Nida kishiyoyina complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Romance

Chapter   33 / 38

96K to 99K   out of 111.9K words

gummies 2200
8 surga wanita 2500
9 khusus 3500
10 majakani 2500

Price din sari=?F?=?F?=?F?=?F?nasan kodaga haka zaku gane A &Z gidan sauki ne=???=???=???=???=???=???=???=???
Masu siyan daidai kuma bambancin kadanne

Muna garin Kano Dan neman Karin bayani Kira ko whaspp 09037870422

Karku manta muna tura Kaya duk garin dakuke inkiyi siyayyama dayawa muyi Miki free delivery =???=???=???yan Kano kayanku har kofar gida cikin aminci>??>??>??

*WANAN LITTAFIN NA KUDINE BIYA 500 TA WANAN ACCT 0272061655 WEMA BANK NAFISA NUHU KO KATIN MTN KO AIRTEL TA WANAN LAYIN 08033719070 DOMIN KI MALLAKI NAKI KI MUTANEN NIGER KUMA KU TUNTUBI WANAN LAYIN*
*+227 96 82 89 84 DUK WACCE TA MIN SHARING NA BAR TA DA* *RABBI ZAI FIDDA MIN HAKKI NA DA IZININ ALLAH DOMIN BA YAFEWA NAYI BA*


*NI DA KISHIYOYINA*

*NA SADNAF*

*PAGE 34*

"Kikace bake kika d'auke min kudi ba Habiba wanan menene"?

Habiba Kuka ta rushe dashi tana "Wlh bani na d'auke ma kudi ba bansan ya akayi kudin ya Shiga Jakata ba"

"Yanzu abinda zaki koma yi kenan Habiba kiringa sata kina d'auke d'auke kudin nan nada kafar da zai zo ya Shiga Jakarki ne? Wane irin mumunan hali Kika koyo haka ace nida gidana ban isa na ajiye abu ba sai kin d'auke?kin canja gabad'aya girkinki ba dadi komai naki ya lalace"?

"Sabitu wlh wlh ban taba d'aukar maka sule biyar ba zan iya dafa maka Qur'ani mai zanyi da kudinka inada sanaar da nake yi,tunda kake dani ka tab'a neman abinka ka rasa kwana biyu rigima kawai kake nema dani, burin ka kawai kaga kana kamani da laifi"

"Ni yanzu ki bani amsa wanan kudin ya akayi suka shigo Jakarki a gabanki dai yanzu kudin Suka Fado daga cikin Jakarki kinyi asara Habiba sata kiri kiri"

Habiba na k'ok'arin Magana ya daka mata wani irin tsawa daya sa Luba dake manne a jikin kofa ta ja da baya tana "ka saketa mana sai wani bata lokaci kake"

Tana k'ok'arin komawa jikin k'ofar waziri dan Sabitu ya shigo fuskarsa a mugun hade dan mahaifiyarsu ta rasu,daga baya sabitu ya auro Habiba ta Kuma rikesu tamkar ita ta haifesu,yana waje da abokinsa yake jin tashin muryarsu hakane yasa ya shigo,ganin Luba yasa ya hade rai dan haka kawai yaji jininsa bai d'auketa ba tunda tazo gidan.

Luba kuwa da sauri ta wayance da "Tun dazu nake Jin tashin muryarsu inaso na Shiga d'akin ne ma ka shigo"

"Bani hanya na wuce"

Yace yana Kara hade rai da sauri ta matsa ya tura k'ofar da sallama

A daidai lokacin da sabitu yake nuna Habiba da yatsa Yana "Wlh bazan d'auki wanan halin da kika tsiromin dashi ba har ki iya d'auke kudin da kika san ba nawa bane rashin kudin na iya sawa a d'aureni, kikayi mirsisi kik'a fitomin dashi toh wlh ko duniya kika haifa min sai kin koma gidan idan kin nutsu sai ki dawo"

"Abba mai ke faruwane?

"Cikin fushi Sabitu ya hau zazzaga masa bayanin kudaddensa da Habiba ke ta d'aukewa ya kara da "Wlh ba Wanda yake d'auke min kudi sai ita duk yaran nan ba mai shigowa d'akin nan dagani sai ita amma ba kunya ba tsoron Allah haka zan shigo da kudi ta kwashe gabad'aya ga kwana biyu girkin da take yi bashida Dadi sam daga ta tsullawa Miya ruwa sai dai kaji gishiri yayi yawa na rasa Ina ta koyo wanan muguwar dabia inaga sai ta koma gida zata nutsu ta shiga hankalinta"

"Haba Abba Aunty Habiba ce zata d'aukar ma kudi"? Haba Abba wlh kowani ne yace ma zata iya d'aukar ma kudi kai mai karyatawa ne shekara nawa Kuna tare bata tab'a tunanin d'aukar ma kudi ba sai yanzu"?haba Abba"

"Toh waye ya d'auke min kudin Waziri yanzu nan Ina caje Jakarta kudin suka fado,kudin suna da kafar da zasuje su shiga Jakarta ne wanan fa zahiri na kamata ba wai labari aka bani ba"

"Abba wlh Aunty Habiba bazata tab'a d'aukar ma kudi ba Allah kadai yasan yanda kudin ya shiga Jakarta"

"Nidai ka zama shaida wlh daga yau na kara neman abu na rasa sai ta koma gidansu dan bazan iya zama da barauniya ba"

Daga haka sabitu ya fice daga d'akin Yana kunkuni ji yayi ma Habiba duk ta fice masa a rai.

Waziri kuwa hakuri ya hau bawa Habiba dake ta rusa uban kuka dan har ga Allah taji ciwon abinda sabitu ya mata a iya saninta kwandalarsa bata taba d'auka ba har yanzu tana ta mamakin yanda akayi kudin yaje cikin jakarta dagaske bata bari Yara su shiga d'akin.

Ita kadai ke Shiga d'akin ta gyara ta kulle sai idan ya dawo ma take bud'e k'ofar.
Dan Sabitu Sam bayaso ma ana shigar musu d'aki Koda kuwa Yara ne.


Dakyar waziri ya kara bata baki Yana "Amma abinan da daure kai yake Aunty Habiba ki kara saka ido ko akwai Wanda yake shigowa d'akin"

"Waziri Abban ku hanya kawai yake nema da zamu rabu wlh ba mai shiga d'akin dan kulle k'ofar nake da kaina idan zanje makaranta sai ya dawo ma nake bud'e k'ofar zancen abinci Kuma Kun san yanda girkina yake haka kawai ya tsiromin da tsirfan Ina tsulla gishiri da ruwa idan rabuwa yake so yayi dani ai ba sai ya biyo ta haka ba gwara ya sauwake min sai na tafi da wanan cin mutunci da wulakancin da yake min"

"Kiyi Hakuri Aunty Habiba nidai Ina zargin Kamar ana shigowa d'akin ki dai kara saka ido"

Habiba bata ce komai ba ya Kara bata Hakuri har yazo fitowa ya dawo baya Yana "Naga mukullin d'akin Nan"

Habiba mik'ewa tayi ta jawo drawer ta d'auko mukullin ta mik'a masa ganin guda uku ne yasa ya cire daya ya maida mata ta karba batare da ta tambayeshi dalilin dayasa ya cire mukullin ba.

Yana bude k'ofa Luba ta ja da baya da sauri tana "Ai najiku shirune shine nace bari naji ko lafiya"

Wani mugun kallo ya watsa mata ya fice Yana Jin sam bai yarda da ita ba daga yanda take kame kame ma bayajin tana da gaskiya dan haka dole yasa ido ya gano mai shiga d'akin,duk abubuwa basu fara faruwa ba sai da tazo gidan.

Luba kuwa Palo ta koma ta zauna kamar ta fashe dan bakin ciki duk wanan uban wahalar da take sha dan ta hada Sabitu da Habiba,sabitu yak'i sakin Habiba sam ba haka taso ba,dan ta d'auka a yau sai ya sallami Habiba sai gashi bai saketa ba,ba kalar makircin da gwara kansu da batayi dan su ringa fada da juna ba,tunda har Habiba ta sokata a gaba da gori dole itama aurenta ya mutu ta danna zawarci taji.

Tana zaune taga Habiban ta fito bata ko kalli wajen da take ba ta fara k'ok'arin shiga kitchen tayi sauri ta mik'e tana "Ni Wai Aunty Habiba mai ya hadaki da mijinki ne haka tunda zu naji Yana waya Yana kin Masa sata ke barauniya ce ya gaji da Zama dake bakiga kalar zagin da naji Yana miki ba har sai da na kasa daurewa na masa magana akan bai dace ba ko me kika masa bai dace ya tona miki asiri ba"


Habiba duk yanda taso danne hawaye da kukan dake neman kwace mata kasawa tayi har sai da kukan ya kwace mata, Sam bataso ma Luba tasan halin da suke ciki ba,taya sabitu zai Kira a waya ya ringa ce mata barauniya abinda tasan bata aikata shi ba.

A ranar bata iya ma girki ba sai da yaran suka dawo Aliyah yarta ta dafa musu taliya zuciyarta fal take da bakin ciki abinda sabitu ya mata.

Koda ya dawo yanda ya hade rai haka ta hade ranta, bakin cikin abinda Luba ta fada mata ya aikata yasa yana shiga d'akin ta bi bayansa cikin kuka ta hau magana tana "Sabitu yanzu nice na zama abar wulakantawar ka yanzu har ka fita waje kana waya akan ni barauniya ce ka gaji da Zama dani ka ringa zagina yanzu Koda halina ne bazaka iya rufamin asiri ba kenan"?har a gaban kanwata ka ringa zagina sabitu kenan bazamu iya fadan mu mu biyu batare da kowa yasani ba"?

"A Ina nayi waya na zageki har na ce ke barauniya ce kanwarki Kuma ba dole tasan abinda Kika aikata ba tunda tana zaune a gidan idan har kinsan kina Jin kunyar wani yasan satar da kike min ai sai ki daina tunda kince ma nace miki barauniya na zageki nayi ki dau mataki ko ki zuciya ki daina satar"

Yaja tsaki ya juya mata baya tare da rufe kansa da bargo.

Habiba kuwa haka ta tsaya tana kallonsa tana danne kukan dake neman kwace mata tariga tasan Sabitu hanya kawai yake nema da zai rabu da ita,
karo na farko da suka raba shimfida dan bargo ta shimfida a kasa ta kwanta tana kukan bakin ciki Sabitu kuwa ya mik'e ya d'auko wandonsa ya tattara kudadensa yayi pilo dasu Yana kafin bacci ya kwasheni a d'auke min kudin.
Habiba a ranar sai bacci barawone ya saceta

Tayi mamkin yanda ya daura damarar fushi da ita dan har abincinta ya daina ci tun tana basarwa har tazo abin na damunta.

Yanda yake kafa kafa da kome ya shigo dashi yafi matukar Kona mata rai tana mugun takaicin irin zaman da suke yi duk yanda ta Kai da tayi zuciya sai ta kasa har sai da ta bashi hakuri,a takaice daga ranar suka kara shiryawa Habiba ta ringa kafa kafa da da duk abinda yazo dashi wai dan Kar ma ya nemi wani abu ya rasa.



ASHRAF

"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun wanan ai Asabe ce kawar Luba Ashraf wai ya kake so ka saka zuciyata ta buga ne"

Cewar Aisha tana kara kallon hoton Asabe da ta karba a hannun Ashraf da yasa muhasim mik'ewa

Ashraf komawa yayi ya tsugunna a gaban muhasim Yana "Aunty muhasim ki kwantar da hankalinki kinji ba abinda zasu iya miki wanan ce ta miki haka"?

Ya Kara karbe hoton daga hannun Aisha dake ta kwada sallati dan a yanzu a rude take mai Kuma ya hada luba da muhasim,mai ya hada Asabe da muhasim kanta ya kulle,ta d'auka hoton Salis muhasim zata gani ta firgice haka,sai gashi hoton Luba da Asabe ne ya firgita ta mai hakan ke nufi"

Jiki na rawa ta tsugunna a gaban muhasim da har lokacin idonta ke kulle jikinta na rawa

Ta ruko hannunta tana "Muhasim ki bud'e idonki na kasa ganewa Salis ne ya Miki fyade taya kuma Asabe ko Luba zasu karkata miki wuya bayan nasan kafin larurar nan ta Sameki a gidana kawai kike haduwa da Luba ki bud'e idonki kiyi min alama nagane dan na kasa gane mai hakan ke nufi"

"Muhasim a hankali ta bud'e idonta da suka kada sukayi ja hawaye na gudu a fuskarta Ashraf ya Kara d'auko hoton Luba Yana "Wanan ce ta miki haka"?

Tsurawa hoton ido tayi har lokacin jikinta na rawa Ashraf cikin dan mamaki ya d'auko hoton Asabe Yana "Ko wanan ce"?

"Nan ma bata lumshe idonta ba illa kallon hoton kawai da take"

Ashraf a hankali ya kalli Aisha yana "Kaina ya kulle hajiya umma duk tambayar da nake mata tana min alama da ido Amma hoton Luba da Asabe banga tana motsi ba"

Ashraf sake gwada Mata mugani dama nace maka Mahaifinku ne yayi mata haka sabida rufin asirinsa"

Hoton Luba Ashraf ya Kara daukowa ya mik'e tsaye Yana kallon muhasim da ta zura masa Ido ya haska mata hoton ya dora hannunsa a wuyansa Yana "Aunty muhasim wanan ce ta karkata miki wuya da baki"?

A hankali ta lumshe Idonta hawaye na gudu a fuskarta.

Aisha ta mik'e da sallati tana "yanzu Luba ce ta miki haka"?

Luba ce ta karkata miki baki sabida karki samu bakin magana mai kika mata?Mai kika tare mata Mai hadinki da ita da zata Miki haka?dama duk tsawon shekarun nan da aka d'auka ana binciken wayanda Suka aikata miki wanan zaluncin Luba ce ta karkata miki wuya ta aure min miji tana baje mulkinta wlh sai na kashe Luba da hannuna sai ta fadamin dalilin daya sa ta miki haka mai hadinki da ita a baya duk abinda tamin nayi hakuri amma wanan karon wlh sai naga bayanta"

Aisha ta karashe tana Mai na mata a rayuwa dana cancanci haka daga wajenta"?mai nayi mata iya sanina ban tab'a mata komai dana cancanci zalin cin nan daga wajenta ba"

"Hajiya umma ki kwantar da hankalin ki yanzu ai asirinta ya tonu duk Inda ta Shiga a garin nan Zan saka a kamota ni nasan duk Abubuwan nan dake faruwa wlh da sa hannunta karki yi mamaki duk sabida Abba ya aureta tayi haka tunda tasan Abba baya kaunarta kema a baya da bakin ki kin fada Mana irin tsanar da Abba ya Mata,ta rasa ta hanyar da zata bi ya saurareta shine ta hada Abubuwan da ta hada ni nasan laifinta yafi na Abba yawa amma bazan saurin yanke hukunci ba sai tazo hannu"

"Ashraf a yau ba gobe ba idan har Luba tana garin nan inaso a kamota wlh sai ta Kare rayuwarta a gidan yari"

"Ba ita kadai ba ai har da kawarta Asabe nasan bakinsu daya a yanzu ma sai na nemo Asaben zanyi wa wani abokina a Nemo duk Inda Luba ta Shiga a kamota"

Aisha a ranar bata iya runtsawa ba sabida tunani Wai Luba ce ta karkatawa muhasim wuya a hankali ta ringa komawa baya tana tuno abubuwa har lokacin tunanin ta ya kasa bata abinda Muhasim ta Mata da zata karkata mata baki,jikinta ba karamin sanyi yayi ba da zargin salis da ta ringayi a yanzu sai taji zuciyarta na rayya Mata Luba nada hannu ma a fyaden da Salis yayi wa muhasim.


Gidan Habiba

Sabitu tun Yana kafa kafa da kudinsa har ya dawo ya cigaba da ajiye kudinsa dan a yanzu yaga kamar Habiban ta nutsu kwana biyu girkinta lafiya Lau ba komai ba Kuma ta masa d'auke d'auke ya kaddara a ransa kila bukatu yasa tayi abinda tayi a baya.

Habiba kuwa sosai ta ringa saka ido dan taga ko akwai mai shigar mata d'aki duk itama tasan ba mai shiga tunda kullewa take.

A yanzu idan akwai wacce ta ji ta takurata ta hanata sakat bai wuce Luba da ta lura tana saka mata ido ba ta rasa yanda zata saka ta bar gidan,dan a gaban sabitu har wani biyaya take mata ko a gida da ta fadawa mahaifinsu Luba na gidanta fada ya rufeta dashi yana ta koreta kafin tazo tana dana sani,duk wulakanci da take mata duk da har kasan zuciyarta baa san ranta take mata haka ba Luba bata gani haka ta cigaba da zama"

Luba kuwa duk wata hanya da tabi dan ta kara hada Kan sabitu da Habiba ta kasa samu,dan a yanzu damar da take dashi a baya bata dashi a yanzu wanan tsinannen dan sabitu Waziri nan ba karamin ido ya saka Mata ba a lokacin da take so ta aiwatar da kudurinta idan Habiban ta tafi islamiya a lokacin yake shigowa palon ya zauna.

Ko a yanzu juyi kawai take a shegen katifar da ta samu aka bata take kwana akai,a laben da tayi taji sabitu na maganar ta ajiye masa kudi jibi zai karba zaiyi tafiya mai gidansa ya aike shi.

Yanda zata samu ta Shiga d'akin kawai take tunani,har washegari sabitu ya bar gidan,Yara suka watse wajen Sha daya Habiba ta shirya ta tafi islamiya.

A Palo ta zauna da b'oyayyen mukulinta da take bud'e d'akin Tana ta Addu'a Allah yasa Kar wazirin ya shigo.

Ganin an tafi minti Ashirin bata ji motsin sa ba yasa ta leka tsakar gida da waje taga babu shi babu alamarsa.

Cikin tsananin farinciki ta rufe gate din gidan ta koma ciki ta nufi wajen d'akin Habiban ta bud'e da mukullin hanunta ta shige tana "insha Allahu ayau sai aurenki ya mutu ba dai ni kike wulakanta wa ba"?

Ta hau birkita d'akin tana neman wajen da ake ajiye kudin.

Waziri dake b'oye a bayan fulawowi a hankali ya shiga gidan cikin sand'a motsin Luba dayaji a d'akin Habiba yasa ya nufi k'ofar ya saka mukuli ya kulle ta waje ya bar mukullin a ciki.

Ya fito waje ya fara Kiran Habiba a waya Yana ta dawo gidan yanzu barawo ya shigo gidan.

Ya katse wayar ya kira sabitu shima a waya ya fada masa ya katse wayar tare da komawa palon Yana yau dubunki ta cika"

Kusan lokaci guda Habiba da sabitu suka iso gidan hankalinsu a tashe har suna hada baki wajen tambayar Ina barawon yake.

Waziri mik'ewa yayi ya nufi dakin Habiban ya murza key din tare da bud'ewa Suka shige gabad'aya Luba dake saman drawer dare dare ta saki ihu tana ta Shiga uku...........



Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne, knuckles,wrinkles,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using sabulun mg's batare da kunbukaci wani Mai b>?? Mai bukata should
Chat=?G?
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391

Team glow>???
@&?



Ayiri yiri =???=???=???=???=???kuna Ina mata matafa nake nufi bamuna mataba =??=??A&Z COLLECTION takawomuku ingantatun supplement=?G?=?G?=?G?=?G?
Muna da supplement na Infection
Munada da supplement na gyaran jiki Wanda zaisa jikinki yayi kyau fata tai laushi da sheki >?p?>?p?>?p?munada na gyaran breast succiko su tashi tsaf gwanin Sha awa>?p?>?p? munada na matsi dazai matsaki ciki dawaje bawai ki iya farkoba kuma yasaukarmiki da ni ima
Muna da na gyaran gashi Wanda zaifitomiki da gashi =?
?=?
?
Dawanda zakiyi haske duka jikinki bawai fari na bleaching ba =??=??

A&Z dealer ce kayanmu suna da sauki sosai price dinmu price din sari ne zaki samu kayanmu cikin sauki alhmdulillah=???=???=???=???
Ga kadan daga ciki

1 Royal jelly karami 2500
2 Juliet Eve 8500
3 Amirna 8k
4 Vitamin c 2500,2300
5 vt e 2k
6 collogen + glutathione 2k
7 whitening gummies 2200
8 surga wanita 2500
9 khusus 3500
10 majakani 2500

Price din sari=?F?=?F?=?F?=?F?nasan kodaga haka zaku gane

33 / 38