Nida kishiyoyina complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Romance

Chapter   35 / 38

102K to 105K   out of 111.9K words

ruwa ya Kara da "ta karfi da yaji takeso na aureta ko ta halin Kaka ko a yanzu inada gajeran recording din abinda ya faru a d'akina dan nasa k'aramin recorder a saman d'akina,idan kotu na bukata zan iya kawowa sabida aga shaidan yanda tazo d'akin nawa,tunda ga lokacin na Kara tsanarta na matsawa matata akan ta rabu da ita amma tak'i rabuwa da ita" dan har ta gwammaci b'acin raina da na kawarta haka ta cigaba da zuwa office dina tana nacin sai na aureta a irin wanan yanayin na wayi gari cikin tsananin bukata da har fita nake a hayyacina idan ban samu nutsuwa ba,a haka watarana Ina tsaka da aiki abin ya motsa min nazo gida Koda nazo sai ban samu matata ba Allah shine shaidata bansan mai ya faru ba sai da na dawo hayyacina naga Ashe muhasim na nema da tana da bakin da zatayi magana da kotu tayi mata tambaya, tundaga lokacin na rasa kwanciya hankalina na rasa mai yake min Dadi,yarinya tabar gidana dan dama a gidana take zaune.

Wata biyu a tsakani tazo ta sameni akan bata ga Al-adarta ba naso ta zubar da cikin dan abin kunya ne ace ni da kaina nayiwa Yar yayan matata ciki,sai tak'i bani hadin kai a zubar da cikin a lokacin Kuma Luba ta matsamin da zuwa office dina

A takaice tiryan tiryan Salis ya bada labarin komai bai boye komai ba har yanda Luba tazo ta same shi akan tasan shi yayiwa muhasim ciki ya Kuma yi mata fyade Inda tace Masa idan bai aureta ba sai ta tona masa asiri ya Kara da "Ni nasan ba wani shakuwa suka yi da yarinyar ba sai idan tazo gidana ma take ganin yarinya bansan ya akayi tasan mai ya shiga tsakanina da yarinya ba,naso na zargi ko tana da sa hannu a halin da na tsinci kaina na yawan bukata tunda ta tab'a saka min magani sai Kuma na cire zargin haka a raina amma Allah shine shaidata baa cikin hayyacina nayiwa muhasim fyade ba zan iya dafa al Qur'ani na rantse"


"A lokacin da ta ringa bibiyar ka tana sanka har ta saka maka magani a ruwa a ranar da kuka tare a sabon gida shin ka fadawa matarka abinda ya Shiga tsakanin ku?sanan Ina matar taka take a ranar da batasan duk abinda ya faru ba"?

"Ban fada mata ba dan gani nake bazata tab'a yarda Luba zata ci amanarta ba dan ta bata yarda dari bisa dari sanan a ranar da ta fara saka min magani a ruwa ta bawa muhasim ta kawo min a ranar muka tare a sabon gida da yan uwan matata da yawa a gidan hakane yasa tace min zata kwana cikin Yan uwanta a ranar ba a dakina ta kwana ba"



Ashraf gyada kansa yayi yace zai iya komawa ya zauna ya juya ya kalli alkali Yana "Ya mai girma mai Sharia inaso kotu ta nazarci maganar wacce ake Kara da shi Alhaji Salis daga abinda ya faru zaa gane dole wacce ake Kara tana da hannu a cikin abinda ya samu yarinyar dan yarinya bata da wani kusanci da ita,da zata ringa zuwa wajenta tana fada Mata halin da take ciki,na biyu idan har dagaske yarinya ce ta fada mata shi Alhaii ya mata fyade idan ba dama tana da wani manufa a zuciyarta ba ya Kamata ace ta sanar da kawarta halin da yarinyar take ciki sai bata sanar da ita ba,daga maganin da ta saka wa Alhaji a ruwa sabida ya sadu da ita kotu zata gane zata iya yin komai domin ta samu cikar burinta dan haka inaso kotu ta sake bani dama zan kira Hajiya Aisha na mata wasu tambayoyi"

"Kotu ta baka dama"

Aisha tunda taji labarin duk abinda ya faru daga bakin Salis tayi mutuwar zaune ta ringa komawa baya tana tuna duk yanda Luba ta ringa sintirin zuwa gidanta da irin kallon da take bin Salis dashi a hankali komai ya fara dawo Mata na yanda Salis ke iya k'ok'arin sa wajen ganin ya rabasu.

Jiki a sanyaye ta mik'e ta nufi wajen da ake tsayawa ta tsaya tana kallon Luba da ta jike da gumi tana mata wani irin kallo,ko kad'an bataji ta wani tsorota ba tasan Ashraf bashida shaidan komai, idan har ta kafe akan karya yake ba yanda za'ayi kotu ta Yanke mata hukunci har sai an samu shaida.

Bayan Aisha tayi rantsuwar zata Fadi gaskiya ASHRAF ya tsaya a gabanta Yana "Hajiya Aisha ko Zaki iya fada mana mai alakarki da wacce ake Kara"?

tiryan tiryan Aisha ta kwashe komai ta fadawa kotu daga alakarta da Luba har zuwa lokacin da ta wayi gari ta aure mata miji ta Kara da "A duk abinan dake faruwa bata tab'a nuna min tasan Wanda yayi wa muhasim fyade ba,bata tab'a nuna min ma tasan muhasim nada ciki ba, shiyasa a yanzu da naji tana cewa tasan har muhasim nada ciki har muhasim taje wajenta kaina ya kara daurewa, dan a gidana take ganinta su gaisheta tunda aurenta ya mutu bata tab'a zuwa gidan yayana ba a gidana dai muke had'uwa har a wane lokaci ta samu kusanci da yarinyar da zata ringa zuwa wajenta tana fada mata halin da take ciki ya mai girma mai Sharia Ina rokon kotu ta taimaka wajen bincikar ta dan Muhasim nasan bazata tab'a tararta ta fada Mata halin da take ciki ba sai dai idan ba dama tasan abu ya Shiga tsakanin muhasim da mijina ba har ta Kuma gano tana d'auke da juna biyu ba"

Aisha ta karashe tana share hawaye dan a yanzu ta yarda Luba tana da hannu a abinda yasamu muhasim.

"Ya isa hajiya Aisha kotu zata miki adalci insha Allahu tambayar da zan miki a yanzu shine shin kafin ku gano anyiwa muhasim fyade dagaske ne akwai lokacin da mijinki ya tsinci kansa da yawan bukata da sai ya samu nutsuwa yake dawowa daidai"


"Eee hakane Rana daya na wayi gari naga yana yawan bukata har yakan dawo gida sau biyu haka ko sau uku"

"Dama can haka yake ko Rana tsaka ya wayi gari a haka"?

"A gaskiya ba haka yake ba dan daga ni har shi lokacin muna ta mamakin yanda akayi ya tsinci kansa da yawan bukata"?

"Kuma baki zargi ko wani abu yaci ko ya sha dayasa shi wanan bukata ba"?

"Aisha shiru tayi ta tafi tunani mintuna a tsakani tace "Wlh bazan iya tunawa ba nadai san a ranar yaci tuwo daya dawo gida daga ya Shiga sama yayi wanka ya birkice min"


"A ranar kinyi bakine kafin ya dawo"?

"Aa Luba ce dai tazo gidan a ranar Tama dage min sai ta tayani girki,baa san raina ba nabarta tayi girkin dan Salis baya yarda yaci girkin da ba nawa ba"

"Kina nufin a ranar da kika fara ganin canji a wajen mijin naki Luba ce tayi girkin da yaci batare shi yasani ba".?

"Eee a ranar ita tayi min girkin"

Ashraf ya gyada kansa cikin gamsuwa

Aisha ta hada tambayoyin da ya mata ta Kara tuna a ranar da Luba ta dage zatayi girki a ranar Salis ya canja ta gwalo ido tana kallon Luba tare da nunata da hannu tana "wlh ita tayi girkin da yaci a ranar har ya canja sai a yanzu na tuna innalillahi wa Inna ilaihi rajiun"

"Zaki iya komawa ki zauna"

Ashraf yace Yana "ya mai girma mai Sharia iya hujojin nan ya isa yasa kotu ta gane hajiya Luba tana da hannu dumu dumu a cikin abinda ya samu muhasim dan sai da taje gidan tayi girkin da shi Alhaji Salis yaci ya zama mabukaci sosai,Wanda kila tayi hakane sabida ta Kara samun damar da zai kusanceta sai Allah baiyi ba har abin yazo da tsautsayi yayiwa Muhasim fyade na biyu duk yanda take da Hajiya Aisha da sintirin da take yi a gidan ko a fuska bata tab'a nuna mata tasan anyiwa muhasim fyade har ta samu ciki ba,Kuma bata da kusanci da muhasim da har zata saki jikinta da ita ta fada mata halin da ake ciki idan ba dama duk ita ta shirya abinda ya faru ba har tasan komai sabida ta samu ya aureta,dan haka Ina rokon kotu da ta taimaka tabi wa muhasim hakkinta Luba ita tayi silar da aka yiwa muhasim fyade ta Kuma karkata mata wuya sabida Kar ta samu bakin da zata Fadi gaskiyar abinda ya faru muna rokon kotu da ta taimaka wajen tilasta mata ta fada mana abinda tayi wa muhasim ta karkata Mata wuya"

Alkali sai da ya gama rubuce rubuce ya tambayi Luba ko tana da lauyan da zai kareta ta girgiza kai akan Bata da lauya.

Alkalin ya Kara rubuce rubuce ya dago yayi bayani akan zaa daga karar zuwa sati uku masu zuwa sabida itama wacce ake kara ta samo lauyanta


Ashraf kuwa dama haka yafiso dan a zaman da za'ayi na biyu zai samo shaidar da dole asirin Luba ya tonu.

Aisha kuwa kuka ta ringa yi wiwi tana nadamar rabuwar da batayi da Luba ba a lokacin da Salis ya dage mata akan ya rabu da ita,sai a yanzu ta tuna daga lokacin da Salis yaci abincin Luba ya canja ashe duk abinan da ya faru Luba ce ta haddasa komai ashe duk abinan daya faru tafi kowa laifi tunda da ace ta rabu da Luba da bata samu damar da zatayi wa Salis abinda tayi har ya nemi muhasim ba,ta riga kowa barin kotun dan kunyar ma hada ido take da salis dan sai take ganin kamar itace ma ta jefa shi a cikin wanan matsalar.

Salis kuwa bai iya jan motar bama sai ASHRAF ne yaja motar dan bai tab'a sanin Ashe Luba ce tayi girkin dayaci har ya zama mabukaci ba,sai a yanzu ya Kara gane Luba ce ta jefa shi a wanan halin har ya nemi muhasim.

Har suka isa gida bai iya ce komai ba sai da yazo sauka ya juya ya kalli ASHRAF yana "Mahaifiyar ku itace silar da ta jefani a cikin wanan masifar wlh Aisha bata min adalci ba,daace ta rabu da Luba da kila duk ban tsinci kaina a cikin wanan halin ba"

"Abba godiya zaka yiwa Allah da gaskiya ta fara halinta nasan a yanzu hajiya umma dasu Yaya mustapha zasu gane cewar ba da gangan kayiwa muhasim fyade ba"

Salis bai ce komai ba ya fito daga motar yayi cikin gidan dan ji yayi kansa na masa ciwo.

Aisha kuwa Koda suka isa gida Yaya mustapha fada ya rufeta dashi yana duk abinan ma daya Faru ita ta jawo tafi kowa laifi dan da ace tayiwa mijinta biyayya ta rabu da luba da duk haka bata faru ba.


Lauyan gwamnati aka samowa luba da Luba ta tsara masa karya gabad'aya ta maida laifin Kan Salis ta dage akan shi ya karkata wa muhasim baki ita batasan komai akai ba ASHRAF so kawai yake ya wanke mahaifinsa sabida shi lauya ne Luba ta ringa kuka akan ya taimaka mata barrister kabeer ya Mata alkawari akan zai taimaka mata.

Ashraf shima sosai ya dage wajen Kara samo shaidu kafin ranar da zaa koma kotu.

A ranar kuwa da zaa cigaba da Sharia kotun tafi koyaushe cika Alhaji Salis na daga gaba Aisha ma gaba ta zauna wanan karon har da muhasim Suka zo da aka turo a keke"

Sai da akayi shariar mutane biyu kafin a kira shariarsu.

Luba ta fito ta tsaya a wajen da ake tsayawa zuciyarta tana Jin kwarin gwiwa zatayi nassara har wani murmushi ta ringa sakarwa Aisha da Salis da ba abinda take hangowa a idonsa sai wuta,tasan da zaa bashi dama zai iya harbeta har lahira.

Duk tambayoyin da Ashraf ya mata haka barrister kabeer ya ringa katse shi ya na kawo nasa hujojjin da "Ya mai girma mai Sharia lauyan Mai kara Yana so yayi iya k'ok'arinsa ne dan yaga ya wanke mahaifinsa ne amma babu tantama shi yayiwa yarinya fyade ya karkata mata baki sabida Kar ta samu bakin da zata tona masa asiri, wacce ake kara tasan sirrinsa ne sabida yawan sintirin da takeyi a office dinsa dan haka Ina rokon kotu da ta yiwa wacce ake kara adalci ta tilasta wa Alhaji Salis ya fadawa kotu gaskiyar abinda yayiwa muhasim ya karkata mata baki ngd ya mai girma mai Sharia

Ya koma ya zauna
Ashraf ya mik'e tsaye fuskarsa d'auke da murmushi Yana "Ya mai girma mai Sharia inaso kotu ta bani dama na gabatar da shaidar da kotu zata gamsu da cewa Wacce ake kara ita take da hannu a cikin abinda ya samu muhasim"


"Kotu ta baka dama"

Luba murmushi ta saki dan tasan ba wani shaidan da ASHRAF yake dashi.

Bakin k'ofa taringa kallo Dan taga shaidar da Ashraf yace Yana dashi.

Shigowar Asabe da mijinta Yusuf da ya ruko hannunta yasa Luba taja da baya kirjinta yayi wani irin bugawa Kamar ya fado taja da baya ta nuna Asabe da hannu tana "A!!S!!A!!B!!E ba kin mutu ba"?..........


Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne, knuckles,wrinkles,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using sabulun mg's batare da kunbukaci wani Mai b>?? Mai bukata should
Chat=?G?
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391

Team glow>???
@&?



*WANAN LITTAFIN NA KUDINE BIYA 500 TA WANAN ACCT 0272061655 WEMA BANK NAFISA NUHU KO KATIN MTN KO AIRTEL TA WANAN LAYIN 08033719070 DOMIN KI MALLAKI NAKI KI MUTANEN NIGER KUMA KU TUNTUBI WANAN LAYIN*
*+227 96 82 89 84 DUK WACCE TA MIN SHARING NA BAR TA DA* *RABBI ZAI FIDDA MIN HAKKI NA DA IZININ ALLAH DOMIN BA YAFEWA NAYI BA*


*NI DA KISHIYOYINA*

*NA SADNAF*

*PAGE 37*


"Ban mutu ba Luba Bakiso ganina ba ko?kin d'auka kin kin kasheni?toh ban mutu ba gani yau a kotu duk zan tona sirrinki da ba Wanda yasani sai ni a tunaninki tunda kin kasheni asirinki ya rufu ko? Toh gani da raina yau zan tona miki asiri asan ke wacece"

Ashraf murmushi ya saki ya nuna mata wajen da zata tsaya yusuf ya saki hannunta ta shige wajen ta tsaya tana kallon Luba da ke wani irin karkarwa har lokacin nuna Asabe take da hannu


Ashraf kuwa ya juya wajen alkali Yana "ya mai girma mai Sharia inaso kotu ta bani dama na yiwa Asabe tambayoyin kafin na mata tambayoyin inaso kotu tasan cewa ita wanan baiwar Allah da zata bada shaida akan Luba ita keda hannu a duk abinda ya samu muhasim kawarta ce Aminiyarta da tasan komai akan ta ko nace tare suke yin komai,daga lokacin da Suka fara samun sab'ani Asabe ta nuna zata tona Mata asiri shine ta caka mata wuka ta gudu, a tunaninta ta kasheta shiyasa da ta shigo ta mata tambayar dama bata mutu ba,?ko a yanzu zamu iya ganin yanayin jikin Asaben dak'yar ta samu tazo kotun dan har yanzu bata warke ba mijinta yazo mana da camera dake d'auke da yanda ta cakawa Asabe wukar ta tattara komai ta gudu iya wanan kawai ya isa kotu ta gane Luba ta wuce duk yanda ake tunani idan har zata iya kashe kawarta Aminiyarta toh ba abinda bazata iya yi ba amma inaso mu ji komai daga bakin Asaben dan ita zata warware mana komai"


"Kotu ta baka dama kayi Mata tambayoyin"

Alkali yace Yana gyara zaman gilashin fuskarsa dan a yanzu case din ya dau hankalinsa tamkar yanda Kowa na kotun ya zaku Asabe ta fara bada labari ciki kuwa har da Salis da Aisha da suke ji kamar suje kusa da wajen da Asabe ke tsaye


"Nagode ya mai girma mai sharia"

Sai da Asabe tayi rantsuwar zata Fadi gaskiya kafin
Ashraf ya nufi wajen da Asabe ke tsaye

Yace "Mallama Asabe ko zaki iya bamu takaitacen labarin yanda kuka fara kawance da Luba ya akayi kika san sirrikanta da ba kowa ya sani ba"

"Luba dai kawata ce na hadu da ita a wani biki a lokacin auren ta ya mutu Nima a lokacin nawa auren ya mutu ganin dukan mu zawara ne yasa tamu tazo daya da ita, dan yanda nake son ado da kwalliya haka take so itama haka ma yanda nake so na samu miji mai kudi na aura dan na huta itama haka ra'ayinta.

A wajenta nake yawan Jin labarin kawarta Aisha yanda take auren miji mai kudi,har take bani labarin Rabin kayan da take sakawa masu tsada na Aisha ne, ai Aishan sam bata dace da auren miji mai kudi ba dan bata da wayo ko kad'an har take fadamin yanda take rabata da abubuwa ta karfi da yaji Kuma ko nawa takeso idan har kudi ne zata d'auko ta bata,a haka tana ta kwadayin Auren mai kudi duk Kuma masu zuwa neman aurenta sai tace bataso tafison ta samu mai kudi irin mijin Aisha kawarta har take bani labarin haduwar gidan da yake ginawa da tsaruwarsa, nima nasan gidan a lokacin bansan na mijin Aisha bane ba, ita dai burinta a lokacin bataso Aisha tafita da komai, tafiso taga ma tafi Aisha ganin bata samu irin dai mijin Aishan ba rana tsaka tazo ta sameni akan ita a yanzu mijin ma Aishan takeso dan batajin zata samu miji mai kudi irinsa

nayi matukar mamakin yanda take da Aisha ace zata iya cin Amanar ta amma ban nuna mata komai ba nace mata ba haramun bane zata iya aurensa,anan take fadamin irin wulakancin da yake mata har yanda ta samu magani ta saka Masa a ruwa dan ta samu yayi amfani da ita ko Allah zai saka ta samu ciki ma ya aureta sai dai a madadin ma ta samu cikar burinta dataje office dinsa duka ta sha a hannunsa ita bata san ya zata yi ta shawo kansa ba tace ko da yanda zan iya taimaka mata ta samu ya aureta"

Shiru Asabe tayi ta

35 / 38