Nida kishiyoyina complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Romance

Chapter   27 / 38

78K to 81K   out of 111.9K words

da rawar da jikinsa keyi yasa shi koma Kan gado ya kwanta ya lumshe ido Yana tuno ranar da Zainab ta fara gabatar masa da harkar da Rabin kudinsa ta nan yake samu,sai yaji dama zai iya maida hannun agogo baya da sam bai amshi tayin da ta masa ba.

"Ana samun mahaukatan kudi am telling you karka tsaya wani dogon tunani Salis,larabawan nan basuda hankali in ponds suke biya"


"Zainab wanan abin is very risk wlh har yanzu jikina rawa yake da abinda nagani bazan iya ba gaskiya wane irin rayuwa ne wanan sai kace ta dabobbi"

"Hahah nima da farko haka na ringa cewa amma bashi zaka duba ba kudin kasan mai za'ayi ni zan baka kudaden da zai fasa ma kwakwalwa Wanda duk ta haka na same su nifa badan Ina kaunarka ba wlh bazan koya ma harkar nan ba idan kana ganin dan albashin wata daya da bai Kai dubu dari Ba zai isheka kayi irin rayuwar da kake so to Shikenan sai na rabu da kai
Ta mik'e ta jawo wani akwatinta sai data ta zura hannunta ta fara fito da bandir din dalolli Salis ya gwalo ido Yana kallonta sai da ta ajiye guda goma ta rufe akwatin tana "wanan ni na baka kyautarsa a cikin irin kudin da nake samu idan har zan iya baka irin wannan kudin kasan ba kananan kudi ake samu ba ka je ka sake tunani"

A cikin irin kudin ya turo gida aka siya masa katon fili ya ringa yo aike ana masa gini.

Daga lokacin ya tsunduma kansa a cikin wanan harka a yanzu zainab din ma baya jin labarinta duk ta Inda zai sameta babu,baisani ba ko an kamata ko baa Kamata ba yasan dai ta samu wani bature ta aura shekaru goma da suka wuce.

Kiran dake shigowa wayarsa ya Kara katse masa tunanin da ya tafi ganin mai Kiran yasa yaji wani sanyi na ratsa zuciyarsa yasan tana kaunarsa fushi yasa ta bar gidan,a yanzu kuma mai haddasa masa fitina ta hana shi zaman lafiya ta bar gidan a yanzu idan Allah yasa asirinsa ya rufu a yanzu ne zai samu nutsuwar da yake so ya samu yasan tunda har Yaya mustapha ya fahimce shi zai tilastawa Aisha itama ta dawo gidansa.

Koda ya d'auka a madadin yaji muryar Aneesa muryar Hajiya Binta yaji ta ratso wayar da sallama.

Sai yaji ya kasa amsa sallamar Yana tsoron Kira tayi akan ya saki Aneesa ba dai Aneesa tana nufin ta shirya rabuwa dashi ba,sunansa da ta kira da "Salisu baka jina ne"?

Can kasan murya yace "Ina wuni hajiya"

"Yanzu haka na baka 'yata wata bakwai kawai yarinya duk ta fige ta lalace Ashe dama zuwa kayi ka hadeta cikin matan ka suke gana Mata azaba alkawarin daka d'aukar mana kenan"?

Salis bai iya magana ba dan bai san mai zai ce ba tunda har Aneesa ta iya fadawa Hajiya Binta karya da gaskiya yasan ta hakura da auren ne so take kawai su rabu tunda ya tafi watani bai bata hakkin ta ba Wanda har hakan yasa ta d'auko cucumber tana so ta gamsar da kanta.

"Ka Aiko min da takardar ta dan ta gama aurenka na Dade Ina hango Mata irin wanan ranar ta kafe ta dage ai ga irinta nan da taji wuya ta dawo Salisu ka aiko min da takardar yata nace kaji ko baka ji ba"?


"Hajiya kuyi hakuri karku yanke hukunci cikin b'acin rai inasan Aneesa itama tana sona"


"Ai bani zan raba ku ba ita da kan ta ta nemi na kiraka akan ka saketa ka saketa ta je ta nemi daidai saanta ta aura Kai Kuma kaje kaji da matan ka na baka nan da kwana uku ka Aiko min da takardar ta idan baka aiko ba idan mun had'u a kotu sai ka bata takardar ta"

Kafin yayi magana ta Yanke wayar,ya ajiye wayar a hankali yana "Allahuma ajirni fi musibati wa aklifnin khairin minha"

Kansa kamar ya fashe sabida ciwo ya rasa ma tunanin da zai yi bai san da wan zai ji ba da asirinsa dake neman tonuwa da barin Aisha gidansa ko da sakin Aneesa ta nema a wajensa.

Mik'ewa yayi daga kwancen da yake dan a yanda yake jinsa dole sai ya sha maganin bacci a bakin k'ofa suka yi karo da Hindatu taci ado sai walwali take hannunta d'auke da faranti.

"Alhaji tun dazu Ina jiran ka fito naji shiru shiyasa nace bari na biyo ka da abinci ka samu kaci ko kad'an ne"

Matsar da ita yayi gefe ya nufi dakinsa dan ko magana a yanzu Kuma baya so yayi burinsa kawai ya sha maganin da zai mantar dashi damuwar da ya tsinci kansa Yana bukatar nutsuwa kafin yasan abinda ya dace yayi babban burinsa yanzu asirinsa ya rufu gani yake komai kuma zai zo masa da sauki.

Koda ya Shiga d'akin drawer dinsa ya jawo ya deb'o magangunan ya watsa a bakinsa ya d'auki ruwa ya kora yana k'ok'arin kwanciya Hindatu da ta biyo shi har d'akin tana k'ok'arin zuba abinci ta dakatar da zuba abincin tana "Alhaji dan Allah ka sasautawa kan ka Wanan damuwar da ka sa kanka ka kwantar da hankalin ka ni nasan idan aka kwana biyu a lokacin zuciyar ta tayi sanyi ai bawa bai isa ya wuce kaddararsa ba hakuri zata yi nima so nake gobe naje na bata baki,ai yanzu matsalar ka ta kau tunda har ka rabu da luba dama itace take haddasa komai"


"Hindatu dan Allah kifita so nake nayi bacci na samu nutsuwa idan na tashi zanci abincin"

"Bari na maka tausa sai kaji dadin baccin"

"Hindatu dan Allah ki fita nace"

Hindatu harara ta watsa masa tayi waje tana "Kamar ni na aike shi yaje yayi wa Yar mutane fyade"

Taja tsaki tare da rufo masa k'ofar.


Aisha

"Yaya kai yanzu duk ka yarda da maganar da ya fada maka wlh Allah karya yake duk yanda zai Kare kansa kawai yake nema,idan har da gaske Luba na bibiyar sa mai yasa bai tab'a fada min tana bibiyarsa ba"

"Idan ya fada miki tana bibiyarsa ai ba yarda zaki yi ba sau nawa yana ce miki ki rabu da ita ko ni nan sau nawa na miki fada akan ki rabu da ita ba matuniyar arziki bace daga lokacin da mamy tace min tana zuwa aron sababin kayan ki,taya duk zai zauna ya tsaramin wanan zancen idan ba'ayi haka ba,ke naga alama bakida zurfin tunani da wayo a yanzu ma baki yarda ta saka mishi magani a ruwa ba a ranar da kuka tare"?


"Yaya duk rashin hankalina dai da yace min ta tab'a cewa tana san shi wlh dole na rabu da ita,ni a lokacin cemin kawai yake na rabu da ita baya santa bai tab'a fada min dalilinsa ba,ni Kuma a lokacin abinda yasa ban rabu da ita ba sabida ba abinda tamin, bansan ta yanda lokaci guda zance mata mu rabu ba,ni yanzu duk ba wanan ba ba maganar Luba na bibiyarsa da yanda ya aureta muke ba ya aka yi ya karkatawa muhasim wuya"?

"Daga labarin daya bani bashi ya karkata mata wuya ba dan har Qur'ani naga Yana k'ok'arin daukowa akan zai dafa na hana shi,a duk zargin da muke yanzu Luba tana da masaniya akan abinda ya samu Muhasim zata iya komai dan ta cimma burinta ni na dade ina zargin ta tun kafin ma mijinki ya aureta nasan ba dan Allah take zaune dake ba kema kinsan na sha fada miki,ki bud'e kwakwalwarki ki fadada tunanin ki ki koma baya ki duba tarayyar ku,daga lokacin da ta fara kwadayin irin niimar da Allah ya baki ya Kamata kisan cewar ba matuniyar arziki bace ba badan Allah take tarayya dake ba zata iya komai dan ta mallaki mijinki ta Kuma yi abinda zata juyashi a yanzu bamu san Wanda ya karkatawa muhasim wuya ba amma a labarin da ya bani yace Luba ita taje har office dinsa tace muhasim ce ta fada mata ya akayi duk ba Wanda yasan hakan sai ita yaushe suka yi haka da muhasim a yanzu bincike dai Ashraf zaiyi a matsayin sa na lawyer insha Allahu zamu gano idan tana da hannu a lamarin nan zan Kuma dage da Addu'a insha Allahu gaskiya zata yi halinta"

"Karki manta tunda har Salis ya saketa zataso kowa ma ya rasa ciki kuwa har dake kiyi amfani da kwakwalwarki"

Daga haka Yaya mustapha ya fice daga d'akin.

Da ido Aisha ta bishi har ya fice tana mamakin zuciya irin na yayanta har mutum ya aikata ma irin wanan zaluncin kuma wai har ka ringa k'ok'arin kareshi kwanciya tayi tana k'ok'arin ture maganganun Yaya mustapha dan Sam bataji ta yarda da Salis ba a yanzu ba abinda salis zai fada Kuma ta yarda dashi.

"Burina inga na samu miji irin mijinki tamkar dai Salisu"

"Kawata wlh baki dace da gidanan ba ni na dace da gidanan"

Maganganun da Luba ta fada mata a baya Suka ringa dawo mata, ta tuno lokacin da suka tare a sabon gida yanda ta dage bazata kwanta ba kallo zata yi labarin da Yaya mustapha ya bata ya sakata mik'ewa zaune "idan har ta saka maka magani a ruwa mai yasa baka fadamin ba"?

"Ni ko dai a ranar yayi wa muhasim fyade tunda a sama na barsu suna home work"

Ta Kara jefawa kanta tambaya tana dafe kirjinta.



Luba

Wasshh tace tana runtse idonta cikin azabar zafin daya ratsa gabanta sabida fitsarin da taje yi jiya kwana tayi tana susa har dan jini jini gabanta yayi har da kukanta.

A tattale ta fito daga bandakin ta zauna a gefen gadon tana "Allah ya tsinewa yaron nan Albarka yaron nan ya cuceni.

Wayarta ta d'auko dan ta Kara duba lokaci taga har tara ta wuce shiru Sultan bai zo ba,ita yanzu ba ta ma abincin karyawar take ba burinta kawai ya Kai ta asibiti ta samawa kanta magani dan bazata iya da wanan kaikaiyin da gambo ya samata ba.

Sai dai tana ta Kiran lambar sultan Yana ta nuna mata busy,batasan wane irin waya yake yi haka ba.

Lambar ilham ta kira sai da ta mata miscal uku kafin ta d'auka bata tsaya jiran gaisuwar ta ba dan tasan sai tayi raayi take ma gaisheta.

"Ina yayanki yake? nake ta kiransa haka Ina ta kiransa Yana waya"

"Bana gida naje makaranta"

"Ilham dan Allah ki baro makaranta kizo ki sameni kinji Yar lelena Ina bukatar taimakon ki banida lafiya"

"Mama muna da test da zamuyi Ina Bintu ta rakaki Mana"

"Ilham nifa mahaifiyarki ce kiji nace miki banida lafiya kizo ki rakani asibiti kice bazaki zo ba na Kira Bintu bansan da bintun ba na kiraki"

"Mama test ne damu da zanzo Yanzu ma ga mallamin nan ya shigo ki sake Kiran ya sultan kila ya gama wayar"

Kafin Luba tayi.magana taji ta kashe wayar.

Luba tabi wayar da kallo tana Jin wani abu na tsaya mata a kirji ta kasa yarda wai yayanta ke Neman wulakanta ta yaran da ta haifa a cikinta har gwara ma sultan da ilham,Koda ta sake Kiran sultan busy taji hakane yasa ta gane blocking dinta yayi.

Tafi minti goma tana zubar da hawaye,cikin kwana biyu ta jigata taga tashin hankali a cikin ma masu gudunta har da yaran cikinta.

Mik'ewa tayi ta had'e kafarta dak'yar dan ita kadai tasan mai take ji a kasanta.

Mayafinta ta yafa tayi waje.

Koda ta fita abin hawa ta tara ta nufi asibitin da suke zuwa dan fitowar ta tunanin haka ya fado.mata dan tasan basu san ma ta rabu da Salis ba dole su bata maganguna.

A takaice da Kuka wiwi Luba ta bar asibitin dan likita yace mumunan infection ne da ita mai wuyan Jin magani ya dai hadota da maganguna akan ta ringa amfani dashi tana Kuma zuwa asibitin a Kai akai.

Sai dai tana dawowa hotel din taga Asabe a jingine a jikin motar ta

D'auke kanta tayi kamar bata ganta ba dan a yanzu bata da k'arfin da zatayi masifa
dan a yanzu ma kaikaiyi take ji ta zura hannunta a zani tana k'ok'arin susa.

"Ke dalla dakata kike d'auke kanki kamar baki gani ba"...

*Assalamu alaikum Yan uwa Ina godiya da adduoi da kulawarku a gareni ngd kwarai Allahu ya bar zumunci na samu sauki Alhamdulillah Ina muku fatan alheri*


Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne, knuckles,wrinkles,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using sabulun mg's batare da kunbukaci wani Mai b>?? Mai bukata should
Chat=?G?
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391

Team glow>???
@&?



Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne, knuckles,wrinkles,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using sabulun mg's batare da kunbukaci wani Mai b>?? Mai bukata should
Chat=?G?
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391

Team glow>???
@&?
*WANAN LITTAFIN NA KUDINE BIYA 500 TA WANAN ACCT 0272061655 WEMA BANK NAFISA NUHU KO KATIN MTN KO AIRTEL TA WANAN LAYIN 08033719070 DOMIN KI MALLAKI NAKI KI MUTANEN NIGER KUMA KU TUNTUBI WANAN LAYIN*
*+227 96 82 89 84 DUK WACCE TA MIN SHARING NA BAR TA DA* *RABBI ZAI FIDDA MIN HAKKI NA DA IZININ ALLAH DOMIN BA YAFEWA NAYI BA*


*NI DA KISHIYOYINA*

*NA SADNAF*

*PAGE 29*

Luba cigaba tayi da tafiyar ta Asabe kuwa ta sha gabanta tana " A wane dalili zaki kira yusuf jiya a Ina kika Samu lambarsa?kin d'auka wasa nake miki ko ke a yanzu bazaki tab'a ramin kanki ba kenan?kin d'auka ni Aisha ce da zan zauna ki kwace min miji?

"Asabe dan Allah ki bani hanya na wuce banasan tashin hankali ni ba da gangan na Kira mijinki ba sultan nakeso na Kira nayi kuskure wajen kiransa"

"Wlh karya kikeyi ni inada lambar mijinki ne da zaki ajiye lambar mijina a wayarki luba banida mutunci idan kika ce zaki ja dani wlh wlh sai naga karshenki ki fito da wayarki ki goge lambar mijina a yanzu nan a wayarki ko na miki rashin mutunci ai sai ma na tona miki asiri daga nan wajen Salisun nayi duk sai na tona miki asiri idan aka kulleki zan ga da yanda zaki na yiwa mutane kwacen miji"

"Asabe ban cancanci wanan zaluncin daga wajenki ba kin kwace min dukiya kin hanani,kinsa inata garari a titi iya wanan bai miki ba sai kin hada da yimin barazana Zaki tona min asiri alhalin koma mai na aikata ke kika bani shawarar nayi haka idan har kinsan hallaci wlh baza ki min abinda kike min ba jiya da na kira yusuf bansan inda zan kwana ba bansan Wanda zai taimaka min ba baba ya rufe ido ya koreni yace bazan zauna masa a gida ba banida inda zanje , korar da Baba ya min yasa na kira yusuf jiya dan na rokeshi kudi ko zan samu na samu na iya kama wajen kwana amma bawai haka kawai na tsiri kiransa ba ko zan yiwa kowa kwace wlh Asabe bazan iya miki ba"

"Ai tunda kika yiwa Aisha ba Wanda bazaki iya yiwa ba Luba kefa kina da san kai da san zuciya halinki da nasani yasa nak'i bari ma ki zauna a gidana amma a yanzu kin dan bani tausayi hajiya Luba zan taimaka miki muje daga mota"

Ta juya Luba ta bita da wani irin kallo tana ayyana abubuwa a ranta

A mazaunin driver Asabe ta zauna Luba ta zauna a daya b'arin hannunta cikin zaninta tana susa

"Luba idan kika min akuya wlh zan miki na wuce duk yanda kike tunani zan barki ki zauna a gidana da sharadin a duk ranar da na kamaki da laifin cin amanata a ranar wlh wlh ba abinda zai hanani tona miki asiri a ranar zan miki abinda har ki koma ga Allah baza ki mantani dani ba,idan Yusuf ya dawo banaso ko motsin ki yaji har lokacin da zai fita ko haduwa bana so ma ku tab'a yi zan yi k'ok'ari naga na baki rancen kudi kije wajen Mallam ya miki aiki akan Salisu duk da kinsan zaman haramun zaku yi tunda ya riga daya sake ki saki uku idan Allah yayi kin koma zaki bani miliyan biyar kin yarda ko baki yarda"?

"Indai Mallam yamin aiki na koma zan baki miliyan bakwai na miki alkawari"

"Jeki debo kayan ki mu tafi"

"Banida wani Kaya sai na jikina ai na fada miki ba abinda nake dashi yanzu ma haka daga asibiti nake banida lafiya"

Tab'e baki Asabe tayi ta jawo murfin motar ta rufe suka dau hanyar gidanta

Luba kuwa hamdala kawai take a ranta zata biyewa Asabe ne kawai dan ta samu cikar burinta dama wajen zaman da babu yafi daga mata hankali idan Asabe tasan wata ai batasan wata ba idan takamarta mugunta zata nuna mata ko aji daya batazo ba.

Koda suka isa bayan boys quaters Asabe ta kaita tana wani huhura hanci ita a lailai ga ta zata taimaka mata tsabar wulakanci duk girman gidan ta rasa wajen da zata ajiyeta sai d'akin da tarkace ake sawa

"Yanzu zan d'auko miki katifa akwai bandaki a ciki nan dai yafi miki babu ko ni fa dan inada zuciya musulunci ma yasa na taimake ki dan ni so nayi wlh na miki rashin mutunci dazu bansan Kuma mai yasa na canja ra'ayina ba ki goge lambar Yusuf yanzu a wayarki Ina kallonki

Luba lambar Yusuf ta dubo ta haska mata kafin ta goge,duk da haka Asabe bata yarda

27 / 38