Nida kishiyoyina complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Romance

Chapter   9 / 38

24K to 27K   out of 111.9K words

hakuri yasan bai kyauta ba.

Ina Jin yayana na fada Aunty mamy na sa bakin cin amanar da yamin ba Haushin auren suka ji ba ya rasa wacce zai Aura sai luba Kuma har tsawon shekara daya badan Luba ta fadamin ba da haka zasu ninkeni kenan inta tunanin aiki kawai yake a Abuja.

Ina ji yana ta bada hakuri Yana ya karbi laifiinsa ayi hakuri,kaddara ta riga fata yayana yace shi dai bazai iya min dole ba ya Shiga daki ya Sameni idan zan iya koma masa shi bashida matsala amma tilasta min ne bazai yi ba.

Ina jin lokacin ya nufo d'akin rashin kwarin jiki ya hanani mik'ewa na Shiga bandaki na rufe k'ofar yarana kuwa tuni suka zagaye shi ban bud'e idona ba dan banasan ganinsa.

Sai da duk ya gama yiwa yaran Wasa yace su fita su bamu guri.

Ina jinsa Yana k'ok'arin d'aukar Nana nasan bazata yarda taje wajensa ba dan Kara kwanciya tayi a jikina ya sa hannu ya d'auki ummi.

Ya Kira Sunana yana "Gani a durkushe a gabanki Aisha dan girman Allah kiyi hakuri ki yafemin bansan yanda zaayi ki gane kaddara tasa na auri Luba ba, ba san raina haka ta kasance ba dan Allah ki yafe min Aisha ki dubi girman Allah da yaran mu kiyi hakuri,na yarda idan kin hakura zamu koma Abujan gabad'aya"

"Wlh wlh na gama auren ka ba abinda zai saka na tab'a koma maka,da ka san tsanar da na ma wlh da baka Soma doso Inda nake ba, Salis Luba fa Luba kawata ka Aura ka d'auketa ka kaita Abuja ka munafirceni ka maidani wawiya a gabana ka nuna ka tsaneta idan na maka maganarta kace bakaso,ashe soyayya kakeyi da ita duk matan garin nan ka rasa da wacce zaka hadani kishi sai luba,ka d'auketa Ka kaita Abuja kukayi zamanku Kuna Shan soyayya ni Kuma ka barni da gadin gida da yaranka idan kazo sati daya sai ka juya ka tafi Wlh ban yafe maka wanan cin amanar da kayi min ba ni na yafe mata Kai kuje can ku karata ka bani takarda sakina"

Na karashe Ina fashewa da sabon kuka kirjina wani irin ciwo yake min Luba fa kawata ita Salis ya Aura.

Hakuri ya cigaba da bani Yana magiya da rantsuwar kaddara tasa ya aureta shi baya Santa wlh shi bai hada san kowa dani ba

Sai a lokacin na bud'e idona banida ma kwari sam dan ji nayi jiri na dan dibana na Mik'e zaune Ina "Kace baka santa ka aureta kayi Mata ciki ta haihu kayi taro da gayya ko? A Abujan mutanen ka waya sani a can ita Luba da ta sansu duk baka santa ka hadata dasu ko"? Salis ba dai kace baka santa ba toh wlh idan kana so na dawo gidanka sai ka rubutawa Luba saki uku yanzu a gabana a cikin mu biyu sai ka zabi daya idan ka zabi rabuwa da ita sai na zauna da Kai idan karin auren kake so sai ka Kara da koma wacce ce idan Kuma ita ka zab'a sai ka daina mafarkin ni Aisha zan dawo gareka"

"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Aisha ki rufamin asiri wanan hukuncin naki yamin tsauri wlh bana kaunar Luba ki yarda Zan saketa anan gaba amma Banda yanzu dan Allah dan Annabi"

"Tashi ka fita Salis idan ka saketa ko nan da shekara Ashirin ne sai na dawo gareka amma bazan hada miji da Luba ba"

Ganin zai cigaba da magiya yasa na saka masa ihu ya mik'e ya fita sauri
Yana fita na Kara fashewa da sabon kuka dan tsananin bakin ciki daga yanda ya nuna min bazai iya sakinta ba nasan ba karamin so yake yiwa luba ba ai tunda har ya Kai ta Abuja nasan matsayina a wajensa.


Haka Salis ya ringa sintirin zuwa ba dare ba Rana har yaransa yasa suka ringa rokona suna min kuka ganin yayana shima yace masa ya daina matsamin ya sakeni kawai tunda ya nuna yafi San Luba yaje ya zauna da iya lubar kawai

Yasa hankalinsa tashi dan ya tabbata dagaske yayana bazai tab'a sa baki na dawo gidansa ba

Washegarin ranar sai ga Hajiyarsa da mahaifinsa sun zo.

Mahaifinsa da ake cewa baffa na zaune a palo Hajiya Kuma ta shigo d'akin da nake kwance.

Har ga Allah tamkar 'ya ta d'aukeni nasan tana kaunata tana shigowa ta hau cewa "Ashe abinda yaron nan ya aikata kenan Aisha"?

Sai hawaye suka hau zubo min ta zauna tana "wlh wlh bamu sani ba sai jiya daddare yaje ya na fada Mana abinda ya aikata har ace Salisu yayi Aure batare da sanin Iyayensa ba ya Kuma rasa wacce zai aura sai kawarki wai ashe har ta haihu ma wlh bai kyauta ba jiya har sai da na buge shi mamana kiyi hakuri matakin da Kika d'auka yayi tsauri taya zaki yarda wata banza tazo ta rabaki da mijinki da tun bashida ko sisi kike tare dashi taya zaki bar mata mijinki?Ina zaki Kai yaranan ki bar mata gidan ita kadai bayan dake aka Sha wahalar ya zama abinda ya zama a yau kinsan mutane basa tsoron Allah wlh karkiyi mamaki asirce shi tayi ya aureta kiga fa ba ke kadai ya boyewa ba har mu da muka tsugunna mu ka haifeshi bai fada Mana ba dan haka kiyi hakuri badan na isa ba ko Zan tilasta miki sai dan girman Allah da yaranki kiyimin wanan alfarmar insha Allahu idan dai har ba dan Allah akayi auren nan ba muna nan dake sai Kinga yanda zasu rabu bare abu da cin Amana kiyi hakuri kinji mamana bari ma na durkusa miki ai bazan yarda nayi Asarar suruka irinki ba"

Sai ta fara k'ok'arin tsugunnawa na rukota da sauri Ina "Dan Allah ki bari hajiya"


Har ga Allah ta d'aureni da jijiyoyin jikina bana kaunar Salis ban hararo yanda wai zanyi zaman kishi da luba ba,bansan da wane idon zan Kara kallon Salis a matsayin mijina ba domin babu digon kaunarsa a raina.

Kuka na naci na gode Allah dan wlh baa san raina zan koma gidan Salis ba.

Mahaifin Salis ma yasa aka kirani ya Kara bani hakuri ya bawa yayana ya min nasiha akan masu hakuri zanga sakamakon biyayyar da na musu na yarda zan komawa Salis din.

A haka suka Mana sallama suka tafi akan karshen sati zan koma gidana.

Yayana shima ya Kara bani baki

Aunty mamy kuwa itama baa barta a baya ba ta ringa bani shawarwarin yanda zan jawo hankalin Salis wajena itama tasan Luba asiri ta Masa ya aureta idan ba haka ba ita bata ga mai zai yi da wata Luba ba.

A ranar lahadi na koma gidana Salis sai rawar jiki yake ya Zama hoto a wajena domin babu kaunarsa a raina zan sauke masa duk wani hakkinsa daya rataya a wuyana amma batun mu koma Kamar da babu domin Salis da luba sun min raunin da bazai tab'a warkewa a zuciyata ba.

Magiya Kam da rarrashi haka ya cigaba da min Inda ya sakomin zancen komawa abuja ya siya wani gidan daban da Zan zauna inyaso Yara sai ya sama musu wani makarantar idan anyi hutu sai mu ringa zuwa

Na girgiza masa Kai akan ba zanje Abuja ba zanyi zamana anan yaje ya zauna da Luba a Abuja ai inaga dama ban dace da zaman abujan ba shiyasa bai tab'a tunanin ya tafi dani ba inda yaga ya dace dani ya ajiyeni ya barni da yayana kawai anan"

Na lura Sam baiji dadin maganata ba ya hau min rantse rantse ba haka bane na share shi ban Kara bi ta kansa ba.

A daki daya dai muka ringa kwana kafin ya tafi Ina kallon yanda yake boye boyen waya nasan Luba ke kiransa wlh sai naji bana Jin haushi ko wani kishi dan dagaske bana Jin komai a kansa.

Duk yanda yaso mu koma kamar da abu ya faskara shopping kuwa har da na banza.

Ana washegari da zai koma Abujan da yamma naga ya shigo da wata jar mota karama daidai na mata nidai tsakanina dashi idone hirar ma shi kadai yake yi.

Ta window tsakar gidan na gane bada motarsa ya dawo ba

Sai da ya shigo yaci abinci ya zauna a gefen kujerar da nake zaune ya ajiye mukulin mota akan cinyata Yana "Bansan mai zan miki na faranta miki ba Aisha banaso na tafi batare da naga dariyarki ba banaso na tafi batare da ko sau daya kin min hira ba ga mukulin mota nan naga karamin mota daidai na Mata na siyo miki burina naga na goge laifin da na miki Aisha komai ya wuce dan Allah"

"Ina ganin Luba ta fini bukatar motar nan ko dayake kila ka dade da siya mata da baka wahalar da kanka wajen siyamin ba dan bana wani bukatar ta tunda ni ba ko'ina nake zuwa ba"

"Wlh ban siyawa Luba komai ba ke Kika fi cancanta na siya miki shiyasa na siya miki dan Allah ki daina hada kanki da luba na rokeki da girman Allah dan ba matsayinki daya da ita ba"

Gyada masa Kai kawai nayi burina ma ya bar gefena wlh ban sake ganin farinsa ba ko duk duniya zai ajiyemin bazai tab'a burgeni ba.

Washegari ya dau hanyar Abuja bayan ya ajiye min kudi mai yawa akan Nan da sati biyu zai dawo.

Luba

Kamar tayi karamin hauka a lokacin da taga Salis ya daga hankalinsa akan Aisha har marinta yayi sabida ta nana Aisha da kasa a lokacin da ta kawo mata mari.

Sai gashi tunda ya tafi katsina fiye da sati biyu bai dawo ba kamar ta mutu dan azabar kishi ko ta kira Salis din baya d'auka hakan ya Kara daga hankalinta Inda ta fara shirye shiryen biyo shi sai gashi ya dawo fuskar nan tashi a hade bakin cikinsa mai yasa ta tona musu asiri.

Koda ya dawo banza ya bawa ajiyarta ta ringa masifarta ita kadai.

Abincinta ma ba ci yake ba abu kad'an zata ga ya dau wayarsa ya Kira Aisha da wayar zai karaci ringing bata d'auka ba.

A haka zata bi wayarsa daddare tana karanta messages din da yake turawa Aisha kamar ta hadiyi zuciya ta mutu,abinda ya fara daga Mata hankali bai wuce sati sati da yake tsirar tafiya katsina ba sai ya shafe sati biyu uku bai dawo ba.

Tuni taji zaman abujan ya isheta wani dawowa da yayi ta sako shi a gaba akan itama zata koma katsina da zama bazata yarda da wanan cin amanar da ake mata ba.

Ta karfi da yaji ya amince zata koma katsina ya sama mata karamin gida daidai ita.

Sai dai tana ganin gidan ta dage bazata zauna ba sai dai ya dawo da Aisha gidan ya maidata wancan katon gidan idan bazai iya ba gwara ya hadesu.


Ba karamin tashin hankali suka ringa da Salis ba dan Salis bayaso ya hada luba da Aisha a gida daya sai yake ganin idan Aisha tana ganin Luba a gidan tamkar zai kara jawowa kansa ne a wajenta.

Hakane yasa ya sake nemo gidan da yafi gidan girma amma Luba ta Kara dagewa akan ita yanzu bataso ma tafi so su zauna gida daya da Aisha dan tafiso duk abinda akeyi ya zama tana gani Kar ma Salis ya ringa cutarta Yana cin amanarta.

Har kudi Salis ya bata mai yawa dan ta hakura ta zauna a gida daban taki akan dole ya tari Aisha da maganar hankalinsa a tashe sai dai ga mamakinsa Aisha cewa tayi su biyun bata da matsala dasu ita samant yaranta take Luba ba kishiyarta bace ba ita ai bata da mijin yanzu"

A takaice da haka Luba ta dawo gidan aka ware mata part din da bai kai na Aisha girma ba.

Tunda kuwa ta dawo gidan bata da burin daya wuce taga ta yiwa Aisha abinda zai saka ta zuciya ta sa Salis ya saketa sai dai haka zata karaci abin ta Aisha bata tab'a tankata ba hasali sai ta kusa sati bata sa Aisha a idonta ba a lokacin da ta gano Jan motar da take gani a tsakar gidan na Aisha ne ba karamin yak'i akayi ba dan sako Salis tayi a gaba akan lailai sai ya siyo mata itama, Salis kuwa ya rantse akan bazai siya Mata ba kullum cikin tashin hankali da fada Idan suna yi Aisha bata yi kamar tasan me suke yi kasan ranta Kuma ta fara yarda da zancen hajiya da Aunty mamy akan asirce shi Luba tayi dan da hankalinsa bata Jin zai dauki rabin iskancinta.

Ganin Abu yak'i ci yak'i cinyewa yasa ta d'auko mukulin motar ta bawa Ashraf akan ya Kai Mata dan taci kwalar rigar Salis akan ba inda zaije sai ya siyo mata nata motar.

Ashraf kuwa Yana zuwa yace ga mukulin mota inji Aisha ta wufce mukulin da sauri tana gwara da aka kawo mukulin da anyi tashin hankali a gidan.

Koda Salis yaje ya samu Aisha akan mai yasa tayi haka ce masa tayi bata bukatar motar indai akan motar suke zubar da mutuncin su a gaban yaranta gwara ta bata kawai.

Kwana biyu a tsakani Salis ya siyo motar da tayi biyun wancan a tsada ya Kara kawowa Aishan

Luba kuwa Kamar ta mutu dan bakin ciki.

Duk takalar Aisha da take da fada da laben da take Mata bata tab'a bi ta kanta ba a haka har suka shekara biyu Allah ya kawo rabon haihuwar Aliyu wata uku a tsakani itama Luba ta haifo danta namiji aka sa Masa Abdul.

Kiri kiri take ganin rawar jikin da Salis yake akan Aisha da ta maida sa baho sosai take kishin Aisha ba yanda zatayi ne.


Aisha ma bata bi ta kanta ballantana su yi tashin hankali da ita.

A irin wanan lokacin Salis yazo da zancen Karin Auren Hindatu Yar Mai gidansa da ya Masa hanyar aikin NGo dan shi ya nemi daya auri Hindatu dan ta gama makaranta ba mijin aure

Salis bazai iya ce masa Aa ba baya kaunar Hindatu amma a haka ya karbi tayin aurenta.

Luba kamar ta hauka ce dan kishi, Salis kuwa ya zagu haka ta nemo gidan su Hindatu taje tayi rashin mutunci inda sai da ya Kai su ga dambe har police station.

A lokacin Hindatu taso ma ta hakura da auren sai kuma taga idan ta hakuran Luba taci galaba akanta.

A haka akayi auren Hindatu da Alhaji Salis ana zuba tashin hankali a gidan

Aisha kuwa tuni ta Kara komawa gefe ta kawo Ido ta zuba musu ba ranar banzan da basa zage zage da Hindatu ko ayi dambe a gaban Yaya suna kallo wanan kenan.

Yanzu Kuma mun dawo labari

Dangin Salisu da hajiya
Tarba mai kyau suka yiwa dangin Aneesa Inda sai a lokacin hankalin mahaifiyar Aneesa ta Dan samu kwanciyar hankali da taga mahaifiyar Salis din tana da mutunci da alama baza'a samu matsala da ita ba matansa ne dai bata sani ba hakane yasa bayan sunci sun Sha lokacin an Kai Aneesa d'akin hajiyar dan da Magriba zata kaita gidanta duk da gidansu Salis din kato ne an Kama musu hotel akan su kwana gobe su wuce.

Mahaifiyar Aneesa kuwa wajen hajiyar Salis tayi tana "zanso na Kara damka amanar Aneesa a hannun kishiyoyinta tunda hajiya Kinga yarinya ce gashi ba gari daya muke ba zanso Kafin a kaita mu fara zuwa can din"

Hajiyar Salis ta saki murmushi tana "karki damu ba sai kinje ba wlh mun karbi Amana matansa basu da matsala abinda ma ba gida daya zasu zauna ba wlh karki ji komai Aneesa ai 'yata ce"

Kwarjinin da Hajiyar ta Mata yasa bata iya Musa mata ba da Magriba suka raka Aneesa dakinta da ya gaji da had'uwa da tsaruwa.

Bayan duk sun mata nasiha Tana kuka haka suka barota suka nufi masaukinsu.

Tafiyarsu da minti Ashirin Salis ya shigo gidan rabonsa da ya tsinci kansa cikin farinciki haka tun kafin ya auri Luba da Hindatu.

Yau tamkar farkon aurensa haka yakeji Yana Kuma doki.

Sai da ya ajiye ledojin hannunsa ya taka ya nufi wajen da Aneesa ke zaune a gefen gado, ya zauna tare da yaye lullubin fuskarta suka hada Ido tare da sakarwa juna murmushi.

Salis ya jawota ya rungumeta Yana sakin ajiyar zuciya wani irin sanyi na tsirga mai a zuciya a yau Yana so daren ya kasance Masa cikin dararakin da bazai manta ba Yana so su raya daren cikin so da kauna.

Dak'yar ya cikata yasan tana kaunarsa bazata wahalar dashi ba kayan ciye ciyen da ya shigo musu dashi suka ci suka koshi ya tafi dakinsa yayi wanka Yana dawowa yaga itama da alama tayi wankan har alwalar ma tayi tana jiransa.

Sai da yaja su suka yi sallah Isha da shafai da wtr ya Kara raka'a biyu sai da ya dan yi musu addua mai tsayi kafin ya shafa ya mik'e fuskarsa d'auke da murmushi Yana bari yaje ya kulle k'ofar gidan.

Yama kashe duk wayoyinsa dan luba sai kiransa take

Yana k'ok'arin danna k'ofar yaga an turo k'ofar da k'arfi Luba ta Fado cikin gidan Tana hucci "innalillahi wa Inna ilaihi rajiun mai kikeyi anan"


"Kai ka Isa ka wulakanta mu ai tunda ka dage ka auri yarinya Nan kayi bankwana da farinciki wlh Allah kana San kwanciya hankali ka rubuta mata sakinta ta tafi gidansu,har mu zaka munafirta kazo ka ware mata gida wacce ita"

Alhaji Salis wani irin fusgo Luba yayi Yana "Zo ki bar gidanan jaka mahaukaciya wlh bazan tab'a sakinta ba"

Suka fara k'ok'awa da Alhaji Salis dake ta k'ok'arin turata waje a daidai lokacin da siririn muryar Aneesa ya ratsa kunnen su "Baby mai yake faruwa ne Kai da waye"?

"Luba a haukace ta kaiwa Salis cizo Yana sakinta tayi wajen Aneesa aguje....

Ammnur _kayan mata tazo muku da zafafan kayan matan da babu algus 09080070762

Ina uwargida da ta haihu vjay dinta ya bude tana bukatar taji ta koma budurwa gam ga ammnur Nan ta kawo muku zafafan kayan mata Ina amare masu Shirin shiga daga ciki,Ina Zawara da suke so suji Basu da bambanci da budurwa

Enjoyment doesnt stop just because you have given birth. The afterbirth package is made to take care of you postpartum sexual needs . This package includes sweetner, wetner, tightener infection afterbirth herbs and more



Sauran kaya da zaki duba a wajen su na qara niima dadi da matsi sanan akwai na tsuma jiki na mata da na amare da uwargida Wato

9 / 38