Nida kishiyoyina complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Romance

Chapter   14 / 38

39K to 42K   out of 111.9K words

komai ya daidaita sai dai abin da Kamar wuya idan ya tuno yanda suka taso Aisha na koya musu yanda zasuyi adduar tonuwar asirin wanda yayi wa muhasim fyade.

Koda ya koma d'akin Aisha a jingine ya tadata akan gado ta lumshe idonta hawaye kawai take zubarwa duk yaran sunyi cirko cirko Afrah na daga gefenta itama kuka kawai take


"Duk ku tafi ku daura alwala an fara Kiran sallah"


A hankali Suka fara ficewa daga d'akin Ashraf ya zauna a gefen Aisha tare da ruko hannunta Yana "Hajiya"

A hankali ta bud'e idonta sai Ashraf yaji ya kasa ma mata magana "Ashraf kasan wacce muhasim ko"?

Gyada Kai kawai ya iya yi

"Yar yayana Mahaifinku yayi wa fyade ta haifi Nana duk tsawon lokacin nan da nake addua Allah ya tonawa duk Wanda ya aikata Mana wanan zalincin ashe Mahaifinku ne iya fyade bai ishe shi ba sai ya hada da karkata Mata wuya da Kai Ashraf wlh wlh sai na kwatowa Muhasim hakkinta ko da zaa daure shi ne sai na yi kararsa"

"Hajiya dan Allah kibi komai a hankali wlh Abba bazai aikata haka da gangan ba dan Allah ki rufa masa sirrin nan daga maganar nan tamkar kin shafa mana bakin fenti ne gabad'aya mutunci Abba zai zube da namu uncle zai daina ganin mutuncinsa"

"Ashraf idan na tashi Kai shi kara ka hanani bai San da mutunci ba ya haikewa Yar yarinya sabida munafiki ne shi ko a fuska ban taba sani ba taya Zan kawo Mahaifinku zai iya haka wlh wlh na gama aurensa Kuma sai nayi kararsa.

Ashraf na k'ok'arin Magana Aisha ta daka masa wani uban tsawa akan ya fita ita bazata ji komai ba.

Ashraf bai tab'a ganin ta harzuka haka ba hakane yasa ya mik'e ya bar dakin Yana Allah ya Sanyaya zuciyarki.

Aisha

Nayi Sallah ne kawai amma baa nutse ba har addua nake inama mafarki nake ba dagaske Wai Salisu ne yayiwa yata fyade ba

Sai a yanzu na ringa tuna yanda hankalinsa ke tashi idan Ina tsinewa Wanda yayi wa muhasim fyade akwai ranar da na dawo daga bauchi kenan yanda na baro muhasim baki a karkace duk maganar da zaka mata sai dai ta biki da Ido sai dai a kwantar a tayar duk mai tausayi idan har yaga yanda take wlh sai ya zubar mata da hawaye da tsananin tausayin ta na dawo garin katsina har nayi girki nayi Sallah tana Raina yarinya mai kyau da hankali ji yanda ta koma bata ma tab'a d'aukar Nana ba sai dai ta bita da Ido,

Koda Salis ya dawo hankalinsa tashi yayi dayaga yanda naci kuka idona yayi ja hakane yasa ya hau tambayata mai ya faru cikin kuka nace masa "Wlh tausayin muhasim nake Abban Ashraf Allah ya tsinewa Wanda ya maida ta haka Allah ya tona Masa asiri bazai gama da duniya lafiya ba"


"Kai Kai Aisha wane irin addua kike haka Kamar ba musulma ba kiyi addua kawai Allah ya bata lafiya a cigaba da nema mata magani na me wanan manyan tsinuwar nan haba Mana kamar bakisan kaddara ba"

"Wlh Abban Ashraf har na koma ga Allah Ina addua da laanta Wanda ya mata haka haba Abban Ashraf zalincin yayi yawa dole nayi tsinuwa

Idan har zanyi tsinuwar sai yamin waazi ya hanani ko ya bar wajen ashe duk shi ya aikata laifin.

Na share hawayen da ya zubo min Yayana ya kaunaceni har a yau duk wani abu daya shafeni ba
Ya Wasa dashi shiyasa a duniyata nakesan farin cikinsa tunda wanan abin ya samu muhasim yayana ke fama da mumunan hawan jini har tsoro nake Kar watarana ya Yanke jiki ya fadi,Banda kudaden da yake kashewa wajen nemawa muhasim magani Ashe duk mijina shi ya jefa yarsa a masifa na tuna lokacin da muka je bauchi duba ta dan bana wata biyu banje ba a ranar na matsawa Salis muka je

Koda mu kaje kin Shiga d'akin da muhasim take yayi duk yanda akayi dashi ya shiga yak'i sai da mahaifiyata ta masa dagaske ya Shiga,sai a yanzu na gano dalilin dayasa Muhasim na ganinsa ta hau zubar hawaye shi kuwa ya sunkuyar da Kai Yana kwarara Mata Addu'a ita kuwa da ido kawai ta ringa binsa ni kuwa na ruko hannunta Ina "Zaki samu lafiya muhasim insha Allahu Uncle Yana ta k'ok'ari wajen nema miki lafiya kinji"

Wlh bantab'a zarginsa ba dan nayi haka tamkar nayi sabo ne ma taya zai nemi Yar cikinsa.

A zaunen da nake akan sallaya tunanin baya kawai nake tunanin daya fadomin yasa na mike tamkar iska zai d'aukeni na nufi d'akin Luba a Karo na farko a rayuwata da nasan Zan shiga dakinta akwai tambayoyin da nake so na mata tunda har tasan shi yayi wa muhasim
Fyade dole zata san Mai yayiwa muhasim ya karkata mata wuya.

A rabe na ganta a gefen gado da alama kuka takeyi Ina tura k'ofar ta mike a firgice sai naji yanzu bana Jin zafinta wlh wanan nauyin da nake ji a kirjina a duk lokacin da naganta na auremin miji da tayi duk sai naji babu.

Koda na isa d'akin zama nayi nima a gefen gadon ban kalleta ba nace "Fada min komai Luba fada min sirrikan Salisu da bansani ba tunda har kika san shi yayi wa muhasim fyade duk tsawon lokacin nan Luba baki tab'a nuna min ko a fuska ba ashe kallon shasha kike min hada Kai kikayi da salisu kuka cutar dani,iya auren cin amanar da kukayi bai isheku ba sai Kun hada kai kun cutar da yata Luba ya akayi Salisu ya karkatawa muhasim baki ki fadamin komai dan Sunanki bazai fito a shigar da karar da zanyi ba


Luba ido ta zubawa Aisha tana tunanin abinda ya dace ta fada mata a yanzu babban tashin hankalin ta rabuwa da Salis Wanda tasan wanan dole ne sai sun rabu dan haka itama zatayi duk abinda zatayi dan taga Aisha ta rabu da Salis zata Kara shafa masa bakin fenti yanda Aisha zata tsanesa gwara duk ayi biyu babu

"Kinyi shiru luba ki fadamin"


"Hmmm akwai Abubuwan da nasan idan na fada miki wlh Zaki iya yanke jiki ki fadi ba Wai iya fyade da karkatawa Muhasim Kai Alhaji Salis yayi ba da ace zaki san abinda yake aikatawa da baki zauna dashi tsawon lokacin nan ba da tuni kin Dade da rabuwa dashi dabiunsa ba masu kyau bane ko ni da Kika ga na aureshi domin biyan bukatar kaina ne bawai dan Ina sansa ba"

Tunda ta fara magana na zuba mata ido Ina kallonta kirjina wani irin bugawa yake "Kina nufin Salisu shi ya karkatawa muhasim kai da Baki"?

"Kwarai kuwa shine Kuma yana neman maza ma Salisu fasiki ne mazinaci idan har patient suka je wajen sa tsautsayi yasa yaga jikinsu sai ya kwanta dasu"


"Ya isa haka luba koma dan yankan kaine ba abinda ya shafeni ki shirya zaki min shaida a kotu"

Da sauri Luba ta mik'e cikin tashin hankali tana "Ba ruwana Aisha karki sake ki sa sunana"


Luba sai mun hadu a kotu
Na mik'e Ina Jin jiri na dib'ana Ina koma wa d'aki na janyo akwatina na fara had'a kayana.

Hayaniyar da naji a waje yasa na dan dakata da hada kayan muryar Alhaji Salis nake jiyowa da alama shi da Luba ne

"Ki fita ki bar min gida wlh ko tsinke bazaki dauka ba shegiya tsinanniya"

Alhaji salis yace Yana jan Luba dake tirjewa akan ya barta ta d'auki akwatinta da mukulin motarta

Alhaji Salis sai da ya kai ta har waje yana "nayi freezing acct dinki,na kwace motata kayan naki ma da kudina na siya filayen da kika siya da duk wata kaddara da kike takamar kina dashi na kwace sai da na fada miki idan kika tona min asiri sai naki ya tonu Luba yanda Kika dandana min bakin ciki wlh sai na dandana miki fiye da yanda Kika dandana min shegiya tsinanniya"


Luba bata iya magana ba har ya shige ta dora hannunta a ka tare da bin jikinta da kallo tanadin da tayi na duk ranar da Salis ya saketa ma bazata yi talauci ba sabida kudin da take dashi da filaye sai gashi Salis ya kwace kudin acct dinta kuwa Allah kadai yasan yawan sa dan idan tsiyarta ta motsa tatsar shi kawai take tana ya bata ko ta tona Masa asiri take zai d'auko kudin ya bata ko nawane sai gashi lokaci guda duk shekarar da ta d'auka tana tara dukiya tamkar d'aukewar ruwa Alhaji Salis ya kwace.

Ta fara bin kantamemen gidan da kallo da babu irinsa a unguwar shikenan tayi bankwana da gidan taya ma zata fara zawarci da girmanta a kuma gidan iyayenta da baifi daki biyu ba san abin duniya yasa bata iya canza musu gida ba ji take Kamar ta fasa ihu dan bakin ciki tuna ta riga da ta raba ma Aisha da Salis yasa ta fara Jin sanyi a zuciyarta tasan bayan duk maganaganun da tayi wa Aisha ba abinda zai saka ta Kara Zama dashi sai sun rabu.

Dak'yar taja kafarta ta nufi gidan Asabe ita kadai ce zata iya taimaka Mata ko da akwai aikin da zaayi akan Salis ya dawo da ita.

Alhaji Salis

Yana komawa ciki yayi kicibis da Aneesa a bakin k'ofa tana Jan akwatin ta

Wani sabon zazzabi yaji yana neman rufeshi a gajiye yace "Ina zaki Aneesa"?

"Abuja zan tafi na gaji da wanan auren tunda na aureka daga wanan masifar sai wanan ban taba samun kwanciyar hankali ba wlh nagaji ka sakeni kawai dan bazan iya ba"


Aneesa tace tana share hawayen dake zubo mata

"Baby kece yau kike cewa na sakeki"?

"Kirani Aneesa Alhaji bansan haka aurenka zai zame min ba dama mummy ta fadamin na dage sai na aureka bansan Ashe wanan tashin hankalin ta hango min ba Ashe har wata ma kayiwa ciki har da su ya wlh bazan iya ba ka sakeni kawai na tafi"

Alhaji Salis da ke jin kansa Kamar ya rabe gida biyu ya hau Jan "innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Allahuma ajirni fi musibati wa aklifnin khairin minha"


Jikinsa rawa kawai yake bai iya dakatar da Aneesa dake cewa ya Aiko Mata da takardar sakinta ba har ta fice.

Muryar Afrah dake kuka yasa yayi saurin waigawa Aisha ce janye da akwatinta hannunta cikin na Nana Afrah Kuma ta rik'e akwatin tana magiya Aliyu da Ashraf na tsaye Suma da alama rokonta suke.


A daidai lokacin da Hindatu ta fito daga dakinta tana "Ikon Allah yau Kuma a haka muka tashi Luba dai ta hargitsa gida Amarya ta tafi ga Hajiya itama zata tafi innalillahi wa Inna ilaihi rajiun


"Ki cika min akwati Afrah ki cika min nace Miki"

"Dan Allah hajiya umma ki rufa mana asiri karki tafi"

"Wlh sai na tafi banga mai hanani ba Kuna da hankali kuwa taya Zan zauna da azzalumun da ya cutar da Yar yayana wlh sai na yi kararsa an bi mata hakkinta "

Aisha tace cikin ihun kuka tare da fusge akwatin ta Ashraf na Shirin magana tace "Duk Wanda ya Kara cewa na zauna wlh sai na masa baki ku kyalleni"

Ta nufi bakin k'ofa Alhaji Salis ya zub'e a kasa Yana k'ok'arin rokonta ta tureshi tana "Wlh wlh sai nayi kararka"

"Idan kikayi haka Aisha kin tozarta yaranki zaki shafa musu bakin fenti"

ko kallonsa batayi ba tayi waje

Alhaji Salis ya runtsa idonsa ya tafi tunanin lokacin da rayuwarsa ta fara tarwatsewa...

Posting Monday to Friday nayi ne yau sabida jiya na Dora cigaba yanzu sai Monday insha Allahu

Naceba=?K?
@&?
Kina bukatan jikinki yazama so fresh ba kwarzane ko daya ballantana kuraje ko tabo, sunburn,acne, ko knuckles? Kije kigwada products na mg's insha Allah zakiga ynd fatarki zedawo fiye da tsammaninki zakigyara jikinki naturally batare da kinbata fatarki ba jikinki yayi fresh kiyi smooth kizama kalar Madara kirar models kiringa walwali kina haskawa duk inda kikayi=?
?
Kidena kokonto cewa kingwada baki Dace ba insha Allah kijaraba products dinsu bi'iznillah zakiji dadinshi=?O? kayansu akwai kamshi especially sabulun kamshin yakama jikinki ko kindade da wanka jikinki zaidinga fidda ni'imtaccen kamshi bayinki ma zakiji kamshin dazai Kama=?
?sunada kit special domin amare Wanda indai kinyi using kit dinnan Baki bukatar kikara Kai kudinki gurin dilke domin ainihin yanda fatarki zehaska yagoge kidinga shining abun sewanda yagani=?
?

Mai bukatar kayan mg's chat:08062991549,07046881166,07067210195
Call:08064532391
Hausawa nacewa adade anayi sai gaskiya Kuma siyan nagari maida kudi gida>??
=??? tested nd trusted
Natural/organic>?p?




INGANTACCEN MAGANIN SANYI TOILET INFECTION MAI WANKO DUK DATTIN MARA KOWANI IRIN SANYI NE ZAI MAGANCE SHI DAYARDAR ALLAH SHIN KINAFAMA DA RASHIN SHA AWA? RASHIN NI IMA RASHIN GAMSUWA SHIN KINYI SHEKARA DA SHEKARU KINA NEMAN HAIHUWA RIKICEWAR JINI CIWON JIKI CIWON MARA YAYIN AL ADA DUKA WANNAN MAGANIN YANA WARKARWA ME CIKI BATA SHAN MAGANIN SANYI NA 4K YAKE INA KATSINA INA AIKAWA KO INA A FADIN KASAR NAN HARDA KETARE MAZA DA MATA MAGANIN SANYI MAI GYARA MU AMALAR AURE AUNTY ZEE MOM MUJAHID
08162859027
KATSINA


*WANAN LITTAFIN NA KUDINE BIYA 500 TA WANAN ACCT 0272061655 WEMA BANK NAFISA NUHU KO KATIN MTN KO AIRTEL TA WANAN LAYIN 08033719070 DOMIN KI MALLAKI NAKI KI MUTANEN NIGER TA KUMA KU TUNTUBI WANAN LAYIN*
*+227 96 82 89 84 DUK WACCE TA MIN SHARING NA BAR TA DA* *RABBI ZAI FIDDA MIN HAKKINA DA IZININ ALLAH DOMIN BA YAFEWA NAYI BA*


*Page 15*

*Waiwaiye*

Alhaji Salis

A rayuwarsa ba wacce ya tsana Kamar Luba kawar Aisha halayen ta na san abun duniya yasa yaji ya matukar tsanarta amma ganin Farin cikin Aisha shine taga tana mu'amalla da Luba yasa ya danne tsanar da yake mata dan ya farantawa Aisha rai,ransa ya b'aci a lokacin da ya gano uban kudin da yake kashewa Aisha a siya mata sutura Ashe Luba take bawa Inda hakan yasa ranar da ya gano ya rufe ido yaci mutunci Luba a ransa Yana tunanin indai da zuciya a kirjinta dole tayi zuciya ta rabu da Aisha.

Sai dai yanda Aisha ta hana kanta walwala ta karfi da yaji har abin na Neman shafarsa yasa ya hakura yace ta cigaba da muamalla da ita.

Dama can ba wani abu dake hadasu sai gaisuwa kafin aurenta ne ma da lokacin da take da Aure suke dan gaisuwar mutunci idan ta kama su tsokani juna idan ta same shi a gida.

Abinda ya fara daure masa kai bai wuce salon da ta bullo masa dashi ba a bayan ya mata rashin mutunci ta cirewa Aisha kayanta ya d'auka ko a hanya ta ganshi ko gaishe shi bazata yi ba ga mamakinsa wata daya a t??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????sakani ranar ya dawo daga wajen aiki a gajiye yaci abinci kenan Aisha na dan mamatsa kafarsa da yaji na masa ciwo yaro ya kwada sallama a tsakar gida wai ana sallama dashi a waje iya saninsa ba wanda suka yi zai zo nemansa har ya ce yaron yaje ya tambayo mai sallama dashi Aisha tace yaje mana kawai yaga mai sallama dashi


Haka kuwa akayi ya fita waje dan ya duba mai sallama dashi

Sai dai ko da ya fita bai ga mai sallama dashi ba hasali mace ya hango nesa da gidan ta saka doguwar riga yana k'ok'arin komawa ciki yaji an Kira sunansa Inda yaji Kiran sunan nasa ya kalla yaga wajen da macen ke tsaye ne cikin mamaki ya nufi wajen da take a tsaye a ransa Yana mamakin wacce wanan

"Kece kike kirana"?

Salis yace cikin mamakin ganin Luba a tsaye

Ta sakar masa murmushi tana ""ee ni nake kiranka"

"Yaushe gidan ya zama bakonki Kuma dama idan Kika zo a waje kike tsayawa Kuma wajena kike zuwa da zaki aika a kirani"?

"Aa gidan ba bakona bane kam ba wajen Aisha nazo ba wajenka nazo shiyasa na aika a Kiraka"

"Ikon Allah toh lafiya"?

Sai ta fara susune kai Salis mamaki yasa yace "Wai kanki kalau kuwa ko Zawarci yasa kin haukace ne mai haka"?

"Hmm Salis kenan kai a rayuwarka kanaso kaga kana cin mutunci na yanzu dan na aika a Kiraka laifine gaisawa kawai zamu yi dama banaso na Shiga ciki sabida dare yayi"

Salis tsananin mamaki yasa yama kasa yiwa Luba dake ta wani karkade karkade magana

"Wai mai kake ta kallona ne"?

"Daga yau karki sake ki Kara min irin wanan haukar ana zaune kalau zaki aika a kirani mai hadina da ke zaki ce gaisawa kawai zamuyi dake Aisha ce kawarki banida hadi dake da wanan zubar da mutuncinki da kike yi da ma wajen uban yayan ki Kika koma ko Kika sake wani auren da yawon bin gidajen mutane da kikeyi kina aron kayan mutane kina sawa"

"Banida mijin Auren ai Salis shiyasa banyi ba ko zaka taimaka ka nemo min namiji mai irin sunan ka mai irin komai naka dai"

Salis tsabar takaici bai kara mata magana ba yaja tsaki tare da nufar cikin gidan ya shige yana mamakin abinda Luba tayi da ya kasa gane mai hakan ke nufi

Koda ya shiga bai damu da ya fadawa Aisha ba dan yasan ko ya fada mata ma ba jawa Luba kunne zatayi ba tunda bata san abinda zai hadasu.


A yau Yana zaune a office wata Zainab ta budo kofar ta shigo kawarsa ce Kuma tsohuwar budurwarsa da suka had'u a kasar waje haduwar sa da ita a waje ta koya masa mumanan dabiu rashin mata a kusa yasa ya fara biyeta suna watsewa ita ta kwadaita masa san yaji yana san ya ringa sanin taste din mata daban daban ta kara da dora shi akan wani harka dake mugun shigo masa da kudi mumunan dabiar da ya koya a waje Kuma sirrinsa da bayaso kowa ya taba sani,har ya kusa gama abinda ya Kai shi can Yana tare da Zainab ba Kuma iya zainab din ba yana neman wasu ma, ganowar da Zainab tayi Yana tsalle tsallen yasa suke yi wani irin fada gata da tsananin kishi duk a tunanin ta bashida aure ta Kuma d'auka zai Aureta din.

Sai da ya kusa dawowa Nigeria ya fito ya fada mata yana da Aure bazai iya aurenta ba.

Kaca kaca suka yi da ita har ya dawo gida Nigeria da kudurin tunda ya dawo wajen iyalinsa zai ajiye wanan halin nasa cikin kudura ta ubangiji Kuma tunda ya dawo bai Kara Neman kowace mace ba duk da wani zubin idan patience

14 / 38