Nida kishiyoyina complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Romance

Chapter   13 / 38

36K to 39K   out of 111.9K words

wuk'ar nan kaga ma ka yanketa"

Alhaji Salis kuwa sabida rawar da jikinsa ke yi yasa ya saki wukar Yana Jin Kamar numfashinsa ya d'auke wani irin kunya yasa yaji kamar ya nutse a kasan a yanzu da akwai yanda zaiyi ya suma da ya sume da idon Aishan da yake ji a kansa shekara sha hudu Yana cikin tsananin damuwa da fargaba kullum Addu'arsa Allah ya rufa masa sirrin nan batare da kowa ya sani ba sai gashi Luba ta bankada shi a gaban Aisha a gaban yayansa gabad'aya da yasan duk da wayon su kad'an ne basu da wayo ya zub'e akan gwiwarsa dafe da kansa Yana sallati

Luba kuwa daki ta fada tana ihun bayanta ta kadu sosai dan ta d'auka zai kasheta din ne da Ashraf bai ceceta ba tasan da yau sai Alhaji Salis ya aikata lahira.

wani sabon tashin hankali ne ya sake rufeta data tuna fa Alhaji Salis ya mata saki uku ta dora hannunta a ka sam tunaninta bai tab'a bata akan idan ta bankada sirrinsa zai saketa ba abinda sirrin nasa shine takamarta shine nata rufin asirin shine abinda ya kaita ga samu ta aure shi sai gashi tsabar rashin hankali irin nata tayi hauka abun ya dawo kanta ba'a saki Aneesa ba an dankara mata saki uku bayan ta wani irin zugi yake amma tashin hankalin da take ciki na sakin da Alhaji Salis ya mata yasa bata ji ba ta hau zirga zirga a d'akin tana cije lebbenta da cutar kanta da tayi tuna wai sakin da ya mata na nufin rabuwa dashi na har abada ta bar uban daular da take ciki yasa ta saki ihun kuka ta haka Ramin mugunta ta fada.

Jikinta na rawa ta d'auko wayarta a gaban mudubi ta hau nemon lambar Asabe a waya bata da Kuma Sama da Asabe yanzu ita kadai zata iya taimaka mata dan Sam bata shirya barin gidan Alhaji Salis ba batasan mai yasa tunanin ta bai tab'a bata zai saketa ne idan ta tona Masa asiri sai dai duk Kiran da take wa Asaben yana ringing bata d'auka ba.

Muryar Alhaji Salis kawai ke tashi a palon yana sallati


Aisha kuwa tunda Luba tace Alhaji Salis ne mahaifin Nana taji duk notikan kanta na kuncewa kalmar kuwa maimaituwa kawai yake a kanta kirjinta na daka wani irin tsalle a tsayen da take so take taji Alhaji Salis yace sharrin Luba ne bashine mahaifin Nana ba sai dai kalmar kin kasheni Luba da yace da binta da yayi da gudu akan zai kasheta yasa kafafunta kasa daukarta har sai da ta kai ga zubewa a kasa yaran sukayi kanta gabad'aya Nana itace farkon kamota tana "Ammi" duk a yaran ita kadai kece mata Ammi sauran kuwa Hajiya umma suke ce mata

Sai ta bi Nana da kallo tana hango fuskar muhasim a fuskarta muhasim dake garin bauchi a killace a daki kanta akarkace bakinta ma haka sai ta tafi tunani

"Uncle Salis dan Allah ka koya min home work dinan bangane ba wlh"

"Wasa ya miki yawa muhasim bakida aikin daya wuce Hawa lilo taya zaki gane bazan koya miki ba kije Auntynki ta koya Miki"

"Kai Abban Ashraf tona min asiri kawai kake so kayi ina zan iya wanan maths din nasu"

"Tunda ga Ashraf nan ai sai ya koya mata tunda shi yafita k'ok'ari"

"Salon ka jawo mata raini kenan tana Auntynsa"

Sai Kuma kiyi

Ya haye sama

"Wai wane irin wasan banza kukeyi haka ke namiji ce da zaki ringa ball"?

"Ashraf ne yace nazo muyi ball"

"Dalla shige ki bani guri"

Muhasim ta dib'a a guje tayi cikin gidan

Yana shigowa nace "Gaskiya Abba Ashraf ka takurawa 'yata kiri kiri ake nuna min anfi ji da Khadija kasan fa muhasim ta wajena ce"

"Ai yarinya ce akwai dan banzan Wasa Khadija ta fita nutsuwa"

Ire iren tunanin da Aisha ta tafi kenan akan muhasim da Alhaji Salis da tasan cewar tsakanin su tamkar uba da ya ne shekara biyu kawai ta bawa Ashraf wai Alhaji Salis din shi yayi wa muhasim fyade ta haifi Nana

Ta saki wani irin ihu tare da kankame Nana tana "Dan Allah kuce min karyane ba Salisu ne mahaifin Nana ba dan Allah kuce min karyane ba Salisu ne yayi wa muhasim yata fyade ba Yar yayana yarsa ce fa innalillahi wa Inna ilaihi rajiun innalillahi wa Inna ilaihi rajiun"

"Hajiya kiyi shiru dare ne dan Allah bashi bane sharrin Luba ne Kamar bakisan halinta ba"

"Hindatu ba Wanda yasan asalin Nana nace muku mahaifiyar ta rasuwa tayi na riketa sabida banaso a goranta mata Nana Yar muhasim ce Yar yayana diya ce a gareni rana daya muka wayi gari an mata fyade bakinta da kanta ya karkace tsawon shekara goma sha biyar muhasim na fama da karkace war baki da kai duk kanenta sunyi Aure Bata iya magana komai yi Mata akeyi,duk zargin Wanda ya Mata fyade ne yayi mata haka ko turen Aljannu har yau yayana bai kara samun cikakiyar lafiya ba sabida larurar ta mahaifiyar ta ma haka dan Allah kuce min karyane ba Salisu mijina ne yayi wanan aika aikar ba,
ba Salisu mijina ne ya kassara rayuwar Yar yayana ba,ba Salisu mijina ne ya Zama silar jefa yayana da matarsa cikin bakin cikin shekara da shekaru ba,
Ba Salisu mijina ne ya haikewa yarinya da bata gama mallakar hankalinta ya cutar da ita Hindatu kije ki tambaya min shi bana so na yarda shi yayi wa muhasim haka ki taimaka min Hindatu innalillahi wa Inna ilaihi rajiun"

Yarana duk suka zagayeni suna nayi shiru na duba wajen da Salis ya zub'e Yana sallati ban ganshi ba. Adaidai lokacin da Hindatu ta mik'e ta nufi bangaren yaran dan can taga Alhaji Salis ya nufa.

Aneesa da Afrah a girme ma ta girmeta ta itama ta matso kusa da yaran ta zube akan gwiwarta hawaye shabe shabe a fuskarta tana "Hajiya dan Allah Mai ke faruwa ne wacce Nana mai Alhajin yayi"?

Na kalli Nana da tunda na fara kuka take kuka wai Salisu mijina shine mahaifinta kirjina Kamar ya fashe haka nakeji jikina wani irin rawa yake na Kai hannuna gefen wuyanta na juyar da fuskarta sak irin bakin tabon wuyan Alhaji shine a wuyan Nana duk sauran yaran ba mai irin tabonsa na Kara zura Mata Ido Ina bin ko'ina na jikinta da kallo sai a yanzu na fara ganin jinin Salisu a jikinta hankalina bai tab'a kaiwa ba wani zubin idan tana tafiya sai naga kamar irin ta Afrah nakan danganta haka da jini ne gashin girarta da set din hakorinta duk irin na Salisu ne,na tuna lokacin da Luba take masifa sai ta daketa Ina jinta a daki tana shegiya mai iirn idon ubanta Ashe duk wanan zagin da take na ubanta Salis ne sai na Kara hada Wai Salisu da muhasim? muhasim fa yata ce fa?

Na tuna lokacin da yazo ya same mu a asibiti da muka Kai muhasim da na fada masa abinda ya faru yanda hankalinsa ya tashi har Yana neman kuka Yana "Wane azzalumun ne yayiwa muhasim haka yarinya karama"

A ranar a asibitin duk Muka kwana har dashi yayana ma ya fishi dauriya dan har yanda ya nuna damuwar sa akan abinda ya samu muhasim yan uwana suka yi ta yabon sa suna masa Addu'a duk matan duniya Salisu ya rasa wacce zai nema sai yar yayana wanan wane irin kwamacala ne kenan shi ne silar cutar muhasim da bakinta ya karkace sabida Kar ta tona masa asiri sai naji kirjina yayi wani irin nauyi Kar dai Salisu ne yayi wa muhasim haka iya fyade bai isa ba ya Kara da karkata mata baki da wuya

Wani irin mik'ewa nayi na Kara zub'ewa a kasa sabida rawar da jikina yake Ashraf yayo kaina da sauri da Afrah dake ta kuka "Hajiya dan Allah mu tafi d'aki ki samu nutsuwa dan Allah kibi komai a hankali"

"Nabi komai a hankali Ashraf na samu nutsuwa?
ta ya zan samu nutsuwa kasan me ke faruwa kuwa Ashraf Muhasim wai Baban ku ne ya mata ciki ta haifi Nana"?

"Abban bazai tab'a haka ba kema kinsani kila sharrine hajiya umma kibi komai a sannu dan Allah"

"Ashraf cikani samun nutsuwata shine naje ya karyata ba haka.bane Ina addua Allah yasa sharrin aka masa domin wlh wlh idan har dagaske Abban ku shi ya cutar da Yar yayana shine Kuma mahaifin Nana wlh tallahi sai inda karfina ya Kare ka sakeni Ashraf"

Nace a tsawace kirjina sai sama da kasa yake tsawan da na masa yasa ya sakeni a tangal tangal na nufi bangaren yaran Hannuna cikin na Nana.

Muryar Hindatu dake tashi a palon yasa na tsaya a bakin k'ofar tare da dafe kirjina da naji idan ba haka nayi ba zai iya fadowa

"Alhaji nidai ka fito ka fada min gaskiya taya ka Zama mahaifin Nana bayan a fadar Aunty Aisha mahaifiyarta Yar yayanta ce Alhaji da gaske kaine mahaifin Nana?dagaske zaka iya irin wanan cin amanar yarinya da tamkar 'ya take a wajen ka duk matan duniyar nan ka rasa wacce zaka haikewa sai ita yar yayar matarka fa kamin magana Alhaji"

Alhaji Salis ya bude idonsa daya kada yayi jajjur tamkar jini yace "Hindatu ko na sake karya ba abinda hakan zai haifar min sai Karin tashin hankali Hindatu a yanzu tausayina ya Kamata kuji bai Kamata ku hade min Kai ba dan girman Allah kije ki rarrashi Aisha banaso maganar nan ta fita ku rufamin asiri dan Allah dan annabi Hindatu kaddara ta afka min nine mahaifin Nana har yau bansan ya akayi hakan ta faru ba"

"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun innalillahi wa Inna ilaihi Alhaji kai ne mahaifin Nana fa kace ? Kaine ka yiwa Yar cikinka fyade? Yar yayan matar ka fa wanan wane irin kwamacala ne?wanan wane irin cin amana ne iya cin amanar auren kawar Aunty Aisha bai isheka ba sai ka kara da cutar da ita ta hanyar yiwa dan yayanta fyade Alhaji yanzu ya Nana take dasu Ashraf kenan?ya yayan Aisha zai ji idan yaji labarin Wai mijin kanwarsa ne yayi masa wanan aika aika tur Alhaji tur wlh Allah idan har zaka iya wanan kwamacalar tsaf zaka haikewa Afrah kenan dama haka kake Alhaji innalillahi wa Inna ilaihi rajiun "

"Hindatu dan Allah ki bari Kar Aisha ta jiyo ki haba Hindatu ya kema zaki juya min baya a lokacin da na tsinci kaina a tsaka mai wuya dan Allah mata ta ki rufamin asiri ki tayani bawa Aisha baki wanan sirrin ne bana so ta sani shiyasa na auri Luba wlh wlh ba dan Ina kaunar Luba ba ku yarda kaddara ya afka min ba halina bane Hindatu ni da mazinaci ne zaku sani shekara biyar banida cikakiyar nutsuwa kullum a cikin fargaba nake Luba shekara Sha biyar Tana azabtar dani akan kuskuren da nayi da nima bansan mai ya kaini ba Kuna kallo yanda Luba ke juyani tana gindaya min sharruda wlh duk wai dan Kar sirrin nan ya fita tunda abinan ya faru Hindatu dauriya nake karki zama tamkar Luba ki taimaka min wajen kwantarwa Aisha hankali wlh kunyarta nakeji kunyar yayanta nakeji wlh nasan ban kyauta ba ya zanyi da kaddara da ta gifta min sharrin shaidan ne

"Alhaji wanan ba sharrin shaidan bane san zuciya ne kawai sai kun gama tsula tsiyarku sai ku fake da kaddara da shaidan wlh Alhaji baka kyauta ba wanan kwamacalar ma da ka aikata bansan ya zan iya bawa Aunty Aisha baki ba Kai daka aikata sai kasan ya zaka shawo kanta ciwo akan ciwo ga nacin amana ga na cuta haba dan Allah ni kaga tafiyata"

"Hindatu dawo dan Allah dawo ki rufamin asiri"


Alhaji Salis yace Yana k'ok'arin bin bayanta a daidai lokacin da Aisha ta shigo ciki jikinta na wani irin kyarma Hannunta damke da na Nana

Alhaji Salis yayi sauri ya durkushe tare da saka tafin hannunsa ya rufe fuskarsa.

Hindatu tace "Aunty Aisha sai hakuri nasan kinriga da kinji komai a wanan gabar sai dai nace Allah ya kyauta kawai"

Ta fice daga d'akin

Alhaji Salis kuwa sallati kawai yake zabgawa

Aisha cikin wani irin murya tace "Mai ka yiwa muhasim bakinta ya karkace da wuyanta"?

"Aisha na rantse da Allah bani bane ba ni na karkata mata baki da wuya ba wlh ki yarda dani na yarda ni na Mata fyade amma wlh banida sa hannu a abinda ya sameta wlh Allah Aisha"

"Idan mun hadu a kotu Salisu zaka fada musu gaskiya"

Daga haka ta juya ta bar palon tana Jin jiri na dibarta kafin ta kai palonsu jiri ya kwasheta yaran suka saki ihu tare da yin kanta gabad'aya.

Ashraf da Afrah hankali a tashe suka kinkimeta sukayi daki da ita Aisha nada farinjini duk a wajen yaran sai gashi duk sun rude da kuka Nana duk muryarta yafi na kowa tashi "Ammi ki tashi dan Allah karki tafi kibarni"

Hindatu kuwa ta buga uban tagumi jikinta duk Yabi yayi sanyi tama kasa bin bayansu.

Aneesa kuwa ta ringa rusgar kuka kukan da take yasa Hindatu daka mata wani tsawa tana "dalla mallama ki rufewa mutane baki ki bar mutum yaji da abinda yake damunsa"

Aneesa tayi dakinta da gudu dan itama tsoron Hindatu take.

Alhaji Salis kuwa ji yake kamar ya Yanke jiki ya Fadi kukan yaransa dayake ji da faduwar da Aisha tayi duk akan idonsa.

Duk wanan tashin hankalin Luba ce ta jefa shi a ciki dakinta ya nufa a fusace da mugun karfi ya daki k'ofar take ta bud'u

Luba dake zarya a d'akin yana bugo k'ofar ta saka wani irin ihu tana k'ok'arin yin wajen bandaki

Alhaji Salis cikin zafin nama ya damkota da hannu biyu ya shake mata wuya babban burinsa ya ga ya kasheta inyaso sai a daureshi kawai ya huta

Kakarin da Hindatu keyi yasa Luba mik'ewa da sauri ta nufi d'akin Luba,yanda taga ya daga Luba sama Yana k'ok'arin kasheta yasa ta saki wani wawan ihu tana "KU FITO ZAIYI KISAN KAI DAN ALLAH KU FITO ZAI KASHETA GA LAIFIN KISAN KAI GA NA FYADE ASHRAF KANA INA"...........


Posting Monday to Friday zanyi gobe sabida ya fada jumaa posting din sai Kuma Monday idan Allah ya kaimu

INGANTACCEN MAGANIN SANYI TOILET INFECTION MAI WANKO DUK DATTIN MARA KOWANI IRIN SANYI NE ZAI MAGANCE SHI DAYARDAR ALLAH SHIN KINAFAMA DA RASHIN SHA AWA? RASHIN NI IMA RASHIN GAMSUWA SHIN KINYI SHEKARA DA SHEKARU KINA NEMAN HAIHUWA RIKICEWAR JINI CIWON JIKI CIWON MARA YAYIN AL ADA DUKA WANNAN MAGANIN YANA WARKARWA ME CIKI BATA SHAN MAGANIN SANYI NA 4K YAKE INA KATSINA INA AIKAWA KO INA A FADIN KASAR NAN HARDA KETARE MAZA DA MATA MAGANIN SANYI MAI GYARA MU AMALAR AURE AUNTY ZEE MOM MUJAHID
08162859027
KATSINA


Ammnur _kayan mata tazo muku da zafafan kayan matan da babu algus 09080070762

Ina uwargida da ta haihu vjay dinta ya bude tana bukatar taji ta koma budurwa gam ga ammnur Nan ta kawo muku zafafan kayan mata Ina amare masu Shirin shiga daga ciki,Ina Zawara da suke so suji Basu da bambanci da budurwa

Enjoyment doesnt stop just because you have given birth. The afterbirth package is made to take care of you postpartum sexual needs . This package includes sweetner, wetner, tightener infection afterbirth herbs and more



Sauran kaya da zaki duba a wajen su na qara niima dadi da matsi sanan akwai na tsuma jiki na mata da na amare da uwargida Wato Madame package, suna da kayan farinjini, favour da kuma mallaka


1)Euphoria 12
2)Gorontula syrup
3)Her exellency cake
4)Exclusive thumi
5)Milky sweety
6)Magic insert
7)Tightening mallaka saop
8)Tightening honey pill
9)Women 001
10)Ebony lady
11) spiced tea
12)Mallaka chicken soup
13)Tightening powder
14) wetness powder
15) favour set
16) attraction set
17) bakar mallaka
18) shu'umar mallaka
19) hatsabibiyar mallaaka
20) horney honey syrup
21) libido booster set
22) breast enlargement
23) hips enlargement


*WANAN LITTAFIN NA KUDINE BIYA 500 TA WANAN ACCT 0272061655 WEMA BANK NAFISA NUHU KO KATIN MTN KO AIRTEL TA WANAN LAYIN 08033719070 DOMIN KI MALLAKI NAKI MUTANEN NIGER KUMA KU TUNTUBI WANAN LAYIN*
*+227 96 82 89 84 DUK WACCE TA MIN SHARING NA BAR TA DA* *RABBI ZAI FIDDA MIN HAKKINA DA IZININ ALLAH DOMIN BA YAFEWA NAYI BA*


*Page 14*

Ihun Hindatu yasa Ashraf ya fito da gudu ya shige dakin luba.

Luba kuwa tuni karfin ta ya fara karewa Ashraf ya ringa ihun Alhaji Salis ya cika luba "Abba karka yi kisan kai Abba dan girman Allah ka saketa karka kasheta"

Sai da Ashraf yayi da gaske kafin Alhaji Salis ya saki Luba da ko motsi ba tayi da alama sumewa tayi.

Hindatu kuwa tayi kanta da sauri

Ashraf kuma ya rike hannun Alhaji Salis da numfashinsa ke sama da kasa yayi waje dashi basu zame ko'ina ba sai bangarensu Afrah sai da ya kai Alhaji Salis har cikin dakinsa ya saki hannunsa Alhaji Salis ya zub'e a kasa Yana jan sallati babban tashin hankalinsa yanzu Aisha tace zata fitar da maganar nan da wane ido zai kalli Yayan Aisha da ya d'auke shi tamkar dan uwa,da wane ido zai iya cigaba da kallan Aisha,ya runtse idonsa sai a lokacin ya samu hawayen dake Kona zuciyarsa suka zubo a daidai lokacin da Ashraf ya Kira sunansa ya bud'e idonsa akansa sai ya tsinci kansa da Jin wani irin kunyar Ashraf sai ya kau da kansa

"ABBA nasan bazaka tab'a aikata abinda Aunty Luba tace ba,dan Allah Abba ka fito ka fada mana gaskiya mu samu hankalin hajiya umma ya kwanta"


"Ashraf banida kowa a yanzu sai Allah sai Kai da kake babban dana nasan zaka iya taimaka min ka shawo min Kan mahaifiyar ka dan Allah Ashraf kaje ka rarrasheta banaso a daga maganar nan kowa yaji kasan yanda muke da Yayanta da kunya yaji labari ni na yiwa yarsa haka dan Allah Ashraf ku rufemin sirrin nan nawa"

"Abba kenan dagaske Kaine mahaifin Nana"?

"Nine Ashraf ban isa na tsallaka kaddarata ba"

Ashraf kasa bud'e bakinsa yayi ya Kara magana ya sunkuyar da kansa Yana tuno Aunty muhasim da yarintar su ya kasa yarda Alhaji Salis zai iya aikata haka abin ya masa wani iri taya zai iya aikata irin wanan danyen aikin tambayoyi ne fal cikinsa amma nauyi da kunyar yasa ya hadiye tambayarsa ya mik'e yayi waje.

Shine babba dole shi zaiyi k'ok'ari yaga

13 / 38