Nida kishiyoyina complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Romance

Chapter   6 / 38

15K to 18K   out of 111.9K words

zuciyata ta daban ce Inda nasan haka ya hada da san da nake yiwa muhasim da tausayin mahaifiyarta da ke fama da larura.

A lokacin da Luba tazo gidana sakin baki nayi Ina kallonta dan wani irin kyau naga tayi Kamar wata amarya,kayan jikinta ma masu balain tsada ta Sha lullubi har saman kanta Kamar dai matar aure.

Ni Ina Kare Mata kallo ita Kuma ta zubawa Nana Ido dake kwance a doguwar kujera tana "A Ina kika Samo 'ya nidai nasan ba haihuwa kikayi ba tunda ga ciki nan a jikinki"

"Wlh yarinyar wata Yar uwarmu ce na karbota dan maman ta tana haihuwa ta rasu.

Ta saki sallati tare da nufo wajen da na kwantar da ita ta d'auketa tana "Allah sarki baiwar Allah kice bata san mahaifiyar ta ba

Kwalla ya zubomin na kashe muhasim da nayi da ranta da tausayin ta hanyar da aka samu Nana Ina "wlh kuwa"

Na share hawayen fuskata Ina cigaba da kallon luba da nidai ta canja min sosai har sai da na kasa hakuri nace "Luba Kinga yanda Kika canja kike kyalli Kamar wata amarya kuwa"?

Ta saki murmushi tana "Ai amaryar ce tunda na kusa shiga daga ciki"

"Dan Allah fa"?

Nace cikin tsananin murna Ina "wa kika samo dan da alama kin samu irin wanda kike so"?

"Wlh na samu Aisha alhamdulillah tunda na kwallafa a raina sai na samo Mai kudi na samu dai"

"Kai Alhamdulillah na miki murna sosai wlh kawata a Ina yake aiki"?

"Gidan mai ne dashi fa sai dan aikin asibiti da yakeyi"

"Kai madalla naji dadi wlh ya turo manyansa?mai mata ne"?

"Ke fa dan baki fiye zama bane amma da duk kin san halin da ake ciki,ya turo manyansa mana a ranar da aka kai kudin kawai aka daura Auren,Yana Kuma da Mata"

"Na saki baki Ina kallon ta cikin tsananin mamaki"

"Wai kina nufin yanzu haka da aurenki"?

Ta saki dariya "kwarai kuwa tarewa ne dai banyi ba sai wani satin"

"Kai wai dagaske kike ko da Wasa"?

"Wlh dagaske nake toh mai abin mamaki nifa ba budurwa bace bazawara ce ni, shima ba saurayi ba wane shiri za'ayi ai kawai Aure aka daura zan tare sati mai zuwa"

Na saki ihu dan har ga Allah wlh kamar na taka rawa haka na ringa ji "Na miki murna kawata wlh bakiji dadin da naji ba Kai Kai Kai ke kinji dadin da nake ji a zuciyata a Ina Kuma zaki zauna"?

"Abuja zan zauna"

"Aikuwa duk da uban cikin jikin nan nawa dani zaa kai ki insha Allahu haba shiyasa wlh da kika shigo naga kina ta walwali Kai Aure ma rahama ne wlh zanso kuwa ganinsa ko baki bashi labarina ba"

"Kai ai yasan da zamanki dan baya garine da dashi zamu zo ku gaisa"

"Ba damuwa idan munje Kai amarya sai naganshi ai"

"Kijiki da wata magana Wai Kai amarya sai kace budurwa ai dagani sai mijina zamu wuce ba mai rakani"

Na saki dariya Ina "Ikon Allah kawata yanzu dai kin Shiga daga ciki kema kin zama matar Aure wlh naji Dadi takaicina daya ba gari daya zamu zauna ba"

"Ke dai bari dadin abin yanzu ai akwai waya kicewa mijinki ya siya miki nima yace zai siyamin sai mu ringa waya"

"Aikuwa wancan sati Salis ke cemin zai siyamin wayar ni kinsan ban wani damu da kyale kyale ba amma ko dan ke dole nasa ya siyamin ko ya zaiji idan nace mishi kinyi aure kullum cikin min yake kice kawarki ta tsayar da hankalinta waje daya tayi Aure"

Ta saki dariya tana "aikuwa dai gori ya Kare an daura min aure"

"Nikam mai zan baki gudunmawa wanan kyalin ma da kike anya angon nan ba Sha zumar amarya ba"

"Toh da ke zai jira"

Na saki dariya tare da mik'ewa dak'yar sabida cikina ya tsufa na Shiga d'aki,dan magangunan da nake siye masu tsada da na jingine a gefe da na daina sha sabida ciki duk na zubasu a leda na bud'e show glass dina da na jera humra da turaren wuta masu balain tsada da aka hadomin daga Maiduguri na d'auko wajen kwalba biyar biyar duk nayi waje na kai mata na ma dai rasa toh mai zan bata.

Ta kuwa washe baki tana min godiya motsin da Nana tayi yasa na d'auketa.

Hira muka yi tayi bata bar gidan ba sai karfe biyar na rakata ta tafi zuciyata fal da farinciki kamar anyi min bushara da gidan Aljanna rabon da na tsinci kaina a cikin irin farin ciki haka har na manta dan tunda yayana ya Shiga tashin hankali nima bana Jin dadin rayuwar amma auren Luba kuwa ya faranta min.

A lokacin da Salis ya dawo ko zama ban bari yayi ba baki a washe nace "Luba kawata tayi Aure"

"Sai naga ya dan zaro ido yana "ya akayi kika san tayi aure"?

"Kai kaji ka da wata magana wlh gidanan tazo dazu nan kasan wlh har ta canza"

Na saki baki na hau bashi labari shi dai ya buga tagumi yana kallona bandai gane maanar kallon da yake min ba"

"Wai dan Allah Abban Ashraf mai yasa baka san kawata ne abin farinciki ya sameta na fada ma ka tsaya kallona"

"Hmm ai wanan kawar taki tsinaniya ce Allah yasa ba ta karfin tuwo ta samo mijin ba"

"Innalillahi haba Abban Ashraf mai yayi zafi haka zaka tsine mata idan bazaka ce Allah ya Sanya alheri ba aikuwa bai dace ka tsine mata ba"

"Hmmm Allah ya kyauta"

Yace tare da d'aukar Nana da ke kwance akan kujera ya hau min wani tambayar duk dan ya Kau da maganar luba.

A takaice sati uku a tsakani na haifi ummi wanan karon banyi wani taro ba amma duk hidimar da Salis ke yawan yimin yamin sosai dan arziki Kam Kara ninkuwa yake inda nafi yarda da sabida Salis nada kyauta da sadaka yasa yake ganin budi,dan ko iya dangina ma Allah kadai yasan hidimar da yake yi dasu ba karamin daga min daraja yayi a wajen dangina ba duk Inda naje sai an fada min abin alherin da yayi.

Luba kam tana Abuja a ta waya na sanar mata na haihu tace min bazata zo ba zata min aike.

Ta kuwa aiko min da kayan jarirai inda na yanke a raina.insha Allahu idan nayi arbain zanje Abuja gidanta tunda anan Salis ke yawan zuwa aiki sati biyu ko uku idan ya tashi tafiya sai na bishi.

Sai dai Koda nayi arbain din na tuntube shi da maganar ya had'e rai akan bazanje ba shi Yama rabani da ita tunda Allah yayi ba'a garin take Aure ba.

Nidai bansan mai yasa yake haka ba.

A haka rayuwa ta ringa tafar mana rungume da yarana da Nana da nake Jin kaunarta na daban a zuciyata lokaci lokaci nakan je bauchi dan na duba muhasim.

Abinda ya fara dan damuna bai wuce zaman da Salis baya yi sosai ba yanzu bashida lokacin kansa sosai kullum Yana tafe hanyar abuja idan yaje sai ya kusa sati biyu ko uku kafin ya dawo.

Ni Kuma a wanan lokacin bansan dalili ba sai naji Ina matukar bukatar shi a kusa dani,yawan tafiye tafiyen sai ya fara damuna, amma tunda nema ne ba yanda zanyi,idan yayi tafiya zai dawo haka zan ta Shirin tarbarsa Ina murna girki kuwa haka zanyi kala kala Ina dokin ganinsa ba iya ni kadai ba har da yarana.


Idan ya dawo kuwa a gajiye tikis sai an samu kwana biyu ma wani Abu ke shiga tsakaninmu dan bacci kawai yake shara idan ya dawo.

Ko ya dawon ma bazai wuce sati ba zai Kara komawa sai an samu sati biyu ko uku kafin ya dawo nidai hakuri kawai na koma yi.

Har maganar nayiwa luba ta ringa min dariya wai ko dai jarraba na karo ai ko shekara zaiyi bai dace na wani damu ba.


A haka dai rayuwa ta ringa tafiya na ringa kula da Nana da ummi da nake ma jinsu Kamar Yan biyu.

Wata rana Alhmis da yayi daidai da auren Luba ya shekara daya ta kirani akan ta haihu.

Na ringa murna Ina alwashin zanje mata tunda Yara suna hutu zan Kai su gidan Aunty mamy idan naje ma na samu lokaci da Salis dan har ga Allah sai naji Ina sha'awar zuwa Abujan dan ban tab'a zuwa ba zan so zuwa har ga Allah a ta waya na Kira Salis da naji muryarsa Kamar Mara lafiya cikin doki nace masa Luba ta haihu dan Allah ya min izini zanzo Abuja inyaso sai na sauka a gidansa bayan suna sai na dawo cikin Yar murya na nuna Masa inama kwadayin san naga ya garin Abujan yake.

Budar bakinsa sai yace min bazani ba shi nan da kwana biyu ma zai dawo na tanade shi ya katse wayar.

Na sake kiransa yak'i d'auka


Wlh har da kukana dan bansan mai yasa bayaso naje wajen Luba ba abinda ma ba gidan Luba zan sauka ba a wajensa zan sauka astagfurullah a ranar har auna masa zagi nayi a raina Koda Luba ta Kira cikin kuka na fada mata ya hanani zuwa ta saka dariya tana ai bazai so nazo ba Kar nayi mamaki akwai abinda yake b'oyemin wayasani ma ko akwai wacce yake da ita a abujan shiyasa ya hana ni zuwa

Wlh sai naji kirjina yamin nauyi kamar ta kwada min katon dutse a ka ban tab'a zargin mijina ba nasan Salis ko.ina ne zan. Iya Masa shaida.

Sai dai me sai naji maganganunta sunyi balain tasiri a raina dan tabbas da yana da gaskiya bazai tab'a hanani zuwa ba tunda a baya shine me cewa zai ringa tafiya dani idan Yara sunyi hutu.

A ranar Sam ban runtsa ba sai naji dama nasan wajen da yake da naje.

Kwana biyu na matsawa kaina da tunanin na Kuma yarda ya ajiye mace a gidan da yake tunda har ya hanani zuwa.

A irin haka muka yi waya da Luba nace dama nasan wajen da yake Abuja wlh da sai dai ya gani Ina Jin maganarta da kamshin gaskiya ta saki dariya tana baki dai yi niyya ba idan har kinaso ki kamashi ki taho zan bincika asibitin da yake aiki bazaa rasa sanin Inda yake zaune ba.

Ai sai naji ba mai kaunata kamar luba sai naji dama yamma batayi ba da na shirya a yau na tafi.

Sai na barwa washegari karfe takwas na dau hanyar Abuja dan ta turomin address din gidanta.

Akan tunda ranar suna akeyi bayan taron zamu nutsu mu nemo gidan Salis.

Tafiyar awa biyar dai sai gani a garin Abuja da na Kira Luba tace na samu taxi na bawa driver ta gaya masa unguwar da zai kawoni.

Ban Sha wahalar samun taxi ba na hadashi da Luba da nake ta Jin hayaniya a gidanta bansan dai yanda Suka yi ba yaja taxi din muka tafi nidai kalle kalle kawai nake sai na tsinci kaina cikin mugun faduwar gaba da bansan mai ya hadasa min shi ba sai na danganta hakan da satar fitar da nayi ne.

Tafiyar minti Ashirin muka iso wani hadadden gida bashida girma sosai amma ya had'u kafin na sauka na bawa taxi kudinsa na janyo karamin akwatina Ina karewa gidan kallo.

Sai na fara k'ok'arin zuge Jakata dan na Kira Luba dan na tabbatar da a gidan aka saukeni.

Muryar da naji yasani dago da kaina da sauri kirjina Kamar ya fado....




MG'S SKINCARE


Dame akafiki yar uwata?
Kyan fatar ko iya gyaran fatar?
Ina riba g macenda t Maida kanta sauran mata?
Shin haryenzu labarinmu kikeji ko kike bayarwa?
Hajiyata miye matsalar?
Fatar takice abun se lahaula?
Kingwada kingwada harkinsare?
Tsakanida Allah yaushe daren yayi balle wayewar garin?

Inbakida labarin MG'S wacce tasanki tasansu,
Gawurtaccen Kuma shahararren kamfanin gyaran fatane,duk lalacewar jiki,duk hautsinewar fata,duk yenda jikinki yazama abun kunya gareki, Ina tallata maki me gabadaya,

Muntarkato,munwarwaro,munqullo duk wani Abu daze maidaki wanke hannu kataba mun qara a cikin kayayyakinmu,muncire,muntsife,munfidda,mun tantance mun hadamaku wasu irin hadaddun lafiyayyun kaya masu masifar goge fata,wallahi duk fitinar fatarki inshallah,kinzo bustop,kisiya kiyikyanda ko mace,kan juyo ta waiwayo ta dubi halittar Allah,

Ga product din kamar hka,
Sabulu 4500

Mg's beauty kit
Karamin kit 12k
Body soap
Facial soap
Body cream
Face cream
Glow oil
Pink lip balm

Flawless skin beauty kit
Babban kit 20k
Body soap
Facial soap
Body cream
Face cream
Scrub
Glow oil
Pink lip balm

Note kowanne d kalanshi nd yanayin packaging dinma aren't the same,

Tsakanida Allah kigafa
Duk wannan garabasar Kuma kinazaune hba taso a dama dake a harkar yar uwata,

Ayi hakuri da sauyin farashi komi yatashine muma b hka mukasoba
Chat:08062991549,07046881166,07067210195,
Call,+2348064532391



*NI DA KISHIYOYINA*

*NA SADNAF*

*E.W.F*


*PAID BOOK*



*Page 7*


Salis ne rungume da farin showel da wasu maza biyu suna "Allah dai ya raya mana Bintu"


Sai a lokacin ya gani nidai lissafi ya kunce min dan bansani ba ko gidansa luba ta saka aka kawoni ba gidanta ba jikina rawa kawai yake dan Luba bata kyauta min ba.

Shi kuwa sallati ya saki da k'arfi Yana "Aishaaaa"

Sai naga yaja da baya a tsorace hannunsa dai rungume da farin showel

Nidai a tsayen da nake wlh banda rawa ba abinda jikina yake Kuma na kasa tunani ko na hasaso mai ke faruwa kamar dai an dasani haka na tsaya ban motsa ba.

Ganin ya koma ciki da balain gudu yasa mamaki kasheni mai ke faruwa ne?

Sai na tsinci kaina da sallati Ina tunanin dai gidansa luba tasa aka kawoni Kuma da kamshin gaskiya kenan Yana tare da wata sai kirjina ya buga da na tuna maganar maza biyun da na gansu dashi suna Allah ya raya musu Bintu"

Ai bansan lokacin da nima na fada cikin gidan aguje ba kirjina na balain faduwa ba dai dagaske Salis yana tare da wata macen ba.

Koda na Shiga gidan canopy naga guda biyu an saka a tsakar gidan Mata da maza a azazaune a fararen kujera da alama dai taro ake.

Sai dube dube nake banga Salis ba.

Sai na doshi cikin gidan a daidai lokacin da wata naga tana k'ok'arin fitowa nayi saurin tareta murya na rawa nace "Baiwar Allah dan Allah waye mai gidanan nazo ne bansani ba ko b'atan hanya nayi"

"Gidan Dr Salis ne ai yau ake sunan Yar sa ko sunan Kika zo ai ki Shiga suna ciki shi da matarsa"

Sai naji numfashina Yana k'ok'arin d'aukewa maganganunta na maimaituwa a kunne na nidai nasan Dr Salis ake ce mishi idan ba ciwon kunne nake ba kamar cemin tayi yau ake suna matarsa ta haihu ?dama Yana da wata matar ne bayan ni? jikina rawar da yake yasa na kasa motsawa sai sallati nake wlh k'ok'awa ma nake da numfashina.

Nafi karfin minti biyar a haka bansan ma Ashe wayata bata hannuna ba Ashe luba da gaske take akwai abinda Salis yake b'oye min shi yasa yak'i barina nazo innalillahi wa Inna ilaihi rajiun.

A hankali na taka dan matatakalar na shiga ciki dan madaidaicin Palo ne sai tsirarun mutane da suke cin abinci idona ya sauka akan kanin luba Nura dake ta loma abinci muryar yayar luba ya doki dodon kunnena "Aa Aisha sai yanzu kika iso"?

Ban iya magana ba sai ido da na zuba mata dan a yanzu Kuma kwakwalwata ta tsayar da aiki inaso nagane wani abu kannen Luba a gidan Dr Salis mai hakan ke nufi mai take nufi da sai a yanzu nazo"

Kallon da nake mata batare da ko kiftawa ba yasa ta ajiye plate din hannunta.

Ta nufo wajena tana "Aisha lafiya kuwa"?

A daidai lokacin da naji muryar Luba kirjina yayi wani irin bugawa na waiga da sauri.

Masifa kawai take tana "Idan bata sani ba yanzu yaushe kake so tasani, salon ka Fadi ka mutu aki yarda cewar na haihu da Kai na gaji da kumbiya kumbiya gwara kawai ta sani a wuce wajen"

Sanye take da shadda ruwan toka ya sha aiki har kasa Ina da irin shaddar har kalar dinkin bambancin nawa yafi nata turuwa ta sha kunshi kina ganinta Kinga mai jego had'a idon da muka yi da ita bai sa ta tsayar da maganar da take ba har sai da ta idda ta Kuma had'e rai tana "Aisha kin karaso"?


Ban bata amsa ba na cigaba da kallonta inaso kwakwalwata ta bani hadin kai na gane mai Luba takeyi a gidan Salisu mijina ita da Yan uwanta.

"Luba lafi??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ya kuwa ya naga Aisha a hargitse haka Ina salisun yake"?

Cewar yayarta ita kuwa tace mata "Yana d'aki yanzu zamu shiga ciki ai"

Aisha kizo mu Shiga daga ciki

Ta juya tare da komawa d'akin da ta fito.

Sai na tsinci kaina da bin bayanta zuwa lokacin nan wlh numfashi jansa nake da k'arfi kaina ma juyamin yake sai inaso nayi tunanin Wai Luba ce matar salis sai na janye tunanin Ina hararo fuskar wata a matsayin matar da Salis ya aura a boye kila matarsa kawar Luba ce shiyasa na gansu a gidan.

Ina tura k'ofar naga salis ya kifa kansa a jikin gado ga jaririya a shimfide a Kan gado Luba Kuma tana jingine da wadrobe din d'akin.

"Salisu"

Na kirashi Kamar an fusgo maganar daga bakina a yanzu tunanina ya bani abinda ke faruwa luba kawata aminiya ta itace Salis ya Aura

"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Aisha kiyi hakuri kiyi hakuri innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Aisha bazan iya dago da kaina na kalleki ba wlh ba a san raina haka ta kasance ba Allah ya hukunta sai na auri Luba tunda ga rabon ya mace a tsakaninmu wlh ba cin amanarki nayi ba innalillahi wa Inna ilaihi rajiun"

"Mtssss Wai kai mai hakane ya kake Abu kamar mace auren da muka yi haramune mtsss wlh karka sake cewa baa san ranka ka aureni ba da san ranka sarai ma dan da baka sona bazaka kwanta dani har na haihu ba,da baka sona bazaka kawoni Abuja wajen da kake aiki sabida ma Kar na nisance ka"

Ta juyo ta kalleni tana "Kawata Salisu shekara daya kenan da aka daura mana aure dashi bisa yarjajeniyar bazaki tab'a sanin ya aureni ba wai nan gaba zai fada miki ya zabi ya ajiyeni anan sabida wai karki tab'a sanin munyi Aure ya Kuma zabi aurena ne sabida kawancenmu ya Kara k'arfi domin kina kaunata Ina kaunarki cigabanki cigabana ne Yana da kyau Kuma kaso wa dan uwanka abinda kaso wa kanka nasan islamiyya daya muka yi kinsan haka dan na auri Salis ba haramun bane ba Kuma haka zai saka Wai kawancen mu ya ragu ba a ganina hakan zai saka mu hade kanmu dake muci arziki tare ba wani abu bane ba auren Salis da nayi bai zai rage

6 / 38