Nida kishiyoyina complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Romance

Chapter   2 / 38

3K to 6K   out of 111.9K words

zama.

Ni tausayinta ma na koma ji dan ta saka damuwa a ranta sosai gashi tana d'auke da ciki.

Ba'a kwana biyu bata zo gidana ba,idan tazo haka zatayi ta mita tana tsinewa Hamza akan ya cuceta a irin wanan halin Nima na samu cikin a lokacin Ashraf ya tafi shekara uku.

Nidai zan iya cewa banida matsala komai dan Asirina kam a rufe yake dan banida wani matsala a gidan aurena daidai gwargwado salis na kyauta ta min.


Cikina wata biyar Luba ta haihu Sanin halin da suke ciki yasa na zage sosai wajen hidimanta mata Salis ma baa barshi a baya ba duk da bashida kudi.

Nidai nasiha da shawara ke rabani da luba da ta balain raina Hamza ni nasan da baya Santa da tuni ya saketa dan Abubuwan da ya mata ma duk sai da ta raina burinta ma kawai ta kashe auren.


A haka nima Allah ya saukeni lafiya na haifi Afrah a haihuwan nan Salis ya min hidima ba kad'an ba,tunda na haihu Luba bata tab'a d'auke kafarta daga gidana ba tun safe idan tazo sai dare take tafiya,kayan fitar sunan da salis ya siyamin take ta juyawa a hannunta tana "Kinsan kuwa tsadar atamfar nan Ina Salis ya samu kudi haka"?


"Kice atamfar nada tsada wai Ashe tunda nasamu ciki ya Shiga adashe shine fa Ina haihuwa ya karbi Adashen ni Ina nasan ma zanin nada tsada"


"Aikuwa da tsada yayi k'ok'ari gaskiya ni Ina naga arzikin Rabin atamfar nan ma wlh Hamza ya cuceni gashi yak'i sakina"

Zama nayi a gefenta Ina "kiyi hakuri Luba mai nema Yana tare da samu ai da ace baya nema sai ki fida rai amma tunda har Yana nema watarana za'a dace insha Allahu Kuma zakiji dadi tunda Yana kaunarki"

"Hmmm kinsan ko Napkin baya iya siyawa Sultan wlh ba irin rayuwar nan na tsarawa kaina ba"

Kwalla ya zubo mata ta share a daidai lokacin da Salis ya daga labule suka gaisa daga bakin k'ofa ya mikomin ledar daya shigo dashi ya fita.

Da zan ajiye ledar sai Kuma na bud'e ledar naga Kayan jarirai ne sai sarka da dankunne da mayafi kala biyu ganin tana ta kallon ledar yasa na fito da kayan ciki na nuna mata ta ringa juya kayan tana yabawa a cikin turamen zanin da aka kawo daga gidanmu na dauko daya na bata dak'yar ta karba tana da na barshi ita wanan haihuwar da nayi bata da abin bani.

Koda tazo tafiya ma sai da Salis ya bata kyautar kudi,na rakata ta tafi.


Ahaka akayi sunan Afrah banaso na sosa mata zuciyarta taji ba dadi Kaya kala biyu kawai na saka.


A haka rayuwa ta ringa tafar mana daidai gwargwado Ina k'ok'arin taimakawa luba indai ta kawomin kukanta zan k'ok'arta naga na share mata hawayen ta Afrah ta tafi shekara biyu wataran Salis ya shigo gidan da takarda a hannunsa cikin tsananin murna Yana nuna min sunansa ya fito a cikin wayanda suka ci scholarship da zasu fita Kara karatun da zai zama cikakken likita.

Ji nayi Kamar na zuba ruwa a kasa na sha dan murna dan duk Wanda yasan Salis yasan burinsa kenan yan uwa da abokanan arziki kuwa sai taya mu murna ake ciki kuwa har da Luba da ke fama da tsohon ciki duk ta fice a hayyacinta sabida damuwa da ta sa a ranta.

Duk kudin da salis ke dashi ya ajiye min akan zai na min aike,a haka ya shirya kayansa ranar tafiya na sha kukana na gode Allah Kamar bazamu rabu ba gashi lokacin sai dai sako ba yawaitar waya ya damka amanarmu a hannun Iyayensa ya tafi.


A takaice bayan tafiyar Salis da shekara biyu komai namu ya Kare kudin haya ma ya Kare gashi banaso na ringa dorawa Iyayensa nauyi dan suma suna da nauyin kannensa akansu sosai,a haka Yayana ya ringa hidima dani, ganin ni kadai ce ba Kuma a yanzu Salis zai dawo ba, yayana yace na dawo gidansa na zauna har zuwa lokacin da Salis zai dawo,dan iyayen mu suna katsina tunda yayi Aure shekara da aurensa rukona ya koma hannunsa.

Yayana shi ya ringa hidima damu ya saka yarana a makaranta.

Luba kuwa tana ta fama ba yanda ba tayi dan ta kashe aurenta ba Hamza yak'i sakinta har magana nayiwa yayana akan ya taimaka mata da ko jarine sabida kawai ta kwantar da hankalinta

Amma duk da ya bata jarin burinta taga ta kashe auren wulakanci kuwa kwando kwando haka ta ringa Masa.


Nidai tsakanina da ita shawara ne abinda nake dashi iya Karfina Kuma Ina taimaka mata dashi a haka kwanaki suka ringa juyawa zuwa sati,satika zuwa watani,watani zuwa shekaru,tunda Salis ya tafi sau biyu kawai ya tab'a Mana aike.

A takaice Kamar Wasa sai gashi har Salis ya tafi shekara biyar saura Masa watani ya dawo ya turo kudi ta hannun yayana aka siya masa katon fili aka fara Masa gini.

Koda na gayawa Luba murna ta ringa yimin tana "Aisha Allah ya baki wasa wasa mijinki ya zama mai kudi"

"Luba kema dan kin k'i kwantar da hankalinki ne ba abinda baya wucewa mijjnki Yana nema ai watarana zai dace insha Allahu"

"Hmm banga ranar ba Aisha nidai banida burin daya wuce ya sakeni dan bazan iya ba"


Shirye shiryen dawowar salis na farayi dan baifi saura wata biyu ya dawo ba shekara biyar ba Wasa ba daga irin ginin da ake kerawa nasan Salis ya samu kudi ni bashine a gabana ba nidai burina ya dawo naganshi dagani har yarana munyi kewarsa.

Saura sati uku ya dawo naje gidansu da yara anan mahaifinsa ke cemin ya turo kudi akan aka ma mana haya.

A takaice gidan hayan ma da aka kama Mana katoton gaske kayan dakina kuwa duk na siyar dan sun zama tsohon yayi a kudin dayayi saura Wanda ya turo na cika na sake sababin kayan d'aki Kamar dai amarya yayana ya taimaka min shima dan ba karya yayana Yana ji dani.

Luba kuwa sai saintyn gidan hayan take tana ai Salis ya zama mai kudi da dukan alamu saura na wulakantata na juya mata baya ni dariya ma take bani dan bana Jin ko mai Zan samu zan ari halin da ba nawa ba ni bana ma fada mata komai,yanzu dan Kar taga Kamar da biyu nake bata labari amma kullum tana tafe dole ta ringa sanin halin da nake ciki...


Presently

Yaran duk suna zaune a palo suna kallo Hindatu itama tana zaune a palon.

Fitowar Aisha daga d'akin yasa ta saki murmushi tana "Hajiya kin fito"

Murmushi Aisha ta saki tana "Eee wlh wai da so nake na leka gidan sunan na idan banje yanzu ba bazan samu zuwa ba"


"Bari na saka mayafina na rakaki"

Hindatu na k'ok'arin mik'ewa Luba ta fito daga dakinta tana "ke dai anyi shugaban munafikai Sam bakiji dadin rayuwarki ba wlh idan ma duk so kike ku hada kai dan ku cutar dani wlh ba abinda zaku iya min"

"Allah ya baki lafiya ku tashi ku koma karamin Palo kafin ta fara kawo muku duka"

"Kambalai kina nufin ni mahaukaciya ce"?

"Toh da fa kina da hankaline.....

MG'S SKINCARE


Dame akafiki yar uwata?
Kyan fatar ko iya gyaran fatar?
Ina riba g macenda t Maida kanta sauran mata?
Shin haryenzu labarinmu kikeji ko kike bayarwa?
Hajiyata miye matsalar?
Fatar takice abun se lahaula?
Kingwada kingwada harkinsare?
Tsakanida Allah yaushe daren yayi balle wayewar garin?

Inbakida labarin MG'S wacce tasanki tasansu,
Gawurtaccen Kuma shahararren kamfanin gyaran fatane,duk lalacewar jiki,duk hautsinewar fata,duk yenda jikinki yazama abun kunya gareki, Ina tallata maki me gabadaya,

Muntarkato,munwarwaro,munqullo duk wani Abu daze maidaki wanke hannu kataba mun qara a cikin kayayyakinmu,muncire,muntsife,munfidda,mun tantance mun hadamaku wasu irin hadaddun lafiyayyun kaya masu masifar goge fata,wallahi duk fitinar fatarki inshallah,kinzo bustop,kisiya kiyikyanda ko mace,kan juyo ta waiwayo ta dubi halittar Allah,

Ga product din kamar hka,
Sabulu 4500

Mg's beauty kit
Karamin kit 12k
Body soap
Facial soap
Body cream
Face cream
Glow oil
Pink lip balm

Flawless skin beauty kit
Babban kit 20k
Body soap
Facial soap
Body cream
Face cream
Scrub
Glow oil
Pink lip balm

Note kowanne d kalanshi nd yanayin packaging dinma aren't the same,

Tsakanida Allah kigafa
Duk wannan garabasar Kuma kinazaune hba taso a dama dake a harkar yar uwata,

Ayi hakuri da sauyin farashi komi yatashine muma b hka mukasoba
Chat:08062991549,07046881166,07067210195,
Call,+2348064532391




LUBA...

*NI DA KISHIYOYINA*

*NA SADNAF*

*E.W.F*


*PAID BOOK*



*Page 3*


Present

"Hindatu wlh taraki nake karki ga Ina kyalleki wlh zan baki mamaki"


"Ke a yanzu akwai abinda zaki yi ki bani mamaki Luba ai banga abinda dai zaki yi yanzu ki bani mamaki ba, asara dai kinyi ta abin kunya dai kin aikata kowa yasani Idan kina haukarki ki daina zuwa wajena kije can ki karata ke daya"

Ashar Luba ta lailayo ta fara zagin Hindatu da taja tsaki tabi bayan Aisha da ta dade da ficewa daga palon dan idan suna abin su ko tankasu bata yi har yanzu tana mamakin halin Luba.

Tare su kaje sunan suka dawo Aisha sam bata bata fuskar da zata mata maganar luba ba dan tana Jan girman ta duk da Hindatu tana iya k'ok'arinta wajen girmama ta tun daga bakin k'ofa suka fara jiyo ihun ummi Yar gidan Hindatu dan yaran hindatu uku da Alhaji ummi itace karama.

Da mugun gudu Hindatu ta Shiga gidan a daidai lokacin da Luba ta kara daga bulalan hannunta zata zabga mata Hindatu cikin ihu tace "wlh wlh sai na rama dukan da kika mata cikin wani irin super ta dira gaban Luba suka fara wani irin k'ok'awa.

Aisha da sai a lokacin ta shigo gidan har zata wuce su ta tsaya tana "Dan Allah yaushe zaku girma ku daina abu Kamar kananan yara ko akauye ba'a irin wanan rayuwar ace kullum sai kunyi fada kunyi dambe a gaban yayanku wanan wane irin rayuwa ne"? Hindatu cikata"


dak'yar Suka rabu suna hucci dan hindatu ta dan fi Luba tsayi da kib'a

"Kinyi asara wai sabida kina Jin haushina kika hau dukar min 'ya toh wlh daga yau duk ranar da kika Kara tab'a min Yara Allah sai na baki mamaki"

"Kafin ki bani mamaki hindatu ni zan baki mamaki"

Ta shige dakinta da sauri tana shiga ta d'auki wayar ta ta nemo Asabe a waya (itace aminiyar luba)

Tana dagawa tace "Asabe gobe Ina nan tafe inaso na koyawa Hindatu hankali"

"Ta Kara hadoku kenan"?

"Eee idan nazo zan baki labari"

"Sai kinzo"

Ta katse wayar tana jijjiga kafa a duniyarta bata da burin ma taga ta raba Alhaji Salis da kowa tafiso taga ta juya taga ita kadai ce a gidan bata san ya akayi Hindatu taga gadon baccinta haka ba"


Past

Aisha

A ranar da salis zai dawo daga ni har yayana shiri mu ka tayi,duk abincin Dana san yana so na dafa masa dagani har yayana munyi tsaf damu bansan dai karfe nawa zai iso ba amma nasan a ranar zai dawo wajen karfe uku sai ga luba tazo wai tazo yiwa salis sannu da zuwa dariya nayi Ina ta kyauta,sosai nake Jin luba a raina tamkar Yar uwata tunda duk ta damu da damuwata,abincin da na girkawa salis na zuzubo mata tana ci muna hira tana bani labarin irin talaucin da Hamza ke fama dashi ko abinci ma babu a gidan,sai naji tausayinta har a raina na yanke idan Salis ya dawo naga yazo da nauyinsa zan masa magana ya taimakawa hamza.

Wajen karfe biyar na yamma muka ji dirar mota a k'ofar gida.

Dagani har yaran muka diba mu kayi waje da gudu shekara biyar ba Wasa ba, ai Salis bai gama fitowa bama na daka tsalle na rungumeshi ina ihun murna,dariya kawai yake Yana na barshi ya d'auki yayansa.

Kaninsa sai dariya yake mana driver taxi din Kuma nata fito da akwatuna da jakankunansa kaninsa ya ringa d'auka Yana Kai wa ciki.

Afrah ya d'auka yana ta fadin girman da tayi daya hannun nasa rik'e dana Ashraf nidai tunda ya sakeni kallonsa kawai nake ya balain canjawa kamar bashi ba ya zama wani dan gayu ya goge Kamar wani bature duk sai na raina ma kwalliyar da nayi na tarbarsa.

A haka muka shiga cikin gidan sai da muka je Palo ya sauke Afrah ya juyo Yana kallona da alama bai lura da Luba dake rabe a gefen kujera ba.

"Gaskiya nayi kewarku sosai no place like home indo Kinga yanda kika canja kuwa Anya kinyi kewata"

"Uhum uhum"

Luba tayi gyaran murya ya waiga da sauri ya kalli wajen da take zaune Yana "Kai Luba wai dama kina palon nan ai ban lura dake ba"

"Ya za'ayi ka lura dani likita bokan turai"

Dariya yasa Ya zauna akan kujera a daidai lokacin dana zuba kunun aya dana hada masa na mik'a masa ya karba yana "Yauwa indona kice kawarki tana cikin masu kular min daku"

"Aikuwa Luba kam ba daga nan ba wlh bata bari munyi kadaicinka ba"

"Aikuwa ta kyauta Allah ya bar zumunci ya mai gidan"


Tuni murmushin dake fuskarta ya kau, salis bai ma lura ba sai tambayoyi yake yiwa su Afrah a takaice Luba sai da magriba ta tafi na lura jakankunan da salis ya shigo dasu take so a bud'e nidai tunda na kai d'aki ban bud'e ba,na dauka ma zata tafi da wuri tunda ya Kamata taga dacewar haka,amma bata tafi ba duk da salis ya shige d'aki.

Nima na matsu na keb'e da mijina amma haka na daure na zauna muka ringa hirar a lokacin da tazo tafiya da yake
girkin da nayi da dan yawa a flask na diba mata da yawa canjin daya min saura na bata ta tafi akan sai ta zo karbar tsaraba nace mata sai tazo.

A ranar kusan raba dare muka yi da salis Yana bani labarin rayuwar da yayi a waje da cigaban da ya samu dan ya dage sai ya dawo ne sun bashi aiki acan amma a Yanzu ma ya samu aiki a wani baban asibiti ga Kuma aikin NGO daga labarin da yake bani nasan Salis ya zama mai kudi babban burina naga na taimaka wa Luba kwana biyu da dawowarsa bayan duk ya hucce gajiyarsa ya dan zaga dangi na shigar Masa da maganar taimakon da nake so a yiwa luba da mijinta.

Cemin yayi zai yi iya k'ok'arinsa amma a Yanzu daya dawo gininsa kawai yake so ya sa a gaba zai bani abunda ya samu na bata kafin ya kamalla gininsa.

Abinda ya bani mamaki Luba bata tab'a sati guda bata zo ba sai gashi tun ranar da Salis ya dawo bata Kara zuwa ba gashi a cikin lodin tsarabar da salis ya kawo mana da yayana na d'aukar mata itama da yayanta tunda itama namiji da mace ne Sultan da Ilham ganin an tafi kwana goma banganta ba yasa na nemi izinin a wajen salis akan zan je na dubata naga ko lafiya danazo tafiya ya bani Dubu Ashirin akan na bata taja jari a lokacin kudine mai yawan gaske tamkar ni yayi wa kyauta haka naji sabida tsabar murna.

A lokacin da na isa gidanta a tsakar gida na sameta Sultan danta a shimfide akan tabarma

Da alama bashida lafiya da sallati na karasa nayi wurgi da ledojin hannuna Ina "Luba dama sultan bashida lafiya"?

"Hmm Aisha kenan yanzu tsakani da Allah tun ba'a je ko Ina ba kin fara juya min baya dan mijinki ya zama mai kudi,har ace baki gani ba kwana goma ko ki nemeni kiji dalilin dayasa ban zo ba"

"Haba Luba Mai yasa kike hakane kefa mai fadawa wani halina ne wlh tunda Salis ya dawo nake ta bak'i Yan sannu da zuwa hankalina na wajenki a yau na samu kaina nace bari nazo na duba ki naga ko lafiya amma har Zaki min mumunan fassara haba mana Allah Kar ya bani arzikin da zai saka na wulakanta mutum wlh banji dadin maganarki ba"

"Aisha kenan Allah ya baki hakuri nidai Ina tsoron kin canja din dan yanzu gani nake ma idan nazo wajenki zaki ga Kamar na takura ki ko nazo maula"

"Allah ya kyauta tashi mu Kai shi asibiti"

Nace dan har ga Allah na ji haushin maganar luba.

Mik'ewa tayi ta Shiga d'aki sai da ta d'auko masa Kaya ta taimaka masa ya cire na jikinsa ta rik'e hannunsa Muna k'ok'arin yin waje sai ga Hamza ya fado gidan da leda a hannunsa.

Luba kuwa ta saki hannun Hamza taje ta cakumo wuyan rigarsa tana "Hamza ka bani takardar sakina na gaji da aurenka maganin naira dari ma bazaka iya siyowa danka ba ka sakeni Hamza bazan iya da wanan auren naka ba"

Hankalina idan yayi dubu sai daya tashi, dan zagi na rashin mutunci haka ta ringa yiwa Hamza.

Luba bata ji bata gani haka ta ringa ihu tana ce Masa idan ya cika dan halak ya saketa sallati na saki da k'arfi a lokacin da naji Hamza ya furta mata saki biyu ita kuwa ta sake shi da sauri tana hamdala akan ya saketa.


Nayi matukar bakin ciki da mutuwar Auren Luba ita kuwa ba abi??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????nda ya shafeta sai ma murna da take da ta tashi ma barin gidan iya kayanta ta dib'a tace yaran suyi zamansu a wajen babansu bazata tafi da kowa ba.

Tsananin tausayin Hamza da yaran yasa kudin da Salis ya bani akan na bata na bawa Hamza ya ringa min godiya yana min Addu'a.

Luba kuwa tayi nisa a hanyar tafiya gidansu da kayanta.

Haka naje gida jiki duk a sanyaye.

Koda na bawa Salis labarin abinda ya faru cemin yayi dama Luba bata da hankali ai ya taya Hamza murna da ya rabu da ita.

Present


ANEESA

Ki sake tunani Aneesa taya zaki rasa Wanda zaki aura sai mai mata har uku kije a ta uku mai zakiyi da tsoho bayan ga dan uwanki nan da ya dade Yana kaunarki,nidai wlh bazan barki ki auri mutumin nan ba sai kace kin rasa mijin Aure"

"Wlh Alhaji Salis Yana kaunata Yama ce ba gida daya zai ajiye mu ba nidai shi nakeso na aura"

Aneesa tace tana zumburo baki

"zan ga kuwa mai aura miki shi"

Mama binta tace tare da mik'ewa ta bar palon.

Adaidai lokacin da Kiran Alhaji Salis ya shigo wayar Aneesa tana dagawa yace "Gani nan a waje na karaso"

"Gani nan zuwa"

Aneesa ta mik'e ta Shiga d'aki tare da d'auko hijabinta ta saka tayi waje......


Nayi typing mai tsayi wlh ya goge

MG'S SKINCARE


Dame akafiki yar uwata?
Kyan fatar ko iya gyaran fatar?
Ina riba g macenda t Maida kanta sauran mata?
Shin haryenzu labarinmu kikeji ko kike bayarwa?
Hajiyata miye matsalar?
Fatar takice abun se lahaula?
Kingwada kingwada harkinsare?
Tsakanida Allah yaushe daren yayi balle wayewar garin?

Inbakida labarin MG'S wacce tasanki tasansu,
Gawurtaccen Kuma shahararren kamfanin gyaran fatane,duk lalacewar jiki,duk hautsinewar fata,duk yenda jikinki

2 / 38