Addininmu Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  S Reza Category :  Love

Chapter   23 / 37

66K to 69K   out of 109.2K words

sai nayi kuka, yanzu gashi ya mutu "No bai mutuba sai de ko yanzu Daddy ya kashe su, amma idan kina son ki ga ɗan uwanki kizo muje gida walhi yana can kuma Daddy zai kashe su. Ai da sauri Titi da Usha suka bi ta a baya, mota suka ɗau ka suka nufi gidan cikin tashin hankali, wanda shidai Usha abun ma mamaki yake bashi, domin har yanzu bai gano komai ba.

Koda suka isa gidan suna zuwa sojojin da suka saka wutar suna barin gurin, ai da sauri Titi ta kira ƴan kwana-kwana, shi kuma Usha ya nufi police ɗin yan sanda, su kuma police jin cewar gidan Comanda ne yasa suka kai zan cen sama, ai kuwa kafin ka ce me, sai ga motocin ƴan sanda haɗi da na sojoji, suna zuwa suka tarar da motar ƴan kwana-kwana har sun iso sun fara aiki. Titi ta tabbatar musu da cewar a kwai mutane a cikin gidan, hakanne yasa suka fara aikin cikin sauri, yayinda wasu daga ciki kuma suka shiga cikin gidan. Wutar sosai ta ke ci, hakanne yasa wanda suka shiga ɗin suka kasa gane ko wacce hanya da zasubi domin shiga gidan, kana ganin wutar kasan sakawa a kayi dubada yanda ko ina keci. Abun mamaki an duba ko ina na gidan babu ko wa, kowani loko da saƙo anduba babu wani ɗan adam hakanne yasa suka fito suna sanarwa da Titi, ai kuwa ta ke Sarah ta sake kwatanta musu inda ɗakin yake. Ai kuwa cikin ikon Allah suka ga ɗakin, suka ɗauki wani abu mai kama da zare wanda da irinsa suke buɗe ƙofa.

Saida suka sha wahala sosai kafin ƙofar ta buɗu. Ai kuwa saiga bayin Allah a yashe a gurin, wuta ta kusa cinye saman ɗakin wasu daga ciki sun suma, wasu kuma sun fita a haiyacinsu, har wuta ta fara faɗowa daga sama a kansu. Da sauri a ka fara fita dasu cikin sauri. Suna zuwa ƴan sanda suka kwashesu a ka sakasu a motoci a ka nufi asbiti da su...📝




*Muje dai zuwa*


*S REZA ✍️*
[10/21 22:06] Aliyu Makko: *ADDININMU*




*S REZA ✍️*

*First Class writer's asso...*


*PAGE3️⃣2️⃣*

.....Da sauri a ka ƙarɓesu a asbiti Titi ta ce "Usha da Sarah su zauna a gurin su Salis ita kuma tananan zuwa yanzu. Tinda ta fita bata dawo ba, sai lokacin Usha ya ce da Sarha ta shiga toilet ɗin asibitin tayi wanka, ita ku wa sai kallon fuskar AJ takeyi wanda idunsa ya kumbura ga kuma bakinsa shema kumbure tsabar duka, batasan lokacin da wasu diraran hawaye suka biyo kuncintaba. Usha ne ya sake yin magana a karo na uku, sannan ta kalleshi ta ce "Wannan shine AJ Daddy ne yasa a ka masa hk. Tana faɗa tabar gurin cikin kuka ta nufi toilet ɗin shi kuwa Usha yabi ɗan yaron da a kace shine AJ da kallo. A fili ya ce "To shi kuma AJ ɗin me ya kawo shi gidan da har za'a haɗa da shi, sannan yana mamaki ganinsa ƙaramin yaro. Ɗakin da su Sarah suke a ciki ne a ka kwantar da Salis da laɗifa da AJ. Sai kuma ɗaya ɗakin a ka kwantar da Muhammad da Hajiya Babba wacce duk tafisu jigatu wa domin ita wuta ta faɗo mata daga sama. Sai Umar sai Usman.

Hannun yayan nata ta kamo a cikin na ta, sannan ta ɗora a fuskarta tana rusar kuka tana cewa "Pld Solo ka tashi walhi ina buƙatar ka a rayuwata Pls And pls, kuka takeyi sosai wanda kana gani sai ka tausaya mata tsabar yanda ta fita a haiyacinta, tana cewa "Dama ashe kana raye, dama baka mutuba? PLs Solo. Amma ina baima san tana yiba. Likitane ya shigo ɗakin yana mai bata haƙuri a kan ta daina kuka anjima kaɗan zai farka babu abunda ya samesa, da kyar dai Titi ta bar ɗakin. Da kudu-kudu ta shiga motarta ta bar asibitin tana tafiya tana kuka har ta isa gurinda zataje.

*DANIYEL POV*

Suna isowa yasa aka wuce da Samuel asbiti domin har yanzu kuka yakeyi yana kiran zafi zafi. Cikin tsoro ya tura ƙofar office ɗin ya shiga, yana shiga ya tarar da manyan Sojoji a zaune a gurin ko wa fuskarnan a murtuƙe, kasa zama yayi sai bin kowa da kallo ya keyi. Caraf idonsa ya sauƙa a kan Titi wacce ke zubar da hawaye tsabar rikici. Ɗaya daga cikin sojojin ne ya umarce sa da ya zauna, ai kuwa da sauri ya zauna yana ci gaba da kallon ƙanwar tasa cikin mamakin me ya kawota nan gurin. Wani ya kalli Titi ya ce "Mai-maita abinda kikace a kan ɗan uwanki? Ai kuwa cikin kuka ta fara zaiyano komai da tasani akan ƙulle ɗan uwansu da yayi, sannan ta ɗora da wutar da yace a saka a gidann, sannan ta ce "She kara kusan ashirin kenan yana kulle wai dan saboda kawai ya koma yin Sallah, kuma bama shi kaɗan ya kulle ba mutum uku, sannan kuma ya kamo family ɗinsa suma ya haɗa a gurin zai ƙone. Titi ta ƙara sa tana fashewa da wani sabon kukan. Kowa dake gurin suka zubawa Daniyel ido cikin tsan-tsar mamaki, da yake a cikin gurin harda Musulmai. Wani ya ce da Daniyel "Kaji abinda a ka ce shin hakane ko ba haka bane? Ya ce "No No is my brother"..."Na ce hakane ko ba haka ba ne? Cewar sojan cikin ɓacin rai wanda shima musulmi ne kuma a gaba dashi ya ke?. Ganin yaƙi yin maga ɗayane yasa Captain ɗin cewa ya cire rigar jikin sa, ta ke ya cireta ya ajiye.

Captain ya ce "A tafi dashi kafin oga ya zo( Wato shugaban sojojin gaba ɗaya) haka a ka tafi dashi ya na sanar musu da cewar ƙaryane shi daii bai yi komai ba. Captain ya ce da Titi ta koma asbiti idan har oga yazo za'a nemeta daga ita har ɗan uwan nasu, haka ta amsa cike da jin daɗin za'ayi adalci.

*ABDALHA POV*

Kallon su tayi tana son tabbatar da abunda Isa ya tsara mata ta ce "To Abdalha kasan da cewar ba kaine ka saceta ba to menene yasa kace kaine? Abdalha ya ce "Momy idan nafito na ce bani bane nasan babu wanda zai yarda dani shine yasa kawai na ɗauki laifin. "Yanzu dai ai tafito ko? Ya ce "Eh Momy "To masha Allah tundade yanzu ta dawo kuma cikin ƙoshin lfy ko? Isa Abdalha suka haɗa baki ƙurin cewa Lfy lau ta dawo. Momy ta ce "To yanzu bari na kira Abbanku sai ka masa bayani domin har yanzu fushi ya keyi da kai sosai. Tin daga nesa Shek Kabir kabuga ya fara ce wa "Duk naji bayanin da kukeyi kuma ka sani idan ma kayi hakane da wata manufa to ina dai-dai da kai, kuma ka ce da wannan yaron dake kusa da kai ya tashi ya bar min gida bana son ganin sa. Cikin mamaki suka kalli gurin da Daddy ke sauƙowa rai a mugun ɓace. Abdalha ya kalli Isa shima Isa ya kalleshi sai Abdalha ya dawo da kallonsa izuwa gurin Daddy. Ya buɗe baki zaiyi magana saiga Sadiya da Nusaiba da Maryam duk sun fito daga ɗakunan su dalilin jin Daddy na faɗa. Basu kula da baƙon dake tare da Abdalha ba saida suka nemi guri zasu zauna idon Nusaiba ya sauƙa a kan Isa da ya kafesu da idu. Ai da wani irin tsalle Nusaiba ta meƙe tana mai kare jikinta kasan cewar kayan barci ne a jikin ta. Itama Sadiya ta miƙe a kunyace ta bar palon. Ita kuwa Maryam guri ta samu ta gyra zama ko a jikinta. Kallon da Abdalha ya watsa mata ne yasa ta saki wani siririn tsaki ta kawar da kanta daga kallonsa.

Kawar da kansa yayi daga kallon ta ya dawo da kallonsa zuwa ga Daddy ya ce "Pls Daddy kayi haƙuri tundade ai yanzu yarinyar sa tadawo kaga ai komai ya wuce. Daddy ya ce "Komai ya wuce amma ya barmin gida domin nan gidan ba gidan ƴan bidi'a bane, idan kuma kanaso daga kai harshi ranku ya ɓaci to? Da sauri Momy ta ce "Tirr da irin wannan halyyar taka, idan har haka sunna ta koyar da kai to tabbas ba sunna kakeyi ba. Manzan Allah Sallallahu alaihi Wasallama yana koran baƙo daga gidan sa? Shin yana gaba da kowa? Koda mutum ba musulmi bane yana kywatata zamantakewar su, kuma muma haka ya koyar damu, dan Allah kayi aiki da iliminka ka ganar da jama'a gaskiyar da kuke ɓoyewa? Daddy ya ce " Bakisan waye Adamu bane shiyasa kike cewa shi ɗin mlm ne . Da sauri Momy ta ce "Kenan a kwai wani abu a tsakanin ku bayan babbancin aƙida? Daddy bai tsaya saurarontaba ya bar palon cikin ɓacin rai. Momy ta baiwa Isa haƙuri sannan ta musu wa'azi mai ratsa zuciya, sannan Isa ya bar gidan cike da tunanin to meye tsakanin Mlm da Daddy. Ita kuwa Maryam duk abunda a keyi tana zaune a gurin tana jin komai dama ita kaɗai ce ta fita Zakka a gidan, domin babu ruwanta da wannan faɗan nasu, sannan ta kafe Isa da ido duk ta hanashi sakewa a gidan har saida ya fita.

Tana zaune a kan gadon ta suna chatintg da Nana yayin da Nana ta sanar mata da cewar mamarta ce ta ce wai idan suka yiwa Abdalha haka to ko anyi auran zai dinga ganinta da mutunci shi fa yasa muka masa wannan cin mutuncin. Ita dai Maryam bata ce komai ba alokacin, sai daga baya Nana ta sake kiran Maryam wai har yanzu Abdalha bai dawo bafa? Ita kuwa Maryam ta dinga mata dariyar, to shine fa yanzu take sanar mata da cewar ai Abdalha ya dawo da Zainab yanzu hk ma tana gidan uban ta, hakanne yasa Nana rikicewa sosai domin tana son Abdalha sosai.

Suna cikin hira da Nana taji ana buga mata ƙofar ɗaki. A ɗan tsorace ta ce "Waye? Shiru babu amsa sai ta sake cewa "Wai waye ne cikin darannan ke haka ta nufi ƙofar tana surfa masifa Walhi Nusaiba kin cika taƙurawa mutum ke babu dama a ɗauki aron abun ki sai kin hana mutum sakew"...Ai bata ƙarasa ba sukayi ido biyu da Abdalha dake tsaye yana sakar mata harara. Cikin tsoro ta ƙara sa buɗe masa ɗakin tana sun kuyar da kai. Ɗakin ya shiga ya zauna a bakin gadon yana bin ɗakin da kallo cikin nuna ƙyama,. A hankali ta kalleshi ganin yanda yake ya tsine fuska yasa ta saki tsaki wanda yasa Abdalha ɗin jin ta. Suna haɗa ido ta rufe baki tana girgiza kai. "Ina wayarki? Ya jefo mata tambayar da sauri ta ƙaraso gurin da yake ta miƙa masa. Ya ƙarɓa ya shiga gurin numbobi ya dawo gurin hotuna. Ganin ya rasa yanda zaiyine kuma baisan mai zaicemata ba ya miƙa mata wayar, kafin ta ƙarɓa kiran Nana ya shigo. Yana son ya tambayeta numbar Zainab ne amma ya kasa.

"Wacece mai kiranki cikin dare?

"Ƙawata ce" Bai ƙara cewa komaiba ya kama hanya zai fita Maryam ta ce "Yaya wani abun kake sone? Bai ce komai ba ya bar gidan gaba ɗaya izuwa nasa gidan duk ransa a ɓace.

Washe gari cikin garin Kano da ma kewayanta gaba ɗaya suka tashi da labarin dawowar Zainab Ambato. Hausawa suka ce wai gani da ido shine sheda. Ai kuwa dai sai ga Zainab da kanta tana bada labarin komai da ya faru cewar ba Abdalha bane ya saceta shine ma ya cetota daga gurin su. Cikin ƙanƙanin lokaci saƙon yazo ko ina, ƴan jarida da gidajen rediyo dana tv duk sun saka hirar, kasan cewar ƴan jarida ne da kansu sukayi hira da ita. Tofa ana wata sai ga wata. Bayan samun wannan labinrin ne kuma Mlm Adamu ya ce shifa sai an masa iyaka da shek Kabir kabuga, saida ɗan sa Isa ya tsaya sosai kafin abun ya lafa. Ƴan gari kuwa kowa yana jajanta abun, to meyasa Abdalha zai ceceta kodai yana sonta ne. Aliyu kuwa tuni ya nemi da iyayensa akan a saka ranar bikinsa da Zainab domin jikinsa nabashi cewar zai iya rasata. Ai kuwa babu wata-wata a ka saka rana wata uku masu zuwa. Labarin bikin ya bazu ko ina.

Lokacin da Nana da mamarta sukaga wannan labarin na dawowar Zainab sunyi ta kaici sosai, domin kuwa sunsan yanzu Abdalha ya musu nisa.

Abdullah kuwa Daddy ya haƙura da duk abunda ya faru, amma har yanzu babu shi babu Mlm Adamu. Sannan ya sake umartar Abdalha ya koma gurin Nana amma ya ce ina shi dai yanada wacce ya keso, idan aka ce wacece sai ya ce ai basu gama dai-daitawa, yayinda shima isa ya tsunduma soyayar Maryam sosai da sosai, hakanne yasa ya sanarwa da Zainab, ita kuma da yake yanzu suna waya domin tinda ta dawo ta kira ta kuma kusan kullum sai sunyi waya, ta bashi numbar Maryam kuma cikin ikon Allah itama ta ƙware masa, amma soyayar ta kasa baiyana. Soyaya ya ce mai ƙarfi ta ƙullu tsakanin Maryam da Isa wanda ta wuce katance. Nusaiba da Sadiya kuma dukkansu kowacce ta fitar da zaɓinta har an saka rana nan da wata biyu masu zuwa. Zainab kuwa daga dawowarta ta sake yin wata ƙasidar mai zafi wanda yasa kowa hawaye saboda tayi ƙasidar ne akan tarihin Manzan Allah Sallallahu alaihi Wasallama, tayi bayanin yanda yake zamantakewar sa da al'umma. Tabbas ƙasidar ta karɓo a gurin bayin Allah.

Amma ai masu iya magana sunce ranar wanka ba'a ɓoyan cibi. Isa da kansa ya tun kari Abdalha da zancen soyayar sa da Maryam, ai kuwa Abdalha yaji daɗi domin wannan hanyar itace mafi dacewa da zasubi su gano ko dai wani abun ya taɓa faru ne a baya. Abdalha nason ya masa maganar Zainab amma yasan babu kyu nema a cikin nema, domin kuwa an saka ranar Zainab,. Amma haka ya daure ya sanar masa da cewar yana son Zainab. Cikin mamaki Isa ya ke kallon Abdalha domin bai taɓa kawo haka a ransa ba. Abdalha ya sanar masa da irin sonsa yake mata tun ba yanzu ba, Isa ya gamsu amma ya ce kasan dai auranta yanzu bai huce wata biyu ba. Haka dai suka sanarwa da Mama ita kuma ta ce ya fara tuntubɓar Zainab domin kuwa itace ta kawo Aliyu kuma Aliyu ɗan gidane, ga kuma an kusa, ita dai batasan abun yi ba.

Bai samu Zainab sunyi mgn ba ya tunkari mahaifinsa da maganar? Zaune suke a palon harda su Maryam da Nura wanda ke karatu a gaban Nusaiba ya na bada hadda. "To muna sauraronka wacece kuma ƴar gidan waye a ƙasar nan tamu? Shek Kabir kabuga ya faɗa yana washe baki domin jin ƴar gidan wani shahararren malamin a cikin malaman sunnha ya samo. Itama Momy murmushi ta keyi tana jiran jin sunan surukar tasu. Ita kuwa Maryam da tasan kwanan zancen domin kuwa Isa ya sanar mata da komai, sai rintse ido takeyi kamar itace zata sanar musu ɗin.

Abdalha ya ce "Am am damafa fa kowa bace sai sai sai amma Zainab Ambato ce ƴar ƴar gidan mlm Adamu. Ya faɗa yana shafa ƙyeyarsa Tsint palon yayi harda Nura dake karatu domin sunji sunan wacce ya kira, ita kanta Momy saida ta tsorata, Sadiya kuwa ido ta ƙwalalo waje, Maryam kuwa rintse idon ta sakeyi tana karanto addu'o'in da suka samu damar isowa gareta. Shi kuwa Abdalha ɗagowa ya yi domin ganin fuskar Daddy...📝






*Please comment ɗinku shine zaisa mugama da wuri*



*S REZA ✍️*
[10/21 22:06] Aliyu Makko: *ADDININMU*




*S REZA... ✍️*


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*


*PAGE3️⃣3️⃣*

..... Daddy ya haɗe fuska babu a lamar wasa ko sakin fuska tsanar ɓacin rai ne kawai ke yawo a kan fuskarsa, tashi yayi ya bar palon ba tare da ya tanka wa kowa ba. Daddy na fita Momy ta sauke ajiyar zuciya ta kalli Abdalha wanda idonsa duk sun cika da ruwan hawaye ganin yanda Daddy ya ƙi tamka masa. "Abdalha me kake nufi da wannan batun na ka? Kanada hankali kuwa? Kana ganin yanda tsakanin ku da ita babu jituwa amma zaka bijiro da wannan zancen har kana iya kallon ƙwayar idon Daddy ka ce wai ƴar gidan Malam Adamu kakeso, to ko ni ban aminceba domin wannan abun zai iya haifar da rikici mai tsanani wanda dukkanmu ba zai mana daɗi ba. Cikin karyewar murya ya ce "Sorry Momy amma gaskiyar kenan na faɗa muku, kune kuka tambayeni wacce na ke so kuma ni ita nakeso kuma ita zan auura, sannan kuma yayan ta wato Isa shima sun dai-dai ta Maryam, saboda haka Momy dan Allah ki goyi bayan wannan abun domin mu kawo ƙarshen wannan matsalar. Maryam najin abunda Abdalha ya ce ta miƙe tsaye da gudu ta bar palon, su kuwa sauran kallon ikon Allah sukeyi wai Maryam da Isa, to ya zatayi da wanda ta ce shi takeso. Abdalha na faɗar haka ya tashi ya bar Momy sake da baƙi ta hanci tana kallonsa.

"Abdul" Abdul" Momy ke zabga masa
kira amma ya sakai ya bar gidan cikin jin haushin wannan ƙiyayyar da ke tsakanin iyayen nasu. Motarsa ya shiga da niyar zuwa gidan sa, sai ya tuno da zancen Mama "Su iyaye ba abin wasa bane, Addinimu bai amince da ƴaƴa su dinga tsaurara kalamamsu a kan iyayeba koda kuwa suɗin suna aikata abinda Addini bai yarda da shiba, ba'a kace kamusu biyeyya akan abunba, sannan ba'ace ku tausasa kalamanku agaresuba. Shiru ya yi yana tabbatar da wannan zance sai kawai ya fito daga motar ya koma cikin gidan. A zuciyarsa yana cewa yau wa'azi na zai fara daga gida, kuma in sha Allah sai kowa ya fahimceni.

Momy ku wa mamakin jin abunda Abdalha ya ce ta ke yi, wai Maryam ma sun dai-daita

23 / 37