Nida kishiyoyina complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Romance

Chapter   36 / 38

105K to 108K   out of 111.9K words

saci kallon wajen da yusuf ke zaune dan fadar ta taimakawa Luba zuwa wajen mallami tamkar ta dab'awa kanta wukane

Kallon da Ashraf ya mata da "muna jinki"

Yasa ta tuno maganarsa da "Fadar gaskiyar ki shi ne naki rufin asirin domin nasan duk munanan Abubuwan da kika aikata kadan daga ciki shine yanda kika sawa kishiyarki guba a Shayi ta sha ta mutu,kinsan kema idan aka gano kin tab'a kisan kai wlh sai an daureki amma idan har duk abinda kuka yi da Luba duk kika fito kika fada a kotu ba mai Jin wanan sirrin naki"!!!!

Asabe d'auke idonta tayi daga kallon barin da yusuf ke zaune tayi ya zuba mata ido kawai Yana kallonta ta kalli Luba da rigarta ta jike da gumi sai girgiza kai take jikinta na rawa

"A lokacin Ina dan fama da jinnu masu kora min samari hakane yasa na dan san mallamai masu taimaka min da Addu'a a lokacin da ta nemi ko Zan taimaka mata shine na bata shawaran ko zata zo na rakata wajen mallamina yayi mata aiki akan Mijin Aisha.

A lokacin sai ta nuna min bata yarda da mallamai ba kudin mutane kawai suke ci,sai na ce mata mu dai gwada zuwa"

A lokacin da muka je Luba duk ta zayyane masa abinda ke tafe damu ce mana yayi mijin Aisha ya mugun tsanarta abu daya zai mata shine zai bamu garin magani a samu a zuba masa a abinci yaci,idan har yaci zai na kasance cikin tsananin bukata,ita kuma a wanan lokacin ta ringa zuwa office dinsa idan har ta samu ya kwanta da ita,ba abinda zai hana ya aureta dan ji zaiyi duk duniya ba wacce yake so sama da ita, ya Kuma ji ba wacce ya tsana sama da Aisha dan bama zai ringa Jin dadin kowace mace ba"


Shiru Asabe ta sakeyi tana sauke numfashi kallon da yusuf ke mata ya Kara daga Mata hankali dan tana tsoron Aurenta ya mutu,amma har gwara aurenta ya mutu da asan itace ta kashe matarsa uwar yayansa.


"Muna jinki"

Ashraf yace tare da gyara tsayuwarsa ya kallo wajen da Aisha ke zaune da ta rufe fuskarta da tafin hannunta da alama kuka takeyi, Salis kuwa idonsa jajjur yayi sabida b'acin rai kallon Asabe kawai yake.

"A ranar da muka karbo maganin bata samu zuwa gidan Aisha ba dan tace min zuba masa magani a abinci abu ne mai balain sauki dan Aisha shashasha ce kwana biyu a tsakani tazo ta sameni akan ta zuba maganin dan itace ma tayi girkin dan haka zata shirya sosai ta tafi office dinsa har take fadamin ai kayan da zata saka ma da kudin Aisha ta siya. Fatan nassara na Mata muka rabu akan zata zo ta bani labari idan komai ya wakana.

Sai dai a ranar daddare tazo tana kuka akan ya koreta ya ma yiwa security gargadi akan karsu sake su kara barinta ta shigo Masa office,taci kukanta ta gode Allah da ta gama na shawarceta akan mai zai hana ta hakura da mijin Aisha ta duba kawai a cikin manemanta ta aura tunda suma suna da kudin,sai ta daka tsalle akan duk uban wahalar nan da take sha akansa tashi daya kawai sai ta hakura ai ita haka zata cigaba da bibiyarsa har sai ya amince zai aureta.

A Kuma ranar take bani labarin ma akwai wani likita Dr Saeed dayace Yana santa a asibitin shima yake aiki da zata iya aurensa idan Yana da kudi sai dai bai kai mijin Aisha kudi ba,kafin ta tafi haka ta zage ta zagi mallamin da mukaje wajensa akan cutar ta yayi.

A haka ta ringa bani labarin nacin da take yiwa mijin Aisha amma baya sauraranta wata uku a tsakani tazo ta sameni bakinta a washe tana na tayata murna ai a yanzu dole ma Salis ya aureta na tambayeta mai ya faru?anan take fadamin ai taje office dinsa security sun hanata Shiga tana zaune taga muhasim Yar gidan yayan Aisha tazo ta shige office din Salis take zuciyarta ya bata wani abun tunda a kwanakin baya da ta zuba masa magani ma Allah ne ya tsallakar da ita da a lokacin zai mata fyade,ta cigaba da bani labarin yanda taso ta Shiga office din taji Mai muhasim taje yi a office din security suka hanata Shiga tana nan a labe taga Muhasim ta fito da gudu tana kuka,itama bata tsaya bata lokaci ba ta take mata baya dan tasan dole gagarumin abune zai saka taje office dinsa har ta fito tana kuka,a lokacin data fito tace muhasim ta mata nisa har sai da ta tari abin hawa suka tadota bata nunawa muhasim daga asibtin take ba tace tazo ta hau su karasa gida,a haka muhasim ta hau tana kuka Luba tace min ta ringa rarrashin ta tana bugar cikinta akan ta fada mata Mai yake faruwa tak'i fada mata har sai da ta mata barazana akan zataje gidansu ta fada akan ba islamiya taje ba, office din Salis taje, dak'yar ta samu Muhasim ta fada mata Salis ne ya Mata fyade ta gano tana da ciki shine yace ta zubar da cikin ita Kuma tana tsoron ta zubar da cikin ta mutu,Luba cikin murna ta cigaba da fadin"Wlh bakiga yanda na tsorata ta akan karta yarda ta zubar da cikin ba idan ba haka ba mutuwa zatayi Asabe ki tayani murna a yanzu nasamu hanyar da dolensa ya aureni"

"Idan kuma cikin ya zub'e fa ya zakiyi"?

Na jefa mata tambayar sai a lokacin jikinta yayi sanyi sai Kuma ta mik'e a zabure tana "Ai janyo yarinyar nan zanyi a jikina wlh bazan tab'a barinta ta yarda ta zubar da cikin ba dan da cikin jikin nan nata Zan ta barazana akan zan tona masa asiri nasan Yana mugun san Aisha bazai so asirinsa ya tonu ba a yanzu ma na nunawa yarinya zan taimaka mata cikin ya zub'e batare da an mata komai ba dan so nake nayita yaudararta sabida Kar cikin ya zub'e"

A ranar Luba ko bacci batayi ba dan a gidan mu ta kwana a haka ta ringa jawo muhasim jikinta tana fada mata duk yanda suka yi da mijin Aisha, ta Kuma cigaba da zuwa office din Salis da har lokacin baya barinta ta shiga,duk halin da suke ciki tana fadamin.

Watarana tazo ta sameni tana "Ke Salis fa ya dage so yake ya zubarwa yarinya nan ciki tace min har makarantar su yake binta dan ya zubar mata da cikin ni kuwa idan har yayi nassarar zubar da cikin nan nasan bazai tab'a Aurena ba"

"Yanzu ya zaayi kenan"?

Na tambayeta sai tayi shiru tana tunani sai ta fara da ko "Saceta zanyi"?

Sai na girgiza mata kai

"Toh yanzu ya zanyi wlh wanan hanyar kawai gareni da zan samu Salis ya aureni"

Nidai a lokacin kaina ya kulle bansan shawarar da zan bata ba,haka tayi ta nazari har dare yayi Muka yi sallama da ita,kwana biyu a tsakani tazo ta sameni akan ta gano abinda zatayi hanya mai mugun sauki da zata samu auren Salis ta Kuma gara shi san ranta.

Ihun da Luba ta saka a gigice tana "ke kika zugani Asabe ke Kika kawo wanan shawarar wlh ba ni nayi niyya ba Kuma ke kika aiwatar da haka alkali a tambayi muhasim aji Wanda ya karkata Mata wuya wlh bani bace itace duk maganar da take karya takeyi so take kawai duk ta Dora min laifi"

Gudumar kotu ya buga akan tayi shiru dan zabure zabure take tana neman fitowa daga wajen sai ihu take.

Yan sandan dake gefenta suka tsawatar Mata tayi shiru tana shesheka Salis ya mik'e tsaye dan ji yayi Yama kasa zama,Aisha Kuma ta dafe kirjinta tana Jan sallati dan sai taji Kamar numfashinta ke san d'aukewa sai da komai ya lafa Ashraf ya kalli Asabe da itama ta fara gumin tana zare ido,

"Muna jinki ki cigaba da bayani"


"A lokacin tace min ta samu saurayinta dinan Dr Saeed akan ya taimaka mata, dan tana soyayya dashi,Yana kashe mata kudi,a lokacin ya nuna mata dama an masa transfer zai bar garin zai taimaka mata amma ita zata aiwatar bashi ba,Kuma shima idan ta samu cikar burinta ta masa alkawarin bazasu rabu ba,zasu cigaba da had'uwa idan ya shigo gari ya kuma yi mata gargadi akan Kar ta sake Koda ta kwabe ta Kira sunansa"

"Wane irin taimako ya Mata akan muhasim din"?

"Ashraf ka yarda dani wlh karya take ita ta hadani da Saeed din abokin saurayinta ne duk ita ta fadamin yanda Zan samu cikar burina muhasim kema zaki min shaida ko"?

Luba tace cikin ihun kuka tana cigaba da "Wlh kema sai na tona miki asiri ke Kika koya min duk abinda nayi"

Sai da aka Kara tsawatar mata aka samu tayi shiru Asabe kuwa sai ta tsinci kanta cikin tashin hankali dan Yusuf mik'ewa yayi tsaye Yana kallonta

"Muna jinki wane irin taimako ya Mata"?

"Allura ya hada mata yace ayi wa muhasim a wuya wuyanta zai karkace bakinta ma haka Kuma bazata tab'a iya magana ba"


Sallati aka kaure dashi a kotun Salis kuwa yayi kan luba da gudu yan sanda suka tare shi tare da ririke shi Salis ya hau ihun"Dama duk tsawon lokacin nan allura kika mata duk tsawon lokacin kika saka mukayi ta wahala Kika saka akayi ta zargina Allah ya tsine miki Luba Allah ya wulakanta keda kawarki Allah yasa ku a wutar jahanama kuka samin magani nayi wa Yata fyade iya nan bai isheku ba kuka karkata mata wuya dan Allah ku sakeni na kasheta inyaso nima a kasheni"

Yanda Salis ke fufusgewa yasa Yan sandan yin waje dashi Aisha kuwa akayi kanta dan numfashin dake mata wahalar shak'a yasa ta sume Yaya mustapha yayi kanta Yana sallati.


Luba kuwa ihu ta cigaba dayi tana "Wlh ita tayi Mata alluran ni rik'e muhasim kawai nayi,wlh bani na mata alluran ba karya take min Asabe kiji tsoron Allah ki Fadi gaskiya tunda asirinmu ya riga da ya tonu"

"Wlh karya kike yi bansan komai ba nidai labari kawai Kika bani"

Yanda kotun ya hargitse yasa alkali buga gudumarsa akan a tafi hutun minti talatin a dawo.

Salis Kamar mace haka ya zauna a barandar kotun Yana kuka, a gaban idonsa Aunty mamy da Yaya mustapha suka fito da Aisha Suka shimfida ta akan wani dakali suka ringa watsa mata ruwa suna mata fifita Koda ta farfado kuka kawai take tana Luba ta cuceta Allah ya Isa tsakaninta da ita.

Ashraf kuwa sai rarrashin ta suke Alhaji Salis daya hango yasa ya mik'e ya nufi wajensa da isarsa ya zauna a gefensa Yana "Abba ba kuka zakayi ba ka godewa Allah da gaskiya ta fito akasan duk abinda ya faru ba yin kanka bane sharrin Luba ne Abba dama akwai alluran da ake yiwa mutum wuyansa ya karkace haka da baki"

Gyada masa kansa yayi Yana "Akwai amma baa fiye samunsa anan ba sai kasar waje nayi matukar mamaki da yanda har suka samu alluran Suka yi mata tunanin mu a lokacin bai tab'a bamu akan allura aka mata ba"

"Kasan to Dr Saeed din"?

"Aaa bansan shi ba may be ta bakin Luba Asaben ce ta hadata da wani likitan amma babu wani Dr Saeed da muke dashi a asibitin a wanan lokacin"

"Abba zaa samu maganin toh da zai warkar da ita tunda angane mai aka Mata"?

Za'a samu idan aka fita da ita waje Luba ta cuceni ASHRAF mahaifiyarka ma ta cuceni dan duk ita ta bawa luba k'ofa taci galaba a kaina"

"Kayi hakuri Abba Allah ya riga da ya rubuta hakan zai faru baku isa ku k'aucewa kaddararku ba ka godewa Allah da asirinta ya tonu"

Salis bai Kara cewa komai ba a daidai lokacin da Yaya mustapha ya nufo wajen da suke zaune.

Ashraf shi Kuma ya mik'e yayi cikin kotun.

Minti talatin a tsakani aka koma cikin kotun gabadaya Luba idonta yayi luhum luhum sabida kuka,Asabe kuwa gumi kawai takeyi dan batasani ba ko itama kotun zasu iya zargarta su daureta.

Sai da Alkali yayi gargadi akan yin hayaniya da magana batare da an bada dama ba kafin yace Ashraf ya cigaba daga Inda ya tsaya.

Ashraf ya karasa gaban Asabe Yana "kikace Dr Saeed shine ya bawa Luba alluran da aka yi wa muhasim bakinta ya karkace da aka bata alluran ta kawo miki kin gani"?

Asabe sai tayi sauri ta girgiza kanta tana "Aa bata kawomin ba sai da tayiwa muhasim din alluran tazo gidanmu take fadamin"

"Ta Baki labarin yanda akayi ta mata alluran a Kuma Ina tayi mata alluran dan Muhasim a bayan makarantar su aka tsinceta a kwance"


"Eee a lokacin cemin tayi a ranar da aka bata alluran washegari taje makarantar islamiyarsu muhasim tace mata ta samo mata maganin da cikin zai zub'e dan haka gobe tazo ta sameta da sassafe ta shafa mata maganin a cikinta tana shafa mata cikin zai zub'e, ta kwatanta Mata gidan da zata zo ta sameta,shine washegarin ranar muhasim tazo gidanmu da sassafe Au taje gidansu Luba da sassafe ta sameta shine ta mata alluran ta tari abin hawa taje ta jefata a Bayan makarantar"

Murmushi Ashraf ya saki yana "Kinaso kice bakya wajen akayi alluran"?

"Eee gaskiya labari tabani"

"Amma yanzu Kuma kince tazo gidanku da sassafe ita muhasim din kenan a tare kuka mata alluran"

"Aaa gaskiya ba gidanmu tazo ba gidansu luban taje"

"Toh menene dayan sirrin Luba da kike san fadawa kotu"

"Yaran da Luba ta haifawa Salis"


Ihuuuu Luba ta saka

Asabe kuwa ta cigaba da magana tana "Bintu ????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? ce kawai Yar Alhaji Salis sauran biyun yaran Dr Saeed ne dan shima barazana ya ringa mata akan idan bata bashi hadin kai zai tona mata asiri"


"Kin kasheni Asabe kin cuceni ke Kika bani shawara fa Asabe ke kikayiwa muhasim allura fa bani ba wlh karya take min

Yanda ta ringa ihu da kururuwa yasa alkali buga gudumarsa Luba kuwa ta Yanke jiki ta Fadi.

Shigowar wani kotun da Yan sanda ke biye dashi a baya yasa Asabe ja da baya cikin ihu tana "Ghali"............


Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne, knuckles,wrinkles,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using sabulun mg's batare da kunbukaci wani Mai b>?? Mai bukata should
Chat=?G?
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391

Team glow>???
@&?




*WANAN LITTAFIN NA KUDINE BIYA 500 TA WANAN ACCT 0272061655 WEMA BANK NAFISA NUHU KO KATIN MTN KO AIRTEL TA WANAN LAYIN 08033719070 DOMIN KI MALLAKI NAKI KI MUTANEN NIGER KUMA KU TUNTUBI WANAN LAYIN*
*+227 96 82 89 84 DUK WACCE TA MIN SHARING NA BAR TA DA* *RABBI ZAI FIDDA MIN HAKKI NA DA IZININ ALLAH DOMIN BA YAFEWA NAYI BA*


*NI DA KISHIYOYINA*

*NA SADNAF*

*PAGE 38*


Asabe jikinta ne ya hau karkawa,Wanda ta Kira da ghali ya tsaya a gefen witness box a daidai lokacin da Yan sanda suka watsawa Luba ruwa ta farfado.

Tana cigaba da ihun kuka ghalin da tayi tozali dashi a tsaye yayi zuru zuru yasa ta saki ihu tana "Alhamdulillah ya Allah ga Ghali nan Asabe idan kina tunanin ni zaki tona asiri naki ya rufu toh gashi nan Allah ya turo shi kema ya tona miki asiri.


Asabe tuni ta jike da gumi tana sallati a ranta tana ta mamakin ya akayi aka kamo Ghali uban me yazo nema a kotun ai indai Ghali ya tona mata asiri ta Kade har ganyenta ta saci kallon Yusuf dake tsaye idonsa jajjur,tamkar yanda shima Salis ya kasa zama har hular kansa ya cire dan fadar yaran Luba guda biyu ba nashi bane ba Abdul da khalifa ya matukar daga masa hankali yanzu duk wahalar da Luba ta ringa bashi akan yaran ba yaransa bane na wani ne, jikinsa rawa kawai yake Luba ta wuce tunaninsa dama duk tsawon lokacin nan tana zuwa wajen wani,taya ma zai yarda Bintu yarsa ce ba Yar wani ba,kallon ita da Asabe kawai yake, sanin Luba bai tab'a zame masa alheri ba sai sharri



Ashraf kuwa tsayuwarsa ya gyara ya maida hankalinsa kan Asabe Yana "kinsan ghalin ne naga kin Kira sunansa"?

Da sauri Asabe ta hau girgiza kanta tana "Bansan shi ba kama yayi min da wani"

Ashraf ya saki murmushi Yana "kinaso kice iya Bintu ce Yar Alhaji Salis sauran bashine mahaifinsu ba"?

"Eee hakane"

"Akwai Kuma wani sirrinta da kike ganin ya kamata kotu ta sani Bayan wanan"?

"Bai wuce juya masa tunani da tayi sai yanda tayi dashi ba,iya sirrinta dana sani kenan"


Gyada kai Ashraf yayi ya juya wajen Luba Yana "Hajiya Luba kinji abinda kawarki aminiyarki tace ke Kika yiwa muhasim allura da taimakon Saurayinki Saeed zaki yarda ki amsa laifinki batare da kin wahalar da Sharia ba ko kuma kina da ja"?

"Ina da ja asirina ya riga da ya tonu zan Fadi iya gaskiyata duk maganar da tayi karya take yi, duk wani abu da na aikata ita ta Sakani na aikata,a lokacin da na gano muhasim na d'auke da cikin Alhaji Salis ban taba tunanin tab'a lafiyarta ba Asabe itace ta bani shawarar haka,Dr Saeed da take magana Kuma abokin saurayinta ne,a lokacin ita ta hadani dashi akan na hakura da Alhaji Salis na auri shi Alhaji Saeed din tunda a lokacin bashida mata matarsa ta rasu,ni Kuma sai nace mata bai yi min ba dan bashida irin kudin da nake so ya zama mijina na da shi,sai ta bani shawarar na ringa wankarsa Yana da sakin kudi,yaso Aurena a lokacin naki yarda a lokacin da maganar muhasim ta b'ullo muka yi ta shawara da Asabe yanda zan samu cikar burina akan Alhaji Salis duk shawarar da muka yanke har na sace muhasim din bai yi ba sai da ta kawo shawarar ko ayi mata allurar da bazata tab'a iya magana ba ballantana tace Salis ne ya mata ciki,a lokacin na dauka iya alluran d'auke magana ne shiyasa jiki na rawa nace na yarda Muka je office din Dr Saeed din a tare,ita ta fada masa

36 / 38