Nida kishiyoyina complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Romance

Chapter   23 / 38

66K to 69K   out of 111.9K words

bazan zauna a gidanan ba sai ya kaini Inda zai ajiye ni shikenan mutum bazai yi kuskure a yafe masa ba idan ma banda kaddara ma wlh ko labarin sakin nawa ba mai ji kike wani tada jijjiyoyin wuya da kudina karki dauka a wulakance nake ko a yanzu kudin nawa Suka dawo hannuna ko da kudinki kema.kinsan baki isa kizo wajen da nake ba"


"Yayi kyau matar mai kudi kinsan kina da kudinki uban me Kika zo nema a gidan namu ai yanzu ki burgeni kije ki nemi gidan da zaki zauna din sanan duk cika baki kike ki bari Abban ya dawo ya Sameki a gidanan kiga yanda zaki kwashe dashi,ba dai ba abinda Kika sani sama da cin amana da wulakanta mutum ba insha Allahu sai Kinga yanda karshen ki zai yi duk wani mugun Abubuwan ki da kike yi a boye duk nasani kallon ki kawai nake domin shi sharri dan aike ne Allah ya baki dama duk kin tsulla tsiyar ki a yanzu lokacin da zaki girbi abinda kika shuka ne"


"Ai insha Allahu kuwa bazaki ga karsshena ba sai dai ni naga karshen ki mugun halin ki yasa bakya cigaba kina nan shekara da shekaru kina fama"


Mik'ewa Habiba tayi da sauri tayi kan luba,Inna ta mik'e da sauri ta tareta tana bata hakuri.

Luba kuwa taja tsaki ta shige daki ta tub'e kayan jikin ta ta jawo soso da sabulun inna dake kasan gado ta fito da daurin kirji sai da ta cika katon bokiti da ruwa ta shige bandaki.

Sai da ta kusa karar da duka sabulun a jikinta dan har yanzu tana Jin warin jikin gambo a jikinta tana Jin Inna da Habiban suna ta magana idan ba kaddara ba mai zai ma kawota har da Habiba zata samu damar mata maganganun banza.


Alwala ta daura ta fito,dan bata yi ma sallah asuba ba gashi ta fara Jin Kiran sallah azahar,kayan ta ta Kara wankewa ta shanya dan bata da kayan sawa dole su zata maimaita dan kayan inna bazasu tab'a shigar ta ba dan tafi Inna kib'a.

Salis ya cuceta da ya hanata d'aukar komai har wayata bai bari ta d'auka ba,bata tab'a zaton zai iya mata rashin mutunci da ya kai haka ba yau da ko iya kayanta ya bari ta kwashe dan kunnenta da sarka kawai sun isheta ga kayanta da duk masu tsada ne wa ma zai yarda motocin ta sun Kai biyu taya ta gama dandana irin wanan daular shekara da shekaru a cikin Rana daya ta zama abin tausayi har da kwana shagon da ko mai gadin gidan Salis bazai iya kwana a d'akin ba ta karfin tuwo sai ta komawa Salis idan bata koma ba gwara ya zauna shi kadai dadin abin Ba Asabe kadai tasan hanyar wajen mallamin ba itama zata iya zuwa duk da Rabin zuwan Asabe ke zuwa, bama tabin ta Kan mallaman sosai Asabe ke mata sintirn zuwa tana cazarta kudade masu yawa

Sai da ta iddar da Sallah ta fito daga d'akin fuskarta a hade tayi hanyar Kitchen dan wani irin yunwa take ji rabon ta da abinci mai kyau tun a gidan Salis.

Tana Jin Inna na ta fito mata daga kitchen

Tukunyar dake kan gawayin ta bud'e.


Tuwo ne da miyar kuka da alama na jiyane aka dumama sauko da tukunyar tayi gabad'aya ta zauna a kitchen din ta fara ci hawaye na taruwa a idonta rabon da taci wai abinci ma ba nama har ta manta ta Kuma Saba din idan abinci akayi ba nama bata iya ci .

Sai da ta Kai hannu taji babu komai ta cire hanunta daga tukunyar ta wanke hannunta ta fito daga Kitchen din.

Da alama Habiba ta tafi dan bata ganta ba Inna kawai ce a tsakar gidan ta hade rai tamkar yanda itama ta hade ran.

A d'akin Inna tayi zaman ta har sai da kayan ta suka bushe ta debo su daga Kan igiya ta saka kayan ta fito wajen Inna tana "Inna zanje wajen Asabe akwai kudadena da yawa a wajenta idan ta bani zan siyi karamin gida nayi zawarcina kawai dan nima nasan na girma da dawowa gida nayi zawarci banda Salis ya hanani d'aukar komai iya zobuna na da sarkokina sun isa na siyi gida har na juya sauran kudina nima Zan fi sakewa ingani a gidana ni kadai idan Kuma Allah ya taimakeni na koma dakina shikenan idan Kuma Asabe ta hanani kudina dole na dawo kuyi hakuri balle ma nasan dole ta bani kudina dan har station sai munje a Kan kudin nan.


"Ba zancen dole sai kin dawo bane muyi hakuri ni dama banida matsala Mahaifin ku ne dai yace bazaki dawo ba Kuma da kina da hankalin Kamata yayi kiyita bibiyarsa kina neman yafiyarsa har sai ya sauko amma dayake bakida hankali yanda zaki siyi gidan da zaki zauna kike nema wato munyi kadan ma ki bimu ki bamu hakuri,ni uwa ce bana so nayi munanan kalma a kanki sai dai nace Allah ya ganar dake gaskiya dan idonki ya riga da ya rufe"

"Inna wane irin hakurine ban bawa Abba ba jiya naga har kuka na ringa masa haka ya rufe ido ya koreni dan kawai ya ga na zama bazawara a lokacin da nake da kudina da mutuncina ai Bai min haka ba"

"A inda na Kara sanin bakida hankali kenan a lokacin da kike da kudin wa Kika bawa Mai Kika tab'a masa nuna min wani abu a gidanan da zaki ce ke kika kawo Kinga zo ki tafi bana san hayaniya lubabatu.

Luba waje tayi tana Jin wani sabon b'acin rai sabida kawai bata zo da nauyinta ba suke mata haka.

Tana fita titi ta samu abun hawa ta shige tare da fada masa Inda zai Kai ta dan ta d'auko dubu uku a cikin jakar Inna a yau ko ita ko Asabe.


Tafiyar minti goma ya karaso da ita gidan Asaben ta bawa mai machine din kudinsa ta fara kwankwasa gate din gidan Asabe bata san halinta bane a yau sai ta tara mata jama'a ta bata kudinta.

Bugun da take da k'arfi yasa mai gadi yazo ya bud'e k'ofar Yana ganinta ya fara k'ok'arin Mai da k'ofar ta kuwa hankada shi da karfinta tayi cikin gidan dan tasan karnukan suna cikin kejin su.


"Da gudu tayi cikin gidan mai gadi na binta a guje Yana tazo ta fita hajiya tace idan tazo Kar a bar ta ta shigo.

A kusan tare suka shiga palon ta kame kugunta dan ko ita ko Asabe.

Asaben dake Kan dining tana waya ta juyo tana kallon Mai gadi dake k'ok'arin fita da Luba katse wayar tayi ta mik'e tana "Jeka abin ka idan zata min hauka zan kiraka kazo min da karnukan"

Juyawa yayi ya fice
Asabe ta nufo wajen da take tsaye tana murmushi da kofin tangaran a hannunta.

Luba ido kawai ta zuba mata tana kallon yanda take walwali a cikin less dinta da ta siya da tsada ko sawa bata tab'a yi ba ta neme shi sama ko kasa ta rasa ashe Asabe ce ta d'auke Mata.

"Bazawara lafiya mai kike nema a gidana ko kin zo ki kwace min mijine tunda aurenki ya mutu"?

"Asabe wanan ba less dina ne a jikinki ba"?

kallon jikinta tayi ta dago da murmushi tana "Idan less din naki ne zaki iya kwata ne"?

"Asabe dama wai haka kike duk tsawon lokacin nan da na daukeki kawa aminiya Yar uwa Ashe fuska biyu ne dake,ki rasa wacce zaki wulakanta sai ni yau duk abinda kike takama dashi Asabe naga nawane baki tab'a tambaya ta abu na hanaki ba sai dan yanzu Aurena ya mutu nace zan zauna a gidanki zuwa wani dan lokaci kafin na samu na yi aiki akan Salis ya maidani gidana Kika fititike kika koreni har da rakiyar karnuka Asabe na cancanci haka daga wajen ki"?


"Luba nayi abinda zanyi ki dauki mataki a kaina har me kika min da zaki zo kina min ihu a ka gidana ne nace bazan bari ki zauna a gidana kimin kwacen miji kamar yanda Kika kwacewa kawarki ba ni ta daban ce da bazaki kwace min miji ba?halinki ne bansani ba ayi miki saki uku dan ke dakikiya ce kice zaki koma na bari ki zauna a gidana kafin na ankara nida mijina tsalle tsalle ne dashi ya hango wanan hancin naki daya cike miki fuska ya auro ki Luba na koreki bazaki zauna min a gida ba na sake fada a yanzu ma ki fitar min daga gida"

"Bani kudina kafin na fitar miki daga gida ai bakida ma gidan da zanzo kudina dake wajenki zaki bani"

Wani irin dariya Asabe ta kece dashi ta ajiye kofin hannun ta a center table ta mike tana "wane kudinki ne a wajena wane kudi kike magana"?

"Miliyan biyar da na baki ajiya da Dubu dari shidda da kikace mu hada muyi sarin Kaya su nake magana ki bani kudina na bar miki gidanki"


"Baki da kudi a wajena luba kudin ki anyi order Kaya Kaya Kuma basu iso ba ba dole na miki Kika kawo min kudinki ba dan haka bazaki zo ki daga min hankali ba"

Wani irin cakuma Luba ta kaiwa Asabe tana "Idan kin isa Allah ya tsine min albarka wlh wlh sai kin biyani kudina biyar dita bazata yi ciwon Kai ba kinji ma na rantse miki wlh idan ta kama har police station sai munje kin biyani kudina"

"Ki cikani Luba"

"Bazan cika ki ba sai kin bani kudina wlh mai ma nake batawa kaina lokaci ai nasan hanyar dakin ki wlh sai na birkita na dauko kudina barauniyar banza barauniyar wofi"


Ta saki Asabe ta fara k'ok'arin yin hanyar dakin Asabe

Asabe tace "Luba sirrinki kaf a tafin hannuna yake a yau ba sai gobe ba a yanzu gidansu Salisu zanje wlh duk sai na tona miki asiri kinsan Kuma Mai hakan ke nufi Kare rayuwarki zakiyi a kurkuku dan nasan ba abinda zai Hana shi daure ki kinsan Kuma nasan daya sirrin naki da idan na fada ba iya Salis ba idan duniya suka San abinda kika aikata kenan ko fitowa bazaka iya yi ba"


Luba a hankali ta juyo ta dawo da baya jikinta na d'aukar wani irin rawa kirjinta Kamar ya fado ido ta zubawa Asabe hawaye na wanke mata fuska

Asabe ta saki murmushi ta koma ta zauna tana "Duk wata kiringa kawo min Dubu hamsin a duk ranar da kika tsallake baki.kawo ba a ranar zan bankada sirrinki"

"Asabe mai na miki dana cancanci haka daga wajenki?Asabe ki cinye min kudina iya haka bai ishe ki ba sai kince na ringa kawo miki Dubu hamsin hamsin a Ina Zan samo dubu hamsin idan dan kudina Yana wajenki Kika b'ullo min ta haka Zan hakura da kudin Allah ya saka min zaki biyani acan lahira dan ba yafe miki nayi ba"

"Daga baya kenan na cinye kudi Luba yanzu kudi zaki ringa biyana na rufin asirin ki"

"Asabe mai na miki dana cancanci haka daga wajenki Asabe duk wani kudi da nake takama Ina dashi Yana wajen ki, duk sauran kudina suna banki Salisu ya hanani wayata ya kulle min acct jiya a shagon Almajiri na kwana biyar bani dashi Asabe Ina cikin irin wanan tashin hankalin zaki bullomin da maganar tonan asirina ko kudi"


"Zabi ya rage naki Luba ko kudi ko rufin asirin ki"

Kuka.luba ta fashe dashi tana " a Ina zan samo Miki kudi Asabe"

"Ba abinda ya shafeni ko kudi ko fallasar sirrinki idan ba kudi Kuma azo a ringa min aiki na kori Yar aikina ki maye gurbin ta kafin mijina ya dawo duk kin gama aikin ki sai ki tafi"


"Ke zanzo na ringa yiwa aiki Asabe"?ni Luba zanzo na ringa miki aiki sabida kawai kin san sirrina zaki tona min asiri ki rasa wulakancin da zakimin sai na zuwa na ringa Miki aiki"?

"Aiki ko Dubu hamsin sai ki zab'a"?


Asabe ta mik'e tayi hanyar waje tana kwalawa Mai gadi Kira.



Aisha


A gefen gadon Yaya mustapha ya zauna tare da dafe kans shiru ne ya ratsa d'akin sai da aka kwashi tsawon mintuna Yaya mustapha ya dago da jajjayen idonsa ya fara magana yana "Har yanzu na kasa yarda Salisu mijinki zai iya aikata irin wanan danyen aikin Aisha,na kasa yarda zai iya haikewa diyata da ta kasance ya a wajenki"?

Na kasa yarda zai iya irin wnan cin amanar?na kasa yarda shi yayiwa muhasim Fyade ya karkata mata wuya"?

Aisha karki.manta irin Fadi tashin da ya ringayi a lokacin da muka gano muhasim anyi mata fyade Aisha ko da zai yiwa kowa haka ban cancanci ni yamin haka ba dan.na d'auke shi tamkar kanina,shekara Sha biyar muhasim tana fama da wuya a karkace nine can nine Nan a nemowa muhasim magani,tunda muhasim ta Shiga halin nan nayi bankwana da duk wani farinciki ke kanki shaida ce a irin wuyan neman maganin da nake duk Rabin kudina a nemawa yata magani Aisha ace duk abinan mijinki Salisu shi ya jefa mu a cikin wnan halin"?

Yaya mustapha ya karashe cikin wani irin murya da ji kukan zuci yake

Duk maganar nan da yake Aisha kuka kawai take.

Sai da ya idda ta dago tana "Yaya shi yasa nace ma sai na yi kararsa wlh sai na kwatowa Muhasim hakkin ta ya cutar damu ya cutar da Muhasim zaluncin yayi yawa Yaya wlh sai nayi kararsa sai na tona masa asiri duniya tasan wanene shi"

"Aisha kiyi kararsa ko ki tona masa asiri bazai canja abinda ya riga da ya faru ba,yau badan ke ba nida kaina sai nayi kararsa bazan yi haka ba dan ba iya sunansa ne zai b'aci ba har da naki tunda kinriga da kin hada zuria dashi bazan yarda kiyi kararsa ba abu daya kawai zaki min shine ki ce ya fada miki abinda yayi wa muhasim wuyanta ya karkace burina yata ta dawo daidai idan ya fada miki shikenan banida matsala dashi........


Ammnur _kayan mata tazo muku da zafafan kayan matan da babu algus 09080070762

Ina uwargida da ta haihu vjay dinta ya bude tana bukatar taji ta koma budurwa gam ga ammnur Nan ta kawo muku zafafan kayan mata Ina amare masu Shirin shiga daga ciki,Ina Zawara da suke so suji Basu da bambanci da budurwa

Enjoyment doesnt stop just because you have given birth. The afterbirth package is made to take care of you postpartum sexual needs . This package includes sweetner, wetner, tightener infection afterbirth herbs and more

Prices




Sauran kaya da zaki duba a wajen su na qara niima dadi da matsi sanan akwai na tsuma jiki na mata da na amare da uwargida Wato Madame package, suna da kayan farinjini, favour da kuma mallaka




1)Euphoria 12
2)Gorontula syrup
3)Her exellency cake
4)Exclusive thumi
5)Milky sweety
6)Magic insert
7)Tightening mallaka saop
8)Tightening honey pill
9)Women 001
10)Ebony lady
11) spiced tea
12)Mallaka chicken soup
13)Tightening powder
14) wetness powder
15) favour set
16) attraction set
17) bakar mallaka
18) shu'umar mallaka
19) hatsabibiyar mallaaka
20) horney honey syrup
21) libido booster set
22) breast enlargement
23) hips enlargement




*HUMKAM INCENSE* gidan kamshi da maganin mata muna turaren wuta na tsuguno Wanda yake matse HQ sosai Yana karawa dandano Yana maganin infection kowani iri muna da shuumar humra, hatsabibiyar turare,bita zaizai Mai abin mamaki munada turauka na daukar hankali
*08132506044*
TILL WE MEET*
*ZARATY* WANNAN HMMMM YA HADU NACE YA HADU SHIN KINTAVA AMFANI DA TURAREN DA ZAISA MIKI LAUSHIN FATA? KINIMI ZARATY YANA DA KAMSHI DA RIKE JIKI YANASA FATA LAUSHI TURAREN KOWA
*Jas oud* 3 IN 1 ZAKI TURARA GIDAN KI DASHI JIKINKI DA KAYANKI JAS OUD YA HADA ABUBUWA DA DAMA YANA RIKE JIKI SOSAI YANS KAMA GIDA YANA RIKE KAYA
*AKWAI HUMRAR MOWA GUMBAR MOWA GARIN MOWAR TSUMIN MOWA DAN MATSI*
*SHU'UMAR HUMRA NA MANYAN MATA MATAN DA SUKA SAN KANSU SIRRINKI A SHIFIDAR DAKIN MAIGIDAN KI MUNADA SHUUMAR TSUMI*
*DESIRE MAINE DA YAKE SAKA JIKI DA GASHI KAMSHI SOSAI IDAN KINA BUKATAR GANIN PHOTON KAYANA KIMIN MAGANA NGD
*AKWAI SABON TURARE ME MATUKAR MUHIMMANCI ACE DUK WATA MATAN AURE DA TAKE DA HALI TA MALLE KESHI (NI DA MIJINA) SHINE SUNAN SA,SAI MOWAR MACE TURARENWUTA NA TSUGUNO YANA MATSE JIKIN MACE YANA MAGANIN INFECTION YANA DAUKE WARIN GABA YANASA KIJI CIKIN JIKINKI YA MATSE SOSAI YANASA KAMSHIN HQ*


*WANAN LITTAFIN NA KUDINE BIYA 500 TA WANAN ACCT 0272061655 WEMA BANK NAFISA NUHU KO KATIN MTN KO AIRTEL TA WANAN LAYIN 08033719070 DOMIN KI MALLAKI NAKI KI MUTANEN NIGER KUMA KU TUNTUBI WANAN LAYIN*
*+227 96 82 89 84 DUK WACCE TA MIN SHARING NA BAR TA DA* *RABBI ZAI FIDDA MIN HAKKI NA DA IZININ ALLAH DOMIN BA YAFEWA NAYI BA*


*NI DA KISHIYOYINA*

*NA SADNAF*

*PAGE 25*

Aisha

"Yaya Salisu bai cancanci rufin asirin mu ba Yaya idan har zai iya Mana wanan cin amanar ya Rasa wacce zai nema sai muhasim yaya bai tsaya iya nan ba ya hada da karkata mata baki sabida Kar ta tona masa asiri zaluncin yayi yawa karka ce zaka yi hakuri sabida ni idan kayi haka bazan ji dadi ba muhasim itama 'yace Kamar kowa ka bari mu kwatar mata hakkin ta karka ce wai sabida ni baka so ayi karar sa mutuncinsa ya zub'e,
Yaya mutuncinsa ya riga da ya zub'e a lokacin da Luba ta tona masa asiri a gaban yayansa,Yaya kila ba iya Muhasim Salisu ya tab'a yiwa irin wanan zaluncin ba kila ya dade yanayi gwara ayi kararsa asirinsa ya tonu sabida a a ceto wayanda zasu Kara fadawa tarkonsa Yaya idan har Salis zai iya neman maza bai cancanci a rufa masa asiri ba Luba duk ta tona masa asiri a wajena ban tab'a sanin mugu nake aure ba wlh irin su Salis a cikin Al umma masifa ne gwara kawai muyi kararsa a kwatar mata hakkin ta"

ido Yaya mustapha ya zuba mata har ta idda magana yana "Kina nufin Luba ce tace miki Salis ne yayi wa Muhasim fyade Kuma har ya karkata mata wuya Yana neman maza Kuma"?

"Itace ta tona masa asiri Yaya"

"Kuma ya amsa da bakin sa shi yayi wa muhasim fyade"?

"Eee Yaya yace Nana yarsa ce da bakinsa ya amsa haka"

Sai da yaya mustapha ya d'au tsawon lokaci kafin ya mik'e Yana " idan har da gaske shi ya amsa da bakin

23 / 38