Nida kishiyoyina complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Romance

Chapter   3 / 38

6K to 9K   out of 111.9K words

yazama abun kunya gareki, Ina tallata maki me gabadaya,

Muntarkato,munwarwaro,munqullo duk wani Abu daze maidaki wanke hannu kataba mun qara a cikin kayayyakinmu,muncire,muntsife,munfidda,mun tantance mun hadamaku wasu irin hadaddun lafiyayyun kaya masu masifar goge fata,wallahi duk fitinar fatarki inshallah,kinzo bustop,kisiya kiyikyanda ko mace,kan juyo ta waiwayo ta dubi halittar Allah,

Ga product din kamar hka,
Sabulu 4500

Mg's beauty kit
Karamin kit 12k
Body soap
Facial soap
Body cream
Face cream
Glow oil
Pink lip balm

Flawless skin beauty kit
Babban kit 20k
Body soap
Facial soap
Body cream
Face cream
Scrub
Glow oil
Pink lip balm

Note kowanne d kalanshi nd yanayin packaging dinma aren't the same,

Tsakanida Allah kigafa
Duk wannan garabasar Kuma kinazaune hba taso a dama dake a harkar yar uwata,

Ayi hakuri da sauyin farashi komi yatashine muma b hka mukasoba
Chat:08062991549,07046881166,07067210195,
Call,+2348064532391
*NI DA KISHIYOYINA*

*NA SADNAF*

*E.W.F*


*PAID BOOK*




*Page 4*

Alhaji Salis k'ofar gidansu Aneesa kawai yake kallo Yana murmushi cikin wata uku da haduwa da Aneesa da bata fi Sa'ar Aliyu ba,duk ta bi ta rikita masa lissafi,asibitin da yake aiki a Abuja taje ganin likitan ido,bata gane office d'in da aka tura ta ba ta fado office dinsa yanda ta saki fuskarta da fara'a ta gaishe shi yasa yaji ta burgeshi anan take ce mishi tana neman Dr Ahmad murmushi ya mata akan ba office din Dr Ahmad bane wanan wanan office din Dr Salis ne idan matsalarta abinda ya shafi mata ne to ta zauna (Dr Salis Gynecologist ne)

Girgiza masa kai tayi tana ita ciwon ido take mik'ewa yayi Yana ta tashi ya rakata wajen sa.

A takaice a yanda ya had'u da Aneesa kenan da yaji kaunarta lokaci guda,zai iya cewa itace mace ta biyu da yaji ya kamu da tsananin santa tunda Kan Aisha bai Kara Jin san wata 'ya mace ba,duk da yana ganin abune mai wuya ma Aneesa ta yarda ta aureshi lura da shi din babba ne,na biyu Kuma taya zaiyi auren ya samu kwanciyar hankali bayan kullum cikin tashin hankali ake a gidansa kuskure kwaya daya tal ya canza masa rayuwa ya hana shi nutsuwa tsawon wanan lokacin.

Kamar wasa daga waya da chatting ya kai wa Aneesa ziyara ga mamakinsa yarinya da alama ta amshi tayin soyayyar sa ba Kuma ya Jin wai dan kudinsa take San shi dan da alama Iyayenta nada kudi.

Wata uku kenan da haduwarsu da ita a wajenta kawai yake Jin wani farinciki dan Aisha ta kulle zuciyarta ya rasa yanda zai goge laifin da ya mata idan hakkinsa ne tana bashi duk wani abu daya rataya a wuyanta tana mishi sai dai sam bayajin dadin yanda ta cire shi a ransa ba abinda baiyi na ban hakuri ba amma duk a banza bata san cewar Shima laifin da ya mata ba a san ransa bane ta Kan dole ya aikata abinda ya aikata.

A yanzu maganar Aure yayi wa Aneesa ta Kuma ce ta amince zata aure shi duk da kasan ransa cike take da fargaba auren baisan Karin auren nutsuwa zai haifar masa ba ko akasin haka,idan ya tuna luba kawai sai gabansa ya Fadi, bai tab'a ganin shuumar mace irinta ba duk tsawon shekarun nan da suke tare bai tab'a kaunarta ba akan dole yake zaune da ita sabida wani boyayyen sirrinsa da yake fatan har ya mutu ba Wanda zai tab'a sani.


Isowar Aneesa da kamshin turaren daya daki hancinsa yasa shi sakar mata murmushi ba ruwan so da tsufa ko yarinta Jin kansa yake Kamar wani matashin Saurayi suka hau hira da yake kuma akwai wayewa sosai a tare da Alhaji Salis tuni ya maida kansa yaro a wajen Aneesa Wanda daga yanda take magana aurensa babu gudu ba ja da baya dan ta bashi go ahead akan yaje ya samu mahaifinta tunda yace bazai tab'a Mata auren dole ba.

Sabida ma Aneesa yake yawan tsiran tafiya Abuja daga luba da Hindatu sun caza masa kai zai bar garin katsina ya tafi Abuja dan a katsina yake zaune wanan kenan.


Dafatan zaku na gane yanda nake tab'o abinda ya faru a baya da yanda nake dawowa cikin labarin banaso ku rikice labarin ne yazo a haka

Past

Aisha

Nidai mutuwar Auren Luba a wajena ba alkhairi bane sam,dan daga lokacin da ta gama idda tayi wani irin gogewa da yake bak'ace sai ta hau shafa mai bata ma bari ta gama idda ba ta ringa sintirin zuwa gidana tana Shan alwashin irin mijin da take so a yanzu ta samu ta aura idan ta tashi min kwatance sai ta ringa cemin "Ni yanzu burina na samu matashin mai kudi wayayye kamar dai Salis mijinki ke fa kin more dan wlh ba ma mai ganin mijinki a waje ya yarda wai ke yake aure dan yafiki wayewa da had'uwa wlh kasar wajen nan gaskiya ta Kara canja shi ya zama wani dan gayu wa zai ce wai Salis mai chemist ne ya dawo haka"

Idan tace haka dariya nakeyi nace Allah ya bata ma fin Salis ba ita kadai ke fadan haduwar salis ba dan ni kaina yanzu sai naga kamar canza min Salis din akayi dan a Rana Salis Yana wanka ya Kai sau uku wani irin tsafta ya Kara koyowa da gayu kananan Kaya kawai yake sawa ni har mamakinsa nake wani zubin nakan ma tambaye shi wanan gayun da yake yi na mene sai yace min yanzu Allah ya rufa masa asiri matsayin aikinsa yanzu sai kana irin wanan shigar sabida raini anan zai hau tsokanata ko dai tsoro nakeji zaa kwace shi ne na kwantar da hankalina ai shi din mijin mace dayane likitoci basa auren mace sama da daya.

Yanda yake siyan sutura haka yake siyamin ya siyawa yarana ni zan iya cewa ma ni wasu kayan ma bansan ya kalansu yake ba dan ba wani bud'ewa nake ba ba Kuma wani fita nake ba ballantana ince zan na sawa iyakacina dai inzan fita naje gidan yayana sai tsirarun dangin babana dake nan.

A lokacin da Luba ta gama idda ta Sako rayuwata a gaba da aron Kaya,ban taba damuwa ba yau zata zo akan na bata aron jaka da takalmi idan na bata bazata dawo dashi ba idan an kwana biyu zata zo aron sarka da dan kunne wlh aron kayana da take bai tab'a damuna wai ko naji a raina bari na hana ta dan Ina ganin ai arzikine ma a ari abu a wajen ka idan ma aka kwana biyu na mata maganar ta dawo min da abinda ta ara sai tace min zata kawo min wlh mantawa tayi idan ta tashi duk zata hado min idan kuwa na sake mata magana anan zata fara "Ke fa matar Mai kudi ce wlh ki dai na haka ke yanzu mai dan ma kin bar min kayan nan yawa kike wlh"

Ta fin k'arfi take rabani da duk abinda ta ara haka zan hakura ban Kuma isa ta Kara aron abu na hanata ba dan yanzu sai tace na mata wulakanci dan mijina ya zama mai kudi.

duk abin nan ban tab'a bari Salis ya sani ba, ba Kuma Ina b'oye masa bane dan wai zai min fada a'a wai dan Kar ya raina luba.

A irin wanan lokacin watarana muka shirya tafiya bauchi dan akwai bikin Yan uwan matar yayana da za'ayi su biyu da yake itama matarsa da nake cewa Mami Yar bauchi ce yaranta biyar akwai Adam Aliyu Rufai Khadija da muhasim.


A lokacin Ina da kudi dan har rasa mai zanyi da kudi nake dan Salis Yana samu ba kad'an ba aikin NGO din da yake da irin kwangilar da yake samu ba k'aramin kudi yake shigo masa dashi ba ko ginin da yake yi kaf unguwar ban ga mai irinsa ba,gudunmawa mai yawa nayi wa Aunty Mami matar yayana domin ta rik'eni da zuciya daya tun Ina K'arama ta har tasowa ta,tana kyautata min sosai, har yaranta sai da nayi wa dinki,Salis ma ba'a barshi a baya ba dan na bashi labarin yanda nake da matar yayana Ina kaunarta sabida bata tab'a cin zalina ba hasali ma Ina yarinya idan nayi laifi har wani b'oyeni take sabida Kar yayana ya dokeni.

Salis yasan manyan kaya Sosai duk kayana ba kananu har cemin yake bai ga abinda zai min da zai Fadi ba dan na kaunace shi a lokacin da bashida komai na zauna dashi a lokacin da ko biyar bashida shi,ya tafi ya barni shekara biyar na rike masa mutuncin aurensa yayana ya rik'e mu ya saka yayansa a makaranta baya jin akwai abinda zai iya biyan su dashi.

Ni kuwa ganin ya d'auke min komai yasa bayan Aunty Mami da yayanta na siyawa mahaifina da mahaifiyata kaya sosai sauran kudin ma na b'oye dan na basu duk da nasan Salis Yana yawan musu aike amma nima inaso na samu albarkar su.

Ana saura kwana biyu mu tafi telar da salis ya bawa dinkina ya kawo min wajen kala biyar ni ba wani sanin kaya nayi ba amma Ina ganinsu nasan masu tsada ne.

Ina zaune a palo Ina cikin daga dinkin sai ga Luba ta shigo da sallama taci doguwar rigata baka ya Sha Jan duwatsu a cikin dogwayen riguna na ina balain san rigar Ina ji Ina gani Luba ta rabani da rigar sawa na daya.

Daidai da takalmi da purse din hannunta duk nawane banda ban leka cikin jikinta ba komai na jikinta nawa ne.

Yanzu idan na dan canza fuska sai tace na wulakantata ta hakane yasa na sakar mata murmushi Ina "Hajiya daga Ina"?

"Unguwa naje fa ke na hadu da wani mai kudi yaseen amma bana Jin dai ya Kai Mijin ki kudi gaskiya amma ya zanyi haka zanyi maneji na aure shi kila ya Kara kudi a gaba ki tayani da Addu'a Allah yasa da gaske yake zai aureni ke gidan nan da Salis yake ginawa wlh Kamar wani hotel kawata kin chaba wlh"

Dariya nasa Ina "Allah ya baki fin gidana Luba wlh tunda nake ban taba sa rai zan tab'a tsintar kaina a cikin irin Wanan niimar ba insha Allahu kema Zaki samu"

"Kai kai kawata wanan shegen less din fa kinsan kudinsa kuwa"?

Ta dauki less din da na ajiye a gefena dana ga ta shigo wai Ina addua ma Allah yasa Kar ta gani.

Ai tuni ta jawo duka kayan ta hau dagawa tana ihun nasan tsadarsu kuwa duk ita ta hau fadamin kudin kayan ta mik'e tsaye ta fara Kara kayan a jikinta tana "Allah ya baki Aisha irin rayuwar da nake mafarki Allah ya baki Salis ne ya siyo miki ko dan nasan ba wani sanin kaya kikayi ba"?


"Eee shi ya dinko min na bikin gidansu Aunty Mami kinsan jibi zamu tafi"

"Gaskiya sunyi kyau kawar rufin asiri aikuwa dole ki bani aron daya dan gobe Alhajin nan zai zo kinsan gwara yasan tanadin da zaiyi idan yaga na saka irin wanan less din"

"Luba nace miki fa dinkunan bikin da zamuje ne taya zan baki aro ai sai dai Kuma idan na dawo sai na baki amma yanzu ko bikin ma banje na sa ba, sai na baki aro"


Sai ta saki less din hannunta take fuskarta ya sauya "ke yanzu aro ne bazaki iya bani ba Aisha aro dai ba kyauta ba wlh ban tab'a tunanin wai akwai abinda zan nema a wajenki ki hanani ba arzkin nan muma zamuyi Aisha bamu fidda rai ba dama nasan lokaci na zuwa da zaki wulakantani sabida kina ganin kin samu abin duniya"

"Kai Luba mai yasa kike hakane dan girman Allah kin tab'a tambaya ta abu na hanaki ko abu Kika gani ban taba sawa ba idan kikace na baki aro Ina baki ban taba hana ki ba wanan biki za muje Salis shi ya Kai min dinkin nan da kansa Kuma shima zaije bikin ai bai dace ace bai ga nasa ba ki fahimceni Mana idan Aron less kikeso ai zan iya dauko Miki wani akwai wayanda ma ko sawa ban tabayi ba ai sai ki zaba a ciki"

"Ki barshi kawai Aisha ba komai muma Allah ya Mana arzikin nan"

"Ta dauki purse dinta fuuu zata wuce na rukota da sauri (akwai abinda idan na tuna wlh kamar na rufe kaina da duka Sadnaf hmm)

"Kai Luba wai mai yasa kike haka ne mai na zuciya dan Allah dan annabi toh ki zabi Wanda Zaki ara din Shikenan ban miki rowa ba"

"Wlh ke din ce da haushi Aisha yanda na d'auke ki wlh ba haka kika d'aukeni ba wlh bana fatan Wai yau ace ke ki nemi abu a wajena na hanaki amma ke daga ki bani aro kin tsaya maganganu"

"Toh naji dauki Wanda kikeso din"

Nace Kamar nayi kuka sai addua nake Allah yasa Kar ta dau wanda yafi shiga raina sai kuwa gashi shi ta d'auka iya nan bai isheta ba sai da ta kara aron mayafin da zai Shiga da sarka da dankunne.

Har ta tafi zuciyata cike take da bakinciki wlh ba wai dan aron kayan ba sai dan less din ya Shiga raina Kuma nasan kila nayi bankwana dashi kenan wane kila ai less ya tafi sai dai nayi hakuri.

Koda salis ya dawo ya tambayeni an kawomin dinkunan ce masa kawai nayi eee nama saka a akwati,ya tambayeni sunyi kyau kuwa"?

Nace Masa kyau kai sai ya saki murmushi Yana "Wlh da tsada na siyesu sosai dan inaso duk Inda Kika Shiga asan matar Dr Salis ce ke Kinga wanan ruwan ganyen yafi dukansu tsada ranar da zaku fi taro Zaki saka"

Sai na saki baki Ina kallonsa dan shi Luba ta d'auka na wayance da aikuwa baka ga kyaun da yamin ba"

"Ai nasan dole ya miki kyau dan nasan kalar dake haska ki"

Nidai a ranar haka na kwana Kamar nayi kuka luba dai tamin fin k'arfi ba Wanda na tab'a fadawa addabata da take da aron Kaya sau daya nasan na fadawa Aunty Mami ita kuwa ta ringa min fada akan ya nake Abu kamar doluwa mara wayo na daina haka ai bai dace na ringa bada aron Kaya ba sai dai idan nayi niyya dai na bar mata.

Duk yanda naso d'aukar shawarar Aunty Mami kasawa nayi dan sai nake ganin kamar bai dace Ina da abu Luba ta tambayeni na hanata ba.

A haka muka je bauchi muka yi sati biyu bayan biki na dan huta a gidanmu da su Ashraf ga cikin dake jikina da ya tafi wata biyar.

Ba laifi Salis ba iya iyayena yake yiwa hidima ba har da yan uwana na Kuma ji dadi ba kadan ba.

Naso barin Su Ashraf ma a gidanmu tunda hutun makaranta ake suka k'i ahaka muka dawo a motar da Salis ya aika mana duk dasu Aunty mamy Mu ka dawo da yaranta sai da muka sauka a gidanmu muka huta suka tafi muhasim tace zata zauna har sai an koma hutu zata koma gidansu itace Yar yayana ta biyu a lokacin tana da shekara goma Sha biyar. Ta girmi Ashraf da wajen shekara bakwai.


Ina dawowa da kwana biyu sai ga Luba ta duro a ranar Salis bai fita ba sabida ranar lahadi ne.

Koda na ganta sai da gabana ya yanke ya Fadi.

Dan less dina data ara shine a jikinta.

Nasan Salis indai yaga less dinan a jikinta sai na Sha fada dan kwanaki da ta sako wani atamfata da ta ara data tafi sai da ya tambayeni nace masa tana da irinsa ba nawa bane yace "Aa toh dan da nakine wlh sai munyi fada kinsan wanan kawar taki bata da hankali Ina tausayawa Wanda tsautsayi zai saka ya aureta"

Murmushi kawai na Masa a lokacin dan har a raina bana Jin dadin yanda yake Mata.

Tana shigowa nayi sauri na mike na fara k'ok'arin janta dan mu Shiga d'akin Yara.

Ai ba muje bakin k'ofa ba naji Muryar Salis a bakin k'ofar d'akina Yana kirana gabana ya yanke ya Fadi na juya a hankali ita kuwa Luba ko a jikinta ta juya itama tana "aa likita bokan turai ashe kana nan?

Bai amsa ba naga ya fara Mata kallon sama da kasa take naga ya hade rai ya juyo ya kalleni Yana "Aisha wanan ba less dinan bane da na siya miki?Mai yake yi a jikin Luba"?

Runtsa idona nayi dan Sam banso Salis yamin haka ba

"Kai likita bokan turai mai dan kayanta ne Ni da ita fa dayane ko ka manta"?

"Na manta me ya zaayi na siyowa matata Kaya kizo ki ara kice min ke da ita daya ne ke na siyowa ko ita? A wane dalili zan siyo wa matata kaya mai tsada sai kizo ki ara ki saka"

"Dan Allah ka bari Abban Ashraf zan maka bayani"

"Bayanin me Zaki min Aisha dama idan na siyo miki Kaya dan kisa kawarki kike bawa sabida wulakanci kwanaki naganta da kayanki kikace min ba naki bane irinsa ne da ita?dama baki San ciwon kanki ba Aisha an gaya Miki kudin banza ne dani? Ko an gaya miki bansan zafin kudina ba na ciri kudi mai tsada na miki dinki ki bawa wata banzar kawarki"?

"Kaga dakata Mallam karka sake ka fadamin maganar banza kai har wani arziki kayi da zaka min rashin mutunci karka manta fa tare kaganmu da ita baka isa ka rabamu ba ko ni keda kayan da take dashi zan bata fin wanan har nawa kayan nan suke da zaka tsaya min rashin mutunci"

"Luba mai haka kikeyi"?


Nace hankalina a tashe dan naga salis idonsa ya kada yayi ja

"Cire min kayana tunda ba ubanki ne ya siya ba wlh sai kin cire ban damu ki tafi ko tsirara ba wlh zan nuna miki ni din banida mutunci maza ciremin kayan nan yanzu idan kawarki bata da hankali ni zan koya mata hankali idan taga kinyi tsirara maza ciremin kayana

Tunda nake da Salis ban taba ganin bacin ransa haka ba ganin ya nufomu yasa na tsaya a gaban Luba Ina "Dan Allah Abban Ashraf kayi hakuri dan Allah ka bari taje gida ta cire ta Aiko min dashi na hadaka da girman Allah"


"Ai wani iirn tureni yayi yana "ba bakida hankali ba yau zan gwada miki rashin hankali har na siyi kaya da tsada ki dauka ki bawa yarinya da bata San ciwon kanta ba ta kashe aurenta sabida babu kuma har tana da bakin ta ringa gaya min magana ciremin kayan nan yanzu ki bar

3 / 38