Addininmu Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  S Reza Category :  Love

Chapter   24 / 37

69K to 72K   out of 109.2K words

da Isa. Kallon Nura Momy tayi ta ce "Nura kira min Anty Maryam yanzu. Da sauri ya miƙe yana ɗan sakin dariya. Kafin Nura da Maryam su zo Abdalha ya shigo cikin palon kai a sunkuye. Yana zama saiga Maryam ta re da Nura ta sakoshi gaba yana kuka.

Da sauri Nura ya nufi gurin Abdalha ya na share hawaye domin kuwa yasan shikaɗaine zai rama masa. Kafin Abdalha ya ce wani abu Sadiya ta ce "Yanzu-yanzu daga shigar sa ɗakinki har kin sa kashi kuka, kawai dan ya je ya miki wasa, kinji kunya walhi. Cikin rashin kunya ta ce "To ni abokiyar wasar sa ce da zaije har ɗakina yana min dariya, ko ni ɗin mahaukaciyar ce? Maryam ta faɗa tana ji kamar ta ɗauke Sadiya da mari. Momy ta kai kallonta ga Maryam ta ce "Kin kyuta Maryam, kici gaba da cin zalin ƙaninki karki fasa. Momy na faɗa ta dawo da kallonta izuwa ga Abdalha. Maryam da Sadiya kuwa sai hararar juna sukeyi, Sadiya tana jin cewar yau da Abdalha baya gidannan da sai ta saukewa wannan yarinyar abunda ke kanta. Abdalha ya sharewa Nura hawaye yana kallon Maryam. Momy ta ce...

"Karna ƙara jin wannan maganar ta auran ka da Zainab da kuma shi Isa da Maryam ɗin, kuma ka tashi ka je ka ba Daddynku haƙuri yanzu nann? Momy na faɗa ta miƙe zata bar gurin Abdalh yayi saurin cewa..."Momy ina sonta kuma ita nakeson aura, shin hakan bai dace bane? Cikin tsananin mamaki ta ce "Eh bai daceba, kuma karka sake min wannan maganar, kema kuma karna sake jin kiyi magana da shi yaron. Momy ta faɗa tana nuna Maryam cikin ɓacin rai. Da sauri Maryam ta gyaɗa kai tana jin cewar ai ku wa ba zata saɓu ba.

Cikin ƙarfin hali Abdalha ya ce "To Momy a kam me? Ya ci gaba da cewa..."Haba Momy karkema ki zama karmar Daddy mana, kecefa kike ƙaramin ƙaurin gyiwa akan abunda muke aikatawa, amma yanzu kema kina so kiyi hani da abunda Allah bai hanaba. Dan Allah Momy ki tayani shawo kan Daddy ya gane cewar badon ɓacin ransa zanyi ba. Momy ta kalli Abdalha taga hawaye sun wanke masa fuska ta kawar da kai ta ce "Abdalha duk abunda zaka aikata mutuƙar babu yardar iyayenka to wannan abun ba zai taɓa albarkaba, kuma kaima kasan da haka, amma yanzu abinda na keso da kai shine..."Kaje ka samu amincewar daddynku idan har ya yarda to nima na amince.

Abdalha ya ɗaga kai ya kalli Momy ya ce "To amma Momy kema ki tayani masa bayani mana ko zai sauƙo da hanzari? Da sauri Momy ta ce "A'a yanzu idan ba sokake dukkanmu ran kowa ya ɓaciba to ka je da kanka. Abdalha ya ce to Momy na gode sosai kuma zan dage da addu'a domin Daddy ya yarda. Momy ta katseshi da cewar "Ita yarinyar ta yarda zata aureka ne? Kuma iyayenta sun amince? Abdalha ya sauke wata a jiyar zuciya ya ce "itama mahaifinta ne kawai matsalar, amma mamarta ta yarda. Saide kuma.... Sai yayi shiru yana sosa ƙeya. Momy ta ce "Uhum sai de kuma me? Abdalha ya ce "Momy har yanzu fa ban ban sa sa nar mata ba.

Momy ta ce "Ban gane baka sanar mata ba? Kafin Abdalha ya yi magana sai jin dariyar Maryam sukayi. Dariya ta keyi sosai ka kace sabuwar kamu ce. Ta ce "Momy Yaya fa yana nufin bai sanarwa da Zainab ɗin cewar yana sontaba.

Sadiya ma abun ya bata dariya amma ta shanye kayarta a cikin ta. Galala Momy ta ke bin Abdalha da kallo ta ce "Da gaske? Ya harari Maryam ya ce "Umm, amma ai tasan ina sonta kuma itama haka dama kawai kune nakeso kuyarda. Momy ta ce "Allah dai ya kyuta. Tana faɗa tabar musu palon itama Maryam ta tashi da gudu ta koma ɗaki. Abdalha ya saki dariya yana kamo hannun auta Nura suka nufi ɗakin Daddy.

Haka dai Abdalh ya ci gaba da shawo kan Daddy amma Daddy ya ce "Mutuƙar shine zai masa aure to bazai aura masa ƴar gidan Malam Adamu ba. Ɓangare ɗaya kuma har zuwa yanzu bai sanar da Zainab cewar yana sontaba, amma dai yana nuna mata alama kuma itama tana gane wa. Sai a kayi Sa'a itama ta na sonsa, saide kuma ya makara domin yanzu haka lokacin auranta matsowa ya keyi. Abdalha kuwa shi ya ma manta da cewar an kusa auran Zainab, burinsa ma hsifinsa ya yarda sannan ya tunkareta. Yanzu haka auran Zainab ya rage wata guda da kwana huɗu, amma har yanzu babu wani canji a gurin Daddy. Abdalha kuwa yanzu hira sukeyi da Zainab ta waya Sosai, amma dai bai furta mata kalmar soba. Haka suma Sadiya da Nusaiba auranmsu saura wata ɗaya da kwanaki. (Wannan kenann)

*BENUE*. *ASIBITI*

Cikin aminci Allah jikin marasa lafiya yayi sauƙi. Yau kwanansu shida a asibitin kuma yaune za'a sallamesu. Dama dukkansu jikinsu yayi sauƙi Hajiya Babba ce dai tafisu shan wahala, sai kuma Laɗifa itama da ta samu buguwa a ƙafarta. A.J kuwa lokacin da ya farfaɗo sunan Innah ya fara kira yana mai sakin wani sabon kuka, amma sai yayi ido biyu da Sarah a bakin gadonsa tana sakar nasa murmushi. Tin baya sake mata hardai ya fara bata haƙuri domin kuwa kunyarta ya keji, kullum idan sun zauna sai yata bata haƙuri ita kuma ta ce ta haƙura ai dama bai mata komai ba. Cikin kwana biyu har suka sake sakewa da juna, Sarah kuwa duk lokacin da ta ganta a gaban AJ ɗinta sai wani sanyin daɗi ya mamaye ta. Tana son AJ sosai sonda bata san asalinsa ba, tanada tarin tambayoyi da take son masa amma tsabar farin cikin da take ciki na ganin sa cikin ƙoshin lafiya yasa duk ta tattara ta ajiye a gefe guda. Titi da yayanta Muhammad kuwa kuka suka sha sosai tana bashi haƙuri akan abunda ya faru, shima yace babu komai. Salis ma ya samu sauƙi so yake a sallamesu yaje ga masoyiyarsa, laɗifa kam ganin babu wanda yaji ciwo sai ita sai kawai ta ƙara lanƙwaɓewa sai zuba shaƙwaɓa takeyi, Ga kuma haushin yanda taga Sarah na mannewa AJ kamar ta sanshi, sannan ga ɓakin cikin rashin Samuel ɗinta, ko yanzu yana wani hali harbin da a kamasa!. Umar da Usman ma duk sun dawo haiyacin su. Cikin sauri Dr ya shigo ɗakinda suke tare da wasu manyan sojoji, suka yiwa Titi da Muhammad tambayoyi game da Daniyel da kuma abunda ya faru. Ai kuwa Titi ta kwashe komai ta sanar musu. Dr ya basu sallama sannan a ka haɗasu da masu kula dasu harna tsahon lokaci, kuma suka tabbatar musu da cewar za'a buƙaci ganin su a kowani lokaci. Dr ya kamo hannun Salis ya ce "To Allah ya ƙara lafiya , saide a dinga kula da Hajiya domin na kula tana cikin damuwa, kuma idan wani abu ya faru za'a iya nemana. Salis ya saka masa numbar sa sannan sukayi sallama.

Anfito za'a tafi AJ ya ce shi abarshi ya tafi gida domin kuwa har yanzu a tsorace yake. Yasan meye aure kuma yasan meye mutuwa kuma ya gane cewar yanzu idan bai rabudasu Hajiya Babba ba to tabbas a kwai matsala, wata zuciyar kuma tana tuno masa da miliyan hamsin ɗinsa.


Salis ya ce "No kazo muje gida idan kayi wanka kaci abinci ka huta sai na rakaka? Sai a lokacin komai ya dawowa Hajiya Babba. Ai kuwa cikin sauri ta ce "A'a ai tunda kaji yace gida zaije to ai kawai abarshi ya tafi, domin ko ya biyomu bazai samu nutsuwa ba, kawai ya je, Allah ya kiyaye hanya. Hajiya ta ƙara cikin rawar murya kamar mara gaskiya. Laɗifa ma ta ce "To dama me zaije ya mana a gida bayan suma sunada nasu gidan, kawai ya tafi abunsa. Ta faɗa tana hararansa. Sarah da Usha da Titi dai basu san me a ke cewa ba amma sun lura da cewar AJ ne keson tafiya gidan su. Muhammad ma ya sa baki a kan yazo amma Hajiya Babba ta ce sam bazaije ba, abun ya bawa Salis maku. Ya ce "Wai Hajiya ko kin manta da cewar AJ dreban kine?

Cikin sauri ta ce "Eh na sani yanzu na bashi hutu harya warware. Kafin Salis ya sake magana Sarah ta ce "Pls My AJ karka ƙara tafiya ka barni dan Allah Pls kazo mu tafi. Take Hajiya Babba ta kalli AJ shima ya kalleta, sai kuma ya tuno da dokokin auransu, ita kuma gabantane ya faɗi jin kamar Sarah ta san shi. Laɗifa ce ta ƙwace hannun AJ daga na Sarah ta na cewa "Rabu dashi ya tafi umma ta gai da Aish. Cikin dabara Hajiya Babba ta yiwa AJ magana da ido alamar ya tafi zasuyi magana ta waya.

Haka kuwa a kayi badan Sarah ta soba suka nufi gidan Hajiya Babba baki ɗayansu. Kowa yayi wanka sannan Muhammad da su Umar suka je shagon aski a ka gyara musu fuskoki aka dawo gida aka fara hirar bayan saduwa amma banda Hajiya Babba.

Hajiya Babba ɗakinta ta shiga ta rufe da maƙulli sannan ta fara zuwa da dawo a cikin ɗakin cikin neman mafita. Afili ta ce "Na shiga uku ni Aisha wannan wani irin masifa ne ke nufoni, yanzu dai a zahirin gaskiya inada aure kuma gashi tsohon mijina ya dawo, to yanzu a ƙaidar Addinimu ko da nasa AJ Ya sakeni to ai dole sai an ƙara ɗaura wani aura. Wata zuciyar ta ce "To kawai ki sanar masa da cewar kinyi aure amma mijin ya mutu sai kawai a ɗaura muku wani auran. Ajiyar zuciya tayi sai kuma ta ce "To Salis da Laɗifa fa ai sunsan banyi aureba, kuma idan suka sani a kwai matsala. Cikin tashin hankali Hajiya Babba ta fashe da wani sabon kuka tana ɗoraj hannu a kai tsabar rashin ma fita.
Muhammad kuwa ganin Hajiya Babba mata gurinne ya kalli Salis ya ce "Ina Aisha? Kafin yayi magana Titi ta ce "Solomon Pls".... Kafin ta ƙarasa Salis ya ce "Pls Anty Titi not Solomon is Muhammad. Ya faɗa cikin wasa ai kuwa dukkansu suka fashe da dariya, Titi ta ce "Ok Oga Salis naji Muhammad. Titi tayi gyara murya ta ce "Wai Hajiya ita aisha ɗin tunda solom or sorry Muhammad ya tafi bata sake yin wani auran bane? Ko dama Addinin naku baya yarda idan mijin mutum ya mutu yayi wani auran? Gaban Muhammad ne ya yanƙe ya faɗi, domin kuwa tambayar da ya keson ya yiwa Salis da laɗifa kenan amma ya rasa ta ina zai fara....📝





*TOFA! ANA WATA SAI GA WATA*


*BY S REZA ✍️*
[10/21 22:06] Aliyu Makko: *ADDININMU*




*S REZA...✍️*

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*


*PAGE 3️⃣4️⃣*
.....Da sauri Salis da Laɗifa suka kalli juna alamar farincikin da suke ciki jin abunda sukayi yau zaiyi rana. Salis ya saki ajiyar zuciya ya na tuno irin rikincin da suka sha a kan hana mahaifiyar tasu aure ashe hakan alkairine a rayuwarsu, idan bai mantaba zai iya ce wa sun kori zawarawa da samari sa ma da guda goma sha, wasuma badan Allah suke zuwa ba sai domin dukiyarta, amma Allah yasa bazasu bari tayi wani auranba, sunyi haka ne badan ko suna tabbacin mahaifin nasu zai dawo garesu bane, sunyine domin basa so su tashi batare da mahaifiyar suba, ko kuma su tashi da ƴan u'ba ba. Itama Laɗifa tunanin da takeyi kenan. Salis ya ce "Anty ai bata yi wani auran ba, mune muka hanata domin masu zowa neman auran na ta duk saboda dukiyarta suke sonta. Cikin mamaki Titi ta ce "Jesus kuna nufin kuce duk tsahon wannan lokacin batayi aure ba? Laɗifa dake kusa da Muhammad ta kwanta a kan ƙafarsa tana ce wa "Ni dama jikina na bani Daddy bai mutuba zai dawo shine yasa mukace bazatayi aureba har sai ya dawo. Muhammad ya faɗa dogon tunani a kan matar tasa...

Anya kuwa Aisha zata iya kaiwa wannan lokacin batare da na miji ba! Yasan wacece ita, ita ɗin wata irin halittace a cikin mata wacce irinsu basu da yawa, ita ɗin ta kasance mai tsananin buƙata, wacce ta rabu da maza a kan rashin biya mata buƙatun aurataiya, amma yanzu ta iya kaiwa wannan lokacin ta na matsayin harija! Salis ya buɗe baki zaiyi maga saiga mai gadi ya shigo yana sanar musu cewar sunyi baƙi mutum biyu a waje. Salis ya ce "Je ka shigo da su. Muhammad ya kalli Sarah waccce ta yi nisa cikin tunanin rayuwa ya ce "Sarah lafiya kuwa? Zo nan kusa da babanki kinji? Cike da damuwa a fuskarta ta zo kusa da shi ta zauna, itama laɗifa ta miƙe tana mai kallon Sarah cikin mamakin yanayinta,. A zuciyata ta ce "karde ace wannan yarinyar tunanin AJ ne ya sa kata a haka, koma de meye zan bigi cikin ta. Kafin kowa ya sake magana saiga Samuel tare da abokinsa Umar sun baiyana a cikin palon yana ɗingisa ƙafarsa.

Da sauri Sarah ta miƙe zuwa gareshi, bata tsaya duba lafiyarsaba ta faɗa jikinsa tana fashewa da kukan da itama kanta bata san dalilin yin saba. "PLs ina Momy And Daddy? Ta tambaye tana mai jin kewar su a cikin ƴan kwanakinnan. Shima Samuel ɗin kuka ya keyi yana mai ta kaicin halin mahaifannasu.

*SAMUEL POV*

Tinda a ka kaishi asibiti bai ƙara ganin Momy ko Daddy ba saida ya yi kwana huɗu, kafin Momy ta zo. Nan take ta sanar masa da halinda mahaifinsu keciki, a kan an kulleshi a gidan sojoji wai har sai ogansu yazo, sannan an hana kowa ya ganshi. Yana jin haka ya kalli Momy ya ce "Kema da sa hannunki a ka rufe Uncle Solomon? Ya yi maganar cikin ɓacin rai, lokaci ɗaya Elixa taji shakkar yaron nata amma ta dake ta ce "Yes so what? Nice ma na bashi wannan shawarin domin kuwa abunda yayi kuskure ya aikata, kana addininka tun na iyaye da kakano amma lokaci ɗaya ka koma wani"..."Is Ok!!! Samuel ya katse ta cikin ihuuuu!.

"Nima zan koma Addininsu idan yaso nima kumin haka! haka a ka ce idan mutum ya koma wani addinin a masa? Momy kunyi kuskure kun aikata abinda bazai taɓa gyaruwa, a da irin wannan abun dama kasheshi kukayi ko kum"... "Wani wawan mari ta sauke masa bata duba cewar yana cikin halin jinyaba. Kan gadon tahau tsabar ɓacinrai ta kamo wuyan rigarsa ta fara maga cikin tsan-tsar jankunne da gar-gaɗi ta ce "Samuel Walhi idan har ka kuskura ka ƙara furta wannan maganar Walhi saina kasheka a cikin ɗakinnan, bakada hankaline kasan halinsu ne? Karna ƙara ji ko gani, kuma itama Sarah ina sane da ita, Walhi sai na ɓata mata rai, har ka kalli cikin idanuwana ka ce zaka kina yin sallar, don't try again. Ganin yana ka-ce-na-cen ƙwace kansane yasa ta sakeshi tana mai kiran Dr. Samuel kuwa cikin zafin da ciwonsa ke masa ya shiga shafa wuyansa yana kakarin amai.

Bayan Dr ya shigone Momy ta ce "Dr karka kuskura ka bar yaronnan ya fita daga asibitinna koda kuwa ya warkene, koda kaga ban dawoba? Dr ya ce karki damu za'ayi yanda kikace? Samuel na jinsu har Momy ta bar asibitin batare da ta ƙara ce masa komaiba. Acikin daran ya karɓi wayar wata noss ya sa Numbar Umar, da mamaki yaga Numbar ta fito da suna, bai ce mata komai ba ya ɗan na kiran sa. Ai kuwa kira ɗaya Umar ya ɗaga yana sallama. Samuel ya ce "Umar nine? Umar najin muryarsa ya tashi daga zaunan da yake izuwa tsaye ya ce "Samuel?

"Yes Umar kana ina yanzu?

"Ina gida lafiya kuwa? Me ya kai wayar zee"...

"Samuel ya ce "Umar saurari abinda zance maka? Cikin tsoro Umar ya ce "Wai lafiya dai ko? Kafin Samuel ta ƙara maga Umar ya ci gaba da cewa... Wai naji ance gidanku ya ƙone Allah dai yasa ba kowa a ciki?

Samuel bai tsaya amsa masa ba ya sanar da shi duk abunda ke faru kuma ya ce yazu da yamma yasan yanda zasuyi.

Umar ya ce " A wani ɗaki kake? Ya faɗa masa shi kuma yace zaizo in sha Allah. A haka sukayi sallama.

Bayan sallar la'a'sar Umar ya shigo har cikin ɗakin da Samuel ya ke. Lokacin da yaga bandeji a ƙafar Samuel ya yi tunanin ko hardasu wutar ta ci. Da sauri ya zo gareshi yana mai ƙurawa ƙafar dake ɗauke da ciwon ido cikin mamaki Samuel ya ce "Umar Pls muyi abunda ya dace domin banaso na sake kwana a asbintinnan. Umar da ke son sanin dalilin ganin ƙafa a ɗaure ya ce "Karka damu, inada budurwa a cikin ma aikatan asbintin kuma nayi magana da ita. Samuel ya kalleshi ceke da tuhuma a lamar dai har yanzu yana sheƙe a yarsa ko?. Ai kuwa haka a kayi da sa hannun wanan noss ɗin Samuel ya bar asbintin. Gidan su Umar suka wuce ai kuwa babu wata-wata Haɗiza ƙanwar Umar tana ganinsu ta ja ta dake a kan arne ba zai shiga musu gidaba.To fa! Samuel dai bayajin me take cewa amma dai yasan hanashi shiga takeyi duba da yanda take hararansa, gashi kuma ɗakin Umar ɗin a cikin gida ya ke. Umar ya gama sakewa Hadiza ta rainashi domin kuwa ita bata tsoran sa, zata iya kamashi da dambe a gaban kowa. ( Dama dai baku manta da Hadiza abokiyar faɗan Laɗifa ba?) Babu ko hijjabi a jikinta kanta babu ɗan kwali ko hula, sai doguwar riga wacce ta matseta, rigar ta gama baiyana surarta ta ƴa mace.

Lokaci ɗaya Samuel ya kafe ƙijin yar yarinyar da kallo ganin yanda take sarfa musu rashin kunya, gashi ta sa hannu biyu ta tare ƙofar gidan a lamar dai bazasu shigaba. Samuel bai iya cewa komai ba sai bin ta yake da ido yana jin mutuƙar buƙatar yarinyar. "Arne a gidan mu Walhi bazata saɓuba, ko dan kasan baba baya gari? To

24 / 37