Hajiya Babba kafin ya buɗe baki ya ce "Kina nufin idan munyi sati ɗaya shikenan saura wata biyar? "Eh saura wata biyar amma fa shima da sharaɗi? A.J ya ce "Wani sharaɗi kuma bayan wanda nake ciki? Hajiya Babba ta kalleshi da kyu kafin ta matso kusa dashi kamar zata shiga jikinsa ta ce "Sharaɗin guda ɗaya ne kawai idan har zaka yarda? Taci gaba da cewa... Banaso kayi waya da kowa har sai mun dawo, abun nufi shine bazaka kira kowaba har mu dawo, kuma..."Bata ƙaraba ya ce "Na yarda. Cikin mamaki take kallon sa kafin ta ce "kayarda? Ya ce "Yes na amince, amma inaso zanyi waya da Nana yanzu? Hajiya Babba ta ce "Badamuwa. Haka ya shiga kiran numbar Nana amma bata shiga, sai ya kira number Innah itama dai bata shiga.
Nann take hankalin sa ya ɗan tashi domin kuwa yasan Nana bata barin waya babu chaji, saida takira yakai sau goma amma dai bata shiga. Har ya haƙura sai ya kira number Sarah, itama dai ga numbar ta shiga amma no amsar, haka ya dage da kira amma dai duk ɗaya, sai kawai ya rubuta ɗan ƙaramin text message ya tura mata sannan ya miƙawa Hajiya Babba wayarta kafin suka fara tafiya. Basu samu damar tafiya a ranarba dalilin babu jirgin da zaitashi, sai zuwa gobe. Ai kuwa washegari haka suka tashi da sassafe bayan ansha amarci, suna zuwa basu daɗba jirginsu yabar Nigeria izuwa ƙasar *MOROCCO*.
Ɓangaren su Salis kuwa, da ƙyar sukaci sa'a police ɗin nan ya amince zasu dinga kawo wa su Innah abinci sau uku a rana, hakanma saida sukayi ciniki da police ɗin, domin kuwa yace idan har a ka kamashi to wallahi korarsa za'a yi. Haka dai har su Innah sukayi kwana huɗu a cikin sell ɗin nan amm Daddy baibi ta kansu ba. Salis da Kamal kuwa kullum sai sunje, dukda basa wani samun damar yin magana dasu, domin kuwa police ɗin yace idan a ka gansu to da matsala. Ananne Salis ya tambaye police ɗin a kan waye ya kawosu police station Kuma a kan meye?
Nan police ɗin ya sanar dashi komai game da Daddy, wato ya ce "Comomda Deniel ne ya kawo..."Ai bai ƙarasaba Salis ya miƙe tsaye ya ce "What!! Daniel? Shima police ɗin cikin mamaki ya ce "Yes Kasan shine? Salis bai tsaya amsa masa tambayar ba ya bar cikin police station ɗin cikin sauri kamar zai faɗi. Shikuwa ɗan sandan ganin irin razanar da Salis yayine yasa yayi tunanin kodai Salis ɗin yasan Daniel ɗinne!?.
*GIDAN SOJA*
Yau kana huɗu kenann da kullesu Samuel wanda yayi dai-dai da kulle su Innah da Nana a cikin sell. Har kawo wannan lokacin Daddy bai ƙara zuwa police station ba, sannan bai ƙarabi ta kansu Samuel da Sarah ba. Yanda ya shirya a ransa shine...kwanakin da ya basu na cika zai ɗau hukunci a kansu. Su kuwa Innah da Nana ya barsune a kan har lokacin da shegen yaron zai dawo, idan kuwa bai dawoba, to tabbas kamar yanda ya ce abaya saide su mutu a haka. Har yamatsu yayi ido biyu da wannan A.J ɗin, domin kuwa tun kafin ya ganshi har ya tsaneshi.
Samuel kuwa sun gama shiryawa da shi da Laɗifa da kuma Umar a kan zasu kawo kuɗin gobe. Bayan haka kuma sun shirya a kan Samuel ɗin zai gudu daga gidan bayan komai yayi dai-dai. Ɓangaren Sarah kuwa acikin wannan kwana huɗu tarame sosai kuma kullum sai sun kira number A.J amma har yanzu bata shiga. Tayi kuka har ta godewa Allah. Samuel kuwa yanzu mugun tausayin ta yakeji, domin kuwa yasan halin Daddy tsaffff zai zaneta a kan kuɗinsa. Kaman yanda yace sau biyu za'a ɗinga basu a binci a kullum, tabbas hakanne, idan kuwa an kawo Samuel zaice Sarah tace itama tace yaci. Haka dai zasu zauna suci don dole. Wannan ɗan zaman da sukayi har sunyi shaƙuwa sosai wanda da basuyi ba....
Ko wannan su yanzu tausayin ɗan uwansa ya keyi, yayinda Samuel yake shirya yanda zai gudu da ita batare da Daddy ya saniba. kallon ta yayi cikin yaransu na tibi ya ce "Sarah yanzu idan wannan kwana shidan ya ciki AJ ɗin bai zoba ya zakiyi?
Cikin kuka da yazama mata aiki ta kwanta a jikin yayan nata ta ce "I don't no! ban saniba, amma inaji a jikina cewa AJ zai dawo gareni, domin kuwa yana sona.
Samuel ya ce "Sister saura kwana biyu fa? kina tunanin zaizo a cikin kwana biyu?
"Ban saniba! Ta baɗa tana kifa kanta a kan ƙafarsa tana fashewa da wani irin kuka mai cin rai!. Tabbas Sarah tana son AJ sosai, domin kuwa ita har yanzu zuciyarta bata yarda a kan cewar kuɗi yayi ya guduba, amma wani ɓangaren daga zuriyar ta tana sanar mata irin son kuɗin AJ ɗin, tabbas tasan aj sosai, tasan halalin sa na san kuɗi, domin yana faɗa mata cewar...
"Sarah duk wani abu da zai kawo min kuɗaɗe to tabbas zanyishi mutuƙar ADDINIMU bai hanaba, inason naga nayi kuɗi sosai kodan na taimakawa Innah ta da ƙanwata da kuma matar da zan aura da kuma ƴaƴana. Sannan zan iya yin komai wajan kare mutuncin family na, zan zamar musu bango a rayuwarsu, bazan barsu suyi kukan rashinaba koda kuwa zan ƙarar da rayuwata a kan hakan.
Da sauri Sarah ta tashi tsaye bayan ta dawo daga tunanin ta ce "No no no AJ bai guduba, bazai iya guduwa yabar family ɗinsaba, a kwai abun da ke faruwa, AJ baisan an kulle su Innah ba da ya sani zaizo koda kuwa Daddy zai yanka shi. Ta ƙarasa da cewa akwai abunda ke faruwa!. Samuel ya kamota yana kuka yana mata sorry. Amma yaƙi sanar da ita cewar harda ita zasu gudu, domin yasan bazata yardaba. Haka dai ya rarrasheta har yayi sa'a tayi shiru tana bai cigaba da tuno magan-ganun Aj akan kuɗi da kuma family ɗin sa.
*LAƊIFA. UMAR. POV*
Kallonta yayi ya ce "Gaskiya ni bazan iya zuwa gidannan ba, domin kuwa mutumin yasanni, kuma ya tsani musulmai sosai, bai ƙaunar addinin Muslunci koda kuwa a gurin kasuwacine bare har wata mu'amala ta haɗashi dasu. Cikin jin haushe da kuma ganin tsoron Umar ɗin Laɗifa ta ce "Kaide wallhi anyi raƙon na miji a gurinnan, gaka dai namiji iya namiji amma sai shege tsoro. Umar ya ce "Aini da kika gani inada kiyaye lafiyata harta ƙanwata Hadiza a bokiyar faɗarki to itama tsoranta nakeyi domin kuwa wallhi yarinyar tamkar mai aljannun, tasha faɗa da maza kuma tayi nasara a kansu, shiyasa ake tsoranta daga maza har mata, kema dande baki santa bane da har kika biye mata.
Laɗifa ta ce "Au dama aljannun gareta!? Ta ƙarasa tana zaro ido.
"Eh tanada su masu shegen ƙarfi ma kuwa. Ya faɗa yana dariya.
Laɗifa ta ce "Kaga yanzu dai faɗa min gidan su Samuel ɗin da kuma sunan Daddy ɗinsu ni zankai tinda kai matsoraci ne. Ta faɗa tana kawar da wancen zancen da sukeyi.
Umar ya zaro ido waje ya ce "Kece zaki kai kuɗin!? Bakiji abun da nace ba?
Ta ce "Please faɗa min bana son wasa? Tafa da alamar da gaske take.
Umar ya fara address ɗin gidan sannan ya ce "Sunan sa Comamdar Daniel!
Cikin rikicewa da nuna alamar mamaki ta ce "What!? me ma kace Daniyal ko wane!?
Shima Umar meƙewa yayi cikin mamaki ya ce "Eh Daniel na ce kin san shine!?
Cikin tashin hankali Laɗifa ta ce "Umar zan kiraka bari naje gida Please, zan nemeka anjima. Bata tsaya taji mai zeceba ta bar shi agurin baki a sake yana binta da kallon mamaki. A fili ya ce "Ninasan bazata iya zuwa gidan wannan ƙaton arnan ba, domin kuwa kowa yasan ƙiyayar sada musulmai a garin nan, ƙwafa yayi yana ɗan taɓa baki irin ko a jikin sa kafin shima ya bargurin cikin jin haushen ta barshi da hawa keke.
*ABDALHA. POV*
Kafin Maryam ta rufo 'kofar d'akin nata har Abdalha ya kamota, kan kace me ya ɗaga hannu ya zabga mata mari, cikin ɓacin rai da jin haushin abunda ta ce ya ce "Ni abokin wasan kine da har zaki kalli idanuwa kice wai sonta nakeyi!? Ya faɗa yana ƙara ɗaga hannu da niyar ƙara mata wani marin, sai sukaga mai gadin gidansu ya shigo har palorn gidan cikin kiɗimewa abunda bai taɓa yiba.
Ganin haka yasa Abdalha ya mayar da kallonsa izuwa gurin mai gadin. Ya buɗe baki da niyar fara yiwa mai gaɗin faɗa a kan shigowa gidanne domin kuwa sun hanashi shigowa, koma me zaiyi ya tsaya daga waje. Mai gadi cikin rawar baki yace "Ranka shidaɗe, ga wasu samari nan sunzo sai bub-buga ƙofar gida sukeyi suna kiran sunan ka suna zagi wai a fito musu da Zainab.
Cikin tashin hankali Mommy ta ce "Ai kagani abunda nake gudu kenann, me ya kaika sace ta!! Shinma wai saceta ɗinne zaisa ta daina waƙoƙin kodai mai!? Mommy ta fara faɗa tamkar zata ari baki. Maryam da Sadiya da kuma Nusaiba da Nura, sai kuka sukeyi, domin kuwa izuwa yanzu suna jiyo ƙarar dukan get d'in gidan. Su kuwa ƴan matan da sukazo ɗaukar katu, jin abundake faruwa ne yasa, suma suka fara ihuuu, domin kuwa ƙarar dukan git ɗin da ƙarfi sukeyi.
Abdalha kuwa hankalin sa ya tashi ganin irin kukan da Mommy da kuma sauran ƙanƴan nasa sukeyi, sannan kuma ga magan-ganun da mommy ɗin keyi. Shi gaba ɗaya ma abun ya ɗaure masa kai, bai masan ta ina zai faraba. Afili ya ce "Tabbas wasu suna bibiyata!! Take ya ɗauki waya ya kira police station ya sanar dasu abunda ke faruwa a gidan su. Suna jikin haka saiga kiran Shek Kabir kabuga, kallon wayan Abdalha yayi wanda shi tsabar ruɗewama har ya manta bai kirashiba. Ya ɗagawa Shek Kabir kabuga ya ce "Abdalha ina ka kai musu yarinya!? Shin dama abun da kake shiryawa a kanta kenan!? Shek yayi maganar cikin ɓacin rai domin kuwa yanzu ya fara ganin saƙonnin da kuma kira akan samari sunje gidan sa. Nann aka fara kiransa har saida ya kashe waccar wayar tasa.
Shiru Abdalha yayi yana mai jin kansa na sara masa. Azuciyarsa ya ce me ke shirin faruwa ne! Harda Daddy. Yana cikin wannan tunani yaji muryar daddy na cewa "Abdulhi bada kai nake bayaniba!? jin aldalha baiyi magana bane yasa Daddy cewa Abdullah..."Kit yaji an kashe wayar. Daddy yabi wayar da kallo yana mamaki, kenann da gaske Abdalha ne ya saceta!?.
Abdalha kuwa yana kashe wayar yayi hanyar fita ba tare da yayiwa kowa maganaba. Jin kiran da Momy kemasa ne yasa ya tsaya yana kallonta, kafin Mommy tayi magana ya ce "Momy bansan me zanceba ban saniba!, ni dai abun da nasani shine tabbas ana bibiyan rayuwana, amma koma waye zan gano!. Cikin ɓacin ran jin maganar da ya ke cewa mommy ta zabga masa mari ta ƙara masa sannan ta ce "Tsabar ka rainamu, ina ji yanzu kuna magana da Daddy ka kashe waya batare da kace komai ba. Nikuma ina maka magana kana fita yanzu kuma kana min wani zance saban. Shin da gaske kaine ka sace ta!? Mommy ta tambayeshi tama mai ƙara fashewa da wani kukan. Abdalha ya riƙe gurin da mommy ta mareshi yana jin abunda tinda yake Mommy da Daddy basu taɓa masaba amma a kan ta amma mareshi. Yanzuma shiru yayi domin kuwa tabbas baisan me zaiceba, abinda yasani shine ana bibiyar rayuwarsa....✍️
*
*PAGE* 1️⃣8️⃣ *Babu editing*
..........Cikin tsananin mamaki Abdalha yake kallon Mommy wacce ta ɗaga hannu ta mareshi a kan abunda batada tabbacin sa, ya kalleta cikin mmk ya ce "Momy ban saniba bansan komai ba wasune suka saceta amma ni bani bane pls Mommy ki yarda dani karki bari zuciyarki ta aminta da wannan zancen. Momy ta kalli ɗan nata cikin tausaya masa tace "Shin me ya kaika gurinta lokacin da abun zai faru? "Mommy bansan komaiba kamar yanda na sanar miki, kuma nuda kaina zan gano komai pls ki yarda dani. Yana gama faɗin haka yabaar gidan cikin tsananin mamaki abubuwan da ke faru kamar wani shirin Film. Lokacin da Abdalha ya isa ƙofar gidan nasu har police ɗin nan sun kama na kamawa sauran kuma sun gudu, kallon police guda biyu da ke jikin ƙofar gidan nasu yayi wanda a ka bari domin basu tsaro yayi, kallon su yayi cikin takaici domin kuwa kallo ɗaya ya musu ya gana ba musilmai bane, a zuciyarsa ya ce "Tabbas wannan shirine kuma zan kawo ƙarshensa yau. Police ɗin dake nufoshi ya ɗagawa hannu a lamar bayan tsaron nasa , amma police ɗin yace ai hakan umarnine dole sai yayi. Haka badan Abdalh yasoba suka shiga motar shida ɗan sandan suka fita.
Ɓangaran gidan su Zainab kuwa har yanzu babu labarinta, yayinda Isa ya dinnga yaɗa cewar Abdalha ne ya saceta kuma tabbas yanda labarin ke bazuwa idan kagani dole ka yarda. Ƴan gurgiyar Abdalh da sukaga abun ya fara yawa sai suma suka fara mayar da martani akan ai shi Abdalh baɗan bidi'a bane yana amfani da ilimin sa, saide kaga majalista ta samari daga hira sai zage-zage sai faɗa. Har takai ta kawo wasu daga ciki suna tono tsoffin asirin wata gurgiyar. Budurwa da saurayi aboki da aboki mata da miji, malami da ɗalibai, uba da ƴaƴansa, maƙofci da maƙofci, dukkan su mutuƙar ba kungiyar su ɗayaba to Tabbas sanadiyar wannan abun Kai ya ƙara rabuwa. Kai abundai ba'a cewa komai domin kuwa lamarin ya gawarta.
*SALIS LAƊIFA POB*
Cikin sauri kamar zata tashi sama tsabar ruɗewa ta banko ƙofar palorn tana ƙoƙarin haurawa sama, sai tayi ido biyu da Salis yana zagayawa a ɗakin cikin tashin hankali. Da gudu ta ƙaraso gurin da yake ta buɗe baki zatayi mgn, cikin harɗewar murya ya ce "Com com comand Comandar Daniel ne ya kullesu?. Ya ƙarasa maganar yana kallon laɗifa wacce Salis ɗin ya ƙara sakata a cikin duhu domin ita bata gane me yaceba, ta daiji yace Daniel amma fata fahimci gaban ba. Ta ce "Pls Yaya banji me kace ba, itama ta faɗa tana kallon cikin idonsa? Salis ya ce "Gajiya Babba dole ta dawo yau ɗinnan domin kuwa a kawai matsala?.
Laɗifa ta ce "Pls Yaya sanar dani abunda ke faruwa ban ganeba fa? Ni nashigo da maganar Comandar kuma kaima naji kana min shin wani abun ya haɗoka dashi ne?
Cikin sauri Salis ya fasa danna kiran numbar Hajiya Babba ya dawo da kallonsa izuwa gurin Laɗifa ya ce "Me zaki sanar min akan Comandar ɗin?
Da sauri Laɗifa ta ce "Shine baban wannan yaron da nace maka inaso wannan Kristen ɗin..."Ai tin kafin ta ƙarasa Salis ya ce "No no no, ya miƙe tsaye yana kallonta wacce itama ta miƙe tsaye ya ce "Bakida hankaline kin matan waye Daniel da har zakije kifara soyayya da yaronsa ko? Kafin ya samu matsayin Comanda ma ya muka ƙare dashi bare yanzu...damade baki sanarwa da yaron cewar kina sonsaba? Ya tambayeta yana son yaji tace masa bata sanarba.
Cikin kuka ta ce "Wallhi Bro bansan shine babansa bane ban saniba, ta faɗa tana ƙara fashewa da wani sabon kukan.
Salis ya ce "kin faɗa masa?
Ta ce "Eh harma mun zama...
Da sauri Salis ya ce "Yanzu haka shine ya kulle yarinyar da nakeson aura tare da innarta basu san hawaba bare sauƙa, kuma ya ce bazaibada Berlin ɗinsuba sai yaga wanda yake nema.
Ta ce "Pls bro mukira Hajiya Babba? Ai kuwa take suka shiga kiran Hajiya Babba amma bata shiga. Itama laɗifa ta shiga kiranta da wayarta, amma duk ɗaya.
Salis ya kalli laɗifa ya ce "Akwai matsala domin kuwa Hajiya bata ƙasar nannn tin jiya number ta bata shiga. Laɗifa ta ce "To ina yaron da suka tafi tare? Sai a lokaci Salis ya tuna da cewar a shefa Hajiya tare da A.J suka tafi, sai kawai ya nemo numbar AJ ɗin domin kuwa yasan tunda ita bata ƙasar to shi yana 9j. Da sauri ya shiga kiran numbar amma shima yaji bata shiga. Kallon juna sukayi suna mamaki, laɗifa ta ce "To ko zamuje gidan su yaron mu tambayeshi da gaske Hajiya tabar 9j?
Cikin ɓacin rai Salis ya ce "Dan Allah malama sunansa AJ ba yaroba! Ko bai girmeki bane? Kuma bari kiji yarinyar da zan aura ɗin ƙanwarsa ce, kuma itace a ka rufe a police station itada innar su, kuma Comandar ne sannan kuma AJ ɗin yake jira ya dawo kafin ya sakesu.
Wani abu taji shuuu ya shiga kunnenta kafin taji alamar iska, ta ce "Ok sai yanzu na gane abunda ya sakaka a tashin hankali a shedai saboda soyayya ne ba dan abunda wancen tsohon arnan ya manaba. To walhi bazamu taɓa haɗa jini da wannan matsiyatan ba, har kake cewa wai ita zaka aura to dan ubanta tazo gidan mu gani.
Cikin kwantar da hankali ya ce "Yanzu dai ni bama wannan ba, yanzu meye abunyi? Ta ce "kawai ka manta da su domin banaso mu ƙara shiga sabgar wannan ƙaton arnan. Abunda Salis bai saniba shine, laɗifa ta gama haɗa kuɗin da zata ƙwato Samuel domin kuwa ta so ta sanar dashi gaskiya amma jin shina Musa soyayya ce ta kaishi sai kawai tayi fuska a kan kowa yaji da damuwarsa abunda Basu samaba.
Salis ya ce "Ban gane na barsuba! Kinaji nace matar da zan aura amma kice wai na barta? Jin tambayar da tamasa yasa ya shiga tunani, tabbas abunda ya kamata ya fara sani kenan Amma ya manta.
"Wai ma me sukayi har ya kaisu police station suna mata? kidan yaga su ɗin musulmai ne ba addininsu ɗayaba. SALIS ya ce "No suma basu san me sukayiba domin bai sanar musuba, amma dolema na sani yau ɗin nan, ya kamata muga AJ. It's dai laɗifa waya ta ɗauka tana kiran Umar domin ita dai bazataje gidan su Sameul ɗin ba.
*GIDAN SOJA*
Da sauri Daddy ya shigo palorn yana kiran Mommy Eliza! Eliza! Kai da jin irin kiran kasan cikin ɓacin rai yake, itama Momy ɗin da sauri ta fito daga ɗakin tana cewa "I'm coming sir. Tin kafin ta ƙaraso ya ce "Zuwa gobe naba yaranki a kan