karta gane cewa baiyi bacceba. Tashi tayi tana sauƙe idan ta a kan fuskarsa sai taga ya ƙara mata kyu. Miƙewa tayi ta saka hijab sannan ta fita. Bayan kamar minti goma ta dawo lokacin shikuma yayi dube-dubensa ko zaiga ina ta ajiye wayar sa amma ya rasa. Tana shiga saiga ɗaya daga cikin ma'aikatan hotel ɗin reƙeda tire na abincin su. Bayan sunci ne Hajiya Babba tace ya shirya da huri zasu tafi. Haka AJ bai ƙara mata zancen wayarsaba ya shirya cikin shigar wasu sabbin kaya da tabashi. Fita ta sakeyi ta kira Salis ta sanar dashi cewar wani aiki ya kamata saboda haka bazata dawo yauba, ya kula da laɗifa tare zasu zauna da AJ amma bazasu huce sati ɗaya ko biyuba, tana jin yana tambayar ina AJ amma ta kashe wayar damin kuwa batason komai ya shiga tsakanin ta da angonta.

Haka suka fito daga cikin hotel ɗin suka shiga motar da sukazo da ita sukaje gidan malamin da ya ɗaura musu auran suka ajiye motar. Cikin mamaki AJ ya ce "Bada motar zamujeba?

"Cikin basarwa ta ce "Ina zamuje da motar?

"Shima cikin ƙosawa ya ce "Gida mana ko a motar haya zamu tafi?

"Sai a lokacin Hajiya Babba ta tuna da cewar a shefa bata sanar dashi da maganar tafiyar bafa. Juyowa tayi da kyu ta kalleshi sannan ta ce "Ƙasar zamu bari amma ba nisa zamuyi muna cikin Africa ina so mu samu Kamar sati biyu ne kafin mudawo kaga lokacin mun ci amarci sosai kaima idonda ya buɗe.

Cikin mamaki da rashin tsammani AJ ya ce "Tafiya waje sati biy!! Ina bazan iyaba, tayaya zanyi sati biyu batare da naga Innah ta da Nana ba, no ai babu wannan tsarin a cikin sharuɗanmu? Kuma koda da wannan bazan iyaba, Ni no no no, ya ƙarasa yana kirkiza mata kai haɗida jadabaya kamar zai ruga da gudu.

Hajiya Babba tayi shiru!!! Sai zuwa wani lokaci ta kalleshi cikin murmushi ta ce "Shekara ɗayane kwangilar mu ko? Aj ya ɗaga mata kai alamar eh.

Hajiya Babba ta ce "To idan har ka yarda muka bar wannan ƙasar har mukayi sati biyu to idan mun dawo gida, wata biyar zamuyi shikenan kaci kuɗinka miliyoyin hamsin. Ina jiranka yanzu, idan kuma baka yardaba to muje gida muyi shekara ɗaya ɗin. Ta ƙarasa tana sakar masa murmushi!!!!....??




PAGE* 1️⃣7️⃣

........*A.J* Shuru yayi yana kallon

11 / 37