Nida kishiyoyina complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Romance

Chapter   16 / 38

45K to 48K   out of 111.9K words

kwaye Mata doguwar rigarta sama ya samu hanyar da yake nema Yana shiga ya samu nutsuwa Kamar Wanda ake cire masa masifar daya ke ji lokaci guda hankalinsa ya dawo jikinsa a yanda yagansa dare dare akan luba ga wandonsa a subale yasa ya dagata cikin tashin hankali Yana "innalillahi wa Inna ilaihi rajiun innalillahi wa Inna ilaihi rajiun mai kike yi a dakina mai haka"?

Luba da hankalinta ke wajen muhasim mik'ewa tayi da sauri ta rufe bakinta da hannu biyu ta fashe da kukan karya tayi waje da gudu tana Jin Salis na rafka sallati.

Ita kuwa tana sauka kasa tayi d'akin da ta tabbatar da na yaran ne dakine da suka ce na Afrah ne tasan anan Khadija yayar muhasim da muhasim din zasu kwana.

A hankali ta tura k'ofar dakinsu ta hango muhasim a can karshen gado ta kankame jikinta ta rufe idonta daga Inda take tsaye tana ganin yanda jikinta ke rawa

A hankali ta taka wajen da take sabida Kar ta tashi Afrah da Khadija da suka yi nisa a bacci ta mik'awa Muhasim hannu tayi kasa da murya tana tazo"

Muhasim hannun ta ta mik'a mata ta kama ta sauko daga Kan gadon suka yi hanyar waje

Palon suka fito ta zaunar da muhasim tare da ruko hannunta tana "Karki fadawa kowa abinda uncle ya miki kinji bashida lafiya ne shiyasa Kika ga ya miki haka ai kinsan Aljannu ko"?

Da sauri.muhasim ta daga mata kai

"Toh Aljannun uncle dinki ne ya tashi shiyasa na ya miki haka Kuma idan har Kika gayawa kowa abinda ya miki Aljanun jikinsa zasu iya kasheki dan haka karki sake ki gayawa kowa kinji"

"Bazan gayawa kowa ba"

"Yauwa karki fadawa kowa Kuma karki nuna wa uncle dinki komai karki sake kiringa nunawa kina tsoronsa idan ba haka ba Aljannunsa zasu gane wanan ya zama sirri a tsakanina dake kinji"?

"Da sauri ta gyada mata kai"

Luba ta saki murmushi tana yawa maza jeki kwanta

Muhasim mik'ewa tayi ta nufi dakinsu da saurin har lokacin a tsorace take jikinta bai bar rawa ba.

Tana shigewa ciki Alhaji Salis na saukowa cikin tashin hankali dan sai da Luba ma ta fita ya kalli jikinsa ya gane me ke faruwa yayi yayi ya tuna yanda aka yi hakan ta faru ya kasa bai ma san lokacin da muhasim ta gama rubutu ba ta fita har ya akayi Luba tasan dakinsa ta shigo har wai wani abu ya Shiga tsakaninsu ta yaya har Luba ta samu sake haka a cikin gidansa da zata na shigowa dakinsa Anya Aisha nada hankali kuwa taya zata bar Luba ta shigo masa d'aki.

Yanda ta sauka kasa Tana kuka ya Kara daga masa hankali yasan Luba mahaukaciya ce zata iya amfani da wanan damar dan taga ta tona Masa asiri wajen Aisha tunda yaki yarda da tayin soyayarta.

Yana saukowa ya ganta a zaune akan kujera ta hada kai da gwiwa

Yana waigen k'ofar d'akin Aisha ya karasa wajen Luba yayi kasa da murya Yana "Mai ya kai ki dakina"?

"Muhasim naje kira kana ganina kayo kaina har sai da ka samu abinda kakeso duk yanda naso hanaka kayi nisa ban tab'a tunanin zaka iya haka ba"

"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun wlh bansan mai ya Sameni ba bansan na aikata haka ba Anya ba wani abu Kika min ba dan haka ya faru ki samu cikar burinki tunda nace banasan ki"

"Luba wlh nasan halinki zaki iya komai Allah ya isa tsakanina dake dan a cikin hayyacina bazan tab'a haka ba"


"Wlh a cikin hayyacinka kayi komai ai muhasim ma tana ganin yanda mu ke kokawa da Kai"

Motsin da suka jiyo daga d'akin Aisha yasa Salis takawa da gudu ya haye stairs Luba Kuma ta kwanta akan kujerar ta rufe Idonta kamar bacci take a daidai lokacin da Aisha ta fito daga d'akin ta tana murtsika ido dan kamar magana take ji a palon haka yasa ta fito,Koda ta fito d'akin su Afrah ta fara lekawa ganin duk bacci suke yasa ta fito ta rufo musu k'ofar tare da nufar wajen da ta hango Luba a kwance.

Ta fara bubuga kafarta tana "ki tashi ki koma d'aki"

Luba ta mik'e tana mik'a kamar gaske tabi bayan Aisha.

A d'akin Aisha Suka kwana zuciyarta fes ta samu abinda takeso burinta Allah yasa ta samu ciki Salis bashida yanda zaiyi dole ya aureta.

Washegari duk yanda taso taga Salis bata ganshi ba bata san Aisha ta zargi komai shiyasa bata hau sama ko tabi Aisha dake ta zarya daga sama zuwa kasa.

Taci uban kwalliya da kunshi gwala gwalan da tasa sai cizon ta yake ji take dama itace a gidan a matsayin matar Salis din idan ta tuna jiya ya kwanta da ita sai taji wani farin ciki ya rufeta lafiyayen abinci suka karya dashi dangin Aisha nata sainty Luba ji take kamar ta daddana musu Ashar tafiyar da suka ki yi.


Sai da Aisha ta dafa abinci rana duk sukaci kafin su fara Shirin tafiya sai a lokacin Wata Aunty hassana Yar yayar mahaifiyar Aisha tace a Kira Salis ace mishi zasu tafi.

Luba zamanta ta gyara tana satar kallon sama taga yanda zai sauko sai dai ga mamakinta Aisha ce ta dawo hannunta d'auke da tulin kudi ta hau raba musu akan Salis yace suyi kudin mota baya dan Jin dadine da ya sauko sunyi sallama

Luba ji tayi kamar ta fashe dan bakin ciki Koda dangin Aisha ma suka watse kin tafiya tayi tana ganin ai dole dai zai sauko bazai dawwama a saman ba.

Aisha kuwa bata damu da rashin tafiyarta ba hasali ma hira kawai take mata idan kuwa ta hau sama ta dade sai Luba taji kamar ta mutu dan bakin ciki.

Bata so ta Kara kwana Aisha taga rashin hankalinta da ta Kara kwana

Wajen magriba tayi shirn tafiya cikin tsokana tacewa Aisha "Nidai bari na tafi naga kamar mijin naki yafi so yaga an watse an barku tunda yau ma gabad'aya yaki saukowa a gaisa"

"Ke Baya Jin dadi fa wlh da asuba da naje d'akin Ashe da zazzabi ya kwanaki ni bansani ba Abban Ashraf da har weekends fita yake tunda kika ga bai fita ba kema kinsan Yana Jin jiki"

"Lailai Allah ya sauwake Kya mishi sannu bari na tafi"

Aisha ta shiga d'aki ta d'auko mata kudi a cikin irin kudin da Salis ke bata da turmin Atamfa

Luba ta karba da murmushi a ranta tana fatan nan da wata shekarar itama haka zata na bawa duk wayanda Suka zo wajenta.

Lokacin ba waya ba da a ranar ta Kira Salis dan tasan yaki saukowa ne sabida ita abinda baisani ba ai dole dai yaje wajen aiki Kuma tasan wajen aikinsa.

Sai da tafin kuwa Salis ya sauko kasa dan ji yayi ya Kara tsanar Luba a jiya daya matsawa kansa da tunanin yanda akayi har ya aikata abinda ya aikata batare da ya sani ba ya gano abu aka sa Masa a ruwan daya sha har sai da ya d'auko kayan gwajinsa ya duba sauran ruwan ya tabbatar da kwaya aka sa masa ya san ba Mai yin haka sai Luba mamakin rashin kamun kanta ya kara sawa ya ji ba macen ma da baya so yaga sama da ita daga abinda ta aikata ya kara tabbatar wa Luba ma na iya Kau da Aisha dan ta samu abinda take so sai dai Aisha tayi nisa a kwance da luba ko mai zai fada mata ba yarda zata yi ba tunda bashi da hujjan da zai tabbatar mata da hakan ita dai ko Mai zai fada akan ta dan ya tsani luban ne abinda ya Kara sa masa zazzabi bai sani ba ko ya kwafsa a gaban muhasim yasan yarinya nada tsoro sai yake ganin kamar ya riketa a jikinsa duk hakan ya kara haddasa Masa damuwa dan gabad'aya yau bai ga ta biyo sauran gaishe shi ba Yana Kuma so ya tambayeta ko Luba ta karbi ruwan daga hannunta dan ya tabbatar da zargin da yake Mata.


Ko da ya sauko a saman dining ya zauna dan abincin dare zasu ci.

Aisha ke ta fama zuba abinci yaran Kuma nata surutu bai ga muhasim ba hakane yasa ya tambayi Afrah Inda muhasim take


Sai suka ce ai ta bi Aunty hassana dazu wai zata koma gida Aisha ta karbe zancen tana "Yau Kuma wulakancin ta ne ya motsa ai haka kawai ta kafe sai tabi su Aunty hassana gida wai zata dawo"

Salis yaci abincin kawai ne amma hankalinsa a tashe yake komawa gidan da muhasim tayi ya Kara tabbatar masa da akwai abinda yayi wa muhasim din kila baa hayyacinsa ba abinda zai iya tunawa kawai yasan yacemin tazo ya Kuma kankame mutum baisani ba lubar ce ko ita sai ya cije lebbensa Yana tsinewa Luba albarka yarinya da take tamkar Yar cikin sa ta jawo masa ya zubar da mutuncinsa a wajenta.


Washegari haka ya shirya ya tafi office zuciyarsa cike da damuwa Aisha ma ta d'auka duk zazzabin da yace yana yi ne.

Sosai ya shirya irin rashin mutunci da zai yiwa Luba idan tazo office dinsa dan yasan sai tazo din.

Sai dai har aka kwana biyu bai ga kafar Luba a office dinsa ba.


Sati biyu a tsakani ganin muhasim bata dawo gidan ba ga Khadija yayarta na nan yasa ya shirya ya nufi gidan su Yayan Aisha sai yake zargin Kamar akwai abinda yayi wa muhasim din bai sani ba wanan wane irin zubar da mutuncine.

Kafin ya isa gidan ya dan yi siyayyar da ya saba idan zaije.

Gidan ba bakon sa bane ba hakane yasa ya Shiga gidan kai tsaye da sallama a bakinsa.

Hada ido yayi da muhasim dake wanke wanke a tsakar gidan tayi daurin kirji.

Yanda tayi saurin sunkuyar da kai yasa Salisu yaji kirjinsa sake bugawa kasa kasa yaji tana "uncle sannu da zuwa"

Bai amsa ba ya ciki yana "Ina Aunty take"?

"Taje suna"

"Abdulrahman fa"?

"Sunje ball"

"Ke kadai ce a gida kenan"

"Eee "

Duk maganar da suke bata dago kanta ba wai kunyarsa take ji yarinyar da tana ganinsa da gudu take zuwa ta rungume shi tamkar ya ya d'auketa Luba ta jawo mai zubar da mutuncinsa a wajenta wanan wane irin abin kunya ne.

Cikin palon ya Shiga ya zauna ba dadewa sai gashi ta shigo
Tana shigowa yaganta sanye da hijabi idan a da ne ma ko a jikinta da haka zata zo ta hau masa surutu duk da wani zubin miskila ce wani zubin magana bata dameta ba

Sai da ta ajiye masa ruwa ganin tana k'ok'arin yin waje yasa ya tsayar da ita yana zo ki zauna tambayarki zanyi"

Kanta a sunkuye ta samu gu ta zauna

"Mai yasa Kika dawo gida"?

"Ba komai"

"Kamar ya ba komai haka kawai zaki dawo bayan hutunku bai Kare ba"?

"Ba komai uncle na dawo ne kawai"

"Muhasim"

Naam

Ruwan nan da kika kawo min na sha waye ya baki ki kawo min"?

"Aunty Luba ce ta d'auko ta bani akan na kawo ma"

Salis shiru ya dan yi na Yan mintuna Yana Jin wani sabon b'acin rai zarginsa ya tabbata Luba magani ta sa mai a ruwa da a yanzu ranar Aisha a dakinsa ta kwana da duk haka bata faru ba

Kamar an fusgo maganar daga bakinsa yace "Na miki wani abune muhasim"?

Sai ta dago ta kalleshi ta Kara maida kanta kasa Yana kallon yanda take ta murza hannunta ko batayi magana ba zarginsa ya tabbata akan ya mata wani abu Inda yake godewa Allah da baiyi mai gabadaya ba.

Bai ma san yanda akayi ya nemi luban ba

Sai da suka dau tsawon mintuna a haka Salis kunyar ce ta hana shi Kara magana tamkar yanda Muhasim ta tsinci kanta itama da Jin kunyarsa sabida har yanzu ta kasa manta yanda ya mata ta Kuma yarda Aljanu ne dashi amma tana tsoron ta cigaba da zama ya Kara Mata hakan dan har ga Allah tsoronsa ma take ji.

"Kiyi hakuri bansan na miki wani abu ba kinji ki hakan bazata sake faruwa ba gobe ki hada kayanki ki koma kinji"


Sai ta gyada masa Kai Salis ya mike Yana ta gayawa Aunty mamy yazo ya gaishe su basa Nan.

A takaice yanda Muhasim ta sake komawa gidan kenan tun tana dari dari har ta dawo ta saki jikinta har suka kamalla hutun su Suka koma makaranta da yake duk makaranta daya ma suke zuwa dasu Afrah Salis shi yake biya musu.

LUBA.

Tana sane ta d'auke kafarta daga zuwa wajen Salis burinta taga ta samu ciki kafin ta neme shi yanda bashida yanda zaiyi a dolensa ya aureta.

Sai dai burin nata bai cika ba da wata ya kama taga period dinta kamar tayi kuka.

A yanzu Kuma batasan ta hanyar da zata Salis ya yarda ya aureta ba tasan yanzu Kara tsanarta zaiyi tunda tasan dole ya gane cewar magani aka sa Masa a ruwa.

Dabarar da ya fado mata akan ta gwada saarta na zuwa office dinsa taga ko Allah zai dorata akansa yasa ta shirya ta nufi office din nasa koda taje bata same shi a office dinsa ba haka ta zauna zaman jiransa har ya dawo daga kallon da yake mata tasan rashin mutunci da ya Saba Mata zai mata.

Bata bari yayi magana ba ta tare shi da "Ina d'auke da juna biyu"

"Idan kina d'auke da juna biyu Ina ruwana,"?

"Ai cikin naka ne"

"Ok a lokacin da Kika saka min magani a ruwa na Sha na miki cikin ko to ba damuwa idan kin haihu ki kawomin abinda kika Haifa".& ..



Naceba=?K?
@&?
Kina bukatan jikinki yazama so fresh ba kwarzane ko daya ballantana kuraje ko tabo, sunburn,acne, ko knuckles? Kije kigwada products na mg's insha Allah zakiga ynd fatarki zedawo fiye da tsammaninki zakigyara jikinki naturally batare da kinbata fatarki ba jikinki yayi fresh kiyi smooth kizama kalar Madara kirar models kiringa walwali kina haskawa duk inda kikayi=?
?
Kidena kokonto cewa kingwada baki Dace ba insha Allah kijaraba products dinsu bi'iznillah zakiji dadinshi=?O? kayansu akwai kamshi especially sabulun kamshin yakama jikinki ko kindade da wanka jikinki zaidinga fidda ni'imtaccen kamshi bayinki ma zakiji kamshin dazai Kama=?
?sunada kit special domin amare Wanda indai kinyi using kit dinnan Baki bukatar kikara Kai kudinki gurin dilke domin ainihin yanda fatarki zehaska yagoge kidinga shining abun sewanda yagani=?
?

Mai bukatar kayan mg's chat:08062991549,07046881166,07067210195
Call:08064532391
Hausawa nacewa adade anayi sai gaskiya Kuma siyan nagari maida kudi gida>??
=??? tested nd trusted
Natural???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?/organic>?p?



*WANAN LITTAFIN NA KUDINE BIYA 500 TA WANAN ACCT 0272061655 WEMA BANK NAFISA NUHU KO KATIN MTN KO AIRTEL TA WANAN LAYIN 08033719070 DOMIN KI MALLAKI NAKI KI MUTANEN NIGER KUMA KU TUNTUBI WANAN LAYIN*
*+227 96 82 89 84 DUK WACCE TA MIN SHARING NA BAR TA DA* *RABBI ZAI FIDDA MIN HAKKI NA DA IZININ ALLAH DOMIN BA YAFEWA NAYI BA*


*NI DA KISHIYOYINA*

*NA SADNAF*

*PAGE 17*

Luba sakin baki tayi tana kallonsa Salis kuwa fuska a had'e ya nuna mata k'ofar waje Yana "Ki tashi ki bar min office Daga yau Kar ki sake zuwa office dina duk abinan da kikeyi wlh Kara tsanarki nake bazan tab'a aurenki ba Koda ba Mata a duniya ace ke kadai kika rage wlh bazan tab'a iya aurenki ba dan ke din munafika ce mai fuska biyu idan har Zaki iya cin Amanar Aisha ta hanyar saka min magani a ruwa wai dan na kwanta dake nasan zaki ma iya kasheta naso tasan wacce ke sai dai bata yarda na fada mata wacce ke duk iya k'ok'arin ta na ta kareki ne batasan ke din shaidaniya bace yanzu banda Allah ya rufamin asiri da kin cuceni kin sa na aikata abin kunya ta hanyar neman muhasim Luba kifita a harkata idan ba haka ba wlh zan baki mamaki a ranar da zan ganki a gidana zan tona miki asiri a gaban Aisha tashi kifita ki daina mafarki zan aureki wlh ba abinda zanyi dake duk ranar da kika Kuma zuwa office dina sai na saka security sun miki duka gidana ma ki rage zuwa dan banasan ganin wanan mumunan fuskar Taki"

Luba na k'ok'arin Magana yayi kanta a fusace dan wlh wani irin tsanarta yake ji har Yana Jin Kamar ya rabata da ranta.

Yanda ya harzuko yasa Luba yin waje da gudun.

Tana tafe tana sharar kwalla wahala kawai take Sha bata ga alamar Salisu zai tab'a aurenta ko ya saurareta ba Koda taje gida ji take Kamar ma ta hakura ta nemi wani mai kudin amma idan ta tuna irin d'aular da Aisha ke ciki da yanda kowa ke san rabar Aishan sabida tana da abin duniya sai taji ina bazata tab'a iya hakura ba kodan wulakancin Nan da Salis yake mata zata san duk yanda zatayi ta Aureshi hanyar da zata bi din ne bata sani ba Asabe kawar da ta hadu da ita a biki ce ta fado mata itama bazawara ce idonta a bud'e yake tamkar ita.

Da yamma ta sake shiryawa ta nufi gidansu Asaben tana zuwa ta tadata a k'ofar gida tana zance da wani kana ganinsa ma kasan mai kudine.

Shigar ma da Asabe take yi na kece raini ne da alama itama masu kudin sun tsaya Mata.

Sai da ta sallami saurayinta suka shiga gidan a tare sai da suka ci abinci Luba ta fada mata abinda ke tafe da ita da shawarar ta da take nema ko akwai hanyar da zata iya taimaka mata.

Budar bakin Asaben sai cewa tayi "Mai zai hana muje ki asirce dan banza ya aureki Ina da wani mallami ya iya aiki sosai"

"Bana san harkar mallamai dinan Asabe yanzu idan na asirce shi ya aureni ai dole watarana asirin zai karye"

"Kafin asirin ya karye ba kinsamu abinda kika Samu ba balle sabunta aiki kawai za'ayi tayi"


"Banasan asirin Asabe idan akwai wani hanya da kike ganin zan bi ya aureni ya Kuma daidaita ni da Aisha ki fadamin kawai wlh burina naga ya aureni"

"Ai daga labarin da kika bani ba wata hanya da zaki bi sama da ki asirce shi
ba ke kika gama bani labarin irin tsanar da ya miki ba"


"Tom shikenan mu gwada zuwa din mu ga idan mai yuwa ne"


Koda suka je luba ce duk ta fada masa abinda take so na auren Alhaji Salis da take so tayi,tana Kuma so ta mallakeshi sai yanda tayi dashi idan Aisha ma zata bata

16 / 38