na cikin kallon yaron ne har yaron ya taso riƙe da ɗaya yaron da a ka shigo da shi ɗa kin nasu ɗazunnan. Kukan da yazo masa ne yasa ya kasa yiwa yaron magana har ya fita. Yana cikin haka ne yaji muryar da ba zai taɓa mantawa da itaba koda kuwa mutuwa yayi kuma ya dawo wannan duniyar bare kuma bai mutu ba. Tabbas baiyi niyar tashi ya fito gurin ba, amma jin yanda yayan nasa yake cin mutuncin Addinin nasa da kuma yana jin cewar Allah ne ya turo wannan ranar domin ta zama warakar damuwar da suke cikin Sudan ƴan u'wansa, hakanne ya sa ya miƙe daga gurin da yake zaune cikin wa su kaya yagaggu sun gama fita a haiyacinsu ga tarin gashi da ya gama mamaye masa fuska, gashin kansa yayi jaa ,sannan ya mur-murɗi, ha ƙoran sa sunyi jaa sun fita a haiyacin su, gaba ɗaya kamarsa ta canja, daga gurin da kake zaka hango ƙashin ha ƙaƙƙarin sa a waje. Ganin yayi hanyar fitane yasa sauran mutum ukun da suke ciki suma miƙewa suka biyo bayan sa, suma cikin irin halin da yake ciki.
An fita da Samuel, shi kuma Salis yana tsaye a kusa da Daniyel ya kafeshi da ido, yayinda Hajiya Babba tayi kan Salis cikin tashin hankali tana kiran sunan AJ. Lokaci ɗaya Hajiya Babba ta fita a haiyacinta tana ƙoƙarin kamo ƙafafun Aj domin fita dashi sai suka tsikayi muryarsa cikin rawar mur yaya ce " Ai ais Aish Aisha? "Timm ka keji Hajiya Babba ta saki AJ ya zube a gurin tsabar ruɗu da harƙizi da suka dirar mata a lokaci ɗaya. Da sauri ta juyo domin kuwa tabbas bazata taɓa mantawa da wannan muryarba har gaba da abada. Tana juyowa sai taga fuskokin mutane har guda huɗu a bakin ƙofar ɗakin, amma hakan bai hana ta gano fuskarsa ba cikin sauri da ruɗani ta nufi gurin sa bata iya ko magana ba tana nunashi da hannu.
Salis da laɗifa sai kallon Hajiya Babba sukeyi domin su dai basu gane waye wannan mutumin mai kama da wanda baya cikin haiyacin sa ba, suna kallo har Hajiya Babba ta rungumeshi dukda irin kayan da ke jikin mutumin. Shi kuwa AJ jin yanda a ka sakeshi ne yasa ya saki wani ihuuu yana buɗe idonsa cikin wahala, domin kuwa tsabar duka har saida ya suma.da sauri Salis ya zo gareshi ya na kiran sunan sa. Cikin mamaki Salis ya duba cikin ɗakin amma baiga Daniyel ba, ai kuwa da sauri ya tashi domin fita waje, ai kuwa yaji ƙofar ɗakin a rufe, ya kalli ƙofar da kyu, ya ja da baya ya zo da gudu ya daketa amma ko motsi batayi ba. Abun da kamar wasa har yayi har ya gaji amma dai ƙofar na ƙulle.
Cikin wata iriyar murya wannan mutumin ya ce "Ya ƙulle ƙofar ne ko? dama nasan bazai barmu mu a gidan nan cikin kwanciyar hankali ba tabbas kashemu zaiyi baida imani, dama ya sanar min cewar duk ranar da wani yasan ina raye to tabbas zai kashe ni kuma ya kashe ku.
Duk wannan maganar yanayi ne a bakin ƙofar da suka zo domin fita. HAJIYA BABBA ta kalli Salis da Laɗifa ta ce "Sa sa Salis shine ba ba ban babanku, shine babanku. Tana faɗa ta sake fashewa da kuka, yayin da Salis da Laɗifa harma da Mlm AJ suka kai kallonsu gurin mutumin, suma sauran ƴan ɗakin da mamaki suke kallon yaran da kusan kullum sai mutumin ya basu labarin cewar ya bar yaransa da matar yan zu baisan a wani hali suke cikiba. Lokaci ɗaya dukkansu kuka ya kuffce musu, sun kasa zuwa gurin baban na su, sai tuno irin wahalar da yashe sukeyi da kuma tuno abun da ke faruwa yanzu sukeyi. Hannu ya ware musu alamar ku taho gareni ai kuwa dukkansu suka nufeshi suna kukan farin ciki.
Alokaci ɗaya Mlm AJ ya sake jin wani sabon ciwon da baisan daga ina ya fito masa ba, shin wai shi yanzu a wani hali yake ne, kuma yaji ana zancen kisa, to har dashi za'a kashe! Lokaci ɗaya ya nemi ciwon da ya keji ya rasa, ya fara tuni Innah da Nana. ita kuwa Hajiya Babba za mu iya cewa harga Allah ta ma manta da wanzuwar wani mai suna AJ agurin.
Sun kwashi lokaci suna koke-koke kafin suka ƙara shiga ƙoƙarin buɗe ƙofa amma shiru. Hakanne yasa suka haƙura suka zubawa sarautar Allah ido.
*(Shin kuna tunanin Daniyel zai buɗesu? Kodai a ciki duk zai haɗa ya kashe kamar yadda ya ce? To wai ta yaya zasu fita daga cikin gurinnan, ga shi dukkansu kowa na ciki😪 Tom koma dai menene muje zuwa domin ganewa idon mu)*
Ganin Muhammad ya fitone yasa Daniel za me jikin sa ya fita daga ɗakin sannan ya sa ɗan mukulli ya rufesu ta waje sannan yayi cikin gidan cikin sauri. Ya na shiga palon gidan nasa yaga har angama cirewa Samuel bulet ɗin an masa aiki agurin ana ƙoƙarin ɗaurewa. Da sauri ya da katar da sojan daga aikin da ya keyi, sannan ya ce ya kira masa sauran sojojin da suke gidan gaba ɗaya. Cikin minti kaɗan sukazo, dukkansu ya sanar musu da cewar zaibar wannan gidan nasa izuwa gidan sa da ke cikin Bokon, kuma gaba ɗaya har da iyalansa zai tafi, saboda haka a je a shirya yanzu-yanzu, ya ware mutum biyu ya ce su tsaya. Bayan waɗan can sun tafi ya kalli sauran ya ce...
"Ku biyu zaku tsaya a nan idan mun tafi kamar da awa ɗaya ku sakawa gidan wuta kuma kubi bayanmu, idan an tararr daku kuce gobara ce. Haka suka yanke shawara sannan suka shiga haɗa kaya, komai na amfani saida suka ɗauka, cikin lokaci ƙanƙani Sojojin sun gama haɗa musu kayan a mota harda sauran motocin gidan duk dasu zasu tafi. Ran Daddy ya gama ɓaci ji yake kawai ya kashesu kowa ma ya huta.
Sai da a kazo tafiya kuma a ka duba sama da ƙasa amma babu Sarah babu dalilin ta. Anduba gidan ko ina amma babu ita, kuma harda ita a ka dawo palon. Nan fa hankali Elixa ya tashi domin kuwa ta damu, aka tam bayi sojojin kodai ta fita ne sukaje su basu ganta ba. Cikin tsananin ɓacin rai da kuma ganin tana son ɓata musu lokaci Daddy ya ce kawai su tafi su barta.
Momy ta ce "To idan itama tana gidan fa har ta ƙone? Cikin haushi ya ce "To idan ta ƙone ni na ƙone? "To wallhi bazan tafi na barta ba. Da kiyr dai Daddy ya fita da baki harta yarda cewar wai kafin sojojin su kunna wutar zasu sake dubata. Haka suka tattara suka bar gidan daga su har kayansu shima Samuel sai ihu ya keyi a kan a barshi a nan amma ina.. ( *to fa )*
*NANA POV*
Lokacin da a ka sallamo su Dr ne ya ɗaukosu har gida a cikin motarsa, Innah sai shi masa albarka takeyi domin kuwa tabbas sun samu kulawa sosai a gurin sa. Innah ta war-ware sosai , yayinda Nana da Dr abota tayi nisa domin har waya ya siya mata , sannan ya saka numbar sa a kan zasu dinga gaisawa, itama ta saki jiki dashi sosai. Shi kuwa Dr so ya ke sai hankalinsu ya ƙara kwantawa kafin ya gabatar da kansa a gurinta, domin yarinyar ta tafi da imanin sa, idan yana kallonta har tsarguwa takeyi, daɗin sautin muryarta kuwa har wani amsa kowa ta ke masa a cikin kunnuwan sa tsabar yanda takeyin maganar kamar bazata yi ba, ɓan garan tafiyar ta kuwa, shi dai a ganinsa ko ɗawisu saide tazo Nana ta koya mata. Hakanne ya sa baya gajiya da kallonta. ( *Kai Dr ai dama duk wata Nana ai duniya ce walla)*
*ABDALHA . ZAINAB POV*
Karo sukaci da Mlm Adamu wanda ke ƙoƙarin fita daga gidan nasa cikin ɓacin ran da matar sa ta ƙunsa masa. Kallon Zainab ɗin ya yi daga sama har ƙasa kafin cikin sauri ya ce "Zainabu ke ce? Bata tsaya bashi amsaba ta fashe da kuka tana rufe bakin ta. Ai da sauri Mlm ya kamo hannuta ya ce "Ya isa haka ya isa, muje ciki Alhamdu lillh masha Allah! Mlm ya dinga hamdala yana riƙe da hannun Zainab, shi kuwa Abdalha na biye dasu sai bin cikin gidan ya keyi da kallo ganin sai shiga da fita a keyi ta ɗaya ƙofar, domin kuwa gidan ƙofa biyu ne. Har suka ƙarasa cikin palon sannan ya fara kiran matar tasa wacce dama itama yanzu ta shiga ciki. Isa ne ya fara shigowa palon sai Mama wacce har yanzu ranta a ɓace yake.
Kallon-kallo a ka far yi tsakanin Isa da Abdalha, domin kuwa yana shigowa idonsa ya sauƙa a kansa, itama Mama shi ɗin ta fara gani. Da sauri Zainab tayi gurin mama tana kuka tana cewa Moma na yi kewar ki. Itama Mama lokaci ɗaya kukan ya kufce mata, ta faɗa jikin mahaifiyar tata tana rusar kuka.
"Ban gane ba ubam me ya ka wo ka gidan mu? Cewar Isa yana nuna Abdalha cikin mamaki. Sai a lokacin Mlm ya ganshi. Ai kuwa kafin Isa ya ƙara cewa wani abu Mlm ya fara nashi cikin fushi. "To ai dama na faɗa cewar wannan ɗan gidan matsiyatan ne ya saceta amma wannana mai taurin kan ta ce zato na keyi. Ya faɗa yana nuna Mama wacce batama san cewar da ita ya ke yi ba.Ya ci gaba da cewa...."bayan ka gama tara mutane kun zageni kai da uban ka to mai ya kaika ga sace ƴata? Ai dama haka halin su ya ke, wato yanzu ya ji cewar zan kai ubansa kotu shine ya dawo min da yarinya, to walhi duk da haka sai ammana sharia da ku. Ganin Abdalha har yanzu
bai nuna koda tsoroba ya sa mlm nufo gurin da ya ke yana cigaba da aibata shi. "Ka fita min daga gida, kuma kaje ga sanar wa da uban naka cewar wallhi zuwa kotu nanan gobe. Cikin tsawa Isa ya ce "Wai dan ubanka bada kai a keyibane ka tsaya sai kallon bakin mutane kakeyi?. Kaman yanda Abdalha ya saba koda kuwa Daddyn sa ne yake masa faɗa, to baya iya cewa komai, kuma idan har bai gaisa da mutum ba haka kana cikin faɗan zai gai da ka. "Ina uni Mlm? Cewar Abdalha yana daga tsayen da yake.
Cikin jin haushe Mlm ya ce "Riƙe gaisuwar ka ba na so tashi ka barmin gida, ba ga irinta nan ba, gaisuwa a tsaye kamar zai giasa da sa'an sa, yanzu wannan itace tarbiya, wannan shine yaron da ya ke tara mutane da sunan wa'azi? Mlm na cikin faɗa ya ji Abdalha ya miƙa wa Mama na ta gaisuwar. "Ina u'ni Mana? Sai a lokacin Mama ta ɗago da Zainab ta ce "Lfy yaro...tare kuke da ita? Abdalha ya buɗe baki zaiyi magana Zainab ta ce "Eh tare muke shine ya sa a ka ƙarɓoni daga gurin mutanan da suka saceni.....📝
PLs Comment
*By S REZA*
[10/21 22:06] Aliyu Makko: *ADDININMU*
*S REZA ✍️*
*First Class writer's asso*
*PAGE3️⃣0️⃣*
......"Ban yarda da wannan zancenba kuma ba zan taɓa yarda ba, idan ma wani abu ya miki kike ɓoye wa to walhi ba zan taɓa bari wannan yaron da kowa ya gama yarda cewar shine ya saciki amma yanzu ki ce wai shine ya sa a ka kar ɓoki! Ka tashi kabar min gidan tun kafin raina ya kai ga ɓaci. Cewar Mlm yana nuna Abdalha cikin tsan-tsar ɓacin rai. Mama ta ce "Am am Zainab bamu gane me kike nufiba? "Eh Mama kamar yandda kikaji na ce bashi bane ya saceni wasu mutanene kuma shine ya je ya ƙarɓon"..."Ya isa haka! Cewar Mlm...Ya zata muma irin mutanan da yake tarawa a gari da sunan wa'azi ya raina musu wayone? Wato saboda yaji na ce zan kai ubansa kotu shine ya fito da ke har ya shirya miki ƙarya kekuma kika hau kika zauna ko? To ga saƙo zan baka ka kaiwa shi mai sa ka yin komai ɗin ka ce masa... Duk da yarinyata ta fito sai munje kotu an'mana iyaka tsakanin gidana da gidan sa, domin sai an mana shari'a! "Haba mana Mlm sai kace ba musulmai ba...
Musulman ma kamar ba malamai bai! Yanzu wannan abunda kukeyi shine zai ƙara haɗa kan addinin Musuluncin ko kuma zai ƙara rabawa!? dan Allah Mlm ka zauna mu saurari wannan yaron muji da mai yazo? Ta ƙara sa ta tana yin ƙasa da sauri ta. "Waye malamin? Wancan ne Malami? Wallhi Kabir kabuga ba malamin gaskiya bane, burinsa sai ya tarwatsa Addinimu kuma Wallhi nidai bana ganinsa da wata kimar malumta, kuma wannan yaron ya barmin gida kafin na dawo, nine zan zauna na saurare shi, kotu ne kuma dole sai anje. Mlm na kaiwa ya bar palon cikin ɓacin rai.
Isa ya ce "Yallaɓai sai a tashi a bar mana gida ko? "Walhi isa idan na ƙara jin bakinka a gurinnan sai na mugun saɓa maka, wato ubanka yamin kaima kamin ko? Ban isa na ce maka a'a ba ko? Isa ya ce "No Mama dan Allah kiyi haƙuri bazan ƙara cewa komai ba kinji!. Zainab kuwa tinda Mlm ya fara magana sai kuka takeyi tana jin babu daɗi a ci mutuncin ubanka a gabanka, ta ɗaga kai ta kalli Abdalha sai taga murmushi ma yakeyi abubsa. Shi kuwa tun lokacin da Mlm ke faɗa sai kawai ya tuno da mahaifinsa,. Azuciyarsa ya ce "Anya kuwa tsakanin Daddy da Mlm babu wani abu a ƙasa bayan rabuwar haƙida, idan bai mantaba shima Momy ce take hana Daddy amma kullum sai ya yi maganar Malam Adamu.
Mama ta kalli Abdalha ta ce "Yaro bamu labarin abunda ya faru? Abdalha ya ce "Kaman yanda abun ya shiga kunnuwan al'ummar gari da ma duniya cewar nine na sace Zainab, to haka nima abun yazo kunnena, duba da cewar ranar da abun zai faru mun haɗu da ita amma bamuyi wata magana ba, sannan na shiga tsananin tashin hankali ganin yanda labarin ya nuna zahirin nine na saceta, bayan ni kuma ban taɓa saka haka a rainaba, hasalima nine mai jawo hankali ga masu irin wannan halayyar. Abun da ya fara bani mmk shine lokacin da naji Daddy shima ya yarda da cewar nine na saceta, lokacin ina gida tare da Momy saiga samari sunzo har ƙofar gidanmu akan saina fito musu da ita, ana cikin hk Daddy ya kirani akan sai na fito musu da yarinya. Hakanne yasa nikuma furta musu cewar nine na saceta. Da sauri Isa ya ce "Nidai nasan shine zai saceta gashi kuma ya faɗa da kansa"..."Kallon da Mama ta masa ne yasa ya ƙuntse sauran maganar tasa yana rufe baki. "Tun daga wannan lokacin na shiga tunanin yanda zan gano komai domin nayi tunanin anyi hakane domin ɓatani, har washe gari ban gano komai ba. Bayan abun da kwana biyu har lokacin banyi magana da kowa ba tsabar bansan me zance ba, ina zaune naji kira a a waya na, ina ɗagawa naji ashe waɗanda suka kamata ne. Take ya kwashe komai ya sanar musu,bai ɓoye ko mai ba.
Cikin kuka Mama ta sake rungumo Zainab tana faɗin "Allah sarki Zainabu Allah zai saka miki koma suɗin suwaye, domin ke baki musu komaiba, kai kuma Allah ya maka albarka mungode sosai, sannan idan Zainab ɗin tayi wanka ta ci abinci zan sakata tayi magana da sauran ƴan gungiyar tata domin suji gaskiyar lamarin, sannan ka sanar wa da iyayenka cewar anga yarinyar? Abdalha ya ce "a'a babu wanda ya sani daga ni sai Dr Musa sai matarsa. Mama ta ce "To idan zaka tafi gida sai ku tafi da Isa ya rakaka domin ayi musu bayani yanda zasu fahimta. Abdalha ya ce "A'a Mama karki ji komai nasan yanda zanyi dasu har komai yayi dai-dai. Mama ta ce "Karka damu ai yanzu an zama ɗaya, idan yaje ɗin zasu ƙara tabbatarwa ne. Kafin Abdalha ya ce wani abu Isa ya ce "Haba Mama ki barshi tinda ya ce komai zaiyi dai-dai mana? Mama ta ce "To sai kaje idan kuma zaka nuna min cewar ban isabane to?. Sai kuma yayi shiru yana sunkuyar da kansa.
Da wannan damar Mama ta fara musu nasiha cikin iya lafazi da yasa dukkansu gano kuskuransu. "Haƙiƙa Allah subhanahu wata'ala yana kallon duk wani abu da muke ai katawa, duk wanda ya yi wa musulmi ɗan uwansa maganin damuwarsa babu shakka Allah zai saka haske a cikin ƙabarin sa, sannan duk wanda ya haɗa mutanan da suke gaba shima tamkar ya musuluntar da mutumne, shikuwa musulumtar da kafiri zuwa ga Allah ladan sa yafi duniya da abunda ke cikinta, addininmu wato addinin musulunci yana tsafta ga sauƙi, shin idan har mutum zai haɗa kan masu yin gaba zai samu lada fiye da duniya da kuma abinda ke cikinta shin to mecece duniyar kuma meye a cikin ta! Inada tabbacin cewar wannan ƙiyayyar da kukewa juna daga gurin iyayenku maza tasamo a sali...
Shin ko kunsan da cewar wannan abun da kukeyi ga ba ce kukeyi? Isa da Abdalha da Zainab kowa yayi shiru. Mama ta ɗora da cewa "Tabbas ga ba kukeyi, kuma duk mai gaba a addininmu mutuƙar ya mutu bai tubaba babu shakka babu Allah zai masa hukunci mai tsanani... Zainab Isa harma da kai Abdalh nasan dukkanku kunyi karatu kuma kunsan gaskiya amma sai kuma ku ka ta keta!? Karku manta yanzu kune jagororin al'umma, dan Allah ku bani haɗin kai domin dawo da ADDINIMU ya zama guda ɗaya, ya zama addinin da Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama zaiyi alfarari da shi harma damu wanda muka tashi tsaye akan sa? Inaso dukkanku kuyi yaƙi da faɗin Allah a kan iyayenku domin dawowa dasu hanyar gaskiya, amma bance kuyi wa iyayenku rashin kunya ba, ku tausasa kalamamku a garesu koda kuwa suɗin ba musulmai ba ne, cewar Allah subhanahu wata'ala. Shin kun manta da rayuwar Annabi Ibrahim Alaihissalam