Nida kishiyoyina complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Romance

Chapter   37 / 38

108K to 111K   out of 111.9K words

abinda muke so ya mana take ya nuna mana da hatsari alluran dan Yana iya zuwa da karar kwana,take naji hankalina ya tashi dan idan har muhasim ta mutu bazan tab'a samun cikar burina ba,sai da yace zai nemo Wanda bashida k'arfi sosai dan ba'a samun sa anan sosai kafin na yarda akan za'a mata alluran duk da a tsorace nake Asabe haka ta ringa zugani,kwana biyu a tsakani Dr Saeed ya aiko ghali akan ya kawo mana alluran baya gari yayi tafiya.

Ghali shine saurayin Asabe.

A lokacin ma Ghali muka so ya mata alluran yace bazai samu zuwa a ranar ba hakane yasa Koda na yaudari muhasim.akan tazo zan taimaka mata Asabe ce tace min zata iya mata alluran.

Washegari da sassafe muhasim taje gidansu Asabe da kwatancen da na mata,dama ta riga ta hadani da wani mai abin hawa na biyashi akan ya jiramu a bayan gida,a lokacin da muhasim tazo sai naji Kuma hankalina ya tashi dan Ina tsoron ta mutu ba Kuma wai dan Zan damu da mutuwarta ba sai dan burina da bazai cika ba.

"Wlh wlh da Asabe ta bani alluran ban iya mata ba rufe mata baki nayi da hannu daya na danne ta Asabe tazo ta danna Mata alluran a wuyanta sai da ta karar da ruwan ta zare daga wuyanta,bani na mata alluran ba nidai na rike muhasim anyi mata alluran,tare muka kinkimi muhasim muka kai ta mota,na hau muka je muka jefata a bayan makaranta,Asabe Kuma itace ta kashe kishiyarta Rabi ta hanyar saka mata guba ghali shine ya hada alluran guban,yanda na ringa muamalla da Saeed da aurena haka take muamalla da ghali wanan shine iya gaskiyar abinda ya faru"


"Wlh karya take min bani na mata allura ba ni bansan wani ghali ba"

Asabe tace hankalinta a tashe Yusuf mijinta kuwa sallati kawai ya ringa kwadawa da k'arfi yanda Ya ringa k'ok'arin yin wajen Asabe yasa Yan sanda sukayi waje dashi.

Ashraf ya kalli Luba Yana "Yanzu Ina shi Dr Saeed din yake"?

"Bansan Inda yake ba dan gaskiya bana Jin Yana shigowa Nigeria yanzu dan indai ya shigo sai ya kirani mun had'u"

"Dagaske ne Bintu kawai ce diyar Alhaji sauran yaran naki na Dr Saeed ne"

"Gaskiya ne Abdul da khalifa ba yaran Alhaji Salis bane yaran Dr Saeed ne"

Gyada kai Ashraf yayi ya kalli Asabe da ta fara kuka dan tasan aurenta ya gama mutuwa idan ba'ayi Wasa bama yau sai an kulleta.

"Hajiya Asabe ko kina da abin cewa"?

Shiru Asabe tayi batayi magana ba

ASHRAF ya juya
wajen alkali yana "Ya mai girma Sharia inaso kotu ta bani dama zanyi wa dayan shaidan nawa tambayoyi"

"Kotu ta baka dama"

"Nagode ya mai girma mai Sharia"

Ashraf yace tare da juyawa wajen da Ghali ke tsaye yana "bawan Allah ko zaka iya fada mana sunanka da dalilin daya sa kazo kotu"?

"Sunana Ghali Usman nazo kotune sabida na Fadi iya gaskiyar abinda na sani Ina Kuma rokon kotu da ta taimaka tamin afuwa nasan nayi kuskure

"Da kyau Mallam Ghali wa ka sani a cikin hajiya Luba da Hajiya Asabe?

"Nasan duka su biyun"

"Mai alakarka dasu"?

"Kamar yanda Luba ta fada ni saurayin Asabe ne abokina ne saurayin luba"

"Ina shi abokin naka yanzu"?

"Allah ya masa rasuwa wata hud'u da suka wuce"

"Dagaske ne Kai ya bawa allura ka kaiwa luba"?

"Eee ni ya bawa ma akan na mata alluran dan a ranar zai bar gari nima a lokacin sai wani uzuri ya tasomin sai nace musu bazan samu na mata alluran ba sai dai su nemi wani ya Mata"

"Kishiyar Asabe da ta rasu ta hanyar shan ruwan shayi dagaske ne kaine ka Kai mata gubar da ta saka mata"

Sai daya dau tsawon mintuna Ashraf ya sake maimaita tambayar Ghali ya gyada kansa yana "ni na Kai Mata gubar bansan kishiyarta zata kashe ba"

ASHRAF wajen Asabe yayi da jikinta kawai ke rawa yace "Hajiya Asabe kince badake aka yiwa muhasim Allura ba gashi Saurayinki yace dake aka yiwa muhasim Allura,Kuma kishiyar ki rabi da ta rasu ke kika saka mata guba a cikin shayi ta rasu,kin aikata haka ko baki aikata ba"?

"Wlh sharri suke min dama Luba tayi alkawarin sai taga bayana ita taje ta biya wanan mutumin yazo yamin sharri amma ni bansan komai ba"


Murmushi Ashraf yayi Yana "Ba Luba ce ta biya shi ba a binciken da na ringayi na nemo shi ko a yanzu yana hannun Yan sanda"

Asabe wani irin ihu ta saka ta yanke jiki ta Fadi a sume"

Ashraf kuwa ya juya wajen alkali Yana "Ya mai girma mai Sharia daga shaidun da na gabatar gaban kotu ya Isa ya gamsar da kotu akan Luba itace silar jefa muhasim a cikin wanan halin tamkar yanda ta amsa laifinta da bakinta,tare suka hadu ita da kawarta suka zalunci muhasim suka kassara mata rayuwa shekara goma Sha shidda tana nan akan keke sai yanda akayi da ita,Ina rokon kotu da ta Yanke musu hukunci daidai da laifin da suka aikata nagode ya mai girma mai Sharia.

Daga Haka Ashraf ya koma ya zauna alkali rubuce rubuce yayi ya dago yana "Ko lauyan mai Kare wacce ake kara Yana da abin cewa"?

"Banida abin cewa ya Mai girma mai Sharia"

Barrister dake Kare Luba yace tare da komawa ya zauna.

Luba kuwa sai a lokacin taji hawayen nadama ya wanke mata fuska jiki a sanyaye ta kalli wajen da Aisha ke zaune da idonta yayi jajjur sabida kuka, ta kalli Salis dake tsaye shima idonsa ya Kada yayi ja daga irin kallon da yake mata tasan da zaa bashi bindiga tsaf zai harbeta,a hankali ta ringa bin mutanen kotun da ido,ba wani jininta dake cikin kotun tsabar bakin halinta,ba mai yarda tana da d'a kamar sultan Koda Wasa bata tab'a hararowa kanta irin wanan ranar da zata tsaya a bainar jama'a ta tonawa kanta asiri har mutane su san abinda ta aikata ba,abu dayane yanzu ya Sanyaya mata zuciya Asabe da ta saka duk ta aikata abinda ta aikata a tare zaa musu hukunci,muryar alkali ne ya katse mata tunanin da ta tafi ya daga zaman kotun zuwa sati biyu mai zuwa a ranar zai yanke musu hukunci ya bada umarni a kama Asabe itama a kulleta,Asabe da ta fafado daga sumewar da tayi ihu tasa tana tirtirjewa a lokacin da Yusuf ya wurga mata takardar sakinta a daidai lokacin da aka saka mata ankwa,aka tasa keyarsu akayi waje dasu.

Ashraf kuwa fadar farincikin da yake ciki b'ata bakine,dan shi yasan bak'ar wahalar dayasha kafin ya iya gano Asabe da Ghali,Yaya mustapha fa kuwa wajen Salis yayi da har lokacin hawaye bai bar zubar masa ba ya dafa kafadarsa yana "Kayi hakuri kaddara ta riga fata Allah ya riga ya rubuta hakan sai ta faru,da ace Aisha ta rabu da Luba tun a lokacin da ka nemi ta rabu da itan da duk haka bata faru ba Aisha ta d'auka yanda zuciyar ta take haka na luban yake bata san ba komai a zuciyarta ba sai sharri"

"Wlh Yaya sai inda karfina ya Kare sai na tabbata anyi mata hukuncin mai tsauri ta cuceni ta zalunceni Ashe shegu duk ta ajiye min a gida ko bintun ban yarda nine mahaifinta ba wlh sai munje asibiti anyi gwaji"


Aisha kuwa har suka isa gida rusa kuka kawai take,ashe duk tsawon lokacin nan duk abinda ya faru laifin Luba ne bana Salisu ba,ta d'auka Salis da gangan yayi wa muhasim fyade,ta d'auka Salis da gangan ya auri Luba,ta d'auka Salis shi ya karkatawa muhasim wuya Ashe Luba da ta dauketa tamkar Yar uwa ta d'auketa da zuciya daya duk itace ta rusa mata gida,ta rusa mata farincikinta ta cutar mata da yayanta,da ace Salis ko sau daya ya bud'e bakinsa ya fada mata Luba tana da wani fuskar akan Wanda tasan ta dashi da ta dade da rabuwa da ita,duk da a lokacin ba lailai ta yarda ba zata dauka sabida kawai ya tsani luban ne,amma dai da ace har ya fada mata ba abinda zai hanata rabuwa da ita,sai ta ringa ji ma Kamar itama tana cikin wayanda suka cuci Salis din,kwana uku cir tayi tana zazzabi,a wajen Aunty mamy take jin cukun cukun da Salis yakeyi na fita da muhasim kasar waje.

Gabad'aya sai taji tana nadamar Abubuwan da ta ringa masa abaya Wanda da ace baya kaunarta ba Kuma shi da hakuri da ya Dade da sakinta yayanta kuwa duk da abinda ya faru ya riga da ya faru haka ya ringa zabga mata fadan ta Kira Salis ta bashi hakuri dan itama ta zalunce shi amma sam ta kasa kiransa dan batasan mai zata ce masa ba.

Salis

Ji yake kamar an sauke masa nauyin da ya dade Yana fama dashi a yanzu idan akwai abinda ya rage masa bai wuce yayi k'ok'arin fito da John da Hajiya Shafa ba dan a yanzu sai yaji ma Yana zargin baa cikin hankalinsa ya fada harkar saffarar yaran mutane ba kila ma Luba tana da hannu a ciki dan har ga Allah baisan ya akayi ya fara harkar ba,a yanzu kuwa ba karamin nadama yake ba,Rabin yaran ya sa an samo su ya basu kyautar kudi,dama bashi Suka sani ba sun san shine a matsayin mai taimaka musu.

Yanzu Kuma babban burinsa muhasim ta samu lafiya hakane yasa ya fara cuku cukun fita da ita ya riga da yayi wa wani likita ba indiye magana akan za'a kawo muhasim.


Luba

Zage zage kawai suke ita da Asabe suna tonawa kansu asiri har sai da ta Kai su ga dambe aka raba musu waje,Asabe kuwa hankalinta yafi na kowa tashi dan bata tab'a tunanin daga zuwa tonawa Luba asiri itama nata asirin zai tonu ba,tayi mugun nadamar zuwa kotun,da ace tasan nata asirin zai tonu da bata ma soma bawa Ashraf fuska ba,karshen dai duk abinda ta aikata gata nan a kulle da bandeji a nade a cikinta a Karo na farko da itama ta fara nadamar mugayen Abubuwan da ta aikata dan ta dame Luba a mugunta ta Shanye babban tashin hankalinta yanzu bata San hukuncin da zaa yanke musu ba zuciyarta cike take da fargaba da zullumi.


Tuni tabi ta rame ta lalace, tamkar yanda take hango Luba itama duk ta fice a hayyacinta matan da suka samu a cell din suma sai azabtar dasu suke.

A yau za'a koma kotu,Asabe kuwa rabon da tayi wani sallah cikakiya har ta manta sai gashi tana daga cell tana sallah da rokon Allah akan Allah yasa ba hukuncin kissa za'ayi musu ba.

Karfe goma aka tasa keyarsu da ankwa a hannnu ita da Luba akayi kotu dasu......


Wane irin hukuncin ya Kamata ayi musu ne>??>??>??>??>??



Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne, knuckles,wrinkles,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using sabulun mg's batare da kunbukaci wani Mai b>?? Mai bukata should
Chat=?G?
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391

Team glow>???
@&?



*WANAN LITTAFIN NA KUDINE BIYA 500 TA WANAN ACCT 0272061655 WEMA BANK NAFISA NUHU KO KATIN MTN KO AIRTEL TA WANAN LAYIN 08033719070 DOMIN KI MALLAKI NAKI KI MUTANEN NIGER KUMA KU TUNTUBI WANAN LAYIN*
*+227 96 82 89 84 DUK WACCE TA MIN SHARING NA BAR TA DA* *RABBI ZAI FIDDA MIN HAKKI NA DA IZININ ALLAH DOMIN BA YAFEWA NAYI BA*


*NI DA KISHIYOYINA*

*NA SADNAF*

*PAGE 39-40*


Kotu

Kotun cike take makil da mutane a cikin wayanda suka zo kotun har da mahaifiyar luba da yayarta Habiba jini ba Wasa ba a lokacin da suka ji labari sai hankalin su yayi matukar tashi a rade radin ma da suke ji a gari wai hukuncin kissa za'a yiwa Luba da Asabe duk yanda Habiba tayi tunanin zata iya share Luba sai taji bazata iya ba ita ta sanarwa mahaifiyar su halin da Luba ke ciki,ko mahaifinsu ma sai da jikinsa yayi sanyi dayaji wai hukuncin kissa za'a yiwa Luba badai nuna a fuskarsa ya damu ba amma jininsa ce Luba sai ya tsinci kansa cikin damuwa,irin wanan ranar ya ringa hangowa Luba fada da nasiha ba irin wanda baya mata har sai da ya gaji ya kawo ido ya zuba Mata,fadan da yake mata akan Asabe tun lokacin da tayi Aure ya gano ba matuniyar arziki bace sai da Luba ta masa rashin kunya ta nuna ba haka ba,yau ga irinta nan duk da itama da nata bakin halin Asabe ta kai ta ta barota

Koda su Habiba Suka tafi kotun bai bisu ba.

Aisha da Aunty mamy a suna daga gaba dan Aisha Allah Allah ta ringa yi gari ya waye dan babban burinta taga an yanke wa Luba hukunci Mai tsauri inta Kama ma ayi mata hukuncin kissa ta hanyar rataya,bazata iya fasalta illar da Luba tayiwa rayuwarta ba.

Daga lokacin da aka shigo dasu kallo daya tayiwa Luba da suka hada ido ta d'auke kanta tana jinjina lamarin ubangiji Wai hukuncin dan Adam ne ya firgita luba haka hukuncin dan Adam ne ya maidata haka inaga ranar da duk zamu tsaya gaban Allah wani irin tsoron Allah ne ya Kara shigarta da ido ta raka Luba har ta shige witness box ko kad'an bata ji alamar tausayinta ba dan Luba tayi abubuwa da yawa da ya Kamata ayi mata hukuncin.

Luba tana daga tsaye da idonta da sukayi luhum luhum ta ringa bin mutanen dake cike a kotun sultan ta hango da ilham suna daga gidan gaba sun zuro Mata ido, d'auke kanta tayi da sauri tana Jin hawaye na kara gudu a fuskarta ta riga da ta makara ba dama ta maida hannun agogo baya ballantana ta gyara kuskurenta,duk abinda ta aikata nasan zuciya bata tab'a tuno da makomar yayanta ba,bata tab'a tunanin halin da zata jefasu a ciki ba,ita dai bukatar da ta saka a gaba shine kawai burinta, a yau sai ta tsinci kanta da kunyar yaran da ta Haifa a cikinta sabida San abin duniya ta rabu da mahaifinsu,ta wulakanta shi,ta watsar dasu taje tayi auren cin Amana duk a san abin duniya,sai a ayanzu ta yarda yan Adam suna da gajen hakuri,da ace yau tayi hakuri ta zauna da Hamza da kila tayi arzikin cikin kwanciyar hankali,yau gajen hakurinta san zuciyarta ya kaita ya baro,ta tashi a tutar Babu, ba miji ba yaranta ba dukiyar.

A hankali ta Kara maida kallonta cikin mutane ta hango mahaifiyar ta da ta rufe bakinta da hannu da gani kuka take tamkar yanda Habiba dake gefenta ke kuka, batasan lokacin da kukan da take rikewa ya kwace mata ba,inama tana da sauran lokacin da zata gyara kuskurenta,inama tana da lokacin da zata farantawa Iyayenta,inama duk rayuwar da tayi a baya ace mafarki ne,inama duk cutar da tayiwa Aisha ace ba dagaske bane mafarkine,lokacin inama inama ya riga da ya wuce,ta cutar da mutane da yawa da ya Kamata ta nemi yafiyar su.

Yanda take risgar kuka haka Asabe itama take risgar kukan,Asabe duk tafi Luba ma shiga tashin hankali.

A lokacin da Alkali ya fara karonta Abubuwan da suka aikata Asabe dafe kirjinta kawai tayi da taji Yana barazanar fadowa,Luba kuwa runtse idonta kawai tayi tana jiran hukuncin da alkali zai yanke musu,Jin alkali yace "kotu ta yankewa Lubabatu Bashir shekaru Ashirin a gidan yari batare da ko tara ko beli ba, Asabe lawan Kuma kotu ta yanke mata hukuncin daurin rai da rai Asabe sakin wani irin wawan ihu tayi tare da zubewa a kasa.

Luba kuwa ta rik'e witness box tana ihun alkali ya mata sausauci shikenan a gidan yari zata Kare rayuwarta nan da shekara Ashirin masu zuwa ai tasan tama mutu,ihu kawai take bata ma Kara sanin mai alkali ke cewa ba har yansandan suka zagayo wajen da take suka saka mata ankwa,Asabe Kuma aka kinkimeta dan sumewa tayi,cikinta Kuma na ta zubar jini,

Ihu Luba ta ringa yi tana mik'a hannu tana "Aisha ki yafe min mama Kinga za'a tafi dani ki yafe min ki rok'a min baba dan Allah Aunty Habiba shikenan rayuwata ta kare Salis ka yafemin, dan Allah karka kora su Abdul ba dan halina ba ka rikesu tamkar kai ka haifesu,bansan inda zasuje ba idan ka koresu tunda mahaifin su ya rasu Ka taimaka min Shine abinda tayi ta fadi har aka shige dasu mota.

Salis kuwa sai yaji ma hukuncin da aka yiwa Luba bai masa ba,yaso ace ita aka yiwa daurin Rai da Rai din,ko bata rokeshi ba Shima baiyi niyyar rabuwa da yaran ba dan

Aisha ma ko a jikinta a haka suka fara fitowa daga kotun,kowa na fadar albarkacin bakinsa.

Salis kuwa da Yaya mustapha suka tsaya a jikin motarsa Yaya mustapha ya hau shigo masa da maganar Aisha akan ya mata magana akan ta koma d'akinta.

Salis murmushi kawai yayi yana "karka matsa mata Yaya idan bataso ta dawo ka kyalleta ni yanzu komai ma ya ficemin a rai wlh"


"Aa sai dai idan Kuma ka daina ra'ayinta ne amma ai dolenta ta dawo"
Salis murmushi kawai yayi bai ce komai ba dan yaga ma kamar Aisha kunyarsa takeji shi dai a yanzu ya samu kwanciyar hankali abinda ya rage masa samun lafiyar muhasim da zasu tashi jibi a cikin masu kaita har da Ashraf.

Yasamu yayi cuku cuku an fitar da John da Hajiya Shafa yanzu Kuma yanda zai gyara lahirarsa kawai yake nema.

Kwana biyu a tsakani aka fita da muhasim waje Salis yaso binsu Kuma ya fasa dan ayyuka sun dan masa yawa.


Hindatu kuwa ganin ba kowa a gidan yasa ta zage wajen San taga ta karkato da hankalin Salis kanta,dan ta lura ta karfin tuwo Aneesa ke san dawowa rayuwar Salis kila ta danna zawarci taji ba dadi,idan Salis yayi bacci haka take d'aukar wayarsa tayi ta duba messages din da take turo masa take kuwa zata goge a karshe ma sai tayi blocking din ta,a yanzu idan akwai wacce take so ta dawo

37 / 38