Idan Kaya Ya Gaji Gammo Ma Ya Gaji 4 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Fareesa Category :  Romance

Chapter   9 / 28

24K to 27K   out of 83.6K words

mu saukeki Labbai zata zauna da lolo sunce ma zuwa gobe zasu sallameta da yau ma suka ce to tunda dai har tara tayi sai kuma gobe"
Sallama Rakiya tayi mun ta kwashe kwanuka ta tafi dasu. Labbai ta hayo gadon tace.
"Mun dai sasanta kanmu da Cicib ke wai kinji kalmomin soyayya lolo illahirin kunya ai lulluSeni tayi. Gashi yanzu gidanshi muka koma da zama. Da yamma ma ni da Shafan shi mukai wanke wanke. To Allah yasa hakan shine alkhairin. In da rabo watarana zai daina daudun zan yi ?o?ari ko Allah zaisa in zama sila. Lolo ki taya ni murna da adda'a"
Wallahi ba ?aramin mugun tausayin Labbai naji ba. Har ga Allah nasan bata da zaSine yasa ta amince zata auri Cicib domin samun mafaka da zama a shinfiWar aure. Amman meye abun burgewa tattare da Cicib illahirin jikinshi babu inda baya lan?wasawa in yana tafiya. Maganarshi kuwa ko tsohuwar karuwa albarka. Amman shima bashi da laifi ta fuskar zati fuskarshi ma ta mata ce, kuma yana da haske saidai yana ?arawa da man shafe_shafe dai
Ajjiyar zuchiya na sauke nace.
Allah ya sanya alkhairi Labbai. Yanzu acan zamu zauna kafin dai a gama ginin gidan ko? "
"Eh a canne. Maigogul fa kuWin haya mijinki ya bashi kinsanshi da maganar kuWi ai.
Ga Sama da Rita suma sun zo suna can gidan wai notis ashe aka basu wata shida to yau ita matar ta tafi aiki, shima ya fita mai gidan yazo ya kulle gidan shine suka rankayo amman matar tasa ana nema musu wani gidan hayar ko a layin su Cicib Winne. "
Iko sai Allah wannan mata ta Sama tana ?o?ari so hana ganin laifi kenan. Yanzu bil ha??i tana son Sama ko Labbai? "
Dariya muka saka harda tafawa tabb
Raujin amon shigowar sa?one ya katse mana hirar tamu.
Ina buWewa ga abinda Alhaji Zaidu ya rubutu.
"Watarana uwar haka a cikin wani dare makamancin haka kina ?irjina ina shafar kanki.
Ni Zaid zan nuna miki gata zan tarairayeki sai na mayar dake fil.
Kiyi bacci mai cike da mafarkan rayuwar aurenmu
Sai da safe jinin jikina.
Mijinki Zaidul'abidin."
Tunda na lumshe idanuna sai kawai na kasa buWewa na shiga wani shau?i mai girma
Jijiyoyin jikina sai amsar sa?on Alhaji Zaidu take yi. Man kaina sai tsiyaya yake yi
Sai kuma naji na faWa fargaban shin danginshi zasu karSeni da mutunci kuwa, matarshi fa wanne irin zama zamu yi?
Da wannan tunanin na jiyo wayar Labbai na rauji Darling Cicib ne ya kirata sun kuwa daWe ainun suna wayar har saida tace mishi bacci take ji.
Washegari ?arfe taran safe aka sallamemu maigogul da mota yazo ya Webemu zuwa can gidan.
Ni dai ina saka ?afata a gidan illahirin mamaki ya kamani.
Dukka ?an gidanmu da iyalan cicib suna tsakar gida kowa fa da abinda yake yi.
Masu karyawa nayi, masu kwalliya nayi, masu wanki nayi.
Gaza dai yana gefe shi da Madamcy suna zuba ma su Rahine abinci.
Uzairu zuchiyata yana kwance a Waki duk jikinshi na cikin Wakin kanshi ne kawai a tsakar gidan yana waya dan masifa ko jin abinda yake faWa ba'ayi.
Rakiya ta yi gurum da kofin shayi a gabanta ga mummu?i a hannunta amman fa bata sha.
Hauwa dasu Layuza suna zaune suna cin Wumamen tuwo ga balango mai yawa an watsa akan tuwon. Jin shigowarmu yasa hankalinsu ya dawo garemu
Cicib yana tsaye yana shanya a igiya murmushi yake ta sakar ma labbai da ?yar na haWiye dariyar tawa kusa da kan Uzairu zuchiyata na rarrafa na zauna. Shima Uzairu zuchiyata sai mur?ususun dariya yake yi danma waya yake yi
Nan aka shiga yi mun yaya jiki.
Layuza ma a taSe ta tambayi jikina. Raliya tace.
"Lolo ashe kuma an Waura miki aure, ai ni bansan ma auren ya mutu ba sai da nazo tukunna nake jin wasu labarai a wajen Hauwa ashe har kotu aka shiga"
Wallahi kuwa Raliya ke dai ki bari kawai. Yaushe kika zo ina kuma yaran? "
Maigogul daya nemi waje ya zauna yace.
"Suna ciki yara har bakwai ta tarkato suka tawo a cikin irin wannan ?adamin. Raliya sai tafi shekara biyar bakwai bata ko le?o ba. Ko haihuwa tayi sai dai wataran inji a wajen Hauwa. Ita kanta Hauwan fa bata san ta haSaka yara haka ba. "
Hauwa tace.
"To wai me akeyi ne da sai dole tazo. Na gabanka ma baka gama dasu ba me kake tsinana musu. Raliya dai kaga yadda dai ta koma kamar ita ta haifeni bani na haifeta ba tsabar muni da lalacewa ta riga da ta dafe ma"
Rakiya tace.
"Amman ai ko bazai tsinana mata komai ba yana da kyau tazo ta duba ubanta ko? Duk dai lalacewarshi ai ubanta ne. Sai fa Raliya ta shekara biyar kyawawa bata tako tazo ba. In ta tashi zuwa sai dai a ganta raSe _raSe da goyo da ciki babu uban abinda take kawowa. "
Gaza yayi dariya yace.
"Ni da ?yar ma na ganeta naga ta dawo ba?a. Ko ni nan da nake busa haya?i ai ban kaita eh duhu ba. Ma'aru Webo mun ruwa in ba Rahine kaji"
Ma'aru ya tashi yana dariya ya Webo ruwan ya kaima Gaza.
"Lolo amshi abinci ko zaki iya ci tuwone harda yajin daddawa"
Cewar matar Cixib godiya nayi mata na karSa. Adama ta haWa mana shayi a ?aton kofin silba ni da Labbai muna ci ana hira.
"Dama sakina hallirun yayi harma na gama iddata shine dalilin dawowar tawa"
Rakiya har da ?warewa. Hauwa kuwa salati ta saka.
"Ahab ni wallahi nasan za'a rina ai ruwa baya tsami banza. Wato Raliya sakin ki akayi sai kika tuno ai kawalin ubanki yananan babu shakka. To kai Maigogul kaji"
Mu?ewa yayi ya shiga tukuntuma ashariya.
"Shine kika tawo mun da bataliyar yaranki dukka? Lallai baki da hankali taraliya. Hiye daga ke har Hallirun baku da madafa. Shi ya sako ki, ke kin tarkato yara kin tawo dasu.
Kinsan Allah sai sun koma. "
Sama yace.
"Eh gaskiya su koma taya ma za'ayi wannan aikin. Yara bakwai ai da yawa. Lokacin da kike gidan auren nunawa kika yi bakya bu?atar uban kowa yazo miki sabida ke ?ar iska ce ?ar tsakuwa samu ki ?i dangi. Yanzu data kwaSe miki shine zaki kwaso yara haka."
Raliya tace.
"Nifa zan ri?esu haya ce zan kama in zauna dasu kamar dai yadda su Adama suka yi. Nasani nima bazan samu muhalli ba bare su"
"Ke ?arya kike yi. Yarannan fa a raba Halliru ya Webi nashi su ragowar ki tarkata ki kaima takarin ubansu inma takarancin zai tafi dasu laba'as amman yau ba gobe ba zaki mayar dasu".
Rakiya tayi shewa tare da jan tsaki tayi shigewarta ciki.
Nima Wakin na shiga na kwanta a katifa idanuna a lumshe ina shirin soma bacci wayata ta soma ruri.
Da mugun sauri Maigogul ya shigo ai kuwa ya runtumo akan Uzairu zuchiyata daya tattare ?ofa.
Da sauri ni da Rakiya muka mi?e.
Hannun maigogul na ri?e ya samu ya Waga Uzairu zuchiyata da yake ta faman wash ?afafuwanshi
Ga kuma dariya kamar zata halakashi har hawaye yake yi tsabar dariya. Dariya maigogul da Rakiya suma suke yi.
"In banda iya shege ya zai zo dokin ?ofa ya kwanta. In yana waya da baturiyarshi baya ji baya gani. Lolo wayarki ce take ruri ko hala Alhaji Zaidu ne. Dan Wazu ma munyi waya nake sanar mishi an sallamoki. Harma na shigar mishi da wata ?ar bu?ata. "
Dam gabana ya yanke ya faWi. A dibibice nace.
Amman maigogul gaskiya bai dace ace ka shigar mishi da wata magana ba. Umara ya biya mana ga gyaran gida zai mana dan Allah Maigogul kayi...."
Kasa ?arashewa nayi bana so ko da wasa in faWa mishi magana mai zafi. Amman ina tsoron kada Alhaji Zaidu yaga kamar bamu da kai"
"A_a Lolona ba wani abun mai girma na tambaya ba. Dama abincine nace ko zai siyo kayan abinci ya jibge mana sabida ni ina jinyarki bazan iya fita ba. Wallahi yace ma ya riga da ya siya suna bayan motarshi tun kafinma inyi maganar. "
Salati Rakiya ta saka. Niko saida hawaye suka zubo mun ?irjina sai dokawa yake yi. Shikenan duk abun kunyar da akayi a gabanshi bai isaba Maigogul shikenan ya samu nayi zaici gaba da Sarar mun da mutuncina.
"Amman Maigogul baka kyauta ba gaskiya wannan wacce iriyar rayuwace. Yanzu duk Wawainiyar da wannan bawan Allahn yayi bai isheka ba. Jibi shayi mai madara yau waye bai sha ba a cikin gidannan. Harfa biredi yau da kuWin jikinka ka siyo kowa yaci duk da dai Allah kaWai yasan nawa ka tatsa. "
Kuka kawai na fashe dashi da naga suna rikici.
Wayarma ya sake kira na kasa Wauka
Maigogul ne yazo yana share mun hawayen da rigarshi.
"Yi shiru lolo bazan sake ba. Duk ma abinda nake so sai nazo na tambayeki tukunna. Dama shine yace duk abinda ake bu?ata in sanar mishi.
?auki wayarki kinji ta Maigogul shalelena"
Uzairu zuchiyata mai zaiyi ne in ba dariya ba.
Hannun Rakiya Maigogul ya fisga suka fice.
Ni kuma na Waga wayar da kira na uku ya kusan tsinkewa.
Ajjiyar zuchiya naji ya sauke da ?arfi.
Ni kuma illahirin kunya tasa na kasa magana
Tagumi Uzairu zuchiyata yayi yana kallona.
"Shalelena ina kika shiga ko jikinne hankalina ya tashi sosai. Duk da Wazunnan muka yi waya da Alhaji Baba yake sanar dani an sallamoku?"
Uhm an sallamomu ina tsakar gida ne lokacin daka kirani. "
"To ina kwana tunda ni ba zaki gaisheni ba"
Kunya ta sake kamani ba shiri na gaisheshi.
"Gani a hanya zanje office daga office kai tsaye Dutse na nufo ko akwai abinda kike bukata na ci ko sha in tawo miki dashi? "
A_a bana bu?atar komai. Ubangiji Allah ya tsare maka hanya"
Wallahi jina nake kamar duk a mafarkine komai yake faruwa ba gaskiya bane. "
Da haka mukai sallama na yafito Labbai da Sadiya suka shigo nake labarta musu zuwan Alhaji Zaidu.
"To me kike ganin za'a dafa mishi Lolo tunda kinga dole zaki shigo dashi ya huta yaci abinci ko? Ga gid dan?am da al'umma kamar bakin masallaci "
Kafin in yi magana Maigogul ya shigo yaji akan duk abinda muke tattaunawa cewa yayi.
"Kada ki damu Lolo ni zan miki girkin da zaki tarbeshi dashi. Zan Wauke ki muje mu yo cefanen komai tunda akwai mota a hannuna kada ki damu"
Murmushi kawai nayi. Wallahi inason Maigogul sosai.
Hakan kuwa akayi bayan nayi wanka, shima.
Ya kintsa Maigogul ya Waukeni a gaban mota muka je muka yo cefanenmu yana ta bani labarai muna ta dariya.
Kaza muka siyo da mai, kayan miya, ruwan gora, da 5alive, sai taliya leda uku, da su karas, kabeji, latas, da koren tattasai, da jan tattasai, sai madarar gari. Kula na cire kuWi na siyo mai uku masu kyau farare, na sai kafet na tsakiyar Waki sabo fil muka dawo gida ana kiraye_kirayen Sallar azahar.
Maigogul na dawowa masallaci ya kuma yo wanka ya zura sabuwar ba?ar jallabiya dan s kwalima ya yage ta.
Ai kuwa ya aika aka siyo mishi kalanzir ya gwafe ya shiga aikin girki.
Ni dai ina kwance a tabarma a waje ina kallon yaran Raliya yadda suke ma gadamur?i cin hauka ko sha?esu bayayi ne oho. Raliya kuwa illahirin kunya ta kamata da taga su nake kallo.
Wayata ce ta shiga ruri Alhaji Zaidu ke kirana.
?agawa nayi da sallama ya amsa mun.
"To yanzu zan kamo hanya shalele na tsaya ne ma a danja zan siyo miki gurasar kano mai sikari kike so ko mai gishiri, ko kuwa duka biyun? "
Murmushi nayi mishi tare da cewa.
Duka biyun. Mai sikarin akwai daWin ci da shayi sosai "
Dariya yayi mun kawai yace.
"To shikenan saina iso ko. Ki turo mun adireshin gidan yanzu a waya inna zo ?ofar gidan zan kiraki sai ki yi mun iso. Ki saka mun kaya mai jan kala a jikinshi"
Murmusawa muka yi tare dashi. Da haka mukai sallama na ajjiye wayar tawa.
Labbai ce ta fito daga cikin Wakin Rakiya.
"Lolo na gyara Wakin dai an shinfiWa ?atuwar taburmai biyu ya rufe ?asar Wakin. Kafet Win sai na saka shi daga ta bango haka zaifi.
Nace tashi in miki tsifa kitson ya tsufa in yaso ko rubon kya saka ki kama gashin.
Tashi lolo saifa kin dage sosai zaki samu zuchiyar mijinki a hannunki"
Maigogul na kalla dan in tabbatar baya jinmu. Ina baya ji ya du?ufa sai kaji yake soyawa ga gidan Hauwa bata nan Rakiya bata nan. Sauran ?an matan kowa bayanan. Sama da matarshi wai sunje ganin Waki ance an samu a ?asan layinnan.
Kafin dai la'asar Maigogul ya gama komai ya barma Adama ta zuba a kula ta jejjera a Waki ragowar kuma ya zubo ma Labbai da Adama dake bacci, ya yafutama su Shafa, Raliya dai da yace bazai bata ba da ?yar na ro?eshi ya zuba musu yaranta suka daka ma abincin wawa.
Ni da Maigogul kuwa a tukunyar muka ci abinci kamar dahuwar kamfani dan daWi soyayyar taliyar inna zuba a baki kamar kada in dena taunawa maggi yabi taliyar yayi lub dashi.
Muna gama ci shi yayi sabon wanka ya sake kaya ya fice.
Adama kuma ta gyara wajen.
Bayan na idar da Sallah ina gaban mudubi ina shafa kwalli, na saka jar atampata mai tsada sosai, na Wakko jan Wankunne da sar?a sababbi na ma?ala. ?aurin ture kaga tsiya nayi har ribon Wina dana tubke gashina ana hangowa, tsayin jelar gashin iya kafaWata sai dai gashin bashi da cika la?wam haka yake, gashi duk ma ya zube sabida rashin kwanciyar hankali na kaWar da gashi sosai.
Ina fesa turare yaro ya shigo wai Sabuwa tazo.
Ni dai jikina a sanyaye ina haWa hanya na fita.
Nayi mamakin da Alhaji Zaidu bai kira wayata ba ya turo yaro.
Ina fita gabana ya yanke ya faWi.
Hmm wai kunsan wa na gani kuwa?
Nasan kun ?osa ko to Madubala na gani cikin shiga irin ta mutunci da kamala gabaki Waya kamanninshi sun sauya fiye da tunaninku.
Madubala kaine? "
Na furta muryata na rawa. Takowa yayi yazo inda nake yake ta murmusawa sai kallon soyayya mai cike da kewa yake yi mun.
"Da ace zaki iya taSa ?irjina da kinji yadda zuchiyata take watsa jini da sauri _sauri bisa rashin ?a'ida. Sabuwa ga madubalanki mai so da ?aunar ganinki a cikin farin ciki. Wanda zai iya bada ranshi fansa a gareki. Nazo in auri abuna duk da lokacin dana fito akace mun tuni kinyi aure lokacin yaranki uku ma. Zafin hakan yasa na koma inda na fito ban sake tako ?afata na shigo Dutse ba. Naji labarin mutuwar aurenki, naji labarin aminiyarki dake auren mijinki na da. Sabuwa a cikin idanun ?ar Shuwa babu komai sai ?iyayyarki gayatan. Banzo gareki bane har saida na tabbatar kin gama iddarki.
Gani nazo miki a matsayin nutsattsen mutum mahaddacin Qur'ani mai halastacciyar sana'a Sabuwata"
Tunda ya matso kusa dani daf ya soma maganarshi nake hawaye nice harda shesshe?a.
?ago kan da zanyi muka haWa idanu da Alhaji Zaidu tsayuwar motarshi kenan idanunshi a kanmu ?ur. Gabanane ya tattake ya faWi
Banyi aune ba naji tsumma a fuskata Madubala na share mun hawayena.
Mrs bukhari.

Gobe Alhamis ba Posting haka ma Juma'a, asabar ma dan girman Allah kada kuyi ?orafi babu Posting sai ranar lahadi.
Wallahi abubbuwane a gabana inata haWa kayan turarukan wuta na masu adashene asabar nake son in sallami kowa to aimun wannan alfarmar nagode=??? [10/4, 10:29 PM] +234 810 593 2041: MRS BUKHARI
8




A hankali Alhaji Zaidu ya sakko a cikin motarshi.
Yana saye cikin farar shadda Winkin malum_ malum, zannar dake kanshi ta matu?ar dace da surfanin gaban malum_ malum Win. Tsintsiyar hannunshi saye da ba?in agogon fata wanda yayi lub akan gargasar dake lulluSe da fatar hannun nashi.
Ba?in haf koba ne a ?afarshi kamala da natija su suka sake ?awatashi. Yafi Babangida kyau da zati sosai, fari Babangida zai nuna mishi da tsayi sabida su su Babangida tsabar tsayi har dorone da mazan gidan nasu.
Sallama yayi mana yana kallon ?wayar idanuna illahirin kunya a wannan lokacin rasa yaya zanyi nayi. Wallahi Allah ba zaku gane bane, ban tsaya domin wani abun ba, kuma jin saukar tsumma kawai nayi a fuskata ba tare dana ankara ba. Wallahi Allah jikina har rawa yake yi a wannan lokacin, a tunaninku zanso wani abun ya Sata ma Alhaji Zaidunku raine? .
Da naga ya mi?a ma Madubala hannu sai nayi zuruf na shige gida gabana nata aikin faWuwa.
Shiru nayi a Waki idanuna a runtse inajin wani irin tashin hankali maras musaltuwa domin bansan wacce iyakar fassara zai yi mun ba.
Muryar Alhaji Zaidu naji a tsakar gida suna gaisawa da Labbai tana mishi iso.
Ita ta soma shigowa ya biyo bayanta da sauri nayi ?asa da kaina kawai.
Gefe ya samu ya zauna suka gaisa da Labbai muryarshi babu daWi gaskiya.
"Anty a nan gidan kuke zaune naga ai gidan kamar ba'a gama gininshi bama. Sannan ai gidan yayi muku kaWan ma"
"E gidan Abokin Maigogul ne. Shine yace muzo mu zauna tukunna"
Shiru yayi can naji yana waya yace.
"Alhaji Isa gani a dutse wanne gida zan samu da zaka bani ko na haya kona siyarwa mai kyau mai girma"
Idanuna na lumshe hawaye suka wanke mun kwalliyata tas har ji nake numfashina na Waukewa.
"To shikenan ka tura mun lambar kiya teka Win sai ya zazzagaya damu muga wajen nagode sai na jika"
Wayar ya kashe yace da Labbai.
"Ku shirya zamu je ku ga gida, inaga gara a sai gida kawai ku shiga sabida ita Shalele ta samu ta tare a Wakinta zanfi samun nutsuwa da kwanciyar hankali. Alhaji Baba baya gidane? "
"E ya fita, amman Babu damuwa akwai wanmu Garzali ko dashi sai mu je babu damuwa. Allah ya saka da alkhairi Ubangiji Allah ya zaunar daku lafiya"
Murmushi kawai yayi ba tare daya amsa ba. Yace.
"Amman babu damuwa kuna ganin ba sai an kira Alhaji Baba ba kuwa ko in kirashi ne?"
Ni dai bama gane mai suke cewa nake yi ba.
Naga dai Labbai ta fita Wakin ya rage daga ni sai shi tsit babu kalma in Wago na kasa. Amman inajin idanunshi na yawo a jikina hawaye sai Wiga yake yi

9 / 28