Nida kishiyoyina complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Romance

Chapter   20 / 38

57K to 60K   out of 111.9K words

Kuma da ka ke misali wlh indai nice Zan yarda dan haka ma Kara karfafa Mana zumunci zaiyi mai a ciki nidai zabi ya rage naka ka bani hanya na wuce"

"Aisha zata iya rabuwa dani akan na aureki Luba mutane zasu ga Kamar naci amanarta"

"Karka damu mutanen da zasu ga kamar kaci amanarta sune na farko wajen tsine ma idan Suka gano cewar kai din mazinacine macuci azzalumu ai bazan ma dole ka aureni ba inaga ko dauka da Wasa nake bazan iya tona ma asiri ba"


Ta fara k'ok'arin yin waje Salis ya tare hanya yana "Na yarda zan Aure ki Luba amma taya zan b'ullowa Aisha"?

Luba sai a lokacin ta saki murmushi ta koma kan kujera ta zauna tana "Yafi komai sauki ai Kai mijinta ne kana sama da ita Kuma dole ta maka biyayya ka fada mata zaka Aureni nasan ka dan tsarata shikenan bata da wani matsala ko zata yi fushin ma na dan lokacine"

Salis dafe kansa kawai yayi Yana Jin wani zazzabin tashin hankali na neman rufe shi taya Luba tasan shine yayi wa muhasim fyade har yanzu kirjinsa bai daina bugawa da tsoron wani yasan abinda ya Shiga tsakaninsa da muhasim ba yasan idan har ya bar Luba ta tona masa asiri ba mai yarda wai bashi ya karkata mata baki ba har yau yana cikin tunanin Wanda ya mata wanan aika aikan.

Tambayar da ke nukurkusan sa da san yaji yanda akayi har Luba tasan wanan abu da yayi Imani ba Wanda yasani sai Allah
"Luba ya akayi kika san ni na yiwa muhasim fyade?

Luba kwanakin baya ke Kika saka min magani Kika sa nayi abinda banyi niyya ba Luba idan har bake kike da saka hannu a abinda ya faru ba ya aka yi kika san abinda ya Shiga tsakani na da muhasim Luba tashi daya na tsinci kaina cikin azabar bukata dake hanani zaman lafiya da sukuni luba kina da hannu a abinda ya faru idan baki da hannu ba yanda za'ayi kisani kin biyo ta hakane sabida kawai ki samu cikar burinki"


"Ta nan ka b'ullo kenan na farko na yarda na sa ma kwaya a ruwa amma na biyun a Ina ka gani da har na saka kayi wa muhasim fyade ? Wlh fyaden da kayi wa muhasim yin kanka ne,yaushe rabon da ka gani a gidan ka ?taya zan San kayi mata fyade har ta samu ciki idan kana so kasan yanda akayi nasani bari na fada maka yarinyar da bakinta, ta fada min na tsinceta a hanya tana ta kuka da na rarrashe ta ta fito ta fada min kayi mata fyade ta samu ciki kace Kuma zaka zubar mata da cikin taki yarda,wlh a ranar tace ita zata fito ta fada wa iyayenta dan taga so kake ka kasheta,ni na rarrasheta akan Kar ta fada musu sabida Ina san rufin asirin ka,a haka ta ringa fada min duk yanda kake bibiyar ta da yanda kake bin ta makaranta sabida kawai ka shawo kanta Salis idan har ba ita ta fada min ba taya zan sani ko washegarin ranar da zaka karkata mata baki mun had'u da ita tace min kace tunda taki yarda ka zubar Mata da cikin zaka yi maganinta tana kuka tace Aunty Luba Ina tsoron ya kasheni nace ta kwantar da hankalin ta duk burga ce ba abinda zaka iya yi,Ina yawan zuwa baa bari na shigo ne amma na Dade inaso na sanar da Kai nasan komai sai Kuma gashi ka karkata mata baki sabida zalunci"

"Wlh bani na karkata mata baki ba Luba nemanta ma da nayi ba a cikin hayyacina bane"

"Ka addana rantsuwar ka zai ma amfani a wajen yayan Aisha da Aisha mutunci ya riga da ya zub'e daga lokacin da asirinka ya tonu ni kaga ma tafiyata ni na fasa ma auren naka nafiso a gane Kai mugune mazinaci"


"Ki rufa min asiri Luba wlh na yarda zan aureki nidai kimin alkawarin ba Wanda zai tab'a sanin wanan maganar har duniya ta nade"


"Indai ka aureni ka yarda nima ba saki a tsakanina da Kai,duk abinda nake so zaka min Kuma zaka kaunaceni kamar yanda kake kaunar Aisha nayi alkawarin ba Wanda zai tab'a sani"

Salis kamar ya dora hannu aka yayi ta rusa ihu zuciyarsa sai rayya masa take da ya hada luba da bango ya shaketa har sai ta daina numfashi bai tab'a sanin muhasim zata iya bude baki ta fadawa wani ba da a yanzu ba lubar ta samu ba kila da ta dade da tona Masa asiri.

Hadiye tsana da bakin luba da yake gani yayi Yana "Luba zan aureki nayi alkawari kin san bazai yu na yaudareki ba sabida rufuwar sirrina ba a yanzu zan aureki ba sai idan an kwana biyu kinsan yanzu ana cikin alhinin da tashin hankalin abinda ya samu muhasim na karkacewar baki da wuya Wanda Allah shine shaidata wlh wlh banida hannu a abinda ya sameta,a yanzu idan na fito da maganar auren ki da yawa za'a dauka ban damu da abinda ya same ta ba a yanzu ma babu kwanciyar hankalin da zamu iya aure dan haka inaso ki daga min kafa har zuwa muhasim ta haihu nan da shekara daya haka da rabi"

"Ina laifin dai tana haihuwa muyi auren wane irin nan da shekara daya har da rabi"

"Ki dai yi min wanan taimakon Luba ai kinsan aure ya riga da ya zama dole idan akayi auren yanzu dukan zai yiwa Aisha yawa ga na abinda ya same su ga na Karin Aure ki bari nan da shekara dayan"


"Salis Ina tsoron ka zaka iya kasheni kafin shekara dayan nan tunda nasan baka kaunata amma inaso ka san cewar idan har ka kasheni Ina da mutane biyu wlh da zasu bankada sirrin ka"


"Rashin imani na bai kai har haka ba Luba bazan iya kashe rai ba"

"Wanda yayi fyade ya karkatawa mutum baki zai iya kissan Kai"

Salis cije lebb'ensa yayi Yana Jin zafi a zuciyarsa ya tsani tace ya karkatawa muhasim bakin nan yasan yanzu wani sabon shafin kaddara ce ta buda masa sai dai yayi addua Allah ya bashi ikon cinye wanan jarrabawa.

A takaice ranar zancen karfi da yaji yayi da Luba ta ringa zuba masa mulki san ranta Koda ta tashi tafiya ma sai dage masa tayi akan shi zai mai da ta gida.

Kamar zuciyarsa ta fashe haka ya maida ta gida.

Daga nan ya nufi gidansa Yana Jin inama Yana da yanda zai gujewa Luba bai hango yanda zai iya auren ta ba.

A lokacin daya isa gida haka ya tarar da Aisha da kumburarren ido,da gani taci kuka ta gode Allah tunda suka gano halin da muhasim ke ciki ta ke cikin wanan halin bai iya Mata magana ba ya zub'e akan kujera ya dafe kansa dake Sara masa Yana bakin cikin ganin Aisha a cikin Wanan damuwar.

Muryar ta ya katse masa tunanin da ya tafi

"Abban Ashraf wlh na kasa daina kukan tausayin muhasim duk Wanda yake da saka hannu a cikin wanan halin da muhasim take ciki Allah ya Hana shi Jin dadin duniya da lahira ga fyade ga ciki ga karkakata Kai wanan wane irin zalunci ne har na koma ga Allah Ina tsinewa Wanda ya mata wanan aika aika"

"Ya isa haka Aisha duk abinda ya samu bawa mai kyau ko akasin haka daga Allah ne ya Kamata ki yarda abinda ya sameta a rubuce yake sai ya sameta Yana cikin kaddararta Allah ya bata ikon cinye wanan jarrabawa addua zamu dage mata dashi Allah ya kawo mata karshen wahalar nan bai dace ki matsawa kanki da irin wanan damuwar ba idan kina haka Mai Yaya mustapha da Aunty mamy zasu ce ai sai ki Kara daga musu hankali ke fa ya Kamata kiringa rarrashin su"

"Tausayin yayana nake ji kaga yanda ya koma sabida tashin hankali Ina tsoron zuciyarsa ta buga Allah ya isa tsakaninmu da Wanda ya mata haka Allah ya tona masa asiri"

"Ya isa haka Aisha ki tashi ki d'auko min abincina ki sausauta wa kanki damuwar nan kafin ki kamu da ciwon zuciya"


Aisha mik'ewa tayi ta nufi kitchen tana share hawayen dake zubo Mata

Salis kuwa ya hau sallati kasa kasa a zuciyarsa hankalinsa na balain tashi idan yaji Aisha na irin wanan tsinuwar yasan bashida hannu a karkata mata baki amma yasan shi ya mata fyade ta samu cikin ko da ta kawo abincin bai wani iya ci ba dan ya aiketa ne sabida ya kau da maganar.

A ranar ko runtsawa bai yi ba Yana ta tunanin yanda zai kaucewa auren Luba da yake ganin bazai iya ba da wane ido zai kalli Aisha yace zai auri Luba taya ma hakan zai yu wane irin kallo mutane zasu masa Luba ta zame masa kaddara da ace yasan Luba zata zame masa balai haka da tun farkon auren sa da Aisha ya rabasu.

Tashin hankalin da yake ciki a yanzu sai ya nin ka na baya dan gefe ga Luba gefe gefe daya ga Aisha da yayanta da ya zama silar jefa su a cikin tashin hankali ba abinda ya Kara karya Masa zuciya sama da kukan da yaga Yaya mustapha nayi da hawaye mutum ne shi mai kib'a sai gashi duk ya zub'e sabida tashin hankalin da yake ciki,taya zai so su tab'a sanin shi yayi wa muhasim fyade har ta samu ciki,cikin da kullum yake Addu'a Allah ya kawo sanadin da zai zub'e idan babu rabon ya zub'e Allah yasa abinda muhasim din zata Haifa yazo ba Rai.

Sosai ya saki bakin Aljihu yake hidimanta musu duk wani magani ko test shi yake d'aukar nauyin su.

Luba kuwa tamkar har ya aureta sabida hidimar da yake yi da ita,kullum a cikin tambayarsa kudi take,ta k'arfin tuwo tasa ya ringa zuwa zance wajenta ya mugun tsanarta amma haka ya daure sabida rufin asirinsa.

Abinda ke Kara bashi mamaki da shu'umancin ta yanda take ziryar asibiti har da dan hidimarta,Yana ji yanda Su Aisha da Yan uwanta ke yabon ta.

Aisha har wani Kara bashi labarin irin damuwar da luba tayi da larurar da ya samu muhasim take baya iya ce mata komai dan Luba ta daina bashi mamaki yanda ta siye zuciyar Aisha da zai fito yace mata tace tana Sansa karyatawa zata yi.

Da Aisha zata nutsu ma ta kalleshi zata san shi ma ba'a hayyacinsa yake ba ko d'akin da aka kwantar da muhasim baya san Shiga dan gani take zata iya bud'e baki ta tona masa asiri.

A Haka har aka sallamesu daga asibiti akan larurarta shafan Aljannu ne,Inda ya dan samu kwanciyar hankali katsina akayi da Muhasim sabida Kar kowa yasan cikin dake jikinta,haka Aisha ta ringa zarya daga bauchi zuwa katsina.

Lokacin haihuwar Muhasim na karatowa Yana addu'ar Allah yasa abinda zata Haifa Kar yazo da rai

A ranar da aka sanar musu anyi mata aiki an cire mata 'ya mace hankalinsa sai da ya kara tashi dan a yanzu gani yake kamar za'a gane yarinyar yarsa ce sai dai cikin ikon Allah bata d'auko kamaninsa ba, a lokacin da Yaya mustapha yace zaa Kai yarinyar gidan marayu ba karamin Dadi yaji ba hakane yasa daya shawarce shi ya bashi goyon bayan a kaita gidan marayun tunda ba'a san waye mahaifinta ba sai dai kwana biyu da dawowarsa sai ga Aisha ta taho da jaririyar wai zata rik'e ta har ga Allah ba haka yaso ba so yayi ya nesanta kansa da jaririyar amma gudun Aisha ta dago shi yasa ya hakura ta hada Nana da Ummi ta ringa shayar dasu,abinda ke dan bashi mamaki bai wuce yanda Aisha ke matukar kaunar Nana ba tamkar tasan nana jininsa ce.

Taya zai so Aisha tasan shine mahaifin Nana bazai so ta tab'a sani ba zai auri Luba a matsayin kaddararsa gwara taji labarin aurensa da Luba da taji labarin shine mahaifin Nana.

Luba kuwa Kamar mai jiran muhasim ta haihu ta sako shi a gaba akan ya tura gidansu a daura musu aure Kuma ita ba anan take so ta zauna ba Abuja take so ta zauna ta hau gindaya Mai sharruda.

Dak'yar ya samu ya shawo kanta akan ta bari a Kara kwana biyu kafin suyi maganar Aure baya so suyi gaggawa ya riga da yace zai aureta ba fasawa zai yi ba.

A takaice da kyar ta yarda aka kara wata takwas a wanan lokacin yafi kowane lokaci shiga tashin hankali gani yake Aisha idan taji labarin auren nan zata iya rabuwa dashi,gashi Luba ta dage akan ita bata San munafirci tafiso a fadawa Aisha.

Da kudi mai yawa ya samu Kan Luba ta yarda akan zai aureta a b'oye idan an samu shekaru zai fito ya fadawa Aisha a yanzu bazai so Aisha ta sani ba tunda dama Yana aiki a Abuja zai ajiye Luba a Abujan kawai yasan Aisha bazata tab'a sani ba.

Dak'yar Luba ta yarda har aka daura musu aure bazai iya lissafa kudin da ya kashe mata a hada lefe ba duk wani Kaya da tasan Aisha na da shi sai da ta saka shi ya siya mata irinsa ban da kudaden da take ta karba a hannunsa.

Sosai yake taka tsantsan baya so Aisha ta tab'a gano shi hakane yasa ya mata karyar ayyuka sun masa yawa a can.

Luba kuwa ko da ta tare baya iya kwanciya da ita sabida baya Jin kaunarta yasan yayi tsalle tsalle a baya,ba Kuma dan Yana kaunarsu ba Luba ce yake Jin bazai iya kwanciya da ita ba.

Karyar rashin lafiya ya ringa shirga Mata ganin an tafi sati daya yasa ta haukace Masa akan sai ya kwanta da ita raina mata hankali yake yi ba abinda yake damunsa ita fa auren da suka yi so take ya gwada Mata soyayya yanda yake gwadawa Aisha idan ba haka ba tona masa asiri zata yi.

Abu kadan sai tace zata tona masa asiri sai da ya tilasta wa kansa kwanciya da ita a haka ma sai ya dirkakawa kansa magani yake iya kwanciya da ita,a cikin wata daya har makota sun san ta,da shishigi ta ringa zaryar office dinsa na Abuja har sai da duk abokanansa suka san matarsa ce da makirci take yawan hana shi zuwa bauchi gangar jikinsa ne kawai a Abuja Amma zuciyarsa na wajen Aisha,tunda ya auri luba zuciyarsa kullum cike take da fargaba akan kowane lokaci Aisha zata iya ganowa ya auri Luba a b'oye,hakane yasa yake ta iya k'ok'arinsa wajen ganin ya hana Aisha muamalla da Luba,sai dai ya lura Luba burinta kawai taga ta tona kowa yasan ya aureta.

A Haka har Luba ta munafirce shi da ta haihu ta gayyato Aisha batare da yasani ba,Aisha bata cancanci haka daga wajensa ba yasan ko me zai ce mata bazata tab'a yarda ba'a san ransa ya auri Luba ba idan yace zai mata bayani hakan na nufin tonuwar asirin sa da yasa Yama auri luban.

A Haka ya samu mahaifiyar sa ta shawo Kan Aishan da tunda daga lokacin da ta ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?gano ya auri Luba ta goge shi a zuciyarsa yayi bankwana da wani farin ciki da Jin dadi kaddara ta Kara shigo Masa da Hindatu rayuwarsa ya aureta shekara da shekaru yana yiwa Luba biyayya sabida kar ta tona Masa asiri shekara da shekaru yana kashewa Luba kudi,shekara da shekaru yana fama da zullumi da fargaban Luba na iya tona Masa asiri a kowane lokaci sai gashi a yau Luba ta tarwatsa masa gida ta hanyar tona Masa asiri agaban Aisha da yayansa,a gaban Aneesa da bata san ma Yana da boyayyen sirri ba.


Present

"Abba Abba"

Yaji muryar Ashraf akan sa

Bud'e idonsa yayi a hankali ya sauke akan Ashraf daya tsugunna a gabansa shima kana ganinsa kasan hankalinsa a tashe yake.

Sai da ya hadiye yawu yace "Abba ka koma cikin daki ka kwanta bana so su ummi suga halin da kake ciki yanzu zan bi bayan Hajiya umma bazan bari ta karasa gidan ba"

Da sauri ya ruko hannun Ashraf Yana "Kayi sauri kaje Ashraf karka bari ta fadawa yayanta dan Allah ka shawo kanta mu rufe sirrin nan idan har maganar nan ta fita mutuncin ku Kuma zai zub'e"

"Abba kayi hakuri da tambayar da zan Kara ma Dan Allah kana da sa hannu a karkacewar wuyan Aunty muhasim"

"Ashraf wlh wlh banida sa hannu a abinda ya same ta da Ina da sa hannu tunda asirina ya Riga da ya tonu Zan fada ma gaskiya amma wlh banida sa hannu a abinda ya same ta nine dai mahaifin Nana "

Ashraf gyada kansa yayi Yana "Bari na bi bayanta Abba"

Yayi hanyar waje

Salis ya mik'e jiri na dibansa yayi hanyar dakin Aneesa tamkar karamin yaro haka ya zube akan gado hawaye na bin fuskarsa.



Luba

"Ai abinda za'ayi gida zaki tafi kafin musan yanda zamu bullowa lamarin nan amma batun na bar ki ki zauna anan kema ai kinsan ba mai yuwa bane haka kawai Allah ya rufa min asiri nayi Aure dakyar Ina lalabawa kizo kimin kwace kamar yanda Kika yiwa kawarki haba Luba da hankalina fa ni ba shashasha bace"

"Asabe yanzu bazaki iya rufamin asiri ba Asabe duk abinda na Miki a rayuwa ni zaki wulakanta na zauna dake din shine bazaki iya ba"

"Ikon Allah uban me kike min wai hala kin d'auka ni Aisha ce Kinga tashi maza ki bar min gida kafin nasa a sakar Miki karnuka"

Luba hawaye ne ya hau zubo mata tana k'ok'arin Magana

Asabe ta mik'e ta fara kwallawa Mai gadi Kira tana "ka bud'e min kejin karnuka Kan nan".......



*HUMKAM INCENSE* gidan kamshi da maganin mata muna turaren wuta na tsuguno Wanda yake matse HQ sosai Yana karawa dandano Yana maganin infection kowani iri muna da shuumar humra, hatsabibiyar turare,bita zaizai Mai abin mamaki munada turauka na daukar hankali
*08132506044*
TILL WE MEET*
*ZARATY* WANNAN HMMMM YA HADU NACE YA HADU SHIN KINTAVA AMFANI DA TURAREN DA ZAISA MIKI LAUSHIN FATA? KINIMI ZARATY YANA DA KAMSHI DA RIKE JIKI YANASA FATA LAUSHI TURAREN KOWA
*Jas oud* 3 IN 1 ZAKI TURARA GIDAN KI DASHI JIKINKI DA KAYANKI JAS OUD YA HADA ABUBUWA DA DAMA YANA RIKE JIKI SOSAI YANS KAMA GIDA YANA RIKE KAYA
*AKWAI HUMRAR MOWA GUMBAR MOWA GARIN MOWAR TSUMIN MOWA DAN MATSI*
*SHU'UMAR HUMRA NA MANYAN MATA MATAN DA SUKA SAN KANSU SIRRINKI A SHIFIDAR DAKIN MAIGIDAN KI MUNADA SHUUMAR TSUMI*
*DESIRE MAINE DA

20 / 38