Addininmu Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  S Reza Category :  Love

Chapter   19 / 37

54K to 57K   out of 109.2K words

yayinda karatun Shek Kabir kabuga ke tashi a cikin motar, kallon yaransa yayi ya na tuna ranar sunan sa saida Shek Kabir kabuga yazo garinnan, murmushi yayi ya na ƙara godewa Allah da ya sa ya gane gaskiya, kuma ya na ƙara roƙon Allah a kan ƴan uwansa. Misalin ƙarfe huɗu na yamma bayan ya taso daga masallacin da yakeyin sallar juma'a, ya na cikin tafiya yaga an sha gaban sa, kafin ya ce wani abu har sun shaƙa masa wani abu sun ɗauke shi da ga cikin motar sun kunna ma motar huta, sannan sun ɗauki wayar sa sun yar da ita a gurin sun tafi dashi. Koda mutane suka zo gurin wutar taƙi mutuwa dole saida ta cinye kafin a ka shiga leƙawa. Bayan an ga wayar sa a gurin ne a ka ga numbar Hajiya Babba sai kira ta ke, sai kawai aka sanar da ita cewar mijinta yayi hatsari motar ta ƙone.

Tashin hankali wanda ba'a saka masa rana kenann. Aisha tayi kuka tayi kuka sosai har sai da ta kwanta jinya. Nan fa Elixa da Titi da Daniyel suka zo har gidan ta a kan wai sai ta fito musu da ɗan uwa, dama ai an ce musulmai ka she mutane sukeyi. Abu fa kamar wasa har saida a kaje kotu, Aisha ta yi kukan rashin kowa na ta, ga ar ziƙi amma sun tashi a babu, domin saida ta ƙarɓi hukunci mai tsanani wanda saida tayi she kara tana jin yar kanta, bayan ta fitone kuma ta ɗauke ƙafa da su, domin taji zafin abinda suka mata. Ɓangare ɗaya kuma bata yarda cewar mijinta ya mutu ba, domin bataga gawar sa ba, kuma jikin ta na bata yana raye amma bata da hujja, amma dai ta ce idan ma ya mutu to ƴan uwansa ne suka kashe shi, tin ta na jiran tsammani har she karu suka jaa, sannan bata taɓa sanarwa da yaran ta komai ba saida wani abu ya haɗe ta da shi Daniyel ɗin, to fa a nan ne suka fara gano wani abun......📝





*Shin wai Muhammad ya mutu kuwa?... Lailai a kwai ƙura a cigaban labarinnan* 😀





*Comments And shering*


*S REZA ✍️*
[10/21 22:05] Aliyu Makko: *ADDININMU*




*S REZA...✍️*


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*



*PAGE* 2️⃣7️⃣

......Haka ta ci gaba da rayuwar ta daga ita sai yaranta, kuma ta na ci gaba da jan ragamar kasuwancin ta har yaranta suka girma, ba ta sake shiga lamarin ɗangin mijin ta ba, sai she karar da ya samu ƙarin girma na matsin Comandar. Ajiyar zuciya ta yi tana kallon ko wa dake cikin palorn san'nan ta ɗora da ce wa "Yau dai yaran ka da na wa ko wa yaji dan gan takar dake tsakanin ka da ɗan uwanka da kasa a ka kashe, kuma yanzu so na ke ka sanar min abun da ya sa ka kulle min yaro? Matsiyacin banza wanda ba zai gama da duniya lafiya ba. Samuel da Salis da Laɗifa harda Sarah da ke cikin ɗaki a ƙulle duk sunji labarin da Hajiya Babba ke bayar wa kaman a ta tsuniya. Elixa ce cikin masifa da jin haushin labarin da ta bayar a gab yaransu ta ce "Wallahi ƙarya kakeyi Aisha baki isa ki kashe mana ɗan u'wa kuma kizo ki dawo mana da zance baya ba, kuma ki fita kibar mana gida kafin ki ƙara ƙarɓar wani hukuncin da ya fi na baya. Ta ƙarasa ta na nu na mata hanyar wa je. cikin ihu!. Comandar Daniyel ku wa mutuwar tsaye ya yi tsabar mamaki da tsananin ƙiyayar da ke wa duk wani wanda ba addininsu ba, harma ya rasa me zaice.

Kafin kowa ya yi magana Samuel ya ce "Daddy dama kana da ɗan u'wa namiji shine baka taɓa sanar damu ba? Cikin abunda ya gama cin ransa ya ce "Kar ka ƙara haɗani da duk wanda ya koma yin Sallah, ba ɗan u'wana ba ne, kuma walhi idan ka ƙara min maganar sa sai na sa an koya maka hankali. Cikin tsananin mamaki Samuel ya ce "Daddy wa ye a'cikin ɗakin tsaro? Ko dai shine? Kuma yan zu ma naga ka sa a kai wannnan yaron da a ka kawo yanzu? PLs Daddy dan Allah idan shine kayi haƙuri ina tausaya masa walhi tun lokacin da na ganshi kullum sai na je na ganshi pl"...Ai kafin ya ƙarasa ya ji an ɗauke shi da mari, an ƙara ma sa, Momy ma ta haɗa ma sa da na ta. Kafin ka ce wani abu har sun fara dukan Samuel ta ko ta ina, har saida ya faɗi a ƙ a sa.

Sarah da ke cikin ɗakin da a ka kulleta kuwa itama ta shiga tunanin wannan mutumin da Samuel ke maga a kai, tabbas itama tin ba yanzu ba ta na jin mutumin kamar ta san sa, domin kuwa ga kamar sa da maman Usha shk, saide shi yanayin yanda ya koma kamar ma haukaci ne ya sa baza ka taɓa gane komai a kansa ba, kuma gashi taga AJ ma can a ka kaishi, a take ta saki wani ihuu wanda yakaraɗe gidan gaba ɗaya duk girma sa, ta ke ta faɗi a gurin a sume.

Hajiya Babba da Salis da Laɗifa sai kallon ikon Allah sukeyi, yayinda gaban Hajiya Babba sai faɗuwa ya ke yi tun da ta shigo gidan. Jin abunda Sameul ke faɗa ne yasa dukkansu kallon junansu, yayin da Laɗifa tayi gurin da a ke dukan Samuel ta na bada haƙuri. Ai sai ji kayi tass itama Momy ta ɗauke ta da wani gigicacan mari wanda ya yi dai-dai da sakin ihunn Sarah. Da sauri Hajiya Babba tayi gurin Laɗifa ita ku ma Elixa (Momy) ta yi ɗakin da Sarha ke ciki, shima Daddy ya bi bayan Momy ya yin da shiku wa Samuel ya tashi da sauri ya nufi ɗakin da a ka kulle Aj. Ganin haka yasa Salis bin bayansa cikin sauri.

*NANA POV*

Har cikin ɗakin da a ka kwantar da Innah ta shiga, ta samu an ɗora mata ruwa sai barci ta ke yi, kallon fuskar ta ta yi taga duk tayi baƙi ga shi kayan jikinta duk sunyi baƙi, ta fita a haiyacinta sannan ga fuskarta da ɗan kumburi, sauke kayan abincin da tazo da su ta yi sannan ta samu guri ta zauna ta na tunanin yayan ta, sai kuma ta fara tunanin kayan da ta gani a ƙofar ɗakin Innah, wa ta zuciyar ta na sanar mata da cewar ko dai AJ ya dawo ne! Haka dai ta zauna ita ɗaya tana tunanin rayuwa, sai yanzu ma ta tuno da Salis. A zuciyarta ta ce "Allah sarki ko yanzu ya na ina o hoo!. Haka dai har washe gari inha bata farka ba. Washe garine likitan ya sanar mata da cewar Innah ta na buƙatar jini. Cikin tashin hankali Nana ta ce "Pls likita a ɗiba na wa idan zaiyi? "No kema kanki kina buƙar jinin amma ki biyoni zansan abun yi, yana faɗa ya na binta da kalllo.

"Me nene sunan ki? Likitan ya tambayeta bayan sun shiga office ɗin sa.

"Nana. "Wannan mamar ki ce?

"A'a kaka ta ce"

"Ok Tom me ne ne ke damun ta? "Nima ban sani ba. "Ko kinsan ta kamu da hawan jini? "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Ta ke ta fashe da kuka ta na ce wa "Wallhi bata sani ba. Da ƙyar ya samu ta yi shiru ya ce "Ku ƴan wacce unguwa ce?

Cikin ƙosawa da tambayar ta ce "Pls likita zata samu lfy kuwa? Shima cikin son jin wannan daddaɗar muryar ta ta ya ce "Ai lafiya Allah ne ka ɗai ke bada ta, am'ma za mu yi iya ƙoƙarin mu sai kuma mu barwa Allah ikonsa. Hk dai Dr ya ci gaba da kula da Innah ba tare da ya am'shi ko sisi daga hannunsu ba. Itama dai ta na son yin magana am'ma ta kasa domin kullum idan ya zo sai ya kafeta wannan manya-manyan idon na sa. Haka dai har kwana huɗu am'ma Innah bata farkaba, an sa ka mata ruwa har sau biyu. Yayinda a cikin kwana ukun nan har Nana ta fara sake jiki da Dr domin yanzu ta na ɗan biye masa idan yazo ɗakin haka zasu ta hira kamar sun san juna.

*ABDALHA POV*

Tinda ya fito daga gidan Dr ya nufi gidan sa ya shirya domin zuwa gidan da Daddy ya ce yaje. Duk abun da ya ke yi ya na tunanin halinda Zainab ta ke ciki, shin wai yanzu ta ya ya zai sanar wa da mutane cewar ba ni ne na sa ceta ba! Afili ya ce "Komai zai yi dai-dai. Da sauri ya yi wanka ya shirya cikin shigar sa ta manyan kaya sannan ya ɗauki wayar sa yana son kiran abokinsa am'ma ya ji yanzu haushin kowama ya keji. Yayi tunanin bi ta gidan su Dr domin duba wa ko Zaiban ta farka am'ma ya fasa. Jin yanda ransa ya ɓaci ne ya sa ya kunna karatun ma haifin sa cikin suratul Maryam. Haka karatun na yi shima yana bin muryar cikin sanyi da nutsuwa har ya ƙara sa gidan. Dai-dai zai shiga gidan shi kuma ma haifin yarinyar wanda ya ke shima babban malamin addinine shi kuma zai fita. Ganin motar Abdalha ne ya sa shima koma wa da baya. Bayan sun gaisa Abdalha ya ce "Daddy ne ya turoni wai kana nemana?

Cikin karannci da dattako ya ce "To-to kazo gurin ƙanwar ka kenan ko? To ai hakan yayi dai-dai kuma na yi farin cikin hakan sosai, Allah ya muku albarka bari na turo maka ita!

Shi dai Abdalh bai ce komai ba har mai gidan ya shiga ya na ta saka musu albarka. Saida ya ɗauka mintunan a ƙalla goma kafin yarinyar ta shigo palorn cikin ɓacin rai da rainin wayo ta banko ɗakin ta ce "Am'ma dai Walhi anji kunya...bayan an gama yiwa al'umma wa azi a kan cewar bidi'a babu kyu, kuma masu aikatawa ma ba malamai bane am'ma shine ka sace ɗaya daga cikin su, bayan kowa yasan cewar kai da ita ba shiri kukeyi ba, shin me ka je ka ai kata mata? Bayan kun gama komai shine zaka zagayo ta nan wai kana sona ko? To Allah ya kiyaye ni na auri ɓarawo, kuma muna cikin addinin! Kafin Abdalha ya ce komai sai ga u'war yarinyar ta fito, kana gani kasa itace ta zugo yarinyar ta ta, itama ta ɗora na ta..."To duk faɗin 9j waye baisan da cewar kaine ka sa ce ta ba, kuma ka fito musu da yarinya ba shine ka lallaɓo gurin ƴa ta to Walhi bada niba.

Sai a lokacin Abdalha ya ɗago kai ya kalli u'war da ƴar sannan ya ce "Ina u'ni Momy? Cikin jin haushin yanda ya yi banza da su ta ce "An iya ladabin banza, da de bamu san halin ka bane sai ka nuna ma na kai ɗin na Allah ne, am'ma munsan komai, abin da na keso da kai shine kaje ka sanarwa da mahaifin ka cewar karama a fara wannan auran ina ba haka ba zasu ai kata da na sani, kuma ka ce"..."ka fin ta ƙarasa Abdalha ya miƙe tsaye ya ce "Sai anjima, bai jira cewar suba ya bar palon cikin mamaki da tsananin ɗaurewar kai. Sukuma suka cigaba da ai bata shi da kuma cin mutuncin sa.

*ZAINAB POV*

Da sauri ta sauƙo daga kan gadon da take ta na bin ɗakin da kallo, sai kuma ta kalli jikinta taga ba kayan da ke jikin ta kenan ba, ɗaga kanta ta yi sai taga ledar ruwa wanda ya ƙare a rataye, har yanzu bata gano komai ba, sai ta ji wani ciwon kai mai ƙarfi ya sameta dalilin tunanin da ta fara yi, ai da sauri ta riƙe kanta tana rufe ido. A hankali ta ji ciwon kan yana ƙaruwa har kan ya ma ta nauyi sosai, jin sai ƙaruwa ya ke yi ne ya sa ta kurma wa ni ihuu ta na reƙe kanta wanda ta ke jin kamar zai rabe biyu. Da sauri Aisha matar Dr Musa ta shigo ɗakin ta na kiran sunan ta.

Al'lurar da Dr Musa ya bata akan idan ta farka da kuka ko ihu ta mata ne ta ɗauka ta ƙara mata ganin kamar bata cikin haiyacinta. Ai kuwa ta ke ta ƙara komawa barci, ita kuma ta kira mijinta ta sanar masa wanda shima ya kira Abdalha ya sanar masa.

Tin kafin ta buɗe ido komai ke dawo mata kaman dai mafarki, hakanne ya sa ta farka ɗauke da addu'ar ta shi daga barci *(Subuhana rabbiyal lazi a'ha ya'na ba'a dama a'mata na wa i'laihim nishur)* Ta na buɗe ido ta sauke shi a kan babban maƙiyinta, wanda a faɗin duniya shine mutum na ɗaya da ya shiga rayuwarta ya keson tauwatsar mata rayuwa, rintse idon ta sakeyi ta na sake tunano komai da ya faru. Tabbas ta tuno komai kuma ta yarda da cewa ba mafarki ta keyi ba. "Ƙwatsam ta ji sauƙar muryarsa a kunnuwanta "San'nu kina lfy? Ya jiki? Babu abun da ke damunki ki. Dr Musa ma ya ɗora da cewa "San'nu me ke damunki yanzu? Cikin dauriya da jajircewa ta ce "Gida na keson zuwa yanzu. Ta faɗa ta na haɗe fuska. Abdalha ya ce "Gida ba yauba sai kin samu lfy. Shima ya faɗa ya na haɗe fuska.

Da sauri ta kai kallonta zuwa gurin da ya ke, ai kuwa suka haɗa fuska cikin ido, yayinda ko wa ya ɗaure fuskar sa kai ka ce ba shine ya gama mata sannu ba. Sun kai minti uku a haka kowa yana kallon juna kuma fuskoki a haɗe babu mai murmushi. Dr Musa da Aisha kuwa sai kallon ikon Allah sukeyi ganin wani irin sabon lamari, wai yau Abdalha Kabir kabuga ne ta re da Zainab Ambato a zaune a guri ɗaya, kuma da a lama wani babban lamari ne a tare da su. Domin shi Dr Musa baisan ta ya ya Zainab tazo hannun Abdalha, ko dai dama soyayya sukeyi a tsakanin su ne, sai kawai ya ɗauki rumut ɗin tv ya kamo wani tasha da suka gabatar da wani abu da ya ɗaure masa kai. Ganin dai har yanzu kallon juna sukeyi ka ka ce faɗa zasuyi tsabar ƙyayar da ke tsakanin su. Dr Musa ne ya ce "Eh kawai ki bari ki ƙara samun lafiya sai kawai ki tafi gida kinji? Ya ƙara maganar ya na kallon saura lokaci kaɗan a fara mai-maita abunda ya keso gani.

Cikin sauri dukkansu suka kawar da kansu yayinda Zainab ta sa ki wani siririn tsaki wanda babu wanda ya ji sai shi Abdalh da ya ga bakinta. Abdalha ya ce "Dr Musa karka damu na gama magana bazata je ko ina ba. Ya na faɗa ya miƙe tsaye zai fita. Yayinda itama Zainab ɗin ta fara ƙoƙarin ta shi daga kan gadon batare da ta yiwa kowa magana ba. Ganin haka yasa shima da wo wa ya na kallon ta. Ta ce "Dr na gode sosai zan tafi nasan yanzu ana nemana a gid"... Ai kafin ta ƙarasa ta ji ana nuna hoton Abdalha a tv ɗin da Dr Musa ya kunna tun ɗazu, a kan ya sace wannan shahararriyar mawaƙyar Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama, wacce kowa ya santa da suna Zainab Ambato. Sannan kuma yanzu gashi mahaifinta mai suna Malam Adam, wanda shima babban malami ne wanda ya yi suna a faɗin duniya gaba ɗaya, ya kai ƙararr ɗan gidan Shek Kabir kabuga wato Abdalha Kabir kabuga, ya miƙashi kotu a kan zargin sa ce masa yarinya.

Kallon tibin da ke ɗauke da hoton Abdalha da Zainab ɗin ta yi, sai kuma rubutu da ke nuni da ranar da za'a shiga kotun. Cikin tsananin mamaki ta kalli Abdalha shima ya kalleta kafin ta kalli Dr Musa wanda shima ya ke son ƙarin bayani domin kuwa abun ya ɗaure ma sa kai sosai....📝





*Barkan mu da ranar Juma'a🕋 Allah ya amshi ibadunmu. Amin ya Allah*



*Labari na tafiya dai-dai kuwa?*
[10/21 22:05] Aliyu Makko: *ADDININMU*




*S REZA...✍️*


*First Class writer's asso...*


*PAGE2️⃣8️⃣*

.........Dr Musa ya meƙe tsaye da ga kujerar da ya ke zaune ya ce "Jiya muna kallo nida Madam naga wannan sanarwar shine abun ya bani mamaki kuma na ce sai na tambaye ku domin kaina ya ƙulle walahi, shin da gaske ne kai ne ka sace ta? Ya ƙara sa maganar ya na kallon cikin idon Abdalh wanda shi kuma ya ke kallon Zainab wacce har idonta ya cika da ruwan hawaye. Cikin kuka da ya kuffce ma ta ta ce "Ba shi ba ne ya sa ceni, ha salima saboda shi a ka sake ni, amma ni ban san dalilinsa na yin hakan ba! "Babu wa ni dalili na wa kawai na yi ne domin Allah da ku ma wanke kaina a idon duniya domin ko wa na tunanin ni ne na sace ki. Dr Musa ya ce "Shek kabuga ni fa ban gane me kuke ce wa ba fa, dan Allah kusanar min da komai, amma to idan ba kai ba ne to su wa ye? Nan ta ke Abdalh ya kwashe komai ya sanar wa da Dr Musa, sannan ya ɗora da abunda ya faru lokacin da ya je gidan su yarinyar da mahaifinsa ya tura sa domin su ga juna. Da sauri Dr Musa da Zainab da Aisha suka kalleshi jin abun da ya ce. "To su yaran da su ka sace ta me ta musu?Cewar Dr Musa cikin mamakin lamarin?

"Wai sabo da waƙar da ta yi ta buɗaɗdiyar wasiƙa. "To suɗin ƴan gidan uban waye da har zasu mata wannan jan aikin!... Kai kuma ka barsu suka tafi baka sa police sun ka ma suba?

Cikin kukan da

19 / 37