Nida kishiyoyina complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Romance

Chapter   11 / 38

30K to 33K   out of 111.9K words

kaimu duk abinda takeso ki tabbata kin mata"

"Insha Allahu Abba"

Alhaji Salis ya juya tare da komawa bangarensu Hindatu ce da girki hakane yasa ya shige dakin Hindatu.

Yanda ya hade rai yasa Daga Hindatu har luba ba Wanda ya doso ma inda yake ballantana su daga masa hankali duk abincin da Hindatu ta kawo masa ba Wanda ya tab'a.

Bayan sallah Isha ya fito ya zauna a Palo Luba ma na zaune a palon ta hade rai Hindatu na gefensa a zaune wayarsa kawai ya d'auko suka ringa musayar message da Aneesa duk abinda Luba takeyi Yana ankare da ita.

Shayin daren da ta Saba dafawa na jarraba ta shige kitchen ta dafo ta zuba a flask ta fito ta ajiye a palon dan sam bataso taje ta kwanta sai ta gama sa Ido.

Hindatu kuwa hamma ta hau yi ta hau hararar Luba tana "Dan balai mace ma ba girkinta bane sai ta sawa mutum ido ta mike tare da shigewa dakinta.

Luba ta bita da harara

Alhaji Salis kuwa ya cigaba da danne
dannensa a waya Luba itama ta cigaba da zama tana kurbar shayinta fitsarin da take ji tundazu daya mugun matseta amma ta kasa tashi sabida bataso Salis yayi wani abin bata gani ba akan dole ta mike da sauri ta shige dakinta dan tayi fitsari.

Alhaji Salis ya fito da karamin kwalban cikin zafin nama ya juye ruwan a cikin kofin shayin ya koma ya zauna Kamar baiyi komai ba.

Dan jarraba ma a waje ta karasa daura zaninta data fito daga d'akin.

Ta zauna tare da d'aukar kofin shayin ta kai bakinta.......



Ammnur _kayan mata tazo muku da zafafan kayan matan da babu algus 09080070762

Ina uwargida da ta haihu vjay dinta ya bude tana bukatar taji ta koma budurwa gam ga ammnur Nan ta kawo muku zafafan kayan mata Ina amare masu Shirin shiga daga ciki,Ina Zawara da suke so suji Basu da bambanci da budurwa

Enjoyment doesnt stop just because you have given birth. The afterbirth package is made to take care of you postpartum sexual needs . This package includes sweetner, wetner, tightener infection afterbirth herbs and more



Sauran kaya da zaki duba a wajen su na qara niima dadi da matsi sanan akwai na tsuma jiki na mata da na amare da uwargida Wato Madame package, suna da kayan farinjini, favour da kuma mallaka


1)Euphoria 12
2)Gorontula syrup
3)Her exellency cake
4)Exclusive thumi
5)Milky sweety
6)Magic insert
7)Tightening mallaka saop
8)Tightening honey pill
9)Women 001
10)Ebony lady
11) spiced tea
12)Mallaka chicken soup
13)Tightening powder
14) wetness powder
15) favour set
16) attraction set
17) bakar mallaka
18) shu'umar mallaka
19) hatsabibiyar mallaaka
20) horney honey syrup
21) libido booster set
22) breast enlargement
23) hips enlargement



*NI DA KISHIYOYINA*

*NA SADNAF*

*E.W.F*


*PAID BOOK*



*Page 11*

Tana kurba ta furzo dashi da sauri dan wani irin kamshi yake Kamar fiya fiya

Ta hau goge bakinta tana kara shinshina kofin shayin,ta kalli Salis da wani irin bakin ciki ya rufeshi tunda ya ga ta Kai kofin bakinta yaji wani dadi ya rufeshi tana furzo shayin ya d'auke kansa ya cigaba da danne wayarsa Kamar bai san mai take ba kasan zuciyarsa Kamar yaje ya danneta ya dura mata dan yanzu babban burinsa ya kau da ita dan ya gaji da barazanar da take masa har wani zubin yakan ji gwara ma ya saketa ta fallasa shin amma idan ya tuno abinda hakan zai haifar sai yaji hankalinsa ya tashi.

"Waye ya zuba min abu a cikin shayin nan Alhaji kaga yanda harshena har ya dade nasan ba mai min aika aikan nan sai Hindatu"?

Alhaji Salis ko kallonta baiyi ba ballantana tasa rai zai kulata ta mike a fusace tare da nufar d'akin Hindatu tana cigaba da goge bakinta.

Hindatu da bacci ya fara daukarta taji ana buga k'ofar da k'arfi firgitar da tayi yasa tayi waje da sauri tana bud'ewa Luba tace "shine zakiyi sauri ki shigo daki bayan kin zuba min magani a shayi kin dauka bazan gane ba Hindatu kifita idona wlh ba abinda Kika isa kimin daga na Shiga bandaki na fito har kin dawo kin zuba min magani mai warin fiya fiya Alhaji na kallonki sabida Yana so shima yaga ya kau dani daga rayuwarsa toh idan ma hada Kai kuka yi wlh yanda kuka gani haka zaku kyalleni"

"Idan har akacewa mutum jaki ne dabba dabiun jakin zai cigaba da yi kinyi kad'an na bata lokacina akanki har na tsaya zuba miki abu da Wanda ya Isa zanyi bake ba mai Kika tare min da har Zaki tsaya min a zuciya nayi tunanin zuba miki magani luba wlh daga miki kafa kawai nake Ina baccina dan jakanci kizo ki tasheni kice na zuba miki fiya fiya toh na zuba din kiyi abinda zakiyi"

Luba ta hau zaginta Hindatu ta fito suka hau zage zage.

Alhaji Salis tuna Aneesa na gidan zata iya jiyo su yasa ya mik'e ya nufi dakin Hindatu duk suna tsaye a bakin k'ofar suna ta balai.

Sunan Hindatu kawai ya kira ta amsa masa tana hucci yace "wuce muje mu kwanta"

"Dole kace ta wuce kuje ku kwanta mana tunda kunsan mai kuka aikata daga naje nayi fitsari kin zuba min fiya fiya dan na mutu toh wlh ba abinda zaku iya min"

Rufe k'ofar Alhaji Salis yayi bai ce mata komai ba,so yake ya kwanta kawai ya sake sabon shiri.

A ranar har ciwon ciki Luba tayi sosai dan ta hadiye yawun bakinta ko bacci bata iya yi ba zargin da tayi da fiya fiya aka zuba mata yasa tayi ta dirkar Madara tana shan maganin ciwon ciki, da haka ta samu saukin ciwon tana fatan samun lafiya tayiwa Hindatu rashin mutunci ko da wasa bata zargi Alhaji Salis ba.

Washegari Alhaji Salis na dawowa daga massallaci yayi zamansa a Palo dan so yake ya duba Aneesa da Aisha amma yasan ba lailai sun tashi ba shi kam bai samu bacci ba sabida tunani a jiya daddare yajawa Hindatu Kunne sosai akan biyewa Luba da takeyi suke daga Masa hankali suna zubar da mutuncinsu a gaban yayansa ya Kara da bai dace Aneesa taga irin rayuwar jahilan da sukeyi ba su ba Yara ba ko a kauye an daina irin wanan abun kunyar na fada akan miji ya Kuma rantse mata duk ranar da suka kara fada da Luba na cancan baki Kamar su daku sai ya saketa ya goranta mata da Kar ta manta rashin miji yasa aka nemoshi aka bashi ita Kuma daga masa hankalin da suke yasa ya Kara auren a yanzu idan sun Kara daga mai hankali sallamarsu kawai zaiyi

Hindatu tuni ta nutsu dan taga da gaske Alhaji Salis so yake ya sallame su ita Kam bata shirya zama bazawara ba ta masa alkawarin bazata sake biyewa Luba ba.

A zaunen da yake a palon Yana ta ganin shige da ficen Hindatu daga daki zuwa kitchen dan ta sallami yara su tafi makaranta.

Karfe bakwai da rabi yaran Suka fara fitowa daya bayan daya cikin Shirin tafiya makaranta sai da duk suka gaishe shi suka gaida luba kafin su nufi d'akin Aisha.

Alhaji Salis so yake dama sai sun tafi sai ya dubo Aneesa.

Sai da Hindatu ta raka yaran har bakin mota ta dawo tana k'ok'arin shiga dakinta Alhaji Salis ya dakatar da ita Yana "Ki bani abincin Aneesa na kai mata kafin ta fito ku gaisa"

Hindatu ji tayi Kamar ta sosoka masa Ashar haka taji amma tunda hanya yake nema da zai rabu da ita dole tayi biyayyar da bata shirya ba

Kitchen ta koma ta hado masa abincin a faranti ta dire masa kafin ta shige dakinta a fusace.

Alhaji Salis sai da ya bubude abincin yagani kafin ya d'auka ya nufi bangaren su Afrah.

Koda ya Shiga d'akin a kwance yaganta tayi rub da ciki tana ta sharar bacci.

Sai da ya ajiye farantin ya hura mata iska a fuska ya bud'e idonta a hankali Suka sakarwa juna murmushi ta mik'e zaune suka gaisa yace "Kinji dadin bacci bani ko ni ko baccin ban iya ba"

"Nima banyi ba sai da na iddar da Sallah asuba bacci ya d'aukeni Baby Anan zan zauna"?

"Aa anjima zaa kwaso kayanki insha Allahu yau sai ki kwana a dakinki ko bayan kwana shidda zan dawo gareki"

"Kwana shidda Alhaji ba kwana uku ba"

Ya saki murmushi yana "Eee 6 days ne kwana bibiyu ne kwanan"

Aneesa bata Kara cewa komai ba dan duk abinta bata tab'a hasaso wai wani raban kwana a tsakanin su ba lailai ta gano abinda mahaifiyarta ta gano da ita bata gane ba lokacin har a zuciyarta sai taji tana mugun kishin ma Alhaji Salis ya rabi sauran matan nasa ta d'auka tunda manya ne matan nasa ba wani rabon kwana da zaayi.

Bata karyawa da wuri amma haka Alhaji Salis yasa taci abinci ta canja kayan jikinta zuwa doguwar riga Alhaji Salis yayi gaba tana binsa abaya dan so yake ya hadata da Aisha da Hindatu tunda Luba kadai ce tasanta.

Kafin ya iso bangarensu yaji muryar Luba na tashi "Har ni Zaki sakawa fiya fiya a shayi Hindatu wlh sai nayi karar ki mai na Miki da kike so ki kasheni jiya ko bacci banyi ba sabida ciwon ciki wai ahaka ma ban sha ba da na Sha fa nasan da yanzu an fara shirye shiryen kaini"

Hindatu na zaune ko daga kanta batayi ta kalleta ba bakin ciki fal zuciyarta sai tara iska a bakinta take tana sacewa dan dauriya kawai take bata tanka Luba ba wanan doka da Alhaji Salis yasa mata na daina biyewa Luba ya cutar da ita.

Alhaji Salis farinciki da ya fito dashi yaji ya kau ya hade ransa a daidai lokacin da Aneesa ta labe a bayansa dan dagaske ta yarda tana da tabin hankali.

Ya san yanzu idan yayiwa Luba magana dizga shi zata yi a gaban Aneesa ta d'auka bai isa da gidansa ba jawo hannun Aneesa yayi daga bayansa ya rike hannunta tare da nufar wajen da Hindatu ke zaune sai da ya zauna Aneesa itama ta zauna kamar zata shige jikinsa sabida tsoron Luba da ta zubo mata ido tana mata mugun kallo.

Alhaji Salis kuwa yacewa Hindatu "Ga Aneesa nan kanwar ki Anjima za'a dawo da kayan ta wancan d'akin,ko ban fada ba kingan ta kinsan yarinya ce baza'a samu matsala da ita ba dafatan zaki d'auketa tamkar kanwarki

"Hmmm"

Kawai Hindatu tace tare da hararar Aneesa kasa kasa har ga Allah wani irin kishi ne ya rufeta da ta tsalleliyar yarinya mai jini a jiki da Alhaji Salis ya auro musu


"Aneesa ga Auntynki ku gaisa"

Aneesa ta sauko daga kujera tana "Aunty Ina kwana"

"Lafiya" Hindatu tace tare da mik'ewa ta bar palon

Ta kalli Luba da take balain tsoro tana "Aunty Ina kwana"

"Yana gidanku kwanan ni zaki zo kina wani susunkuyar da kai bayan abinda nasani kema kinsani toh wlh bakizo gidanan ki huta ba wahala da bauta kawai kika zo sabida shegen kwadayi iyayenki Suka d'auko ki Suka bawa tsoho"

Alhaji Salis rada yayi wa Aneesa a kunne akan haukarta ne ya motsa Kar ta kulata ya rike hannunta suka Mike tare da nufar d'akin Aisha

Luba kuwa ta cigaba da masifa

Da sallama suka shiga d'akin Aisha.

Aisha da ke Shirin yafa mayafi akanta ta amsa dan tana Shirin tafiya wajen Aunty mamy zasu je wani gaisuwar mutuwa,ganin Alhaji Salis da Aneesa yasa ta saki fuskarta.

Aneesa kuwa ta zube a kasa ta hau gaisheta ta amsa cikin sakin fuska tana ya bakunta ta sunkuya da kai tana Alhamdulillah

Alhaji Salis tarbar da Aisha ta mata ba karamin faranta masa yayi ba inama iya su biyune matansa duk abinan Aisha bata kalli Inda yake ba Alhaji Salis yace "Aisha ga Aneesa kanwarki nan anjima zaa kawo kayanta d'akin dake can karshe zata zauna dafatan zaki riketa da Amana"

"Ai wanan ba kanwata bace sai dai 'ya kanwarsu Luba ce tsakanin uwa da yarta ai sai mutunci da girmamawa insha Allahu diya na d'auketa sai dai na nace Allah ya kau da fitina"

Sai Alhaji Salis yaji zuciyarsa ta sosu da abinda tace wato ita bata daukeshi ma a matsayin miji ballantana tayi kishinsa.

Mayafin kanta ta kara gyarawa tana "Yata ni zanje wani gaisuwa sai na dawo"

"A dawo lafiya Aunty"

Allah yasa

Daga haka tayi waje Salis ya juya yayi bayanta Yana cewa Aneesa ta fito ta koma dakinsu Afrah.

Koda suka fito Luba na zaune a kujerar dake kallo k'ofar sai girgiza kafa take

Ba wanda ya kalli Inda take Duk da kananan maganganu da take Aisha tayi waje Alhaji Salis yabi bayanta Aneesa Kuma tayi bangaren su Afrah.

Aisha na fita wajen motarta ta nufa bata nuna ma tasan salis na bin bayanta ba sai da ta bude ta Shiga Salis ya sunkuyo ta wajen glass Yana "Aisha banji dadin maganar da Kika yiwa Aneesa ba bai dace kiringa nunawa a koina bakya kaunata ba bai dace kiringa nuna wa mutane irin zaman da muke dake ba haba Aisha"

"Salisu kenan ni ba abinda nayi idan Kuma ba rigima kake nema ba zanje Aunty mamy na jirana"

Daga haka ta rufe motar Salis yace adawo lafiya taja motar ta fice daga gidan.

A takaice Yara na dawowa suka taya Afrah gyara d'akin da Aneesa zata zauna bisa umarnin Alhaji Salis Luba kuwa kamar tayi bindiga dan duk hauka Salis da Hindatu Suka manna mata har dukan Yara tayi dan suyi magana ba Wanda yabi ta kanta har suka gama Aneesa ta koma dakinta Inda ta kudurce a ranta ta ringa zaman daki tana kulle k'ofar ta tunda akwai komai na bukata a d'akin dan karamin d'akin ajiya Salis ya maida mata shi kitchen da komai na bukata har ga Allah ba yanda zatayi ne amma bataji dadin kawota da Salis yayi cikin matansa ba a wajen Aisha kawai ta samu sakin fuska.

Luba burinta Aneesa ta Kara karbar girki ta jibga mata aikin gidan,dan tasan bata isa ta iya dafa musu abinci suci ba,Karin bakin cikinta da ranar girkinta ya zagayo har Alhaji Salis ya gama mata kwanakinta ko tab'ata baiyi ba ko da tayi magana ma manna mata hauka yayi,ita a wajenta ba bukatar ne ya dameta ba burinta idan girkinta ya zagayo ta wahalar dashi ta tara masa gajiya yanda idan ya koma d'akin koma wacce bazai iya tab'uka komai ba.

Duk burin da taci na cin uban Aneesa idan girkinta ya zagayo sai gashi Alhaji Salis yace Aneesa bazata yi girkin duk gida ba zata ringa girkinta daban tana ci su masu yaran su cigaba da yanda sukeyi,nan Luba ta daka tsalle ta dire akan ba Mai yuwa bane.

Alhaji Salis ko ta kanta bai bi ba ,tsananin tsoron Luba da Aneesa keyi yasa ko fitowa bata iya yi,kullum tana dakinta idan kuwa Alhaji Salis ya fita haka zata zo ta ringa buga mata kofa tana zaginta itama Hindatu idan kishi ya motsa mata sai ta hau taya Luba,dan tunda kuma Alhaji ya auro Aneesa yake wulakanta su a yanzu ko shakkar Luba baya yi inda Luba hankalinta ya Kara tashi tanaso taji mai ya taka a haka Aneesa ta samu wata biyu a gidan idan har ranar kwanan Aneesa ne Luba bata bacci haka zata zo tayi ta musu labbenta a garin labbenta ta jiyo wa kanta mugun tashin hankali da ya sa zuciyarta kusan bugawa a ranar ko runtsawa batayi ba Alhaji Salis na fita daga gidan ta tafi d'akin Aneesa ta hau bugu dan burinta ta bud'e kawai ta mata mugun duka

Jijjiga kofar kawai take tana

"Shegiya karuwa idan kin isa ki bud'e k'ofar nan har mu zaki zo kiringa yiwa bariki Yar mitstsiya dake"

Luba tace cikin hucci tana bubuga k'ofar dakin Aneesa da k'arfi.

Hindatu kuwa tana daga gefe tana "kefa kike ganin laifin yarinya nan wlh Alhaji shi yafi bani kunya wai ace Saar Yar cikinsa yake zuba kwartanci da ita a gida har zaa ringa Mana ihu dan a bata Mana tarbiyar Yaya na rasa uban me yagani a jikinta ma ya aurota naga idan farar ce akwai ta a gidanan idan Yar lukutar ce ma akwai a gidan nan idan ma mumunan ce ma duk ya hada"

Luba wani irin kallo ta fara bin hindatu dashi tana "wacce mumunar"?

"Oho kinji na Kira Sunanki ne"?

Luba Kan hindatu ta koma suka fara zage zage

Aisha dake yanke farcen ta ta mik'e da rezar hanunta ko kallon wajen da suke batayi ba ta shige dakinta zaman daki isarta yake wani zubin tana san zaman palon amma tashin hankali da fada da Luba da Hindatu keyi ke hanata zama sai gashi bayan tsawon lokaci da ta dan fito yau dan ta Sha iska sun fara fada.

Aneesa ..






*Mg's skincare*

Yan'uwa indai gyaranjiki kukeso inamai Kara gabatar muku da kayan mg's domin kayansu dayane tamkar dubu =??? tested nd trusted sa'annan kayansu yanagyaran jikine naturally domin bawai na bleaching bn natural/organic zaidai gyarajikine yafiddo ma mutum da ainihin kalarshi wato natural beauty dinku'

Sister nace ba pimples ne matsalan,spot(tabo), sunburn,acne, black heads, knuckles,ko Mai Kika shafa yabatamiki jiki ko fatarkine take tattarewa?
Kinasone kawai kikara gyara jikinki fatarki tayi clear tazama smooth tadinga glowing sister's kunemi kayan mg's 08062991549 insha Allah bama kuba har customers saikun kawomusu=??

Sannan fa bana tafi bara kyau domin sunkarama products dinsu ingantattun abubuwa wnd zaifito Miki da baiwar halittar da Allah yamiki Dan duk inda kikayi se anjuya=?
?inamasusan suyi haske Suma bana bleaching ba pls kuyi mgn fatarki zatai haske naturally batare da Kun lahanta fatarku ba akwai hadin amare shima bama cika Baki kicire kokwantan kinjaraba abubuwa bemiki ba kigwada kayansu zakisha mamaki bi'iznillah

Soap price:4k
Small beauty kit:12k
Flawless skin beauty kit:20k

Chat:08062991549,07046881166,07067210195

Instagram:glow_with_mgs
Facebook:mg's skincare

Team glow=??



*NI DA KISHIYOYINA*

*NA SADNAF*

*E.W.F*


*PAID BOOK*

Last free page

*Page 12*

Aneesa

Wayarta ta d'auko jikinta na rawa ta nemo lambar Alhaji Salis Yana d'auka ta fashe da kuka tana "Baby Nagaji wlh Nagaji Aunty nan so take ta kasheni gata nan sai buga k'ofar take,bby Kar ta fasa k'ofar ta shigo indai ka bar gidanan haka nake zama cikin tashin hankali nidai ka taimaka min ka dawo kazo ka fitar dani daga gidanan na gaji ban Saba da hayaniya ba"

Ta Kara rushewa da kuka har ga Allah ta fara nadamar Auren Alhaji Salis ko muryar Luba taji sai gabanta ya Fadi,ta Kuma karanci Luba boss ce a gidan ko Alhaji

11 / 38