Addininmu Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  S Reza Category :  Love

Chapter   2 / 37

3K to 6K   out of 109.2K words

sosai ga yunwa dake addabar cikinta ga tsoran abunda Daddy zaimata in ya kamata, domin kuwa tasan da cewa ta kamu.

Tana cikin hakane taji dawowar su, harda Samuel da Daddy harda Mommy, da sauri ta kwashe kud'in ta mayar gurin da ta d'auka sannan ta tashi ta koma 'kar'kashin gado ta sake 'boyewa.

Ai kuwa cikin sauri Daddy ya shigo d'akin yana shiga ya tsaya cak yana mai bin d'akin da kallo...sai ya nufi gurin da ya ajiye kud'in yana mai bud'e abun ya zubawa kud'in ido kamar mai son gano wani abu, sai Kuma ya koma bakin kofar d'akina yana dubawa kodai bai rufe da Kyu bane, domin kuwa Tabbas an shigo d'akinnan. Kayansa ya cire ya rage daga shi sai gajeran wando na sojoji, Wanda Zahrah tana ganin sa a haka ta rufe ido cikin tsoro, toilet ya fad'a ya rufo 'kofar, ai kuwa yana shiga itama ta fito, har zata fita sai kuma ta dawo da baya ta bud'e gurin ta kwaso kud'in ta saka a cikin jins d'in dake jikinta dama ya katseta, sannan tayi hanyar barin d'akin Amma ta sake jin 'kofar a rufe.

Cikin rekicewa ta saki wani ihuuu d'an 'karami amma tayi saurin toshe bakinta da hannu, sai ta hango kin d'akin a kan kadonsa gurin da ya cire kaya, nann ta d'auko ta bud'e, sai ta dawo ta ajiye da niyar fita sai daji alamar shigowa d'akin, ai da sauri ta koma bayan 'kofar ta 'boye ai kuwa Mai shigowar Yana tura 'kofar yashiga ciki yana shiga ita kuma ta sand'a ta fita, ta nufi d'akin ta cikin rikicewa, tana shiga ta boye kud'in sannan ta saki a jiyar zuciya.

Samuel kuwa, yana shiga ya samu gefen gado ya zauna Yana jiran fitowar Daddy, ai kuwa yana zama Daddy na fitowa. Cikin tsananin mamaki da firgici Daddy ya ke kallon Samuel ya ce "Samuel what are you doing in may room? Kafin Samuel yayi magana ya ga durowar kud'in abud'e ga kuma 'kofar d'akin nasa ta ciki ya rufe Amma yaga Samuel aciki gakuma kofar a bud'e.

*ABDALHA* *VOP*

Zaune suke agaban Mommy dukkanin su, abdalh Maryam da Sadiya da Nusaiba sai autansu nura... Kallon su tayi kafin ta ce "meya had'a ka da Maryam? Cikin tsananin jin haushin abun da Maryam d'in tayi ya ce "Mommy wai wannan yarinyar d'an bidi'a zata kawo mana gida a matsayin mijin aure! Saboda ita mara kunya ce, shine harda cewa Wai in Abba yazo zata sanar masa, Mommy ta ce "Wai ni abdullha kaida babanka bansa me kuka d'auki mutanan ba, sumafa musilmai ne kamar ku, Allah mu d'aya annabin mu d'aya, littafi d'aya muke karantawa wato ALQUR'ANI mai girma, kaga kenann ADDINIMU d'aya, to meyasa don an d'an samu rebewar Kai sai ku dunga ai batasu kuna kafurtar dasu!?

Kafin wani yayi magana sukaji ana cewa "Mu ba d'aya muke dasuba, domin kuwa mu bamuyin abun da Annabi Muhammad sallalahu a w s, baiyiba Kuma Allah baice a yiba, saboda haka, nidai zuria'a ta bazasu had'a jini da suba, cewar Abba yana shigowa d'akin. Kafin kowa ya sake mgn Nusaiba ta ce "Ni fa wallhi bana musu kallon musilmai domin kuwa wani lokaci in sukayi wani abun Kamar basa karanta ALQUR'ANI, .

Sadiya ma ta ce "Ni Wallhi tinma ba wannan Zainab Ambato d'inba gaba d'aya 'kasidun ta babu wani tsari da ma'ana amma a haka zakika kowa Zainab Ambato Zainab Ambato. Mayarm ta ce...

"Ashede kina jin 'kasidar tata da har kika san babu tsari, kafin kowa yayi magana Abba ya ce "Andullahi meya faru? Abdullha ya ce "Abba Maryam ce tazo da wani yaro Wai shi takeso kuma d'an bidi'a ne. Daddy kuwa dama yagama sakarwa abdullha ragamar gidan duk abun da ya yanke a kan 'kannennasa to yayi. Nann shima ya tabbatar mata da cewa Babu ita bashi, in auren takeso ta nemo mari'kin sunna shi zai aura mata, Yana gamawa ya bar d'akin ya nufi nashi d'akin dama yanzu ya shigo.

Mommy ta kalli Maryam ta ce "mamana ki rabu dashi tindade Abbanku da yayanki basaso kinji? Kafin ta Kara'sa Nusaiba ta ce "Toma mommy in banda zubar mana da kima yaza'ayi ta kawo mana dan la'ilo tace yazama suriki a gidannan.

Itama Sadiya ta ce "Allah da nagan shi da sai na gaya masa maganar da bazai manta da itaba, "Ai kuwa kema da namiki abunda bazaki manta da niba. Ina ruwanki da saurayina? Duk abun da zakuyi ku tsaya a iya matsayinku karku shiga gonar da ba takuba domin kuwa ba tsoran aji kanmu daku nakeba. Maryam tana kaiwa nann ta fito da wayarta ta Kuna qasidar Zainab Ambato mai taken *GANI ASO* , tabar su a gurin ri'ke da baki.

Mommy ta ce "Nace kudaina shiga hankarta yanzu tana kan ganuwar girman balaga tanajin kanta yanzu dai-dai daku saboda haka kubarta tayi raruwarta, Kuma karku fad'a wa yayanku tana jin 'kasidar Zainab Ambato kunji? ceke da takaici Sadiya ta ce "Yasin Mommy Maryam ta rainamu, ace agidannan ana jin kad'e-kad'e Kuma kice Kar a fad'awa yaya, shida yakeyin wa'azi akan kid'a babu kyu sai Kuma a samu a gidan sa, ai dolenema yaya yaji wannan zancen, tana kaiwa ta tashi fuuu tabar d'akin izuwa nata d'akin.

Mommy ta ce "Allah dai ya sa mudace, Kuma Allah ka barmu a musulumci kuma Allah ka had'a kan al'ummar musilmi na duniya Baki d'aya. Nusaiba ta amsa da amin.

*ZAINAB* *VOP*

Kallon yayan nata tayi kafin ta ce "Wai kuwa kasan gobe zan bogowa wancan banzan wata 'kasida mai harshen damo? Isa ya ce "Nifa Allah yaron mamaki yakebani shifa burinsa Wai ace shi ma malami Kuma wallhi bai Kai ya had'a kansa da keba, yanzu duk Wanda kacewa Zainab Ambato, d'an izalar da ma Yan 'dariqar bawanda bai San dakeba, shifa, in kace... Abdalh in dai Baki had'a da sunan baban saba Wallhi za'a ce waye haka, Koda acikin masu d'an gelallan wandonne, take suka bushe da dariya dai-dai lokacin MLM wato babansu ya shigo.

Kamar yanda d'abi'ar su take ta girmama duk wani babba ta hanyar rusunawa har 'kasa sugaishi haka yanzuma har 'kasa suka rusa suka gaida MLM. Bayan ya amsa ne ya saka musu albarka sannan ya ce "Zainab d'azu su Alhaji Bashir sunce ranar JUMA'A suna gaiyatarki zaki musu majalasi a gidansu zai aurarr da yarinyarsa. Kuma na amince masa, ina fatan dai kinada lokaci?

Cikin girmamawa ta ce "to MLM ai koda bani da lokaci tinda suka biyo ta hannun ka ai zan samu lokaci. MLM yayi mata godiya sannan ya ce "Saide wani hanzari ba guduba... Gidan Alhaji Bashir d'in jikin gidan wannan mara kunyar yaronnanne 'dan gidan Shek kabiru. Take isa da Zainab suka had'a baki gurin cewa, Abdalh shek kabir kenann kake nufi? MLM ya ce "eh wannan. gaskiya yaron bashi da kunya ahakan ya kurarin su malamaine Amma suna cin mutuncin mutane, nasan yanda kuke dashi saboda haka kisan abun da zakiyi. Zainab ta ce "to MLM nagode ranar JUMA'A ko? "Eh ranar JUMA'A.

Sannan ta tashi ta bar d'akin ciki da jin dad'in haka, Isa dake bayanta ya ce "Ashe a gurin za'a fara jin sabuwar 'kasidar kenann? Ya cigaba da cewa "ya sunann gasidar? Itama cikin tinani ta ce "Sunann ta bud'ad'd'iyar wasi'ka...📝



*PAGE0️⃣3️⃣*

.......Cikin mamaki Isa ya kalleta ya ce "Bud'ad'd'iyar wasi'ka Kuma? Zainab ta ce "Eh dama ai nace maka 'kasidar mai harshen damo ce saboda haka kaide ka saurari fitowarta kasha mamaki. Isa ya tsaya yana mata kallon mamaki domin kuwa yasan 'kanwar tasa Allah ya bata ilimi ga dogon tinani, in har ta bugo 'kasida tofa sai tayi dad'i, haka dai shima ya tafi cike da son jin wannan sabuwar'kasidar.

*A J. VOP*

Mai Okada bai sau'keshi a ko inaba sai 'kofar gidan su Salis. Bayan ya sallami mai mashin d'in ne ya nufi bakin get d'in gidan cike da kwarin gyiwa, yana zuwa ya bubbuga cikin 'kan-'kanin lokaci mai gadin ya bud'e. kafin A J yayi magana mai gadin ya ce "Kaine AJ ko? Da sauri AJ ya ce "Eh nine.

Ai kuwa take ya bashi hanya had'i da cewa "yace in kazo ka shiga ciki. Tin daga harabar gidan AJ yake sake bin gidan da kallo sai yaga gidan kamar ya 'kara kyu, kamar ba gidan da suka zo shekan jiyaba, sai da yaje 'kofar palorn kafin ya danna abun da yaga Salis ya danna wancen lokacin kafin ya nemi guri ya tsaya kamar dai yanda sukayi wancen karan d'in.

'Yar aikin gidan ce tazo ta bud'e kamar wancen lokacin, yana shiga ya hango Hajiya zaune a d'aya daga cikin kujerun dake cikin palorn, da sauri AJ ya fara kwasar gaisuwa. Hajiya ta amsa sannan ta ce "Tashi daga 'kasa ga guri ka zauna, babu musu ya zauna yana kallon hanyar da zaiga Salis ya fito.

Hajiya ta ce "Salis baya nann dama nice na sa ya kiramin kai, tin ranar da na ganka agidannan kaida my son naji ina son in d'aukeka wani ai ki mutu'kar zaka iya? Cike da mamaki AJ yake kallon hajiya kafin ya ce "Hajiya ni in dai zan samu kud'i kuma ADDINIMU bai hana ba Wallhi ko menene zanyi. Cike da jin dad'i hajiya ta ce "Ok tom kazauna cikin shiri nann da wani lokaci zan fad'a maka wani irin aikine zakayi, kuma zaka samu kud'i sosai domin kuwa in har ka yarda to daga ranar bakai babu ta lauci.

Jin abun da hajiya ta ce ne yasa AJ cewa "To hajiya a fara sanar dani aikin mana tin yanzu sai na fara shiri? Hajiya tayi dariya tana kallon sa cikin burgewa ta ce kar ka damu yanzuma kanada wani babban kaso daga cikin kud'in aikin na ka ina zu. Hajiya ta me'ke tsaye ta nufi d'akin ta, shikuwa sai bin ta yake da kallo har ya daina ganin ta. Ai kuwa take ya saki wani dariya yana cewa "kai Yasin AJ ni na daban ne, irin wannan farinjini hk! Yana cikin hakane hajiya ta dawo. Ta mi'ka masa bandir din yan dubu-dubu guda d'aya wato dubu d'ari kenann.

Cikin rikicewa AJ ya ce "Haji hajiya Wann wann Wannan nawaye?

Hajiya ta ce "Ko baka sone?

"Ina so wallhi inaso sosai makuwa. Kai hajiya na gode sosai Allah ya saka da alkairi. Amma hajiya wannan wani irin aikine?

Hajiya ta ce "Aikin bashi da wani wahala kaide ka zauna cikin shiri. "Ai kuwa hajiya a shirye nake wallhi. Haka AJ ya bar gidan cikin tsan-tsar farin ciki, kasuwa ya fara zuwa ya musu siyayar kayan sakawa shida Nana da innah kafin ya tsaya a gurin mai kaza ya seyo musu ko d'aya, yaje ya siyo musu yourgot kafin ya nufi gida cike da farin ciki.

*ZAHRAH*. *VOP*

Fitowa da kud'in tayi ta girga taga dubu d'ari harda tara, aikuwa ta bud'e baki da hanci tana mamaki me yasa ta d'ebo da yawa, take ta saka a cikin jakar school d'in ta, sannan ta shiga toilet ta watsa ruwa gamida sau'ke abun da ta tara a cikin ta tsabar far gaba. Riga da wando ta saka na Adidas sannan ta nufi kiching domin samun abun da zata ci, tana shiga tayi karo da Mommy a ciki tana had'a musu abincin yamma.

Cike da mamaki Mommy take kallon ta, cikin yaran su Mommy ta ce "Daga ina kike?

"Mommy nadawo tin d'azu zan shiga gida naga kun rufe gidan shine na koma sai yanzu nadawo. Mommy ta bud'e baki zatayi magana taji muryar Samuel a d'akin Daddy yana ihuu ai kuwa suka nufi gurin da gudu. Cikin fushi Daddy ya ke cewa "I see wer is my money? Samuel na kuka yana cewa "Daddy banine na d'auka ba Allah nima yanzu na shigo.

Mommy ta shiga tsakanin su sannan ta mi'kar da Samuel ta ce

"Samuel what happened?

"Mommy I don't no.

Ta juya gurin Daddy ta ce "What happened?

Cikin fushi Daddy ya sanar da ita komai, sannan ya d'ora da cewa... "Dubu d'ari harda wani abufa ya d'auka.

Mommy kuwa ta ce "Amma kuma ai tare da Samuel muka shigo gida, kuma kace ta ciki ka rufe 'kofar d'akin naka, to tayaya Samuel zai iya shiga? Kafin Daddy yayi magana Zahrah ta ce

"kokuma Daddy bai rufe 'kofar d'akin da kyu bane shine Samuel d'in ya shigaba.

Ai kuwa Daddy ya ce "Yes of course hakane ma. Samuel ya harareta yana jin kamar ya kamuta ya fara tattakata. Mommy ta ce "No inda shine da bazai zauna a d'akin ba tafiya zaiyi.

DADDY ya ce "Ya tashi ya dawo masa da kud'i kafin yasa sojojin waje su karkaryashi, Samuel de sai kuka yakeyi, shikuwa Daddy ya kafe akan dole shine ya d'auka.

Zahrah kuwa take taji ta daina jin yunwar tsabar tsoro, Daddy baya dukansu sai sun kaishi bango, yanzu da ita ya kama haka zaitama wannan dukun! Sai kuma ta fara tinaninn shimafa Samuel d'in tasan dole sukwaso riki dashi in ya warke. Take Kuma ta tuno da rabin ran nata tana jin in ta kai masa wannan kud'in ai za'a daina renashi tin da zai siya babbar waya. Take ta nemo number sa ta ai ka masa da Kira.

*ABDULLHA* *VOP*

Da sauri ya 'karasu gurin Abba yana mai d'an du'kawa kad'an ya ce "barka da yamma Abba gani?. Cikin sanyin murya da ta Saba da karanta ALQUR'ANI mai girma Abba ya ce "Abdullha kaga yanzu mutane suna ta magana a kanka akan zaman ka haka, kasan ba mutum baya cika mutam har sai ya ajiye iyali, yanzu fa kai ba 'karamin mutum bane, duk in da kashiga a 'kasar nann ansanka, kai harma wasu 'kasashien, kuma kaga kai ne mai yiwa mutane wa'a zi a kan aru'ke sunna a bar bidi'a, Amma kuma kai bakayiba shin hakan zai yu kuwa?...

Saboda haka abun da nakeso dakai shine kafitar da wacce kakeso ka yi sure domin al'umma su sake ganinn ka da kima. Abdullha ya dubi mahaifin nasa ya ce "Gaskiyane Abba, amma Abba duka-duka shekarata nawa da har zan fara maganar aure? Shekara tafa 26 zuwa da 27 Amma Zan fara zancen aure. Abba ya ce "Abdullha ka duba matsayin ka ba shekarunka ba, yanzufa mutane masu shekara. Arba'in ma girmamaka sukeyi, saboda haka nidai yanzu umarni zan baka akan ka fitar da wacce kakeso a cikin wannan shekarar.

Abdullha ya ce "Tom Abba tindadai kace umarnine in sha Allah Zan fitar. Abba wato shek kabiru kabuga, malimin sunna wanda yayi suna wajan ru'ko da sunna a fad'in duniya, wanda tin yaronsa wato abdullha Kabir yana 'karami yake tafiya dashi duk in da zashi kuma yake ja masa a'ya awajan wa'a zi. Har take yanzu shima abdullha yazama jigo ga al'umman dake tare da ma haifin nasa. Abba ya saka masa albarka sannan ya tashi ya tafi.


Abdullha kuwa gidan sa ya nufa yana shiga ya fad'a toilet yayi wanka sannan ya zauna ya fara rera karatun ALQUR'ANI mai girma cikin muryarsa mai sanyin dad'i, saida yayi izufi biyar (5) sannan ya shafa addu'a kafin ya zauna ya shiga tinanin maganar Abba...

To ni yanzu daba soyayya na keyiba ina ni ina wata budurwa! Nann take Aisha ta fad'o masa a rai, amma yayi tsaki yana cewa, wannan yarinyar batada kamun kai, haka dai ya dinga tufka da warwara, harma yayi banza da maganar ya kama har kokin gaban sa. Take yatina da cewa abokin safa ya gaiyace shi gurin bikin sa, amma ba wa'a zi zaiyiba zaije gurin walimar ne, walimar da uwar amaryar ce ta shirya, haka ya tashi ya shirya domin halartar gurin, kafin lokaci ya 'kure, domin kuwa abdullha yana kiyaye Al'kawari.

*ZAINAB*. *VOP*

Washe gari ta shirya tsaffff domin zuwa wani taro biki da a ka gaiyaceta zatayi qasida a gurin, Saida taje gurin Mama suka gaisa, sannan ta ce "Mama ina Aisha ne? Mama ta ce "Sun fita da Isa wai zata rakashi kasuwa. "Ok tom mu zamu je majalisi sai an jima zamu dawo, nann take Mama ta saka mata albarka sannan tamusu fatan nasara kafin ta fita, tabi d'akin mlm shima yasaka mata albarka kafin ta fita.

Tana zuwa waje taga halifiyar tata wato Maryam wacce duk wani taro ko mauludi in an gaiyaceta to tare suke zuwa, wani lokaci ma in Bata da time ita take turawa. Maryam tazama tamkar 'kawace ga Zainab sannan kuma yarinyar ta. In ana cikin hadaya na yabon Annabi Muhammad sallalahu a w s, girma take bata sosai, in kuma a zahirine ko a gida, zaka gansu acikin wasa da dariya.

Haka suka tafi cikin wasa da dariya. Suna isa gidan, matar da ta kirata tazo da gudu ta rungumeta tana kuka cike da mamaki wai yau gata ga Zainab Ambato. Ta ce "Zainab Ambato wallhi na kasance duk anguwarmu nafi kowa son ki da 'kasidunki, domin kuwa duk wata sabuwa gasidar ki in tafito sai na d'auko ta, tin kafin yarinyata ta samu mijin aure nayi Al'kawarin sai na gaiyatoki walimar auran kuma, gashi Allah yayi. Matar harda kuka, yayin da yarinyar matar ma tazo ta rungumeta sunata saka mata albarka.

Ita kuwa Zainab Ambato me take in banda mamaki cikeda farin cikin ganinn irin wannan tsan-tsar soyayyar. nann fa al'umma maza da mata suka fara murnar ganinn ta sai zuwa sukeyi ana hoto.

Da kyir aka samu a ka barta ta fara gabatar da majalusinta. Nann fa duk 'kasidar da ta fara sai kaji muryoyin al'umma tamkar sune sukayi, haka zatayi shiru al'umma sunayi kuma basa mantuwa, uwar amarya kuwa babu kunya ta ce yau ranar farin cikin tane, tafara rera 'kasidar Zainab Ambato kamar ita tayi. Ana cikin hakane a kazo kan 'kasidar da ta saka kwanannan wato *GANI ASO*. zokaga al'umma. Ana cikin ha sai ga ango da abokansa...

Angon shi kad'ai ne sai mutum biyu acikin abokannasa... Kana ganinn su kaga malamai aikuwa nannn al'umma suka hango Shek abdullha d'an gidan Shek kabiru kabuga. Nann fa suka fara mamakin mai ya kawoshi nann bayan bayason wannan wa'ke-wa'ken, tin daga nesa suka fara jin muryar mutane ana jin wa'kar Gani aso, dai-dai gurin da take cewa, ( *narantse da ilahumma ma'aiki bani da wani wanda nakeso ya maa'aiki Allah shine masanin

2 / 37