ƙyar suka ɗauke shi a kan suna da ma'aikata, yaci sa'ar dai ya taɓa aiki a gidan ne kuma lokacin da yayi aikin basu taɓa gamashi da wani laifi ba. Dubu goma za'a dinga biyansa duk wata ɗaya, haka ya nuna farin cikinsa sannan ya kama aikinsa ba wasa. Ita kuwa Nana kaman yanda Aj ya ce ta kama kanta ta riƙe maraicinta ta nutsu ta mai da hankalinta a kan karatun ta, hakan tayi domin bin maganar Yayan nata. Wayar hannunta ya karɓa ya sayar, da kuɗin wayar ya sayo musu duk wani kayan buƙata domin yace bazai kwaso nasu na da ba. Rayuwa ta yi musu tsanani sosai, hakan kuma baisa ya nunawa ko wa cewar yana cikin damuwaba, harta kawunsu baisan da haka ba, wani lokaci abunda zasucima wahala yake musu, ɗan sauƙin abunma a kullum yana zuwa da bredi kida, daga ƙarshe ma Nana daina zuwa school ta yi, sai islamiyya, shiɗinma dai ana binsu bashin kuɗin wata. Duk da haka ya ce duk lokacin da Hajiya Babba zataje asbiti to baya buƙatar suyi amfani da komai nasu. Da farko Muhammad bai yardaba amma ya ga AJ ɗin kamar hakan yakeso, hakanne yasa komai idan za'a yi sai an sanar masa, albashin sa na farko ma a kan yaron ya tafi, hakan ma dan an rage masa kuɗin ne. Izuwa yanzu rashi da damuwa sun fara nunawa a jikinsu, duk da irin halin da suke ciki bai hana Kadija gabatar da kanta a gurinsa ba, amma ya mata kace kace ya ce idan a kan haka take zuwa gidansu to karta ƙara zuwa. Yanzu yana yawan zuwa gidan kawunsa kuma duk lokacin da zaije sai ya ruƙo musu bredi ya kai musu. Har Wannan lokacin bai manta da Sarah a ransa ba amma yasan babu komai yanzu a tsakanin su, yanzu itama ta daina kiransa , sai kawai yaji baiji daɗiba. Lokacin da abubuwa suka rincaɓe masa sai kawai ya siyar da wayarsa ya sayo ƙarama, kuɗin wayar kuma ya fara siyan kayan jinjiri, sannan ya biya wa Nana kuɗin school taci gaba. (Wannan kenan)
*ABDALHA POV*
Kamar da wasa abubuwa sun chakuɗe masa, Duk gurin wanda yake ganin zai tayashi domin shawo kan mahaifinsa a kan lamarin auransa amma abun yaci tira. A kan wannan abun yasa iyayen nasa sun samu matsala, yanzu haka mahaifinsa ya cire hannunsa a kansa gaba ɗaya, yanzu haka ya dawo gidansu da zama kasan cewar bashi da lafiya, ciwon zuciya ya sa shi a gaba, Daddy yayi tunanin Abdullah yana yin hakane domin ya amince da auransa , baisan cewar ɗansa ya faɗa cikin kokin love ba. Wayarsa ya ciro yana daga kwancen ya nemo numbar Isa, kira ɗaya ya ɗaga yana sallama.
"Yauwa Isa ya kukayi da shi? Yayi tambayar cikin Muryar da kanaji kasan yana cikin wani hali.
"Isa yaja doguwar ajiyar zuciya ya ce "Wallhi kunyarsa nake ji, bansan da wani ido zan kalleshiba, bansa ma mai zance masa ba.
"Kwana nawa ya rage? Cewar Abdalha yana lumshe idonsa?
"Kwana takwas? Ya bashi amsa yana jin babu daɗi ga tausayin halinda Abdalha ke ciki.
Azuciyarsa ya furta "Takwas! Sai ya kashe wayar yana jin cewar dama haka a ke ji idan kana son mutu! Gani yake babu wanda ya taɓa jin irin abunda yakeji a kan Zainab, sam bai yarda da cewar wani ne zai aureta ba, yana mata son da zai iya ja da kowa domin mallakatarta, gani yake shi nashi salon son daban yake, duk lokacin da ya tuno da cewar auranta saura kwanaki kaɗan sai ciwonsa ya tashi. Numbar ta ya kira yana jin cewar zai samu mafita daga gareta.
*ZAINAB POV*
Mutuƙar wannan auran da zatayi zaisa mahaifinta farinciki kamar yanda ya ce, to tabbas zata auri Aliyu badan tana sonsaba, zatabi zaɓin mahaifinta kodan ganin yayi alfahari da ita kamar yanda ya ce, ta yarda da cewar tana son Abdalha kamar yanda yake sonta amma wani ƙaramin abu ya shiga tsakani yayi baƙe-baƙe babu damar kaucewa. Hirar su da shi ta jiya ta tuno lokacin da ya ke ce mata "Kar zuciyarki ta raya miki cewar zaki auri wani baniba, domin haka bazai taɓa faruwa ba, kisa a ranki nine mijinki, bansan soba sai a kanki, haka zaluka bansan komai game da shiba na sa ƙafa ta a ciki, bansan komai ba ban saniba! Ya ƙara sa yana kallon wayar kamar ita zai gani. Kawar da idanunta ta yi itama daga kallon wayar tana jin cewar sonda take masa yafi wannan abun da ya lissafo kawai dai shi ya fito da nasa filine.
Ajiyar zuciya ta sauke tana jin zuciyarta na mata zafi kamar ana ƙoƙarin cirota da ga ƙirjinta. Tashi ta yi izuwa gurin Mama. Tana zuwa mama na magana da watar ƙanwarta da tazo gidan bikin, domin dangi na kusa-kusa duk sun fara zuwa. Ganin Zainab ɗin yasa Mama mayar da hankalin ta izuwa gareta. "Lafiya dai ko Zaiban? Cewar Mama tana jin tausayin ta, domin tasan Zainab bata son wannan auran kawai dai ba yanda zasuyi da Malam ne. Zainab ta buɗe baki zatayi magana kira ya shigo wayarta, ganin sunan Abdalha yasa ta kasa cewa Mama komai sai ta bar ɗakin tana ɗaga wayar.
"Isa zaizo dubani inaso kuzo tare ko da ganinki ne nayi ko zan samu sauƙin zuciyata? "Kamar bazatayi Magana ba ta ce "Ba zan iyaba! Bana fito ko ina ina gida, tun ba yauba na sha faɗa maka cewar ba'a barina fita ko ina. "Kinaso na shiga wani haline Zainab? Ya faɗa da wata murya da tasa jikinta ƙara yin sanyi? Kinsan mai nakeji a zuciyata kuwa? Wallhi ji nakeyi idan har ban gankiba zan iya rasa rayuwata? Ya ƙarasa yana tari. "Abdalha dole muyi haƙuri mu rungumi ƙaddara mubi zaɓin iyayenmu domin samun albarkasu, ka daure ka manta da ni a rayuwarka ka zama mai girma-ma zaɓin mahaifanmu domin bazasu zaɓar mana abunda zai cutar da muba, saboda haka kayi haƙuri ka daurewa zuciyarka da rashina yanzu saura kwana kaɗan na zama mallakin wani, kuma daga ranar dole mu rabu, rabuwa ta har abada Please! Tana kaiwa nan kuka yazo mata. Tana faɗa ta kashe wayar tana fashewa da kuka.
Da a ce wani ne zai faɗa mata cewar ita Zainab Adam zata iya yin kuka saboda mutumin da tafi tsana a rayuwar ta to da tabbas kallon mahaukaci zata ma koma waye wannan ɗin. Bata damu da duk abunda zaifaru a gurin al'ummar gari ba, mutuƙar zata samu abunda takeso, amma hakan ba zaisa ta yi abunda mahaifin ta zaiyi fushi da itaba kamar yanda ya ce mata.
Kulawa da kyautatawa da damuwa da ita da irin soyayya da yake nuna mata ba dare ba rana hakanne yasa itama ta faɗa a cikin soyayyarsa batare da ta shirya ba. Ya bata kulawar da wani ɗan Adam bai taɓa bataba, sannan shine sanadiyar kuɓutarta daga hannun ƴan iskan da suka kamata, bazata iya mantawa da Abdalha a rayuwarta ba, Haka ta koma ɗakin mahai fiyar tata tana ƙirƙiro fara'a ta maka a kan fuskarta.
Da ƙarfi Maryam ta saki plet ɗin abincin da ta kawo masa a ƙasa tana kiran sunan Momy. Momy da ke palo ita da Daddy tana ƙara sanar dashi irin halin da Abdalha ke ciki ya ce "Indai a kan auran wannan yarinyar da kowa ya mata shaidar banzanne to wallhi na cire hannuna a kan Abdul, ƴar bidi'a a cikin zuri'a ta! kuma ma yar gidan Adamu! To Wallhi ko mata sun ƙare a gari sai dai Abdul ya zauna a h"....'Ai bai ƙara sa ba suka jiyo ihun Maryam.
Kwance suka sameshi a ƙasa yana tari jini na fitowa daga bakinsa idanunsa sunyi jazurr kamar gauta. Ihuu Maryam take yi tana kiran sunan Daddy, hakanne yasa Sadiya da Nusaiba suma suka fito daga ɗakunansu. Kuka sukeyi dukkansu suna kiran Abdalha amma tarin bai tsayaba, duk tari sai jini ya fito daga bakinsa, ana haka Maryam ta hango wayarsa a ƙasa taje ta ɗauka. Haka suka daukoshi dukkansu suka fito da shi izuwa mota. Shek Kabir kabuga kuwa kallo ɗaya ya musu ya kawar da kansa ya na jin cewar ba a'man jiniba ko aman kwata zaiyi shidai ba zai yarda ɗan sa ya auri ƴar bidi'a ba. Nusaiba ce taja motar batare da sun jira dreban nasuba. Maryam da Sadiya ne suka shiga motar Momy kuma ta koma domin shiryowa tabi bayansu. Tinda suka shigar dashi mota Momy ta kira Dr Musa ta sanar masa, hakanne yasa tun kafin su isa a ka shirya tarɓarsu.
Momy na shiga palon ta ga ba kowa sai ta nufi sama ɗakin Daddy. Tana shiga ta sameshi yana waya yana dariya alamar dai wanda yake wayar dashi mai muhimmanci ne a rayuwar sa. Cikin damuwa da halin da ta ke ciki ta ce "Haba Shek yanzu wannan abunda kakeyi ya dace kenan bakaga halin da yaronnan ke ciki bane? A'man jini fa ya keyi, ciwon zuciya fa kenan baka tsoran mu rasa shi? Saida ya kashe wayar sannan ya juyo ya kalleta cikin rashin nuna damuwa da zan cen nata ya ce "Idan muka rasa shi ai ba shi kaɗai muka haifaba, kuma karki sake zuwar mini da zancen yaron da ban isa dashiba. Ya na faɗa ya kawar da wannan zancen ya ɗaoko wani yana sakin fara'a a fuskarsa.
"Idan zaki iya tuna wa da wani mutumi da ya musulunta yaran Alhaji Salisu, dake garin Benue Makurdi, har Alhaji Salisu ya bashi auran ƴarsa, lokacin da suka samu ƙaruwar yaro na miji har suka gaiyaceni garin nayi wa'azi? Momy ta ce "Eh ai bana manta lokacin domin a ranar na haifi Abdalha. "To amma ba kace mutumin ya rasuba? Momy ta faɗa tana tuno ranar da a ka sanar musu da rasuwar mutumin saida Shek ya kwanta rashin lafiya.
Daddy ya ce "Eh haka a ka ce, amma wai a she yana raye bai mutuba, yanzu haka yau ɗinnan yana hanyar zuwa gidannan iji Malam Nura abokinsa. Momy ta waro ido waje ta na cewa "To ina yaje tsawon shekaru? Ko dai ya gudu yabar Musulunci ne? Daddy ya ce "Yanzu haka ma wai da wasu zaiso suma zasu koma ADDININMU. Sannan ya ce "Ki ajiye tambayoyinki har sai yazo domin nima bansan komaiba, abunda nasani dai shine mutumin kirki ya dawo. Daddy ya ƙara sa yana tunano irin abun arziƙin da ya masa lokacin da ya je garin.
Daga haka Momy ta dawo da maganar Abdalha, amma Daddy ya ce "Yanzu haka yana cikin farin ciki karta ɓata masa rai. Hakanne yasa ta ce "To zan tafi asbitiin Yanzu idan ka amicen? Amma Daddy ya mata Wani irin kallo ya maka mata ya ce "Yanzu nace miki munada baƙi amma kina zancen tafiya yawo, to yanzu inaso ki kira su Sadiya su baro gurin su dawo domin a haɗa musu kayan tarɓa. Momy ta ce "Wato yarona na gadon asibiti zanje gurinsa shine zakace zanje yawo ko? Ta faɗa tana jin zafin kalmar yawon da ya ce. Daddy dai bai ce komai ba ya bar ɗakin domin zuwa tarɓar babban baƙonsa. Haka Momy ta kira Nusaiba da Sadiya ta ce Maryam ta zauna a gurin Abdalh ɗin.
A ranar suka iso garin Kano, amma basu iso gidan Shek kabuga ba suka nufi gidan su Ogan sa kuma sirikinsa wato Salisu uba ga matarsa Hajiya Babba. Su kansu basu san da dawor Muhammad ɗin ba , domin Hajiya Babba tayi hannun riga dasu tun rasuwar mahaifinta da mijinta. Ita Hajiya Babba ganinta dunta iyayen ta suka rasu a hanyar zuwa garin sai ta ɗauki abun tasa a ranta, hakanne yasa ta daina nemansu kwata-kwata.
Suma sunyi mamakin ganin Muhammad kuma sunji daɗi da ya zo musu da jikarsu gida. Lokacin da sukaji bayanin auran da Hajiya Babba tayi ne kuma ransu ya ɓaci , amma a ka basu haƙuri da cewar ai yanzu sun rabu da mijin amma tana ɗauke da cikinsa. Haka suka dinga lallaɓata Salis da laɗifa dama su suna ɗan zuwa garin, hakanne yasa suka saki jiki dasu. Samuel da Sarah dai sai bin laɗifa da Salis sukeyi. Washe gari suka shirya izuwa gidan Shek Kabir kabuga.....📝
*MUHAƊU A GIDAN SHEK*
*COMMENTS ƊINKU SHINE ABUN ALFAHARINA*
*S REZA ✍️*
[10/21 22:06] Aliyu Makko: *ADM*
*S REZA...✍️*
*First Class writer's asso...*
*PAGE4️⃣4️⃣*
........Misalin ƙarfe tara na safiya suka isa gidan Shek Kabir kabuga, kana ganin Shek kasan yana cikin farinciki da zuwan wannan baƙon nasa. Kafin Hajiya Babba ta tafi saida tasa a ka kira yayan mahaifinta Malam Adamu. Tarɓa ta mutunci Muhammad da iyalansa suka samu daga gurin iyalan Shek. Sosai Shek da Muhammad suke cikin farincikin ganin junansu, kana ganin kabuga kasan a kwai magan-ganun a bakinsa. Itama dai Momy tana nunu nata farincikin daidai yanda zata iya. Bayan an kawo musu abubuwan da a ka tana dar domin sune kowa yaci abunda zai iya ci kafi a ka sake sabuwar gaisuwa tsakanin su. A taƙaice Muhammad ya basu labarin abunda ya faru da su tsawon wannan lokacin, kuma ya tabbatar musu da cewar ɗan uwansa ne ya masa. Da mamaki Momy taga Shek na kuka yana tausayawa Muhammad, shima kansa Muhammad ɗin yayi mamaki. Bayan ya gama ne ya fara masa nasihohi a kan wannan jarabtar da ta sameshi. Sosai Muhammad da su Samuel suka ƙara yarda da Addinin musulunci, yanda sukaji irin alkairin da Allah ya tanadar ga masu yafiya idan an cucesu, sosai son Addinin Musulunci ya ƙara shigarsu har suna ji cewar zasu iya komai cikin koyarwar Addinin Musuluncin.
Shek ya kalli Salis ya ce "Kardai ka ce min wannan shine mai sunan Alhaji har ya gyrma haka? Muhammad yayi murmushi ya ce "Eh fa shine har ya zama saurayi. Ya faɗa yana dariya dukkansu. Hajiya Babba ma saida abun ya bata dariya, itama Momy dariya tayi tana kallon Salis ɗin da ke sunne kai. Ganin shek na ta kallon su Sarah ne yasa Muhamd gyra zama ya ce....
"Wannan shine babban ɗana. Ya faɗa yana nuna Salis. Sai ya ƙara nuna laɗifa ya ce "Wannan itace auta Ladifato. Sai ya dawo da kallonsa izuwa gurin Samuel ya ce "Wannan kuma shine ɗan gidan yayan nawa, shine babba sai ƙanwarsa gata nan ya faɗa yana nuna Sarah. Sannan ya ɗora da cewa..."Sannan sune suka buƙaci shiga Addinin Musulunci da kansu. Momy da shek da su Maryam da sauran suka amsa da AllahuAkbar! Fuskokinsu cike da annuri jin cewar ADDININMU zai samu ƙarawa. Momy ta ce da Maryam ta je ɗaki ta taso Abdalha. Tayi maganar ne batare da kowa yajitaba. Maryam ta sanar mata da cewar ai tun jiya da sukawo daga asbiti bai fito wajeba, ya ce kar kowa ya dameshi, sannan Dr Musa ya ce a barshi ya samu barci sosai. Badan Momy tasoba ta bar maganar amma hankalinta naga ɗanta.
Shima shek ya gabatar da yaransa ga resu. Cikin tsokana Muhammad ya ce "To a cikin su ukun suwaye a maran da za'a aurar? Shek ya nuna Sadiya da Nusaiba. Duk da hakan dai ya ce "Banga magajin Malam ba? Abokin Salis... domin bana mantawa da tsiran sati ɗayane tsakanin su? Da sauri Hajiya Babba ta ce "Ai nasa yanzu ya zama magidanci? Da sauri Momy ta ce "Allah sarki ai bashi da lafiya yanzu haka ma yana ɗakinsa a kwace baisan halin da ya ke cikiba. Salis ya ce "Allah sarki ai ina jin sunansa amma bamu taɓa haduwaba, shine Abdllah Kabir kabuga ko? Yayi maganar ne bayan ganin hoton Abdalha da mahaifin nasa a palon. Maryam ta amsa da eh shine.
Daga haka suka ranƙaya ɗakin da Abdalha ɗin ya ke. Sosai suka tausaya masa ganin yanda ya rame ya fita a haiyacinsa. Muhammad ya tambayi mai ke damunsa,? Mai yasa ba'a kai shi asibitiba? Shi kansa shek sai yanzu ya ƙara tabbatar da cewar ciwon ɗan nasa na gaskene ba yanda yake tunaniba. "Ciwon nasa bana asbiti bane na gidane! Cewar Momy cikin wata iriyar murya. Hajiya Babba da Muhammad har haɗa baki sukeyi na tambayar kamar ya? Ganin haka yasa Shek barin ɗakin yana jin wani irin abu na masa ciwo game da ciwon Abdalh ɗin. Take Momy ta kwashe komai ta sanar musu da komai, tun farkon gabar dake tsakanin yaran har ta dawo soyayya. Salis yayi mamaki sosai jin cewar a kan soyayya Abdalh ya koma haka. Da sauri Muhammad ya fita izuwa gurin Shek. Hajiya Babba da Momy ma suka bi bayan sa. Bayan fitarsu Momy suma ƴan matan suka fita. Salis da Samuel kuma suka zauna a ɗakin suna jiran ya farka. Ai kuwa basu wani daɗe a ɗakinba ya tashi. Yana tashi zaune ya fara bin Salis da Samuel da ido. Salis ne ya matso kusa dashi ya ce "Shek Abdalha Kabir kabuga Sarkin soyayya? Ya faɗa da a lamar tsokana?
Kafin Abdalh ya sauƙo daga duniya mamakin ganinsu a ɗakinsa Salis ya ɗora da cewar..."Damafa an ce malamai sunfi iya soyayya, domin su ta gaskiya sukeyi shiyasa suke shan wahala...kasan fa ita soyayya tafi wahalar da mai yinta dan Allah kamar dai ku Malamai. Izuwa yanzu Abdalha ya bar mamaki sai tsoro. Kallon Samuel yayi da ya ke ta faman dariya, sai ya dawo da kallonsa izuwa ga Salis. Ya buɗe baki zaiyi magana Salis ya ƙara so kusa da shi ya ce "Kardai a ce tsoro kake ji? Kana jarimi a soyayya amma"... Salamu'alaikum? Cewar Maryam tana shigowa ɗakin riƙe da tiran kayan marmari. Tana shiga saiga Sarah da Laɗifa suma sun shigo.
Salis ya kalli Maryam cikin dariya ya ce "Maryam wacece take wahalar min da abokina, ƴar gidan waye a wannan ƙasar faɗa min yanzu muje mu jawo mata a'ya da hadisai? Maganar tasa saida taba Abdalha dariya, sai ya ɗan murmusa yana kallon Maryam a lamar tambaya jin Salis ɗin ya ƙira sunan Maryam. Kafin Maryam tayi magana Abdalh ya ce "Wai dama mazama suna zuwa gurin aure tin aure yana saura sati guda? Yayi tunanin ko