Nida kishiyoyina complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Romance

Chapter   34 / 38

99K to 102K   out of 111.9K words

A &Z gidan sauki ne=???=???=???=???=???=???=???=???
Masu siyan daidai kuma bambancin kadanne

Muna garin Kano Dan neman Karin bayani Kira ko whaspp 09037870422

Karku manta muna tura Kaya duk garin dakuke inkiyi siyayyama dayawa muyi Miki free delivery =???=???=???yan Kano kayanku har kofar gida cikin aminci>??>??>??




*WANAN LITTAFIN NA KUDINE BIYA 500 TA WANAN ACCT 0272061655 WEMA BANK NAFISA NUHU KO KATIN MTN KO AIRTEL TA WANAN LAYIN 08033719070 DOMIN KI MALLAKI NAKI KI MUTANEN NIGER KUMA KU TUNTUBI WANAN LAYIN*
*+227 96 82 89 84 DUK WACCE TA MIN SHARING NA BAR TA DA* *RABBI ZAI FIDDA MIN HAKKI NA DA IZININ ALLAH DOMIN BA YAFEWA NAYI BA*


*NI DA KISHIYOYINA*

*NA SADNAF*

*PAGE 35*

Habiba da sabitu cikin tsananin mamaki suka zubawa Luba ido, da har lokacin ihun ta shiga uku take hannunta rik'e da jakar Habiba daya hannun Kuma kudin sabitu ne da ta d'auko a karkashin gado zata saka a jakar duk da sun Kamata ta kasa sakin jaka da kudin.


"Luba mai kike nema a dakina ya akayi kika Samu mukullin d'akina"? Mai jakata keyi a hannunki da kudi"?



Luba tsabar tashin hankali kasa motsi tayi

Waziri kuwa ya saki murmushi Yana "Aunty Habiba har sai kin tambayeta mai take nema a dakin ki Allah ne yayi yau asirinta ya tonu dan tunda tazo gidanan kuke samun sab'ani da Abba hakane yasa na fara zarginta, a ranar da Abba yace an kwashe mishi kudi na Kara gasgata zargin da nake mata dan dana shigo Kamata nayi tana muku labe, hakane yasa na Kara saka mata ido Allah cikin ikonsa na gano ita take zuba ruwa a Miya ko gishiri idan kika gama zubawa Abba girki a ranar bata san na ganta ba da biyu na karbi mukulin k'ofar dakin ki dan nasan kila itace take d'aukewa Abba kudi dan kawai ta hadaku fada a yau ma ta d'auka ba kowa a gidan shiyasa ta shigo dan ta Kara sacewa Abba kudi ni kuwa na kulleta a d'akin na kira ku dan kuga shaida"

Habiba rawan da jikinta yake yi yasa kafafunta kasa d'aukarta dan ta kasa yarda duk abinan dake faruwa luba ke haddasa mata,Luba kanwarta da ta kasance uwa daya uba daya tasan Luba zata iya aikata komai bata tab'a tunanin har ita da take jininta zata iya mata haka ba"

"Luba mai na miki kike san ki kashe min Aure"?Habiba tace tana fashewa da kuka

Sabitu kuwa jikinsa har wani rawa yake sabida mamaki da b'acin rai "dama kece kike kwashe min kudi kika ringa Sakani zargin Habiba"?

Dama kece kike ta hadani fada da Habiba?

Dama kece duk kike haddasa min fitina a gida"?


Luba sakin jakar hannunta tayi da kudin tunanin daya darsu a ranta yasa ta gwalo idanunta waje tana "Bama san hayaniya ku fita kubar d'akin nan Sarauniya tace Kar a dameta"

"Sarauniya taci ubanta sabitu yace tare da nufar wajen drawer"

Luba duk da ta tsorata ta cigaba da "Zaku gamu da fushin sarauniya idan kuka tab'a ta"

Sabitu kafafunta ya janyo ta fado tim a kasa kafin yayi wani motsi yaji muryar Habiba ta bayansa ta matsar dashi gefe ta jawo luba ta hau kirba tana " A yau ko Aljannun ne dake wlh sai naci ubanki waziri d'auko min Ashana a kitchen na Kona Yar iska"

Waziri dake kunshe dariyar dake cinsa na Aljannun karyar da tayi yayi waje.

Sabitu kuwa cewa yake"ba sai an d'auko Ashana ba bari na dauko dorina a cire mata Aljannun"


Luba ganin idan har bata yi magana ba zasu iya Mata dukan tsiya ko su kasheta yasa ta saki ihu tana "wlh karya nake banida komai kuyi hakuri ku yafemin sharrin shaidan ne"

"Kece ai shaidan din luba,har ace duk abinda ya Sameki duk halin da kike ciki baki daddara kinyi nadama ba Ina yayarki so kike kiga bayana,yanda aurenbki ya mutu so kike nima ki kashe min aure toh wlh daga kaina bazaki Kara kulla sharri ba

"Ai Habiba kinfi kowa laifi dama kinsan haka halinta yake shine baki fada min ba kika barni na barta zaune cikin gidana,anya shaidaniyar nan jininki ce"? Ai wlh sai tama fito min da duk kudina da ta sace ko na mik'ata wajen yan sanda"

"Aunty Habiba ki rufamin asiri!!

Marin da Habiba ta d'auketa dashi tare da rufeta da mugun duka ya katse Mata magiyar da take.

Sabitu kuwa cewa yake sai ta biyashi kudinsa.

Sai da Habiba tayi wa Luba jina jina ta jawo hannunta tayi hanyar waje da ita, tana tsine mata albarka.

Tana bud'e gate din gidan bakin motar Yan sanda ta faka a k'ofar gidan da wani karamin mota.

Abinda yaja hankalin Aunty Habiba da sabitu suka saki baki suna kallon Yan sanda maza uku da suka sauko daga motar da Yar sanda mace guda daya.

Luba wani sabon tashin hankalin ne ya Kara rufeta dan ta d'auka mijin Habiban ne ya kira mata yan sanda.


Wajen sabitun tayi da gudu tana "Na tuba dan Allah ka rufa min asiri karka kulleni"

"Wlh sai kin Kare rayuwarki a kurkuku"

Taji muryar Aisha ya daki dodon kunnenta

A hankali ta juya kirjinta na bugun tara tara dan idan ba kunneta ke san yaudarar ta ba muryar Aisha taji.

Koda ta juya hada ido tayi da Aisha da ta sha farin hijabi har kasa fuskar nan nata a mugun hade sai hucci take gefenta Kuma Ashraf ne a tsaye ya harde hannayensa a kirjinsa Yana kallonta.

Mace yar sandan ta nufo wajen da take tsaye tana "Madam you are under arrest"

Luba ja da baya tayi tana "Mai nayi da zaa Kamani"?

Fusgo hannunta mace Yar sandan tayi tana "idan munje station sai kiji"

"Ku tafi da ita duk abinda ake zargin ta da aikatawa zata aikata ta wuce duk Inda kuke tunani"

Habiba tace tana hararar Luba da ake sakawa ankwa a hannu hankalinta a mugun tashe sai cewa take mai tayi tana cewa Aisha "wane Sharrin kike bibiyana dashi duk da na rabu da mijinki"

Aisha ba karamin k'ok'ari tayi wajen danne abunda take ji a ranta ba,bata tab'a tunanin zata yi ido biyu da Luba bata shaketa ba,tunda Suka gano Luba na da sa hannu Ashraf ya hau nemanta,ba inda basu dubata ba itama kanta burinta taga Luba tazo hannu hakane yasa ta matsawa Ashraf akan kamo Luba har sai da a garin bincike suka gano Luba na gidan Habiba dan mahaifin ta ne ya fada musu da suka je gidan.

Yana Kiran Aisha tace bari ta fito tafiso a kama Luba a gabanta a cikin mota Ashraf ya ringa rokonta akan Kar tayi wani abu ta bari hukuma suyi aikin su.

Luba kuwa har suka isa station jikin ta rawa kawai yake da ace tasan Yan sanda zasu kamata da bata zo bauchi ba a cikin Abubuwan da ta aikata bata san wane asirin nata ya tonu ba, Rabin Abubuwan da ta aikata tasan ba wanda yasani sai Asabe,Asabe ce kawai zata iya tona mata asiri,ta kuma dade da aika Asabe lahira da wanan tunanin taji hankalin ta ya dan kwanta dan koma mai ake zargin ta aikata tasan basuda shaida idan ta kafe dole su rabu da ita.

Da isarsu station aka watsa ta bayan canter.

Awa daya a tsakani wani dan sanda ya daka mata tsawa akan ta fito.

Fuska a daure ta fito dan taga alamar sai ta hada da fuska da borin kunya

Koda aka karanto mata zargin da ake mata dan sanda ya hada da "Karki wahalar damu ki wahalar da kanki idan har kinsan kina da hannu a abinda ya samu yarinya nan kifito ki fada mana gaskiya ba sai kin wahalar da mu ba ta hakan zaki samu sausauci a hukuncin da zaa miki ya akayi kika karkatawa yarinya nan wuya da baki"?

"Officer wlh banida hannu a abinda ya samu yarinya nan nidai nasan tsohon mijina ne yayi mata fyade daya ga asirinsa zai tonu shine ya karkata mata baki"

"Ke ya akayi kika san shi ya karkata mata baki, kina wajen ya karkata mata baki"?

"Bana wajen amma nasan shi ya karkata mata baki"

"Karki wahalar damu ki fada mana gaskiya idan kinfi san Kuma a saka ki fadi gaskiya ta karfi da yaji sai mu saka ki"

Luba ko gezau batayi ba ta dage akan batasan komai a Kai ba su kamo Salis shine ya karkata wa muhasim wuya.

A takaice duk da uban azabar da suka ringa ganawa Luba,kafewa tayi akan bata da hannu akan case din Salis ne ya karkata wa muhasim wuya.

Ashraf kuwa yariga da yasan wacce luba a binciken da ya karayi ya Kara gano mugayen halayen Luba.

Burinsa yanzu ta amsa laifinta ta Kuma fada musu da me ta karkata wa muhasim baki.

Tuni ya nemi a mik'a case din kotu dan shi zai tsaya akan case din dan Aisha ta dage masa burinta kawai tasan mai ta yiwa muhasim wuyan ta ya karkace.


Kotu

Cike take dam da jama'a a cikin wayanda suka zo kotun har da Yaya mustapha Aisha da Aunty mamy,Salis ma baa barshi a baya ba sai dayazo.

Dan burinsa kawai gaskiya tayi halinta,shima a yanzu ba wacce yake mugun zargi sama da Luba.

Sai da aka gabatar da Sharia wajen biyu kafin a kira case din Luba da yan sanda biyu suka sakata a tsakiya

A cikin sati guda duk ta fice a hayyacinta kamar ba ita ba,tana kallon yanda Salis ke jifanta da mugun kallo Kamar ya jawota ya rabata da ranta.


Sai da ta shiga wajen da masu laifi ke tsayawa ta tsaya duk da jikinta rawa yake haka ta dake dan ko bindiga zasu saka mata bazata tab'a karbar laifinta ba a yanzu ma burinta a Kama Salisu suyi zaman yarin tare.

Koda aka karanto zargin da ake mata Ashraf ya nemi izini a wajen alkali sabida ya Mata tambayoyi dakewa tayi ta Kara fada musu Salis ne ya karkatawa muhasim baki sabida Kar ta tona masa asiri asan shi ya mata fyade


Ashraf ya saki murmushi yana "Mallama luba kikace tsohon mijinki shi ya karkata mata wuya sabida rufin asirinsa shin kina wajen ya karkata mata wuya ya akayi kika san shi ya karkata Mata wuya"?

"Yanda akayi nasan shi ya aikata mata wanan danyen aiki a lokacin kafin muyi aure Ina yawan zuwa office dinsa dan mu gaisa,toh a lokacin baya wani bani fuska lokaci lokaci idan na bushi iska nakan je dan mu gaisa a irin wanan lokacin watarana naje kafin na Shiga ma asibitin naga ita muhasim ta fito daga asibitin da gudu tana kuka inda take hankalina ya tashi dan nasan yarinya tunda Yar yayan kawata ce take nabi bayan yarinya dan naji mai ya sameta ta fito daga asibitin tana kuka.

Koda nabi bayanta sai da na rarrasheta da kyar na samu ta fadamin tsohon mijin nawa shi ya mata fyade ta Kuma gano tana d'auke da ciki,shine ya dage akan sai ta cire ko ya kasheta idan ba haka ba zai mata abinda bazata samu bakin magana ba a lokacin kwantar Mata da hankali nayi nace Kar ta damu ba abinda zai iya mata ni zan masa magana.

A washegarin ranar naje na same shi a office na nuna masa nasan abinda yayiwa Yar yayan matarsa dan haka idan baiyi wasa ba sai na tona masa asiri.

Hakuri ya bani akan Kar na tona masa asiri,jinsa kawai nayi a lokacin dan na yanke a raina Zanje na samu iyayen yarinya kawai.na fada musu.

Kwana biyu a tsakani yarinyar tazo ta sameni tana kuka akan Salis yace ko ta yarda ya zubar mata da ciki ko ya kasheta daga islamiya ma tazo ta sameni dak'yar na rarrasheta akan ta tafi gida a gobe sai na tona masa asiri.

Washegari ban kai ga naje gidansu yarinya ba naji labarin an tsinceta a bayan makarantarsu an karkata mata baki take nasan ba wanda zai iya aika aikar nan sai shi, a ranar naje na same shi a office dinsa na nuna masa nasan shi ya karkata mata wuya dan rufin asirinsa yanda yaga na dage zan sanarwa yan sanda yasa yayi tamin magiya akan na rufa masa asiri sharrin shaidan ne yanda akayi nasan shi ya karkata Mata wuya kenan"

Ashraf gyada kansa yayi Yana

"Hajiya Luba ya akayi duk yanda kike da kawar taki baki fada Mata abinda ke faruwa ba kike b'oye mata sanan kince yarinya zuwa take wajenki ta fada miki duk yanda tayi da shi tsohon mijin naki,ya akayi bata zabi ta sanarwa kowa ba sai ke"

"A lokacin banaso na raba kawar tawa da mijinta shiyasa ban fada mata ba"

"Toh mai yasa baki sanarwa Iyayenta ba"?

"Anan ne nasan nayi kuskure da ban fada musu ba"

"A lokacin da abin ya faru kunyi Aurene ko bakuyi aure ba"?

"A lokacin bamuyi aure ba sai da abin ya faru mukayi Aure"

"Ya akayi kika yarda kika auri wanda ya iya yiwa yarinya fyade har ya karkata mata baki bayan Kuma kinsan Yana da irin wanan mugun halin Kika yarda kika aureshi daga Kuma labarin da kike bamu tamkar dai shi tsohon mijin naki mijin ka?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? warki ne"?ke kinsan shi ya aikata irin wanan danyen aikin bakiyi kararsa ba kike nemi ki rufa masa asiri sabida kema ki samu cikar burinki ya aureki ko"?

"Aaa a lokacin gani nayi idan na fito na fada zan Zama silar da zan rabashi da kawata shiyasa ban fada ba"

"Shin a gidanki muhasim ke zuwa ta Sameki ta fada miki halin da take ciki ko kuwa ke kike zuwa wajenta dan kisan halin da take ciki"?

Luba shiru tayi tana kallonsa Ashraf ya gyara tsayuwarsa Yana kallonta dan so yake ya biye mata kafin ya fito da shaidun da yake dasu akanta.....


Wlh nayi typing nayi mistake na goge sai da na sake wani sorry for the late update



Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne, knuckles,wrinkles,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using sabulun mg's batare da kunbukaci wani Mai b>?? Mai bukata should
Chat=?G?
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391

Team glow>???
@&?



*WANAN LITTAFIN NA KUDINE BIYA 500 TA WANAN ACCT 0272061655 WEMA BANK NAFISA NUHU KO KATIN MTN KO AIRTEL TA WANAN LAYIN 08033719070 DOMIN KI MALLAKI NAKI KI MUTANEN NIGER KUMA KU TUNTUBI WANAN LAYIN*
*+227 96 82 89 84 DUK WACCE TA MIN SHARING NA BAR TA DA* *RABBI ZAI FIDDA MIN HAKKI NA DA IZININ ALLAH DOMIN BA YAFEWA NAYI BA*


*NI DA KISHIYOYINA*

*NA SADNAF*

*PAGE 36*

"Ba gidana take zuwa ba muna dai had'uwa da ita a hanya ne"


Ashraf murmushi ya saki yana "yanzu kinyi magana biyu kenan kince yarinya tazo ta Sameki tana kuka akan shi tsohon mijin naki yace mata idan bata yarda ya zubar mata da ciki ba zai kasheta sai Kika rarrasheta akan ta koma gida zaki tona masa asiri" A ranar a hanya kuka had'u ta fada miki Kuma a wane hanya kuka had'u ta fada miki yace zai kasheta"?

Luba sai ta dirirce ta rasa ma karyar da zata masa




Ashraf ya juya ya kalli alkali Yana ya mai girma mai Sharia

inaso a bani dama Zan kira tsohon mijin ta na masa tambayoyi"

"Kotu ta baka dama"

Salis bai tab'a tunanin Ashraf zai neme ya fito ba,taya Ashraf zai masa haka kiransa da zaiyi na nufin tonan asirinsa a bainar jama'a ko kad'an bayaso ana maganar yayi wa muhasim fyade.

Ashraf sai da ya kara masa ido akan ya fito ya tashi jiki a sanyaye sai yaji Yana nadamar ma zuwa kotun ba haka yayi da Ashraf ba taya a bainar jama'a zaice yayi wa muhasim Fyade.

Koda ya fito wajen dake kallon Inda Luba ke tsaye ya tsaya suna fuskantar juna.

Sai da Alhaji Salis yayi rantsuwa akan zai Fadi gaskiya magatakarda ya koma ya zauna Ashraf ya tsaya a gabansa ya dago suka hada ido da Aisha da tayi saurin kau da kanta.

Karo na biyu da ya Kara tsintar kansa cikin tsananin kunyar abinda ya aikata sai yaji a ransa gwara ya Fadi iya gaskiyar abinda ya sani.

ASHRAF kuwa dakewa yayi Kamar ba mahaifinsa ba dan a binciken da yayi zai Kara wanke Salis ne a fyaden da yayi wa muhasim a wajen Aisha da Yaya mustapha.


"Alhaji ko zaka iya fada mana wane danganta ne tsakanin ka da wacce ake Kara"?

"Tsohuwar matata ce kawar kuma matata uwar yayana"

"Naji kace kawar matar ka ce Kuma ka aureta,shin Auren soyayya kuka yi ko kuma dai Auren ta kayi sabida ta rufa maka Asiri game da zargin da ake ma akan kayi wa yarinya fyade?zaka iya gayawa kotu yanda aka yi Kuka yi Aure"? Ya Kuma akayi kayi wa muhasim fyade"?


"Ita dai Luba kawar matata ce zan iya cewa Aminiyarta ce a lokacin da muka yi aure ita batayi ba sai daga baya,ni Kuma a lokacin bata jima da auren ba na samu scholarship na fita waje Kara karatu.
Ta silar matata na santa matata na mugun santa da har nake ganin bata kaunar b'acin ranta akan nawa,daga baya ma na lura ita kawartata ba matuniyar arziki bace ba sabida halayensu ma bai zo daya ba,tana da san kai da san abin duniya,a lokacin da ta kashe aurenta sabida mijinta bashida hali naso rabata da matata dan duk Wanda zai rabu da kai sabida babu ba mutumin arziki bane ba.

Koda na nemi matata ta rabu da ita k'i tayi a san na faranta mata na rabu da ita badan Raina naso ba dan gani nake yau da gobe zata iya sawa matata ta canja hali itama.

Tiryan tiryan Salis ya bada labarin yanda Luba ta hau bibiyarsa yana wulakanta ta sabida bazai iya auren cin amana ba har zuwa yanda Suka tare a sabon gida ta saka masa magani a

34 / 38