Nida kishiyoyina complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Romance

Chapter   7 / 38

18K to 21K   out of 111.9K words

ki da komai ba tunda bai rage kaunarki ba wani abu bai ragu a jikinsa ba,ni a ganina boye mikin da yake shine munafirci amma ni ko lokacin da muka tsayar da magana wlh naso na fada miki ya hanani ko ranar da nazo dinan Kika ringa cewa kamar amarya nake ba karya kikayi ba kwana uku da daura mana auren ko zuwan da nayi wlh nayi niyyar fada miki sai Kuma na fasa dan ya rokeni sosai akan bayaso kisani,ni sai nake ganin da ya gaya miki sanin da na miki wlh bazaki hana ba dan naga kina balain san nayi Aure duk Yan gidanmu sun d'auka da yardarki akayi auren shiyasa kikaji Aunty Walee na tambayata lafiya kuwa kinsan baa nan take aure ba.

Nidai abu daya danasani boye miki da yayi bai kyauta ba abin na ta damuna taya zaace a boye miki kinsan bana boye miki komai shiyasa na yanke fada Miki wlh sabida halin rayuwa baa san gawan fari ba yazo ya Fadi ya mutu ke bakisan da auren ba Yan uwansa basu sani ba azo rabon gado ace baa san zance ba wlh shiyasa na fada miki dafatan hakan bazai saka wai mu yanke kawancen mu ba kawai mu rungume mijinmu mu faranta masa"

"Luba baki kyauta min ba baki min adalci ba Luba da ace nasan abinda zakimin kenan wlh da bansoma yarda da aurenki ba yanzu da wane ido kikeso na kalli Aisha wane bayani zan mata ta gane Aisha fa kawarki ce karki manta"

"Ikon Allah wai haramune auren nawa ka isa ka aureni ne idan ni din ba matarka bace wlh bana Jin dadin abinan da kake yi kamar kana tsoron Aisha magana ce fa ta fatar baki kayi abu kamar namiji Mana idan bamuyi aure ba Ina zaka Kai rabon dake tsakanin mu zata hana abinda Allah ya hallata ne kaga mallam nidai ka zaunar da ita ka kara.mata bayani kai ya Kamata kayi mata magana ka barni da mata magana Haramun muka aikata kake ta sallati naga dai sai da ka bada sadaki aka daura mana aure kamin lefe ka aureni da daraja to na me a yanzu zaka ringa kame kame agabanta mtssss nidai na baku waje kuyi magana bari na sa a kawo mata abinci.

Ta nufo wajen k'ofa ta karkata ta wuce dan a bakin k'ofar na daskare a tsaye kallon Salis kawai nake Yana ganin ta fita yayi sauri ya juya bayansa duk da duk abinan bai dago mun hada Ido ba sai sallati da yake Yana Aisha kiyi hakuri dan Allah nasan ban kyauta ba dan Allah kiyi hakuri"

Zuciyata wani irin kunna take na kasa gasgata wai Salis da ya balain tsanar Luba shine yau a matsayin mijinta wai har ya mata ciki ta haihu ashe duk tsawon lokacin nan ninkeni baibai suka yi soyayya sukeyi a gaban idona yake nuna Mata kiyayya kawata aminiyata da ba abinda bata sani akaina ba itace Salis ya Aura a matsayin kishiyata,ashe dadewar da Salis yake yi a Abuja sabida auren Luba da yayine yana nan da kawata Yana Shan soyayya sai ya mata sati biyu uku ya dawo wajena na tafi kunshi nayi ado nayita girke girke Ina murnar tarbar mijina Ina tunanin yanda nake dokin kasancewa dashi haka yake dokin kasancewa dani sabida an dade baa hadu ba,idan ya iso kuwa jikina yayi ta rawa kawo wanan d'auko wancan ni ga mijina ya dawo sai dare yayi yace min a gajiye yake likis cikin tausayi zan raba dare Ina masa tausa dan nasan duk sabida nida yarana yake Neman kudi ashe baccin gajiya da kawata ta tara masa yake, sabida kaunarta da yake ya kai ta abuja sabida ma Kar tayi nisa dashi.

Na d'auke kallona daga kan shi na maida Kan jaririya Wai Salisu ne yayi wa Luba kawata ciki,na runtse idona hawaye na gudu a fuskata kirjina kuwa kamar ya fado Ina Jin numfashi na min wahalar shak'a,na runtse idona dana tuna lodin magungunan da na bata da Sunan ta jiyar da mijinta dadi har tana cemin a waya mijinta ya isheta da jarraba sabida kyan maganin ko aiki yaje sai ya dawo yayi, Ashe Salisu ne ya isheta da jarraba Ashe Salisu take bani labarin yanda yake santa kamar ya hadiyeta har Ina Jin na raina san da nawa mijin yake min.

A daidai lokacin da Luba ta dawo d'akin da farantin abinci ta ajiye a gabana tana "baki gaji da tsayuwa bane ki zauna mana nan ma fa gidanki ne kin kwaso gajiya kici abinci sai ki watsa ruwa kizo kiga diyar taki.

Sai Kuma ta sunkuya ta d'auki abincin da bansan wane kala bane dan wlh a yanzu tsananin mamakin Luba Kuma nake tana ta abu Kamar irin ba komai dinan ta nufo gabana dashi tana "kawata wai me haka dan Allah"

Har lokacin hawaye kawai ke zubomin kalmar kawata da tace yasa na Kara Jin kirjina yayi nauyi kawata Luba dai itace yanzu matar salis har suka haihu tare magangaunta suka Kara dawo min "wlh karka sake cewa baa san ranka ka aureni ba da san ranka sarai ma,dan da baka sona da bazaka kwanta dani har na haihu ba sai na runtse idona tare da cije lebbena da baka sona bazaka kawoni Abuja wajen da kake aiki sabida Kar na nisance ka ba"

Sai naji hannunta saman hannuna "zoki ci abinci nidai matan abokanan Salis suna ta jirana Kinga ba dadi na barsu su kadai"

Sai na fusge hannuna daga nata hawaye sai gudu yake a fuskata na ma rasa Mai zance mata na bud'e bakina da kyar Ina "Luba mai na miki dana cancanci irin wanan cin amanar daga wajenki Luba duk mazan duniyar nan ki rasa Wanda zaki aura sai Salis mijina Luba"? Idan shi baiji kunya ba bai san ana barin halak dan kunya ba ke Sai ki biyeshi ki aureshi kina matsayin kawata aminiyata Luba ki auri mijina shekara guda batare da nasani ba"?

Duk maganar da nake hawaye kawai nake muryata na rawa

Sai ta turo dankwalinta gaban goshinta tana "Tambaya daya zan miki ki bani amsa, Haramun ne dan kawa ta auri mijin kawarta?idan har Kika kawo min Inda aka haramta auren mijin kawa ni Kuma na Miki alkawari Zan saka ya sakeni Aisha dama haka kike ke yanzu wani abune dan mijinki ya aureni"?

Bansan ya akayi ba na ciri hannu na d'auketa da mugun mari kafin ta dawo daidai na kara d'auketa da wani marin kafin na sauke hannuna naji tayi sama dani ta makani da kasa a daidai lokacin da naji duhu na neman rufemin ido numfashina na k'ok'arin d'aukewa naji sallatin Salis sama sama ban Kara sanin Inda kaina yake ba.

Sai bud'e ido nayi na gani a gadon asibiti da Karin ruwa a hannuna sai da na dau tsawon mintuna kafin na tuna abinda ya faru na maida idona na rufe Ina Jin bugun kirjina da kuguna dake min ciwo inaga bugani da kasa da Luba tayi ya haddasa min ciwon.

"Sannu Aisha kin farka"?
Naji muryar Salis a kaina banasan ganinsa haka yasa ban bud'e idona ba"

Ina jinsa ya zauna a gefen gadon murya na rawa ya hau magana "dan Allah dan Annabi kiyi hakuri Aisha wlh nasan ban kyauta ba amma wlh tallahi bana kaunar Luba kaddara ce tasa mu kayi aure wlh baa san raina ba kwanciyar da take magana wlh magani ta saka min a lemo wlh wlh bana kaunarta kinsan bazan tab'a cin amanarki ba,wlh tunda na aureki ban tab'a kallon wata mace naji Ina santa ba bayan ke wlh matsayinki daban yake a zuciyata ki yarda dani matata kar ki bari shaidan ya rabamu wlh burin Luba taga mun rabu dan Allah kiyi hakuri na yarda ki min kowane irin hukunci.

Wlh kamar feshin wuta haka nake Jin maganganunsa a kunnena daga lokacin da na saka kafa a d'akin na hangosa a d'akin na tabbatar da zargina naji sansa na ficewa daga zuciyata tsananin tsanarsa na mamaye min zuciya babban burina yanzu nagani a gidan yayana dan wlh na gama auren Salisu.

Ban tabbatar da muryata zata fita ya jini ba nace "Allah ya isa tsakanina da Kai Salisu wlh har duniya ta nade bazan yafe maka ba duk matan duniya ka rasa wacce zaka Aura sai Luba da kasan kawata ce Aminiyata ySalisu ka aureta ka b'oye min har tsawon shekara guda ka daukota ka kawota Abuja baka Santa kayi mata ciki ta haihu kayi taro tare da gayyatar abokanan aikinka da matansu,ashe Sabida ita ne baka zuwa wajena sai ka shafe sati biyu ko uku baka zo ba,na maka maganarta ka zageta Salisu kawata fa wanan wane irin cin Amana ne Wlh bazan yafe ma ba"

Na fashe da wani irin kuka zuciyata na min k'unna

Hakuri ya cigaba da bani ko muryarsa banaso naji na saki ihu akan ya fita banaso na gansa.

Ina jinsa ya tashi.

Rashin kwarin jiki yasa ban fusge ruwan daga hannuna ba dan burina yanzu naga na bar garin.

A takaice washegari wani likita yazo dubani Ina kallon Salis a rabe a jikin kofa.

Tun jiya wlh hawaye bai tsaya min ba idan na tuna irin cin amanar da Salis da luba suka min.

Koda likita ya gama dube dubensa naga ya cire min robar ruwan da Ina tunanin na Sha ya kai biyar mik'ewa nayi zaune cikin muryata da bata fita sosai nace "Likita ka sallameni tafiya zanyi"

"Hajiya ai baki warke ba ya kallo Salis dake bakin k'ofa Ina tunanin dai asibiti daya suke aiki.

Ni kuwa ban bi takan likitan ba na Mik'e zaune Ina dube dube duk ji nake kamar iska ya d'aukeni Ina ganin mayafina na d'auka tare da cije lebbena sabida kaina da naji ya Sara min.

"Aisha Dan Allah ki bari kiyi hakuri bakida lafiya ki bari gobe sai na Kai ki gida da kaina jininki fa ya hau Aisha dan Allah ki koma ki kwanta.

Kafata ba takalmi inuwarsa ma basan kallo nake ba nayi hanyar wajen.

Ya sha gabana da sauri kallon da na masa yasa ya bani guri nayi waje Ina jinsa a bayana Yana "Aisha ba inda kika sani a Abuja kizo muje gida Dan Allah dan Annabi gobe sai mu tafi.

"Inzo muje gidan Luba ko Salisu"?

Sai yayi shiru

Na girgiza Kai na cigaba da tafiya duk da nasan bansan ma Ina ne Tasha ba amma dai matambayi baya bata.

A takaice taxi na tare akan ya kaini Tasha.

Ina Hawa Salis ya Shiga shima Yana ta magiya.

Shattar mota na dauka ni kadai duk yanda Salis yaso bina na hana driver daukarsa.

Wlh dauriya kawai nake dan har yanzu da zazzabi a jikina kaina kamar ya rabe biyu.

Tafiyar awani ya kawoni garin katsina bai zame dani ko Ina ba sai gidan yayana Koda na Shiga kudin Mai motar kawai na karba na bashi na baje a kasan kafet din palon wani sabon zazzabin na rufeni yarana duk suka yanyameni.
Har da Nana da Ummi Aunty Mamy kuwa duk ta daka musu tsawa akan su bar kaina ta cigaba da tambayata lafiya ta gani haka dan duk Wanda ya gani yasan ba lafiya ba.

A daidai lokacin da naji muryar yayana Yana "Mai ya samu Aisha"?




Present

Alhaji Salis zuciyarsa cike take da fargabar auren da zaiyi a yanzu da lokaci ya matso sai yake Jin zuciyarsa cike da fargaba dan ya nunawa Iyayen Aneesa matansa basuda matsala duk zasu rik'e Aneesa da Amana.


Duk da sunje katsina sunyi jeren dan a cikin gidajensa daya gina na siyarwa ya zabi daya ya gyara dan Aneesa ta zauna kafin yasan yanda zai fadawa su Luba.

Aisha ma ko ta kansa bata bi ballantana yace ta damu da auren da zaiyi.

Sai dai abinda ya daga Masa hankali bai wuce mahaifiyar Aneesa da tace tanaso taje gidansa ta damka wa matansa amanar Aneesa ba,taya mahaifiyar Aneesa zata je gidansa bayan Aisha ce kawai tasan zai Kara Aure.

Har aka Shiga satin bikin zuciyarsa cike take da fargaba Yana ta tunanin yanda zai bullowa Mahaifiyar Aneesa dan tace da ita za'a kawo Aneesa ya lura mahaifiyar Aneesa ba san auren take ba.


A haka har aka fara shagalin biki Sam baiso wani shagali ba dan shi kansa yasan ya girma da haka amma yaga Kan Aneesa na rawa dan dak'yar ya samu ya k'aucewa pre wedding din da ta dage masa suyi dan yana gudun Luba ta gani.

A haka har aka daura Auren shi da Aneesa ranar jumaa akan za'a kawota ranar littinin.

Washegarin daurin auren Alhaji Salis ya nufo katsina zuciyarsa cike da fargaba dan dole ya fada Luba da Hindatu Auren da zaiyi idan ya tuna tashin hankali da Luba tayi a auren shi da Hindatu sai yaji wani sabon tashin hankali ya rufeshi idan Kuma yak'i fada mahaifiyar Aneesa Suka kawota fa yasan halin Luba dambe za'ayi da ita.

A lokacin daya iso gida Luba har wani cancada ado tayi dan itace da girki.

Shima Alhaji Salis ranar ya saki fuskarsa Yana ta janta da hira dan yafi jinta akan Hindatu Luba kuwa sai falli take tana kyakyata dariya sabida ta kunsawa Hindatu bakin ciki ta kuwa ji Dadi tana jinta tana tsaki a Palo tana kananan maganganu.

Shi dai Alhaji Salis har da yan adduoinsa a zuciyarsa kafin ya ruko hannun Luba da ta wani narke tana "Alhaji nawa Ni kadai"

Ya saki murmushin karfin hali cikin dauriyar da ta zo masa yace "kinsan bawa bai isa ya k'aucewa kaddararsa ba ko Kamar dai yanda kike fada,auren nida ke Allah ya rubuta sai munyi Tom yanzu Allah ya kara kaddara min sake Aure a yau aka daura min Aure da wata yarinya Aneesa"


"Kutumar uba Mai kace maimaita min naji"?

Luba tace tana karkada kunnenta.....



INGANTACCEN MAGANIN SANYI TOILET INFECTION MAI WANKO DUK DATTIN MARA KOWANI IRIN SANYI NE ZAI MAGANCE SHI DAYARDAR ALLAH SHIN KINAFAMA DA RASHIN SHA AWA? RASHIN NI IMA RASHIN GAMSUWA SHIN KINYI SHEKARA DA SHEKARU KINA NEMAN HAIHUWA RIKICEWAR JINI CIWON JIKI CIWON MARA YAYIN AL ADA DUKA WANNAN MAGANIN YANA WARKARWA ME CIKI BATA SHAN MAGANIN SANYI NA 4K YAKE INA KATSINA INA AIKAWA KO INA A FADIN KASAR NAN HARDA KETARE MAZA DA MATA MAGANIN SANYI MAI GYARA MU AMALAR AURE AUNTY ZEE MOM MUJAHID
08162859027
KATSINA


*NI DA KISHIYOYINA*

*NA SADNAF*

*E.W.F*


*PAID BOOK*



*Page 8*

Luba

Ta mik'e da sauri tana "Alhaji kaga idan Wasa kake min ka daina banaso kai yanzu ko sadakar mace aka Kara baka Kamar yanda aka baka waccan basumudiyar zaka yarda ka karba ne"?

Salis ya had'e rai yana "Luba inaga ban tab'a miki zancen Wasa ba ko karki manta ba ke kadai ce matata ba yanda kike takamar ke matata ce kina Kuma so da kishina haka sauran ke sona Aure dai an daura min jiya ranar litinin za'a kawo ta aure dai da na Kara inaga ba haramun bane tamkar lokacin da kike fada da na aureki akan Karin Aure ba haramun bane tom inaso wanan waazin da Kika min a yanzu sai kiyi wa kanki Yarinya na aura baza'a samu matsala da ita ba idan Allah ya yarda"

"Wlh kaci karya Salisu ka wulakantani har ni zaka cewa an daura ma Aure ka Kara cin amanata a Karo na biyu wancan jakar kace min tilasta ma ita akayi yanzu kuma baka ji kunya ba kace min an daura ma Aure ba ma neman auran kake ba sai da aka daura kazo kana fadamin bayan a yarjajeniyar da muka yi da Kai ba Karin Aure daga ni sai Aisha zaka zauna damu"

"Ba inda muka yi yarjajeniya dake akan bazan sake Aure ba luba na gaji da tashin hankali da kukeyi a gidanan ke da Hindatu Kun k'i ku sama min nutsuwa Karin Aure Yana cikin kaddara ta ban isa na kaucewa kaddara ta ba nidai na fita hakkinki dan ban munafirce ki ba tunda it Aisha a lokacin da na aureki bama tasani ba har aka shekara da haka nayi mi ki sai kice naci amanarki na munafirceki dan haka ranar litinin za'a kawota banasan tashin hankali"

"Idan ka isa Allah ya tsine min ka rasa lokacin da zaka Kara aure sai da na manyanta zaka auro yarinya karama ko kunya baka ji ba dan masifa ka ajiye mata har uku amma sai ka Kara auren ta hudu,a Ina kaga kwarin rik'e mata hudun mu ukun ma da cutuwa nakeyi ko gamsar da mutum baka iya yi kana daya zaka baje ka hau bacci inaga ka karo ta hudu,? idan su basa gamsar da Kai baka isa kace ni bana gamsar da kai ba dan rabin kudina a gyara suke tafiya, wlh Alhaji idan kana san zaman lafiya a gidanan ka janye auren nan idan ba haka ba wlh tallahi ruwa ma bazaka iya sha a gidanan ba Kuma ka jawowa Yar mutane balai dan wlh dukanta zan tayi har sai ta koma gidan iyayenta.

"Wlh baki isa ki hanani Aure ba luba ba'a aurowa aka auroki a lokacin da kikeso na aureki ta karfi da yaji wane irin wa'azi ne baki min akan Karin auren ba? wane irin magana ne baki min ba dan kawai na aureki? Ashe Aisha ita ba mutum bace sai ta yanki jiki ta Fadi tunda ke kawarta ce na aureki ba kuma ki tab'a Jin komai ba kina ganin ma ai ba wani abu bane sai dan yanzu na Kara aure zaki min hauka.

Wlh wlh Luba abinda na dauka a baya bazan dauka ba ayanzu kinji na rantse miki sai dai duk abinda zai faru ya faru"

Ya mik'e fuuu yayi waje

Luba ta bishi tana "Na rantse da Allah kuwa kayi auren nan sai na baka mamaki abinda nayi nima a baya kadan ne akan wanan da zanyi banda jarraba kana da manyan samari zaka Kara aure,kake hadani da jakar matarka ita tasan ciwon kanta ne nida ita ba daya bane wlh sai na baka mamaki wanan karon abinda kake gudu wlh sai ya faru ka Kara auren kagani"

Alhaji Salis kuwa ko kallonta bai Kara yi ba yayi kwanciyarsa a dogon kujera Luba a ranar kwana tayi tana balai ko runtsawa Salis baiyi ba har sai da Hindatu ta fito taji labarin abinda ke faruwa itama ta kadu da Jin labarin aure zaiyi sai gashi

7 / 38