Nida kishiyoyina complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Romance

Chapter   30 / 38

87K to 90K   out of 111.9K words

ya fara Shiga gidan ba jimawa ya fito yace mata ta shigo.

Gidan da gani na hayane ba mutum daya ne a gidan ba dan sai da suka wuce dakuna wajen biyar kafin taga dan acaban ya Shige wani daki, tabi bayansa.

"Ga matar nan madam dan Allah a taimaka mata ta kwana zuwa gobe ko jibi ko abinci bata saka a cikinta ba"

Matar kallon Luba kawai take kana ganinta kasan ba bahaushiya bace ba dan ga tsagun fuskarta Nan irin na yarabawa.

Da broken tacewa dan Acaban ba komai yayi tafiyarsa kawai Luba godiya ta ringa musu har da dan acaban da ya mik'e ya tafi.

Tunda kuma dan acaban ya tafi daga Luba har matar ba wanda ya cewa kowa komai Luba sai da ta gaji da zaman tace "Madam dan Allah ki taimaka min da abinci wlh yunwa nake ji"

Matar mik'ewa tayi ta fita waje Jim kadan ta dawo da plate a hannunta ta ajiyewa Luba bakin Amala ne da miyar wake.

Luba jiki na rawa ta fara Loma abincin a bakinta a takaice a kasa ta kwana a palonmatar ta shige daki da yaranta.


ASHRAF

Ya Sha zargin Mahaifinsa da ba ta hanyar halal yake samun kudinsa ba amma bai tab'a kawo tunanin mahaifinsa na safarar mutane zuwa kasar waje ba, dama gidan marayun da ya bud'e badan Allah da annabi ya bud'e ba dama taimakon Yara da yake akan karatu badan Allah bane ba?bakin fentin da Salis kesan shafa musu kenan,ga fyade ga mumunan Sanaa baya Jin zai iya tsayawa Salis, ya mahaifiyar su zata ji idan ta Kara gano wanan mumunan halin da Salis ya jefa kansa a ciki.

A ranar Ashraf ko runtsawa baiyi ba sabida tunani baya jin zai iya Kare Salis a kotu dan abin ya girmama tunaninsa yafi karfinsa sai dai Salis ya nemo wani lawyer din ya tsaya masa.

Kwana biyu a tsakani yan sanda Suka Kara zuwa neman Salis da ko waje baya fitowa a yanzu ya sadakar da asirinsa ya riga da ya tonu, dama yasan Ashraf bazai iya tsaya masa ba,sabida abinda ya aikata ya munana"

A yanzu wani irin nadama yake Mara amfani, Addu'arsa kawai Kar maganar taje kunenn Aisha da Yaya mustapha duk da yasan abune mai wuya tunda shi din sanane ne.

Tunda ya bawa Ashraf labari bai Kara saka shi a idonsa ba yasan Ashraf.kunyar abinda ya aikata yake ji.

Kwana biyu a tsakani yan sanda suka Kara zuwa har cikin gida suka zo suka tafi dashi.

A ranar sai da suka kulle shi dan munana ayyukans a na Kara fitowa hajiya Fauza ta sha azaba ta fito ta ta fadawa yan sandan gaskiya hakane yasa Suka Kara Kama Salis suka kulleshi.

Sai dai duk yanda Suka so Salis ya amsa laifinsa da bakinsa kin amsawa yayi.ya dage sharri aka masa ba halinsa bane ba.

Ashraf ma duk yanda yaso ya Kara karbar belin mahaifinsa basu bashi ba.

Tsabar tashin hankalin da yake ciki shima har wani ramewa yayi.

Gwamnati tuni ta kwace lasisin asibitin Salis aka rufe gidan marayunsa.

Aka cigaba da gudanar da bincike ana shirye shiryen mik'a Salis kotu.

Ashraf kuwa shima shiri kawai yake dan bazai iya zuciya ya bar Salis a cikin halin nan ba duk da mahaifinsa bai cancanci haka ba amma haka zai daure ya tsaya masa dan yaga ya wanke shi a idon jamaa.

Ana saura kwana biyu zasu fara zaman kotu yaje gidansu Yaya mustapha dan su gaisa da Aisha dan kwana biyu kenan baije ya gaishe su ba tunda ya gano.sirrin mahaifinsa ya ke iya k'ok'arin sa wajen ganin ya wanke Salis dan ji yayi bazai iya juya masa baya ba.

Yana Shiga cikin palon yaga Aisha a zaune tana bawa muhasim kunu,sai da ya gaisheta ya maida hankalinsa kan muhasim banda lamarin Salis ya kunno masa Kai da tuni ya gano Wanda yake da hannu a karkacewar wuyan ta.

Muryar Aisha ne.ya katse.masa tunanin da ya tafi "Ina Abbanku"?

"Yana.gida.mana.hajiya umma"


"Ashraf kenan duk halin da mahaifin ku.yake.ciki nasani Ashraf nayi matukar nadamar Aurensa ban tab'a sanin bata hanyar halal yake ciyar.damu ba baku dace da uba nagari ba ya cuceni ya shafawa yarana bakin fenti ASHRAF ka yarda Salis ne ya karkatawa muhasim wuya,idan har zai iya kwasar marayu ya kaisu waje dan biyan bukatar kansa da san abin duniya Ashraf Salis zai iya kisan Kai Koda baka zo ba Ina Shirin nemanka a waya Ashraf tun.kuna Yara na Sha cewa ku rik'e.gaskiya ku tsaya akan gaskiya ASHRAF ban yarda.ka tsayawa masa ba"


"Hajiya umma Dan Allah karki hanani tsaya masa Abba a yanzu Yana bukatar taimakon mu ki barni na tsaya masa bansan ma yanda akayi kika ji labari ba"

Ashraf ban yarda ka tsaya Masa ba nace duk baisan Rana irin wanan na zuwa ba ya ringa Kai bayin Allah waje banda San zuciya irin nasa mai yake nema Kuma a gidan duniya nayi nadamar saninsa a rayuwata"

Aisha ta karashe tare da fashewa da kuka a wajen Yaya mustapha take Jin labarin duk halin da Salis ya jefa kansa a ciki,dan tuni magana ta bazu koina tunda aka rufe asibtin.


Gidan Asabe

Mai gadi ya Saba shigowa da safe su gaisa da Asabe,Bayan sun gaisa ita Kuma sai ta d'auko masa abincin karyawarsa.

Sai dai sau uku Yana zuwa k'ofar palon Yana buga sallama shiru Kamar ba kowa a gidan.

Ganin har sha biyun rana ba motsin kowa,
yasa ya shiga cikin gidan dan yasan ba lafiya ba Asabe bata tab'a kaiwa wanan lokacin bata farka ba.

Sunan hajiya ya fara Kira daga Palo shirun da yaji yasa ya fara leka kitchen kafin ya doshi d'akin Asabe.

Koda ya tura k'ofar ba kowa a ciki amma kayan cikin d'akin nata a hargitse har kayan sawa.

Mai gadi tuni hankalinsa ya tashi ya cigaba da kwalawa Asabe Kira Yana dube dube a haka ya bud'e bandakin.

Asaben daya gani kwance cikin jini yasa yasa ki ihu jikinsa na rawa,sai a lokacin ya tuna luba na bayan gidan.

Bayan gidan yayi da gudu Yana sallati dan ya fada mata sai dai Yana tura k'ofar dakin yaga bata ciki.

Hankali a tashe ya d'auko wayarsa ya kira yusuf a waya ya sanar dashi abinda ke faruwa.

A takaice a ranar yusuf ya dawo hankalinsa a tashe baiyi wata wata ba ya kinkimi Asaben daya san ba numfashi take ba ya kaita asibitin daga tambayoyin da yayiwa maigadi da labarin da ya bashi na nuni kashe Asabe akayi kuma dole Luba ita zata kasheta.

Addua kawai yake Allah yasa Asabe ba mutuwa tayi ba tsawon awa uku a tsakani likitan ya fito yana "Tana raye dogon suma tayi ta zubar da jini da yawa aje a nemo Mana jini a Kara Mata...

Aski yazo gaban goshi yafi zafi kuringa hakuri dani am almost there insha Allahu

Assalamu alaikum Barkanmu da wannan Rana PROMON da zanyi sati 2 inaso nayi amfani da wannan dama dan na tallata maku maganin nan zaku dadinshi Kamar yanda kuka yarda da maganin aunty zee insha Allah bazan baku kunya ba iya sati 2 ne zai kare masu haramar saye ku yi maza ku kwashi garabasa bucket 200 ne zanyi tallah da kudina zan Kara kunsan meman kudi Saida kudi 14/10/2022
Zuwa 28/10/2022
gamasu bukatar tura kudinsu kutura tanan
3968303018
Zainab Shu aibu
Fcmb
*PROMO **PROMO PROMO* *WAS 8K*
*NOW 4k*PROMO 2WEEKS*
*MAGANIN* *GYARAN* *NONO* *MAI CICCIKO DA* *TUWON NONO SUYI* *DUMUR* *DUMUR DUK ** *YAUSHINSU* *KINDADE KINA FAMA* *DA* *MATSALAR* *YAMUSHEWAR* *NONO* *OGA YA* *TABA YAJISU KAMAR* *TSUMMA* *KINYI MAGANIN* **BAKI DACE BA HMM* *MATSO KUSA* *AUNTY ZEEv KU ** *MATSO KUSA DA WA* *ANDA SUKA* *YAYE DA YAN MATA* *HAR MA DA* *ZAWARAWA INA* *KATSINA INA* *TURAWA KO INA A* *FADIN KASAR AN* *HARMA DA KETARE* *WANNAN PROMON DANAGAMA WALLAHI KUDINSHI 8K NE MAGANIN NAN DA KUDINA ZAN HADA TALLAR MAGANIN ZANYI KAMAR YANDA KUKA SANI*
*AUNTY ZEE MOM* *MUJAHID TAKUCE* *KIRA KO CHART*
08162859027


Naceba=?K?
@&?
Kina bukatan jikinki yazama so fresh ba kwarzane ko daya ballantana kuraje ko tabo, sunburn,acne, ko knuckles? Kije kigwada products na mg's insha Allah zakiga ynd fatarki zedawo fiye da tsammaninki zakigyara jikinki naturally batare da kinbata fatarki ba jikinki yayi fresh kiyi smooth kizama kalar Madara kirar models kiringa walwali kina haskawa duk inda kikayi=?
?
Kidena kokonto cewa kingwada baki Dace ba insha Allah kijaraba products dinsu bi'iznillah zakiji dadinshi=?O? kayansu akwai kamshi especially sabulun kamshin yakama jikinki ko kindade da wanka jikinki zaidinga fidda ni'imtaccen kamshi bayinki ma zakiji kamshin dazai Kama=?
?sunada kit special domin amare Wanda indai kinyi using kit dinnan Baki bukatar kikara Kai kudinki gurin dilke domin ainihin yanda fatarki zehaska yagoge kidinga shining abun sewanda yagani=?
?

Mai bukatar kayan mg's chat:08062991549,07046881166,07067210195
Call:08064532391
Hausawa nacewa adade anayi sai gaskiya Kuma siyan nagari maida kudi gida>??
=??? tested nd trusted
Natural/organic>?p?

*WANAN LITTAFIN NA KUDINE BIYA 500 TA WANAN ACCT 0272061655 WEMA BANK NAFISA NUHU KO KATIN MTN KO AIRTEL TA WANAN LAYIN 08033719070 DOMIN KI MALLAKI NAKI KI MUTANEN NIGER KUMA KU TUNTUBI WANAN LAYIN*
*+227 96 82 89 84 DUK WACCE TA MIN SHARING NA BAR TA DA* *RABBI ZAI FIDDA MIN HAKKI NA DA IZININ ALLAH DOMIN BA YAFEWA NAYI BA*


*NI DA KISHIYOYINA*

*NA SADNAF*

*PAGE 32*

Luba

Matar da dan acaba ya kai ta wajen ta, kwana biyu kawai tayi ta fara masifar yaushe zata tafi duk da biyayyar da take mata tana bauta mata ta hanyar yi mata aikace aikace wai duk dan kar ta gaji da ita,abincin ma kanzo take zubo mata,haka yaranta zasu ta mata rashin kunya a yau ma tana rabe a gefe wani dan ta yazo yabi takan kafarta ya wuce olu taji tana kiransa dashi da gangan ya taka ta dan yaran matar duk basu da tarbiya sabida bata Jin turanci suke ce mata aboki ta lura hausawa suke cewa aboki,tuni taji zuciya yazo mata bata san sanda ta mik'e tsaye ta jawo shi tare da gaura masa mari ba ya tsalla wani uban ihu har sai da matar ta fito daga dakin ta da gudu da harshen turanci tana waye ya tab'a shi,sai a lokacin Luba tasan ta kwafsa ita da ake taimaka wa mai ya kaita tab'a dan masu gida.

Da turanci da hausa ta hau bayanin dan ta kare kanta a lokacin da matar tayo kanta tana masifa da turanci akan daga taimako zata zo har tana jibgar mata d'a,kafin ta Ankara ta kwasheta da mari,karshe sai da suka yi mata taron dangi da yayan suke jibgeta tare da watso da ita waje.

Luba haka ta hau neman taimako tana kuka zuwanta legas bai zame mata alheri ba sai sharri gashi dan acaban da ya kawota bai cika alkawari ba wajen waiwayarta.

Duk yanda taso samun wajen kwana da taimakon mutane bata samu ba haka ta cigaba da dab'awa a kafa duk da bata san Inda zata je ba,tasan dai ta fito kamar cikin gari sabida wajen da ta b'ullo akwai yawaitar jama'a a wajen,Yan acaba tagani kaca kaca a wani karkashin gada,ga masu siyar da abubuwa da yawa haka kawai taji sanyi na ratsa zuciyarta dan ta fara hango yan uwanta hausawa a karkashin gadar da sauri ta tsallaka duk da batasan wajen wa zata je ba taje ta samu inuwa ta zauna tana huta gajiyar tafiyar da ta sha a k'afa dan ta kusa fin awa tana tafiya a zaunen da take tana ta karewa masu siyar da abinci kallo rabin su ma hausawa ne da alama zaman legas yasa Suka koyi turancin broken da yarabanci.

Wata ce tafi d'aukar hankalinta dake ta hada hadan siyar da abinci Yan acaba sun mata rubdugu suna ta siyan abinci,bere taji suna ta kiranta ta basu abinci na kaza ta basu abinci na kaza,Kamar ita kadai ke siyar da abinci a wajen sai da mutane suka ragu sosai,Luba ta mik'e ta nufi wajenta "katuwa ce Yar lukuta mazuanan ta kamar ba na mutane ba,sabida girma duk tabi ta cika kujeran,lebbenta bakine sosai Kamar mai Shan sigari.

Luba gefenta taje ta hau gaisheta cikin sakin fuska ta juyo tana amsawa tana mai za'a Baki"?

Luba labarin yanda ta gamu da tsautsayi ta bata ta bata labarin komai tare da fashewa da kuka tana "Ni a yanzu Wanda zai bani kudin mota na koma garin mu nake nema wlh bazan iya rayuwa a garin nan ba Hajiya idan da akwai yanda zaki taimaka min dan Allah ki taimaka min ni ko wanke wanke ne na ringa miki har na tara kudin komawa garin mu"


Dariya matar ta saka tana "Ba kince kudi kika zo nema ba sabida me Kuma zaki hakura ki koma garin ku?ai legas gidan kazo nazo kenan legas gidan bariki idan baka iya bariki ba ka Shiga uku zan taimaka miki idan Allah ya yarda ba sai ma kin min wani wanke wanke ba a yanzu dai bari na zuba miki abinci kici"

Luba washe baki tayi ta hau yi mata godiya rabon da taci abinci mai yawa da dadi haka zata iya cewa tun tana gidan Salis dan har nama ta saka Mata.

Koda ta koshi haka matar ta hau janta da hira kamar irin ta santa dinan,abinda ya d'an daure Mata Kai da ita bai wuce yanda take tafawa da maza har wasu na kai mata duka duwawunta ba,haka dai suka zauna duk da abincinta ya Kare bata tashi sun tafi ba ta cigaba da hira da maza ita dai Luba wani irin rayuwa take gani da bata saba gani ba dan matar ta manyanta bai dace ta ringa Abubuwan da take ba.

Bacci kawai take ji ga fitsari da ya matseta da kaikaiyi bata ga alamar akwai wajen da zata iya fitsari ba gashi dai ta gama siyar da abincin amma tak'i tashi su tafi,sai nunawa maza take ita tana ga kanwarta nan.

A takaice basu bar wajen ba sai wajen Sha biyu na dare ita ta taimaka mata ta d'auki wasu kayayakin ta ta d'auka ko zasu hau acaba sai taga da kafa suka ringa takawa basuyi wani tafiya mai nisa ba suka iso wani katon gate da tun kafin su karasa taji kida na?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? tashi Luba ita dai zare ido kawai take tana kalle kalle har suka shiga ciki dan bata Jin ma gidane dan da suka shiga wawakeken fili ta hango da speakers wasu na tsakiyar fili suna rawa ita dai sakin baki tayi tana kallo matar da ta biyo da taji ana cewa bere ta ringa yiwa maza magana ita dai sam bata gane Inda ta kawota ba dan bata ga alamar gida ba so take mata tambaya amma tana tsoro ita kam taga rayuwa da mutuncin ta da komai sai gashi ta jawowa kanta garari a titi da kila bata yi haukan da tayi ba da kila tana can gidan Salis tana zuba mulkinta san ranta.

Duwawunta da taji an kaiwa duka yasa ta waiga da sauri taga wani ne kato ta bayanta hannunsa d'auke da sigari yana "Bere wanan cikar fa"?

"Kai bakuwata ce bana san iskanci ku ba dama kuga bakon fuska kizo ki wuce mu tafi kinji"

"Hajiya duwawuna ya kawowa duka fa wanan wane irin iskanci ne da Aurena da komai"


"Au kina da Aure dama"?

"Inada Aure mana hajiya"

"Toh mai kikazo yi a legas"

"Kudi nazo nema hajiya dan mijin nawa baya nan guduwa yayi ya barni"

"Kuma garin ku bai isheki Neman kudi ba kika taho legas,ai shikenan biyoni muje"

Luba bin bayanta ta fara yi har lokacin tana ta mamakin matar ita dai taga Kamar dai matar Yar duniya ce duk da ta manyanta ta Ina zata soma irin wanan rayuwar da girman ta da komai.

Wani irin kumbul kumbul dakuna Suka ringa wucewa ta baya ko kad'an bata kawo wai akwai wajen Zama a wajen ba har sai da suka zo gaban wani daki da aka kulle da kwado.

Ta sauke farantin kanta ta d'auko mukuli daga cikin jakarta ta bud'e tana "Bismillah"

Luba binta tayi cikin d'akin bashida wani girma sosai sai tarkacen kaya da katifa da aka saka a kasa.

"Nan shine dakina anan yawanci irin mu masu Neman kudi muke haya sabida bashida wani tsada ni a kyauta ma nake zaune dan haka kafin kisan Kan komai Zaki zauna anan kafin ki Saba da komai"

"Hajiya naga Kuma ana ta kida a gidan"

"Toh ai gidan drama ne nan ta baya aka bada haya ai bazan iya Kama gida a legas ba nan shine daidai karfin talaka kowa rayuwarsa kawai yake anan ba ruwan kowa da kowa karki wani damu a hankali Zaki Saba"


Luba shiru tayi badan ta gane bayaninta ba a karantar dai da tayi matar ba matuniyar arziki bace daga ma yanda ta ringa cin Karo da maza da Mata.

"Kwanciya zakiyi ko zaki dan watsa ruwa"?

"Da zan samu na watsa ruwan da naji dadi dama ko sallah banyi ba"

A takaice ita ta rakata wajen bandakin da ba rufi sai k'ofar kwanu duk da ta kulle k'ofar a tsorace take da sauri sauri ta ringa watsa ruwan dariyar da taji a saman katangar bandakin yasa ta dago da saurinta wani ne ya mata kuri ta katangar Yana kallonta kamar ya samu tv,da sauri ta jawo zaninta ta rufe jikinta tana "Allah ya isa uwarka kake kallo bani ba"
Dariya tya kyalkyale dashi har ta fice daga bandakin da gudu a hanya ma sai da ta hadu da wani ya dumbula mata nono da gudu ta karasa d'akin tana Shiga ta fara "Hajiya dan Allah ki rufa min asiri idan akwai wajen da Zaki maidani ki maidani wlh bazan iya wanan rayuwar ba da girmana da komai da manyan yarana ake biyoni ana tab'a ni wani har da lekena hajiya nidai ki taimaka min dan Allah bazan iya ba"

Dariya bere ta saka sai da tayi mai isarta tace "ikon Allah ni yanzu ban miki k'ok'ari ba ban sanki ba nayi niyyar taimaka miki naga kuma kina Kara neman wani taimakon legas kika zo fa banida wajen daya wuce nan a hankali ma zaki Saba idan kika ga bazaki iya ba Kuma nayi iya k'ok'arina zaki iya saka kayanki ki tafi"

"Kiyi hakuri hajiya banida mai taimaka min amma Ina neman arziki ki musu magana kice musu ni matar aurece"

Dariya ta saka tana "idan kikace kina da auren nan dariya kike bani wlh toh naji zan fada musu"

Luba kayanta ta fara k'ok'arin mayarwa jikinta bere tace ta bari ta d'auko mata t

30 / 38