Addininmu Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  S Reza Category :  Love

Chapter   36 / 37

105K to 108K   out of 109.2K words

cikin mawuyacin ciwo. Saidai kuma tana zuwa gidan uban nata taji bazata iya zamaba saboda takura da matar ubanta da dangi suke mata, kasancewar anji labarin yaranta sun koma yin Sallah. Kasancewar mahaifinta babban Pastor ne sai yace dole taje ta dawo da yaran dangin su, ita kuwa ganin yanzu yaranta sun koma rayuwar farinciki da kwanciyar hankali ga annuri dake tashi a fuskokinsu ne yasa ta ce sam bata san da wannan zancen ba. Hakanne ya jawo mata suka a gurin ubanta da matar ubanta domin suna jin cewar itace tasa suka bar addidinsu.

Lokacin da Ibrahim yazo gida Sadiya ta sanar masa da cewar mahaifinta yazo ya tafi da ita. Ai kuwa har gidan yaje ya dawo da ita sannan ya musu gargaɗi da cewar su fita a harkarsu. Alokacin da pastor yaga Ibrahim saida gabansa ya faɗi ganin yanda ya cika masa fuska, lokaci ɗaya yaron ya masa wani baƙe-baƙe sai kace ba Samuel ɗinsaba.hakanne yasa ya kasa cewa komai har ya bar gidan.

Muhammad ya kira Salis da Ibrahim ya zaunar dasu a kan batun aiki. Ya sanar musu da cewar kafin a ɗaura auransu ya kamata a ce dukkansu sun fara aiki. Ibrahim ya shida masa cewar ai shi takardunsa sun ƙone a wancen gidan nasu. Shi kuma Salis ya ce "Dama shi yana ɗan zuwa saidai ba sosai ba. Muhammad ya sanar masa da cewar kar yaji komai za'a samar masa wata takardae. Ibarahim ya ce "No Daddy takardun sunanan domin gaba ɗaya mommy ta kwashesu lokacin da zamu bar gidan. Cikin ikon Allah kuwa yaje ya tambayi Momy ta kwaso masa harda nata da na Daniyel, Zara kuwa dama ita bata kammala Secondry school ɗinta ba. Take Daddy ya ce da Salis a je campaign su na Abuja a ma Ibrahim intabiyu idan yaci a bashi opiece. Ai kuwa takardunsa sunyi kyu domin kuwa yanada ƙoƙari. Haka a ka masa intabiyu kamar yanda a kewa kowa kuma yaci. Daddy ya mallaka masa gida a habujan domin a can zai zauna da matarsa, sannan Daddy ya ƙara siyan wani gidan ya ce na su Daniyel ne, idan ya warke zasu koma can. Ibrahim ya share hawaye ya ce "Ka manta da cewar a kwai hukuncin kisa a kansa koda ya warke? Kawai kabar siyan gidan Momy kuma zamu zauna tare a gidana, yanzu babban burina shine ace Daddy ya karɓi kalmar shahada kafin su kasheshi. Daddy da Salis suka amsa da amin in sha Allah zai karɓba.

*BAYAN WATA BIYU*

Zaune yake kamar yanda ya saba a koda yaushe ya ƙurawa waje ɗaya ido yana sauraron maganar da matarsa take masa a kan cewar gobe ne auran Samuel da Sarah dukda kuwa yasan da zancen. Tana maganar ne badan tasan zai amsa mata ba amman dai tasan yana jinta. Da mamaki taga ya gyaɗa mata kai yana son yin maga amma ya kasa. Tana cikin haka Salis da Zara da Ibrahim da Laɗifa da Muhammd da Hajiya Babba riƙe da Hajara da ta fara wayo suka shigo ɗakin suka zauna suna kallonsa. Burinsu shine Daniyel ya furta kalamar shahada kafin ranar Lahadi, domin kuwa sojojine sukazo har gida a kan cewar ko ya warke ko bai warkeba ranar za'a yanke masa hukumcin. Zancen ya bazu a ko'ina har gida rainiyo da jaridu, domin kuwa babu wanda baisan Commanda Daniyel ba a lokacin sa. Babu yanda basuyi dashiba amma ya kasa magana sai kallonsu ya keyi, yau sama da kwana goma kenan suna so ya furta koda kalmar shahada ce amma ya kasa cewa kimai. Ibrahim yaje ya ɗauko takarda da biro wai ya rubuta kalmar shahadar amma ya kasa ɗaga hannayansa ma bare a je ga rubutun. Zara da Momy sai kuka sukeyi. Zara ta kalli mommy ta ce "Pls Momy kema ki dawo Addininmu addinda shine na gaskiya Please! Momy ta gir-giza kai alamar bazata iyaba babanta zai kasheta. Babu yanda busuyi da itaba amma ina Eliza ta ce "bazata iya barin addininsu ba.

Haka dai suka bar gidan cikin tausayin halinda suke ciki. Washe gari da safe a ka ɗaura auran Salis da Nana sai Ibrahim da Hadiza sai Abduljabaru da Fatima Zara. Ɗaurin auran ya samu halarta mutane sosai, duk wani maaikacin dake aiki a ƙarƙashin su Salis to saida ya halarci taron, haka shima AJ mai mutane kala-kala. Shima Ibrahim haka ta ɓangaren abokansa musulmai dama wanda basuba sun halarta. Amarya Hadiza tasha kwalliya kamar ba itace wannan ballagazar ba, ta natsu tayi kyu cikin kayanta na amare. Gefe guda kuma ga angonta fuskarsa cike da annuri da kuma damuwa duk a tare da fuskar tasa.

Kasancewar ranar juma'a a ka ɗaura auran kuma ranar Lahadi ne Daniyel zai karɓi hukunci irin na sojoji, hakanne yasa a kace sai ranar juma'a ta sama kowace amarya zata tare a gidanta, Auran dai kawai a ka ɗaura. Ɓangaren Laɗifa kuwa sai a ranar tayi ido huɗu da Hadiza ai kuwa kallo ɗaya ta mata ta ganeta, cikin wani tsananin mamaki take Binta da kallo domin ko shekka babu itace wannan mara kunyar yarinyar kuma ballagaza. Ita kuwa Hadiza tana haɗa ido da ita ta ga kamar ta ganeta, domin kuwa ita har ga Allah ta manta da ita, domin kuwa ita batasan adadin mutanen da tayi faɗa ko zage-zage dasuba. Hakanne yasa laɗifa shiga wani hali tana neman Umar akan mai yasa bai sanar mata da cewar ƙanwarsa ce yarinyar da Ibrahim zai auraba har saida a ka ɗaura auran ta sani. Abunka da wanda bai san komaiba sai yaudaran ƴan mata da ya sabayi a baya, bai duba irin halin da take ciki ba a wannan lokacin kawai ya furta mata kalmar da tun safiyar yau yake ta bitarta kafin ya fito daga gida, ya aiyanawa kansa cewar ko kasheshi zatayi saidai tayi amma sai ya sanar da ita.

"Tasss" Kakeji ta ɗauke shi da wani gigicacan mari tana nunashi da hannu cikin huci da ɓacinrai..."Baka da hakalune harni zaka kalla kace kana sona saboda na sakar maka fuska ko? To Wallhi idan na sake ganin ka a gidannan saina sa an ɓatar da kai wawa ɗan matsiyata. Tana kaiwa nan ta koma ciki ta barshi a gurin riƙe da kunci yana kallonta har ta shige gida. Murmushi yayi ya ce "Zan iya jure komai a kanki domin kuwa ina sonki!.

Ɓangaren Salis kuwa a daran ranar da a ka ɗaura auranne ya saci jiki ya nufi gidan su Nana ganin AJ baya gidan yana tare da su Abdalh da sauran abokansu. Gidan ba mai gadi sai ya sauƙo ya buɗe get da kansa ya shiga gidan, guri ya samu yayi paking sannan ya nufi ciki harda haɗawa da gudu, kasancewar ba'a gidan a ke bikin ba sai bai ga mutaneba sai kawai ya nufi palon domin kuwa ba baƙonsa bane gidan. Yana tura ƙofar palon zai shi sai kuwa yaji sauƙar flet a kan hancinsa, kafin ya ankara saiga gorarr ruwa ceke da ruwa shima a kan goshinsa. Ai da sauri ya saki ƙofar ya koma da baya yana riƙe hancinsa.

Safara'u da Kadija kuwa da suke faɗa basuma san da shigowar Salis ɗin ba, ita kuwa Nana a kan idonta abun ya faru, domin lokacin da Safara'u ta jefo plet ɗin Kadija kuma ta sun kuya sai tabi flet ɗin da kallo. Da sauri tabi bayan Salis ɗin. Ai kuwa ta sameshi a bayan ƙofar har hancin yayi ja, ga kuma jini yana zuba. Abun sai yayi kamar abin dariya, amma sai ta dake tana masa sannu. Da gyar ya ce "Kuna kiwon mahauka a gidanku ne dama shine baki sanar min ba? Wannan karan kam sakin dariyar tayi tana ce wa "A'a ba mahaumkata bane. Cikin zafin ciwo ya kalleta ya ce "Au ke abunma dariya ya baki ko? Ta ƙunshe dariyar ta ce "A'a to ma wai kai me ya kawo ka gidan nan a wannan lokacin? Tana maganar tana ɗauko gorarr ruwan tana zuba masa a fuskarsa yana wanke jininn. Sai da suka gama wankewa ya bata amsa da cewar "Rabon hancina ya fashene ya kawoni.

Ya faɗa yana matsowa kusa da ita riƙe da hancin da yayi jaaa. Ta ce "Please za"...."Shiiiiiiii. ya katse ta yana ɗoro hannusa a kan bakinta. Ganin yanda ya matso dafda itane yasa jikinta fara rawa tana neman hanyar arcewa. Salis ya matso da bakinsa kusa da nata saura kaɗan ya haɗe sai sukaji an daki ƙofar da sauri wanda yasa duk saida suka tsorata. Da ƙarfi ta tureshi ta buɗe palon ta shiga a kunyace. Lokacin kuwa Kadija da Safarau sun bawa hammata iska sosai, domin kuwa mai rabun batanan. Da mamaki Salis yake kallonsu ganin yanda suka lalata tufafin jikinsu, wata har jinine a bakinta wata kuma a hancinta. Ga kuma palon shima an faffasa abubuwa. Gaba ɗaya kallonsa sukeyi domin kuwa babu wacce bata sanshiba. Ya tambayi ba'asin abinda ke faruwa. Suna cikin tsara masa saiga AJ ya shigo gidan.

Cikin ɓacin rai ya ce dukkansu su tattara a darannan subar masa gida. Nana ta ce "No yaya zunzo taya amarya kwana nef"..."Amaryar banza! Ya faɗa ransa a ɓace. Ai kafin kace cass har sun bar palon suna hararar juna. Saida ya rakasu har waje kafin ya rufe gidan ya dawo, yana jin yanda Safara'u ke cewa zata ɗauko kayanta amma bai ko bi ta kantaba. Yana shiga palon idonsa ya sauƙa a kan hancin Salis. Dariya AJ yayi wacce rabonda yayi dariya a gaban Salis har ya manta domin kuwa har yanzu kunyarsa ya keji. "To oga zamu rufe gida? Salis ya ce "Nima a nan zan kwana" Nana ta waro ido waje ta ce "No a'a wallhi ba ruwana. AJ ya ce "To kawai ka ɗauki amaryar mana katafi da ita ba sai kamin tashin kunya ba. Salis ya ce "Tom nidai koma me zakuce Allah bazan tafi da fashenshen hanci ba. Ƙarshe delo a gidan ya kwana...📝 ( *Muhaɗu a gurin harbe Daniyel)*

*Comments ɗinku shine abun alfaharina*

*S REZA ✍️*

*ADDININMU*

*S REZA ✍️*

*Watpad*
Salis m Reza.

*Feecbook*
Salis m Reza

*Arewabooks*
Salis m Reza

*Gimal*
salisuadam115@gmail.com

*Whasoop numbar*
08100785178

*Instagram*
*Salis m Reza.

*A ko'ina inada gurin zanta wa da kowa idan da buƙatar hakan🥰🥰*

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

*PAGE5️⃣0️⃣END* babu editing sai hakuru

........*RANAR LAHADI.* Kamar yanda suka faɗa cewar ranar Lahadi ko bai warkeba to zai ƙarɓi hukunci irin nasu na Sojoji daidai da abunda ya aikata. Saidai kuma wani abun da ya baiwa kowa mamaki shine... a washe garin ranar lahaɗi sai kowa yazo ya ga Daniyel lafiya lau babu wannan ciwukan na jikinsa, kansa ya dawo daidai haka hannayensa da ƙafafunsa. Shi kansa mamaki yakeyi domin shima haka ya tashi yaga kansa. Ya buɗe baki zaiyi magaba nannma yaji muryarsa ta fita kamar da lafiya lau, ai kuwa ya fara ihun kiran sunan matar tasa Elixa!. Cikin tsananin farincin Eliza ta kira Muhammd da sauran yaran ta sanar musu cewar Daniyel ya warke. Kowa ka gani bakinsa a washe domin kuwa abun ya basu mamaki. Ana cikin hakane saiga Umar da Usman sunzo gidan tare da matayensu domin Muhammad ya sanar dasu su cewar ranar Lahadi suzo gidan. A nanne Umar da Usman suke sanar dasu cewar wai ai jiya wanda yayi tsfin ya war-ware komai kuma ya kirasu ya sanar masu. Da mamaki Muhammd ya tambaye su waye? Suka kalli juna cikin rashin son faɗan sunan wanda yayi ɗin. Kafin suyi magana Daniyel ya ce "Basai kun faɗa ba ni nasan waye. Muhammad da Sadiya (Titi) da Elixa sukace waye? Daniyel ya ce "Sarkin garin ne, domin kuwa ya sanar dani cewar zanga abinda zai sameni domin kuwa na cimasa mutunci saisai. Muhammad da sauran suka cika da mamaki domin kuwa harda Sarkin a ke neman wanda sukayi a sarin a she shine da kansa yayi. Umar da Usman suka sanar musu da cewar wai sarkin ya ce saboda kaine ma yasa ya karya asirin badan ba da saidai ta ƙare a haka. Jin haka yasa Muhamd sauke a jiyar zuciya yana tausayin yayan nasa.

Suna cikin haka ne saƙon Sojojin yazo musu cewar an bashi a'wa huɗu ya gama komai domin idan sukazo tofa komai nasa ya ƙare babu wani ɓata lokaci da zasu jira. Acikin wannan a'wa huɗun sun cinye a'wa guda da koke-koke. Muhammad ya naimi ɗan uwan nasa da ya karɓi kalmar shahada kafin lokaci yayi. Daniyel ya ce "Solomon yanzu babu wani abu da ragemin aduniya kaga koda na koma addininku ai babu wani amfani kawai yanzu ka yafemin duk abunda na maka kaida Titi harda matarka". Muhammad ya ce "Na yafe maka duniya da lahira n
Muma Allah ya yafemana kuma kaima ka yafemin, sannan shi Allah mai karɓar addu'o'in bayinsane a koda yaushe, saboda haka dan Allah zan baka kalmar shahada kafurtata kuma kasa a ranka cewar kayi hakanne har cikin ranka. "Nayi Laifuka da dama wanda ko a Addinimu ni ba mutumin kirki bane, saboda hk bazan koma addininkuba, addininda na tarbatar shine addinin Allah, kuma shine addinin gaskiya, kuma addinin mutanan kirki ba irinaba. Anan Daniyel ya fara faɗo irin abubunda ya aikata a rayuwarsa game da Musulmai. A nanne ya ke sanar musu cewar musulmai ne suka kashe mahaifinsu a gabansa hakanne yasa ya ɗau alwashin babu shi ba duk wani mudulmi, daga baya ya gano a she musulmain irin marasa addininnane masu fashi da makami, amma dukda na gano gaskiya naji zuciyata taƙi yarda da musulmai, hakan yasa nake amfani da muƙamina na babban Soja ina kashesu ta yanda babu wanda zai zargeni, to yanzu a hakan ne Allah zai yafemin? Ya ƙara sa yana kuka yana kallon kowa dake ɗakin yana jin abunda yake cewa.

"Eh Allah shene kaɗai wanda yakeso idan kayi laifi ka koma gareshi ka tubu, to hakan nasa Ubangiji yaji cewar lallai wannan bawan nasa ya yarda da cewar shine kaiɗai mai yafiya kuma mai jin ƙai. Allah zai yafe masa ya kuma karɓeshi hannu bibbiyu kuma Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama yayi alfahari da shi. Muhammad ya shiga masa bayani yanda zai gane cewar babu irin laifin da bawa zaiwa Ubangiji ya kasa yafe masa saidai laifi tsakanin bawa da bawa ko kuma shirka. Itama shirkar malamai sunyi bayani a kan cewar Allah na yafewa mutuƙar mutum ya tuba ya dawo gareshi. Jin haka yasa Daniyel cewa "Na yarda zan koma na yarda na yarda. Kowa dake ɗakin ya ɗau hamdala suna murmushi. Saida Daniyel yaje Muhammd ya koya masa yanda a ke alaula da wanka irin na Musulunci kafin a ka bashi sabuwar jallabiya fara da hularta aka fara bashi kalmar shahada. Itama Momy Elixa ta ce zata koma. Haka cikin aminci Allah da yardar sa da kuma amincewarsa Daniyel da Eliza suka dawo addininsa addininmu Addinin gaskiya.

Anan cikin palon Daniyel ya ce "Nima sunan Muhammadu na keso a bani. Ai kuwa Muhammad ya ce "to daga yau ka koma Ahamad, ko da bayan ranka haka zamu dinga kiranka. Haka kuwa a kayi kowa ya kirasa da sunnansa na Ahamad, kuma ya amsa. Ibrahim ya fita ya samo mai hoto ya ɗaukeso dukkansu, sannan ya dinga ɗaukarsu ɗaya bayan ɗaya. A nanne Ahamad ya sanar da Muhammd cewar a kwai ku ɗaɗe masu yawa a account ɗinsa , sannan ya sanar da shi cewar Zara da Ibrahim suma kowannansu ya buɗe masu nasu account ɗin kuma yana sa kuɗi a ciki, sannan ya bashi wasu ta kardu na filayensa da kuma shaidar tabbatar komai ɗin nasane. Muhammad ya ce "Dama Kanada wannan amma kuma ka tsaya neman gurin zuwa kaida matarka? "Idan na nuna cewar nawane to sai sojoji sun kwace domin kuwa haka dokar take. Muhammad yayi kuka sosai yana jin inama da abun da za'ayi a fasa harbe ɗan uwan nasa.

A wannan lokacin ne kuma motar Amoka ta sojoji tazo unguwar tare da motocin manyan Sojojin ƙasar ta Nigeria. Haka dai su tattara shi suka tafi dashi, sannan suka naimi mutum ɗaya wanda zaibisu. Muhammad ya bisu har filin gurin da za'a harbesu ɗin. Mutane huɗe ne a gurin an rufe kansu da baƙin ƙyelle sannan an ɗaure hannayensu ta bata. Gurin filine mai girman gaske wanda ba'a iya hango ƙarshensa, saida a ka yi wasu yan zantuka a ka haɗa connecting kafin a ka sakesu suka fara gudu, sannan a ka baiwa sojojin damar harbi. Ahmad yana kudu yana maimaita kalmar shahada da Muhammad ya sanar dashi har lokacin da yaji shigar bulet a jikinsa.

Kuka sosai Muhammd keyi lokacin da yaga ɗan uwansa a kwance ba numfashi, nan take ya fara roƙa masa Allah. Haka ya ɗauko gawarsa izuwa gida a ka sallaceshi. Lokacin da Shek Kabir kabuga da Malam Adamu sukaji labarin abun sunyi masa addu'ar samun tsira daga mahaliccin mu, sannan suka jinjinawa Muhammd ɗin da irin ƙoƙarin da yayi. Haka su kaɗai suka yi zama makoki har na kwana uku. Ranar juma'a kuma a ka kai kowacce amarya ɗakinta. Ibrahim da Sadiya Abuja suka huce, Salis da Nana su kuma sabon gidansu da ya ke kusa da tsohon gidan da su Hajiya Babba suka taɓa zama. Zara da AJ kuwa sabon gidansa a ka kaita ita ka ɗai a gidan.

Shiru tayi tana kallon zara-zaran yatsun kafafunta tana tariyo komai cikin ranta, tun daga ranar da suka fara haɗuwa da AJ har Kawo yau da take cikin gidan sa. Godiya tayi ga Allah da ta tunoinaemahaifinta da mahaifiyar ta sun karɓu addinin musulunci.tana cikin wannan tunanin ya fito daga wanka ɗaure da tahul. Bai kalketaba har ya gama saka kayansa kafin ya ce "Nasan na miki laifi amma bai kai a ce har zuwa yanzu kina fushi dani ba, na baki haƙuru amma har yanzu magana ma kin kasa min haba my Zara? Yanzuma bata ko tanka masa ba ta shiga toilet itama tayi wanka da alaula ta fito ta sameshi ya haɗa kai da ƙafa yana kallonta. Ganinn hk yasa itama

36 / 37