Nida kishiyoyina complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Romance

Chapter   29 / 38

84K to 87K   out of 111.9K words

yanzu kayi yanda zakayi a bada belina muje daga gida tukunna zan gaya maka komai"

Ashraf sai da yayi dagaske Suka bada belin Salis sabida yaje musu a matsayin lawyer Salis.

Koda suka d'auko hanyar gida ba Wanda yacewa wani komai Salis kuwa rufe idonsa kawai yayi Yana Jin inama duk abinan dake faruwa a mafarki ne,a lokaci guda duk asirinsa ya tonu.

Yanda zai bawa Ashraf labari kawai take tunani yanda zai samu ya wanke kansa daga zargin da ake masa kawai yake dan sauran dan mutuncin nasa daya rage idan har labarin zargin da ake masa ya fita yasan zub'ewa zaiyi a idon kowa har gwara.masa ma fyaden muhasim da wanan abun kunya da Allah wadai dake neman samunsa.

Dana sani keya ce Allah yasan yayi matukar nadamar halin daya jefa kansa zai iya cewa san zuciya ya kai shi tunda Yana dan samun na rufin asiri ta harkar Ngo din da yake zainab da dage ta ringa kwadaita masa har sai da ya tsunduma harka Yama fita zakewa a harkar.

Koda suka isa gida d'akinsa ya shige sai yaji Yana Jin kunyar Ashraf Mai yasa bai tab'a tunanin irin wanan lokacin na zuwa da asirinsa zai tonu yaji kunyar mutane da na yayansa.

Sallah kawai yayi ya kwanta baisan Kuma binciken da za'ayi iya wajen da zai tsaya ba,baisan ya akayi har aka gano su ba.

Shigowar Ashraf d'akin yasa yayi saurin maida idonsa ya rufe Yana jinsa har ya zauna yasan kallonsa yake tsawon mintuna biyar a tsakani Ashraf ya fara magana yana "Abba inaso ka bani labarin sirrin da kake boyewa da har ta Kai da asirn ka ya tonu da tun farko ka fadamin da kila na samu maka hanyar da asirinka zai rufu Abba lokacin boye boye ya wuce ka fadamin kawai iya gaskiyar ka ni lawyer ne zanyi iya k'ok'arina domin na kareka duk da nayi rantsuwa akan goyon bayan gaskiya duk runtsi duk wuya amma babu yanda zanyi tunda rufin asirinka rufin asirin mu ne gabad'aya"

Ajiyar zuciya Salis ya sauke kafin ya bud'e idonsa ya sauke akan Ashraf cikin wani irin murya ya fara bashi labari


Waiwaye

Da Zainab kawai yake muamalla a lokacin dayaje waje karatu,hasali ma zai iya cewa ita ta makale mishi duk da kana ganinta kasan kudi ya zauna mata a matsayinsa na dalibi haka take kashe masa kudi,kamar bata san ciwon kudin ba har yakan yi mamakin yanda take samun kudin,dan a labarin da ta bashi Iyayenta sun rasu ba kuma samari yake ganinta dasu ba ballantana ya zargi ko su ke.kashe mata kudi,abinda ya kara daure masa kai ba iya shi kadai take kashewa kudin ba duk wayanda take mu'amalla dasu suna morarta,abinda ke dan daure masa kai bai wuce yanda take muamalla da mata da yawa a wata Kuma zatayi tafi kasar Dubai sai ta kwana biyu kafin ta dawo.

A lokacin da tayi tafiya salis Kuma ke samun damar da zaiyi nashi tsalle tsallen dan a gidanta ma yake zaune.ita ta sabar masa da wani irin rayuwa na san Mata.

A irin wanan lokacin ta dawo daga tafiya Yana makaranta yana dawowa ya tarar da ta dawo.

Da niki nikin akwati sai da suka samu nutsuwa da juna suna hira yake tsokanarta da Ina tsarabar da ta yo mishi dariya ta saka masa tana ba ta kawo.masa wani tsaraba ba shi kuwa ya mike yana bata isa ba baiyi wata wata ba yayi wajen akwatin nata ya fara k'ok'arin bud'e k'aramin.

Kafin ta taso har ya bud'e akwatin

A tsorace ya mike tsaye Yana gwalo idonsa waje dan.tunda yake bai tab'a kudi mai yawa haka ba,ita kuwa ta karaso ta rufe akwatin tana dariya yanda ya zaro ido.

A ranar ya kasa hakuri har sai da ya tambayeta da Ina take samun kudi haka?

Tace mishi ya bata lokaci zai fada mata idan shima yanaso ya zama mai kudin duk zata nuna masa hanya.

Haka ya ringa naci Yana binta dan ta fada masa Inda take samun kudin amma tana kakaucewa a karshe da ta gaji da nacinsa ta masa alkawarin tafiya dashi.

A haka watarana ya shirya yabi Zainab zuwa dubai,a nan ya gano kazamin rayuwar da Zainab take kudi ke shigo Mata,ita ke nemo wa larabawan masu kudi Yan mata da suke muamalla dasu,muamallan ma irinta da dabobbi su Kuma su biyata ita Kuma ta biya yan matan.

Larabawan basu dauki bakakken fatan a bakin komai ba dan ba iya amfani suke dasu ta baya ba har idan zasuyi ba haya ko wani abu a jikin matan sukeyi da suka zabi neman kudi ta karfin tuwo zainab bata tsaya iya nan ba ta hada da muamalla da miyagun kwayoyi.

A ranar salis bai iya bacci ba sabida tashin hankali ya kasa yarda da irin rayuwar da yaga masu kudin nayi da yan matansu bak'akk'en fata wani ma bashi ke amfani da macen ba karensa zai samowa mace lafiyaye shi ma yaci dadinsa da mutum.


Har suka dawo zainab bata gane kansa ba dan shi dai abinda ya gani ya daga masa hankali daga labarin da Zainab ke bashi tana safarar Yan mata da kwayoyi ta kaiwa larabawan nan su bata kudi,tana nunawa Yan matan taimakon su zatayi da hanyar nema musu aiki ko wani abu basa sanin ainihin aikin da zasuyi sai idan ta Kai su.

Ta Kara da "sabida kaunar da nake ma na gwada maka hanyar da nake samun kudi,aikin likita ko wani abu ba inda zai Kai ka idan dai har kana so kayi mugun kudi sai ka hada da wanan sana'ar da nake da ke shigo min da kudi kafara da safarar cocaine sannu a hankali idan ka koma kudi sun zauna maka sai ka fara hadawa da wanan da shi yafi shigomin da kudi"

"Zainab bazan tab'a iya wanan sana'ar ba har yanzu da nake zaune Ina ta mamakin abinda na gani wanan wane irin rayuwa ne sai kace ta dabobbi Ina ma zan samo mutane Kai bazan iya ba harkar cocaine dinan akwai hatsari"

Murmushi zainab ta masa a ranar ta Masa kyautar daya kusa fasa masa kwakwalwa tuni yaji tunaninsa ya rabu gida biyu duk da bai ji zai iya ba haka zainab ta ringa kwadaita masa da kad'an kad'an ya fara harkar cocaine din har shima kudade suka fara shigo masa ta hada shi da masu kudin gaske.

A haka watarana zainab ta kamashi da wata kawarta sukayi kaca kaca da ita dan har maganar Aure take masa wanda ko mahaukacin Kare ne ya cije shi ba abinda zaiyi da ita.

Koda ya dawo gida Nigeria a haka ya cigaba da sana'arsa a boye ba Wanda yasani da larabawan nan da Zainab ta hadasu,a hankali suka fara masa maganar ya musu hanyar da zai na turo da Yan mata da samari zasu rubanya kudin da suke bashi.

Tuni ya fara tunanin ta yanda hakan zai yu batare da an tab'a gano shi ba hakan yasa ya Nemo wata Hajiya fauza wata bazawara ya bata wanan kwangilar akan ta ringa musu hanyar zai na bata manyan kudi.

Ita ta bashi shawaran ya bud'e gidan marayu su fake da taimakawa marayu da marasa gata idan yaso sai su fake da turasu kasar waje karatu suna turasu wajen larabawan.

Da haka Salis ya hada kazaman Sanaa guda biyu idan Suka tura Yara waje da Sunan karatu wajen hajiya jidda da ta silar zainab yasanta a wajenta yaran ke sauka ita ke musu aikin daga can shima Salis na biyan ta John ke jigilar kai su yaran da suke kaiwa basa tab'a sanin ba karatun aka tura su ba sai sunje daga can shima sai an kwana biyu.

Shi dai Salis direct shi ake turowa kudin.

Kasa bud'e idonsa yayi a lokacin da ya gama bawa Ashraf labari Yana Jin Ashraf na sheka sallati shi kansa a zaunen da yake ji yake kamar kasa ta bud'e ya shige sabida kunya taya zai so mutane su san ba dan Allah ya bud'e wanan gidan marayun ba sai a yanzu yake matukar nadama da bai tsaya iya safarar cocaine din ba.


Fitar Ashraf daga d'akin da karar rufe masa k'ofar da yayi yasa ya bud'e idonsa a hankali yasan a yanzu Ashraf ya tsane shi sai yaji Kuma Yana daya sanin bashi labarin.


Luba

Bata tab'a zuwa Lagos ba tasan dai garin akwai nisa ba kadan ba tun tana kalle kalle tana tunanin sun kusa isa Lagos har sai da tazo bacci ya d'auketa a motar karar bindiga da taji kamar a mafarki yasa ta bud'e idonta hankalinta a balain tashe duk fasanjojin motar su rude da ihu motarsu zagaye da kattin maza duk hanunsu rik'e da manyan bindiga har wasu ma sun shigo cikin motar duk fasinjojin sun durkusa akan gwiwarsu sun daga hannayensu sama yanda Luba taga sunyi itama haka tayi tana sallati tana "Allah karka Basu ikon ganin akwatin nan Allah ka rufamin asiri iya kudin nan da gwalagwalan su kadai nake dashi ya Allah ka rufamin asiri"

Bata ma san a fili take adduar tana kuka ba sai da suka dora mata bindiga aka tayi saurin yun shiru suka cigaba da caje motar tsabar bata san ma a rabata da akwatin Bata yarda sun ajiye mata boat ba agaban ta ta ajiye akwatin.

Jikinta rawa kawai yake a lokacin da suka fara k'ok'arin jan akwatin a sabida dukiyar nan ta kashe Asabe taya lokaci guda zata bari su rabata dashi.

Rik'e akwatin tayi tana "Kumin rai dan Allah na baku Rabin kudin nan karku rabani da akwatin nan" na!!!

Gindin bindigar Suka buga Mata akai bata Kara sanin Inda kanta yake ba,bata san tsawon lokacin da ta d'auka a sume ba sai da ta farfado ta ganta a wani waje kamar tasha idonta ya sauka a saman rubutun da akayi a wajen da take zaune this is Lagos shine your eyes"

Zumbur ta mik'e ta fara dube duben akwatin ta har lokacin a cikin motar take amma ita kadai ba kowa da alama sun iso Lagos din.

Ihu ta kwalla tana "Ina akwatina"

Wani wada ne ya leko motar da broken yace "you Don wake up" (kin tashi"

Since yesterday we Don reach Lagos since you Don wake up come down come dey go your house (tun jiya muka iso Lagos tunda kin farka sauko ki tafi gidanki)

"Ina jakata"?

Luba tace a haukace tana cigaba da dube duben motar ko ciwon da taji kanta nayi bataji ba haukace musu tayi da kuka da ihun sun bata Jakarta ita bazata sauka ba.

Tuni mai motar ya watso da ita daga motarsa wayarta ma sun d'auke hannu ta dora aka ta fara kuka wiwi tana asirinta ya tonu...


Naceba=?K?
@&?
Kina bukatan jikinki yazama so fresh ba kwarzane ko daya ballantana kuraje ko tabo, sunburn,acne, ko knuckles? Kije kigwada products na mg's insha Allah zakiga ynd fatarki zedawo fiye da tsammaninki zakigyara jikinki naturally batare da kinbata fatarki ba jikinki yayi fresh kiyi smooth kizama kalar Madara kirar models kiringa walwali kina haskawa duk inda kikayi=?
?
Kidena kokonto cewa kingwada baki Dace ba insha Allah kijaraba products dinsu bi'iznillah zakiji dadinshi=?O? kayansu akwai kamshi especially sabulun kamshin yakama jikinki ko kindade da wanka jikinki zaidinga fidda ni'imtaccen kamshi bayinki ma zakiji kamshin dazai Kama=?
?sunada kit special domin amare Wanda indai kinyi using kit dinnan Baki bukatar kikara Kai kudinki gurin dilke domin ainihin yanda fatarki zehaska yagoge kidinga shining abun sewanda yagani=?
?

Mai bukatar kayan mg's chat:08062991549,07046881166,07067210195
Call:08064532391
Hausawa nacewa adade anayi sai gaskiya Kuma siyan nagari maida kudi gida>??
=??? tested nd trusted
Natural/organic>?p?


Ayiri yiri =???=???=???=???=???kuna Ina mata matafa nake nufi bamuna mataba =??=??A&Z COLLECTION takawomuku ingantatun supplement=?G?=?G?=?G?=?G?
Muna da supplement na Infection
Munada da supplement na gyaran jiki Wanda zaisa jikinki yayi kyau fata tai laushi da sheki >?p?>?p?>?p?munada na gyaran breast succiko su tashi tsaf gwanin Sha awa>?p?>?p? munada na matsi dazai matsaki ciki dawaje bawai ki iya farkoba kuma yasaukarmiki da ni ima
Muna da na gyaran gashi Wanda zaifitomiki da gashi =?
?=?
?
Dawanda zakiyi haske duka jikinki bawai fari na bleaching ba =??=??

A&Z dealer ce kayanmu suna da sauki sosai price dinmu price din sari ne zaki samu kayanmu cikin sauki alhmdulillah=???=???=???=???
Ga kadan daga ciki

1 Royal jelly karami 2500
2 Juliet Eve 8500
3 Amirna 8k
4 Vitamin c 2500,2300
5 vt e 2k
6 collogen + glutathione 2k
7 whitening gummies 2200
8 surga wanita 2500
9 khusus 3500
10 majakani 2500

Price din sari=?F?=?F?=?F?=?F?nasan kodaga haka zaku gane A &Z gidan sauki ne=???=???=???=???=???=???=???=???
Masu siyan daidai kuma bambancin kadanne

Muna garin Kano Dan neman Karin bayani Kira ko whaspp 09037870422

Karku manta muna tura Kaya duk garin dakuke inkiyi siyayyama dayawa muyi Miki free delivery =???=???=???yan Kano kayanku har kofar gida cikin aminci>??>??>??



*WANAN LITTAFIN NA KUDINE BIYA 500 TA WANAN ACCT 0272061655 WEMA BANK NAFISA NUHU KO KATIN MTN KO AIRTEL TA WANAN LAYIN 08033719070 DOMIN KI MALLAKI NAKI KI MUTANEN NIGER KUMA KU TUNTUBI WANAN LAYIN*
*+227 96 82 89 84 DUK WACCE TA MIN SHARING NA BAR TA DA* *RABBI ZAI FIDDA MIN HAKKI NA DA IZININ ALLAH DOMIN BA YAFEWA NAYI BA*


*NI DA KISHIYOYINA*

*NA SADNAF*

*PAGE 31*

Luba

Ba Wanda ya bi ta kanta haka aka ringa wuceta tana kuka wiwi sarkokin asabe sun kai guda biyar da ta d'auka ko iya su kawai sun isheta rayuwa kudi kuwa zasu yi Dubu dari shidda sabida kudin ta kashe Asabe sai gashi tashi daya barayi sun rabata da komai daga ita sai hijabin jikinta da atamfar jikinta,duk kukan da take tana birgima ba Wanda ma ya tsaya ya tambayeta mai ke faruwa ballantana ta sa ran zata samu taimako a wajen wani, hasali ma wani ma tsawa ya daka mata a akan ta koma gefe ta zauna a bakin hanya da ace tasan haka legas yake da bata soma zuwa ba da tasani ma Abuja ta tafi,wanan wane irin rashin saa ne.

Haka ta koma gefe tana cigaba da kuka da kalle kalle bata San daga Ina zata fara ba wajen wa zata dosa ba wanda ta sani a Legas ballantana tace zataje ta nemi taimako Rabin mutanen ma da take gani duka yarabanci suke sai turanci,bata ga alamar bahaushe dan uwanta ba.

Tsawon awa shidda tana zaune ga kaikaiyin da ya dameta,ga mugun ciwon Kai,sai a yanzu take nadamar ma kashe Asaben da ta sani ta rufawa kanta asiri ta cigaba da mata wanke wanken tana jurewa,da ta sani ma iya kudin ta kwashe ta kulle Asabe a bandakin da kila duk bata tsinci kanta a cikin wanan balain ba.

Mik'ewa tayi tana cije lebbenta sabida kafafunta da taji suna mata ciwo zaman waje daya bazai kareta da komai ba gwara ta bazama neman taimako ko zata dace.

Fitowa tayi daga tashar tana cigaba da dube dube garin Legas din ma a hargitse ta ganshi kowa ta kansa yake tasan da ace wani garin taje da an samu mutanen da zasu tambayeta Mai ya sameta take kuka haka.

Tafiya kawai take batasan ma Inda zata dosa ba motoci da babura ma kamar sunfi mutane yawa haka take gani.

Wani waje ta hango da ake siyar da abinci ta nufi wajen tana Addu'a Allah yasa bahaushiya ce mai wajen,Koda ta isa da muryarta data dashe ta hau sallama.

Sai dai ba Wanda ma ya dago ya kalleta Yan Mata ke ta kaiwa suna kawowa da abinci suna sallamar mutane duk da ga shigarsu tasan ba hausawa bane ba Kuma musulmai bane dan guntun skirt suka saka.

Sai da ta Shiga ciki daya daga cikin Yan matan ta waigo tana tambayarta mai zaa bata da harshen turanci.

Luba bata iya turancin sosai ba amma duk abinda zaace tana ji "Taimako nake nema Dan Allah Ina Mai wajen take"?

Wani irin kallo yarinya ta mata da tasan ilham yarta ma zata girmeta

Da turanci tace mata idan ba abinci zata siya ba ta fita ta bata waje ta barta a tsaye.

Duk abinan wayanda suke wajen suna cin abinci ba Wanda ya dago wai ya kalleta ballantana su san taimako take nema Kuma ko magana zasuyi yarabanci sukeyi.

Tana ji tana gani Yan matan nan suka koreta gashi magriba ta kawo kai yanzu ta inda zata kwana kafin ta san nayi take dan legas ba wajen zamanta bane gwara ta nemo taimako ta koma wani garin dan bata Isa ta doshi bauchi ba.

Gajiya tayi da tafiya kukan ma ta gaji da yinsa bata ga alamar akwai Wanda zai taimaka mata ba hakane yasa ta Kara samun waje ta zauna ta buga tagumi.
Minti talatin a tsakani taji wani dan acaba da ya sauke fasinja a gefen titi yayi magana da hausa.

Wani irin mik'ewa tayi ta nufi wajensa da mugun gudu,dan k'ok'arin tayar da machine yake.

Zubewa tayi a gabansa tana "Ka taimaka min dan uwa ni bakuwa ce bansan kan garin nan ba Ina hanya zanzo Yan fashi suka taremu sai da suka kwace komai a hannuna hatta wayata sai da suka rabani dashi basu barni da komai ba ka taimaka min na samu wajen da zan kwana kafin na samu kudin da zan koma garin mu tunda safe nake bulayi a garin nan ina neman musulmi bahaushe da zai taimaka min dan uwa dan Allah ka taimaka min"

"Ke mai kika zo nema a garin Legas kinsan legas kuwa"?

"Tsautsayi dan uwa tsautsayi ya sakani zuwa duk dukiyata na tattaro na taho da zumar na zo na ringa kasuwanci sai gashi duk sun rabani da komai ba Wanda nasani a garin nan ma ballantana naje ya taimaka min nidai dan Allah ka taimaka min"

Shiru dan acaban yayi yana karewa Luba kallo Luba kuwa ta cigaba da magiya

"Ya isa haka ba taimaka miki ne bazan ba wlh bansan inda Zan kai ki bane dan nima maneji nakeyi da wani abokina a shago daya shirun da kika ga nayi inata nazarin Inda zan Kai ki ne kafin ki san nayi"

"Nidai ko Ina ne ni ko zaure ne zan kwana"

"Toh shikenan ki hau mu tafi akwai wata bayarabiya da nake kaiwa kasuwa muna mutunci da ita sosai bari na Kai ki wajen ta ko zata barki ki kwana"

Luba mik'ewa tayi da sauri ta haye machine din ya jasu suka tafi.

Tafiyar mintuna suka iso wani gida unguwar ma gabadayan ta sai a hankali ba wani gidan arziki a wajen Luba kalle kalle kawai ta ringa yi.

Koda ya sauka shi kadai

29 / 38