Idan Kaya Ya Gaji Gammo Ma Ya Gaji 4 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Fareesa Category :  Romance

Chapter   27 / 28

78K to 81K   out of 83.6K words

ne na tambayeshi.
Masta kunyi waya da Hajiya ta samu sakkowa daga sama kuwa, ya kuma jikin nata kunyi waya kuwa? "
Murmushi yayi ya matsemun hannuna da yake ta murzawa tun tasowarmu.
"Kina ji da Antinnan taki. Hajiya munyi waya jikin dai tace babu laifi Hajiya Mansa ?awarta tazo shine ta Wan warware"
Kai na gyaWa nace.
Allah sarki wannan Hajiya Mansan tana ji da Hajiya sosai "
"Ahh tsakaninsu sai dai a barsu aminiyarta ce sosai. Amintakar tasu ma muma saida ta shafemu tsabar yadda shi yake yawan kawota gida, da yadda nima nake yawan zuwa kaita ko Wakkota. Kuma kasuwanci iri Waya suke yi. Wazirat al sa'ada Baban Rahine gobe zai zo fa, zai sauka a can gida sabida zamu je dashi kamfani in zazzagaya dashi ko'ina ko? "
Allah ya nuna mana ameen hakan yayi nagode sosai Masta"
"Masta ko? Zaki ga masta bari dare yayi zaki yi bayani da manyan ba?i uhm"
Dariya muka yi dukkanmu.
Maigadin gidansu Uzairu zuchiyata ne ya wangale mana get muka shiga muka ajjiye motarmu a rumfar motoci.
"Ki yi zamanki al sa'ada zan buWe miki da kaina"
Fita yayi ya zaga ya buWe mun motar. Yana murmushi ya mi?o mun hannayenshi, nima ina murmushin na Waura hannuna a hannun nashi na fito. A jere muke tafiya har zuwa ?ofar shiga falon. Mun Wan jima muna bugawa har zan kira Maigogul sai ga Wan masu gida ya buWe mana yana saye da gajeren wando da amles Waya daga cikin kayan da muka je Canada.
"Ahh ashe manyan ba?ine damu. Na zaci su Labbai ne har suka iso ai. Alhaji bismillah, ke kuma ki koma Lolo"
Dariya muka yi dukka Uzairu zuchiyata ya bamu hanya muka shiga tare da ya da zango a falo.
Gaisawa Uzairu zuchiyata suka yi da Alhaji Zaidu. Ya dubeni yace.
"Ke bakya gaisuwa ko lolo zanyi maganinki. Ka ganta Alhaji gani take yi ma ta girmeni sabida kawai ina abokinta"
"To ai Yaya Uzairu ai ?awarka ce shi yasa, bana shiga tsakaninku hakane Wazirat al sa'ada uhm? "
Ya ?arashe yana kallona cike da kulawa.
Uzairu zuchiyata ina ganinshi yana haWiye dariyarshi. Fitowar Maigogul saye da jallabiyya ba?a da carbi a hannu ne yasa Alhaji ya dena kallona. ?amshinshi ya karaWe falon har haske da wani kyau naga Maigogul ya ?ara yi wallahi to ya samu nutsuwa.
"Alhaji ashe kun ?araso. Haba nace ma ita Hajiya kamar ana buga ?ofa ashe dai kune"
Tsugunnawa Alhaji Zaidu zaiyi Maigogul ya ri?eshi.
"Dan mahammada rasurulillahi ka dena ba girmanka bane kai Uzee maza je kasa a kawo ruwa da abinci. Bari in kirawo Hajiya"
Saida ya zaunar da Alhaji Zaidu a kujera kana ya tafi bagazan _bagazan jallabiyyar tana ?ara.
Mai aiki ce ta kawo mana abun sha, Uzairu zuchiyata kuma ya kunna mana TV sai ga Hajiya ta fito tare da Maigogul tana a cikin ado abunta sai fara'a take yi.
"Alhaji Zaidu kai da Amaryane a gidan? To sannunku da zuwa"
"Mun same ku lafiya Hajiya? "
Ya faWa kai a ?asa.
"Lafiya lau ya Hajiya da jikin nata ince dai ta warke ko? "
Jikin da sau?i Hajiya ina wuni? "
Na faWa ina dariya. Itama da dariyar muka gaisa.
"To taso mu shiga ciki kinji ga la'asar ma tayi suma nasan masallaci zasu shiga. "
Jakata na Wauka nabi bayanta muka shiga Wakinta.
Ina zaune akan kujera Maigogul ya shigo ita kuma Hajiya tana gaban firich.
"Lolona bari in yi alwala muje masallaci mu dawo sai inzo muyi magana kafin su Labbai su ?araso ai zaku jira zuwansu ko? "
E zamu jira Maigogul ka faWa mishi"
"To to shikenan zamu yi maganar"
BanWaki ya shige.
"?ata ga wannan sha rabi"
Ta mi?o mun wani abu kamar tsumi a gora na buWe na sha rabin da tace mun in sha.
Wani ta kuma bani a kofi na shanye.
Maigogul ya fito ya tsaya a gaban madubi yana ta fesa turare.
"Hajiya zamu je masallaci, babu wani abun ko? "
"Babu Honey adawo lafiya Allah ya tsare ya kare"
"To ameen Hajiyata"
Ya ?arashe da dariya ya fita.
Nima dariyar nayi Hajiya Balaraba tace.
"Dariya iyayen naki suka baki Lolo? Bari in dama miki wannan gumbar ta musamman je ki Wauro alwala kafin in gama"
Mi?ewa nayi na Wauro alwala na fito ta bani gumba damammiya taji nono wadatacce na shanye tas na tada Sallah ita kuma ta fita.
Ko wacce kusurwa ?amshin turaren Anty Badiat yake yi turaruka masu inganci da kama waje babu algus kenan, sai dai kace yai tsada ba dai kace bashi da kyau ba. Gaskiya kana kunna turarenta wlh kasan ba da ka take aikinta ba, cikin ilimin abun take yi. Humrar matan aurenta da Kulaccham Winta ta matan Aure mai suna Laiya wato dare gaskiya duniya ce.
Ina zaune akan sallaya na kira Adama da ?yar na sameta.
"Hmmm Lolo gani a gaban tukunya ina aikin tuwon dare na bataliyar gidan Alhaji.
Nadawo kishiyarmu tayi yaji wai ita ba zata zauna da yayar Wan daba ba. Ragowar matan kuma sun dasa kishi sabida sunga yadda na sake kyau da kuma kayayyakin alatu dana tawo dashi. Ke ni dai ganinan dai"
Ajjiyar zuchiya na sauke nace.
Amman Adama me kike ganin zaki dinga siyarwa da sai in baki jari ki Wan dinga jujjuyawa, nima in da kasuwancin naki zaiyi ?arfi sai in saka kuWina ko Wan kunnena in siyar ki dinga juya mun.
Duk da gobe zan soma zuwa ofis kuma ina da albashina"
Adama tace.
"To Lolo da kuwa naji daWi zanyi tunanin da Wan bincike inga mai ya dace in yi. Zan kiraki gobe da safe, kafinnan na Wan nutsa."
Da haka mukai sallama hayaniyar yaran gidanma ta hana in jita da kyau yadda ya kamata.
Mai aikice tayi sallama ta shigo da kula biyu a tire da robar zuba abinci da cokali harda abun sha ta ajjiye ta fita.
Abinci na zuba tuwone na shinkafa miyar nama dagargajajje ina saka abincin a baki na saki dariya wannan WanWanon girkin Maigogul ne tabbas. Wato shi yake girki soyayya daWi su Kayi nayi ana can uhummmm
Ina cikin ci Hajiya ta dawo.
Abinci yayi daWi ai Maigogul ya iya abinci sosai.
Dariya tayi tace.
"Hiye ashe har kin gane abincin Babanki ne wannan? Uzee ma yana ci ya gane, dama yace har a can Dutse yana musu girki in ta ciciyoshi.
(Miyar namannan duniyace wallahi daWinta baya musaltuwa itace asalin miyar da malam Bahaushe ke cema tuwon girma miyar nama=??)
Muna haka Maigogul ya shigo ya nemi waje ya zauna.
"To ni kam bari in baku waje ku Wan zanta"
Cewar Hajiya data mi?e ta fita. Maigogul ya ?an?ance idanunshi ya kalleni fes.
"Lolo kinga kishiyarki ba ?aramar muguwar tantiriyar kiriminal bace. Amman in tasan wata bata san wata ba wallahi tayi da Wan halak. Yawon duniyana gogewar dana samu da buWewar ido, da ilimin rayuwa, da gogewa wajen karantar mata akanki zaiyi aiki. Taci sa'a na koma ga Allah da a dare Waya zan Sarar da ita ko wanne irin boka take bi. Ke ko oremi take mata aiki shugaban bokaye mace a ?abilar yarbawa to wallahi da inna dinga turen aljanu gidannan saita fita ta baki waje ni bana wasa bane amman sa'arta Waya dai wallahi al'mura
Mrs Bukhari
[10/8, 9:15 AM] BADA'AT IBRAHIM: MRS BUKHARI
22

wai ni kamar ni Maigogul kishiyarki ta zaunar dan ta bamu abinci take neman dukan cikina.
Kinji yadda take jero maganganu kamar wacce take karantawa a rubuce kuwa?
Lolo nayi mamaki gaya.
Tsam nayi inata nazari bata da gaskiya wallahi nina faWa miki wannan maganar.
Amman zan Wauraki akan kirsa da kisisina da maWe, da duk abinda kika sani na janye hankalin namiji.
Kema ki haWa da wanda kika sani. Babu cuta ba cutarwa
Kin zauna da kishiyoyi fin tara ko goma ma kada ki sake kiji tsoro. Jibi a sanadin wannan auren yadda na zama Lolo har mace na samu ta aureni inci ?wai, inci kaza, inci talo _talo in kwanta a ac ke ko wuta aka Wauke za'ayi maza a kunna jen sai mu kwana cur dashi, ga Wa ta ri?emun babu nuna ?yama.
Lolo ki buWe kunnuwanki da kyau ki saka idanu sosai akan Hajiya, ki nutsu ki gama karanceta fes, duk abinda zata yi miki kada ma ki nuna kin gane balle ki Sata ranki ko wani abun. Shi ya?i Wan zamba ne, da salon da take neman halakaki, dashi zaki yi amfani kema.
Ki fita kirki da kyauta, ki nuna ma mijin ai ke kinfi sonta sama da yadda take sonki. Da kanta zata zame jikinta asalin kalarta ta bayyana ta bada kanta. Kada ki sake ta gane logonki domin ko mutuwa zaki yi ba zaki gane nata logon ba. Daidai da rana Waya kada ki sake ki kai ?ararta wajen miji. Kada ki sake dangin miji duk sha?uwarki dasu su Webo magana su yi miki akanta ki tofa.
Mijinki kuma zagewa zaki yi ki nuna duk duniya babu yashi a wajenki ki girmamashi fiye da yadda take mai. Ki fita iya kwalliya ko da zata fiki da kaya masu tsada da gwala_gwalai kema da sannu zaki tara naki kayan adon, dan naga gwala_gwalai sawar alfahari take musu.
Ki fita iya rangwaWa da sauke ido da sauke murya
Ke ki mata fintinkau a ko ta ina, kuma ko da marinki zata yi kada kiyi faWa da'ita nuna mata jikinki bashi da wannan ?warin na faWa, da haka zata iya zagewa ta dakeki kinga ai asirinta ya tonu ko, dan dole aji ba'asi.
Shi kanshi mijin ki dinga narkewa kina yin abu kamar baki da ?ashi, ki ?ir?iri yanayin da zai zama naki ne ya ri?eshi har abada dashi zai dinga ganinki.
Kamar misalin
shagwaSa
Sanyin murya
SaiSi yayin wani abun
Yawan son jiki
Da shagwaSar nuna kanki na ciwo, ko zazzaSi kike ji dan Auna girman matsayinki a wajenshi da gwada yadda ya Wauki lafiyarki da mahimmanci. Wataranma ki barshi har asibiti kuje su basa rasa cewa ga abinda ke damun mutum, ko na maleria su baki ki watsa.
In zai fita ki haWashi da abinda zai ri?eshi har yaje ya dawo da tunaninki.
Lolo zan dinga zuwa akai a kai domin tabbatar da komai na tafiya daidai.
Sannan ki dinga yin sallar dare.
Hajiya Balaraba tace sirrin nasararta kenan kullum saita tasheni nima munyi tare kema ki ri?a yi ki dage kinga wannan Auren? Sai mutuwa in sha Allah. Kiyi iyakacin yinki wajen kafa kanki.
Kada kiga muna faWa da Rakiya ta cukumeni muyi dambe. Wallahi Lolo tasani sarai tana da matsayi na musamman ne a wajena. Wallahi Rakiya a zuchiyata bata da tamka. Tsiyarta ke haWani da'ita kawai. Yanzu nan haka taita aiko mun da ruwan zagi da ashariya ni dai sai kashe wayata nayi. Kinsan da yau zamu tafi Dutse wallahi wani abunne ya taso ma ita Hajiya amman gobe tare dasu Labbai zamu tafi"
Maigogul a wannan ranar saida ya buWe mun kaina ya wanke mun tas na zama sabuwa fil har wani ajjiyar zuchiya na sauke wallahi tsabar farin ciki.
Maigogul nagode sosai kuma naji daWi.
Amman ai inaga gara mu dinga yin waya ba sai kazo ba"
"Nanne kuma baki Waya isaba"
Ya hauni da tijara.
Ba wai sabida komai bane sabida ita Hajiyarne tunda mu bamu san manufarta a kanmu ba. Kada yawan zuwanka ya haifar da matsala, sannan ko bai haifar da matsala ba zai zubar mun da mutunci. Gashi kaga na shiga babban falimi kada dangin mijina su dinga zargin ko kana zuwane dan wani abun su fassaraka ai bazanji daWi ba.
Ni nayi maka al?awarin duk abinda Alhaji ya yanke mun na albashi zan dinga baka rabi duk wata amman su Rakiya zaka dinga yima cefane, in kuma suka ce baka yi. Kayi nayi zan koma turama, duk da itama na ware kuWin da zan dinga bata duk wata tana hidimarta dashi wannan yawon kayi nayi nake so ta watsar ta zauna waje guda taci abinda take so"
Shiru yayi can yace.
"Amman zaki mishi magana ya bani jari mai tsoka? Shagon saida yadinan maza da shaddajo, da takalman maza nake da sha'awar buWewa wallahi Lolo in dinga fita ina zamana Kano garine na kasuwanci sosai, Hajiya Balaraba ma mun tattauna harma ta ?aramun ilimin za'a dinga Winka wasu kayan ya zamana akwai Winkakku da marasa Winkin. Itama zata bada gudunmawa mai tsoka, shima ki mishi magana ya taimaka duk a gagganWa. Ita kayi nayin har nawa haka zaki dinga bata a watan to? "
Murmushi nayi nace.
Zan maka duk abinda kake so ko da kuwa zan siyar da gold Winane in dan?a maka kuWin. Amman Maigogul da sharaWin shagon zaka yi. Amman kasan kan harkar ne? "
Dariya yayi yace.
"Sabuwa kenan. Ai wannan Win tsohuwar sana'atane nayi yaron shago, kuma nasan harkar sosai a lokacin ogan ya buWa mun harkar sabida ya yadda dani sosai bana cutarshi barni da son kuWi amman bana Waukan na kowa. To shima fa ina zaman zamana yaran shagon sukaimun sharri wallahi inaji ina gani aka koreni a ba?ar leda kayana suke haka ya jefomun su kala uku bana mancewa"
Tausayi ya bani sosai nace.
Amman Maigogul ba zaka nuna mana dangin Mahaifinka ba, ko da bakasan dangin mahaifiyarka ba, tunda kace tare da iyayenta suka fito cireni, kuma dukka Allah yayi musu rasuwa. To tunda dangin mahaifinka sunanan mu nemesu mana"
"Hmmm yaro yarone akace ko da Wan giwane. Lolo ai waWannan mutanen barsu kawai. Kinsan Allah dani da Isuhu so sukai su kashemu ma sabida dukiya kawai. Lolo munsha azaba bata wasa ba, mahaifinmu yana da dukiya da tarin ra?uma da cilallai na gwal duk suka handame kuma suka sa muka bi duniya. Ni dasu har gaba da abada in sha Allah. Nace baki faWa mun nawa zaki dinga ba kayi nayin ba, nima baki faWa mun nawa zaki dinga bani ba Lolona"
Muryar Labbai ne ya katse mana hirarmu. Amarya labbai ta sha lace tayi kyau abunta.
"Ahh kuna ciki Maigogul kaine ka sake fari haka?"
Tana dariyarnan tata.
"To kinga yadda na koma duk na sake haske. Cicib Win na falo? "
"E yana can suna gaisawa da Hajiya"
Da gudu Maigogul ya kwasa ya fice.
Tafawa muka yi da Labbai.
"Sun haWu zasu tusa mijinki a gaba kuwa su zubar da galan_galan a gabanshi kuwa. Lolo manya kin samu duniya fa sai she?in Amarci kike yi"
Dariya nayi nace.
Nice nake she?i ko kece kike she?i ku gashi har kun tawo honimod Winku ni gani a nan harfa Abuja kuka je biki"
Dariya ta tuntsure dashi harda tsugunnawa.
Menene ya baki kuma dariya? "
"Wayyo Allah cikina"
Ta sake kwashewa da dariya kafin tace.
"Ke kinga Maman Shafa da Cicib yace mata zamu je Kano. Wallahi tuburewa tayi wai ita bata yadda ba, ita tunda nazo na janye mata miji. Dama zuwana matarnan ta sai siket na gwanjo in yamma tayi sai ta saka wallahi harda janbakinta majigi fa"
Dariyace ta kuma cin ?arfin Labbai wannan karon nima dole na dara wallahi. Duk da hankalina yana kan Alhaji dake falo duk da Hajiya na tsakaninsu dole wani abun ba zasu yi ba. Duk da in Maigogul da Cicib suka haWu babu damane.
Muna ta hira dai da dariya.
Taso muje in gaisa da Cicib. "
"Munafuka kiga mijinki dai zaki ce. Muje to, su Rakiya da Hauwa ma sunzo ganin waje ai.
Da zagi in zaga da Rakiya suka rabu. Ke har ri?e Maman Shafa akeyi wai zata daki Rakiya fa. Wai ke kinga dirama kuwa"
Muna dariya muka fito kafin mu shiga falo na saisaita kaina.
Idanu muka haWa da Alhaji Zaidu yana zaune a kusa da Cicib anata hira su Cicib shaddace dai ya saka amman babu hula gashi kanshi da suma sosai a cunkushe yayi na wata mace dan zaiyi kitso fes gashi ba?i kullum cikin yin dai yake. Ba kamar Maigogul da yake ado da furfurarshi ba.
Idanu Alhaji Zaidu ya lumshe yana mun kyakkyawan murmushi.
Gaisawa muka yi da Cicib wallahi kamar zai tsugunna mun sai kirana Hajiya yake yi sabida kwaWayi.
Gaishe da Alhaji Zaidu nayi da wata murya ta musamman harda Wan tsugunnawa ta gefen ?afarshi.
Maigogul ya jijjiga kanshi yana mun murmushin hakan yayi.
"Barka dai. Anty Labbai tazo shine na jiki shiru ko? "
Murmushi nayi wanda wallahi babu mahalukin dana taSa yima shi a rayuwa.
Ajjiyar zuchiya ?arama ya sauke.
Kaci abinci ka ?oshi ina fata ko? "
Kai ya Waga mun sabida kamar bazai iya magana bane.
Hajiya ce ta kira wayarshi, su Maigogul kuma suna ta hira dasu Hajiya har da Labbai Uzairu Zuchiyata kuwa baya nan.
Wayar na zare a hannunshi na matsa gefe na Wauka.
"YallaSai har yanzu baku tawo ba? "
Nice Hajiya. Wallahi kinga bamu tawo ba sai munyi sallah tukunna zamu tawo dake gida muka je Yayata ce tazo da mijinta.
Amma dama yanzu nake shirin kiranki inji yanayin jikin naki, in kuma baki ha?uri akan wallahi ni na ri?eshi laifinane ai mun afuwa uwargida ran gida"
Sai ta yi dariya har a muryarta cike da fara'a babu ko Wigon damuwa.
"Ahh Amarya kece ashe ai babu komai ni kaina na kira wayarki ma kafin in kirashi Wagawane baki yi ba shi yasa na kirashi ma.
Jikin da sau?i duk da a kwance nake wallahi komai ciwo yake yi mun. Da ?awata Hajiya Mansa tazo ne ma na ?warara jikin nawa"
Murmushi nayi mata nace da'ita.
Ayya Allah ya baki Lafiya Hajiya sai mun dawo"
"To Amarya mai maganar sikari sai kun dawo Ubangiji Allah ya tsare muku hanya ku dawo cikin aminci"
Datse wayar tayi, nayi murmushi kawai ina Wan nazari dai haka.
Dawowa falon nayi a lokacin Labbai da Cicib suna cin abinci Maigogul kuma yana jan Alhajina da hira, tunda dai na zauna Alhaji ya raba hankalinshi biyu.
Hajiya Uzairu zuchiyata fita yayi ne? "
Na tambaya ina fara'a.
"Uzzi ya fita ?ila ko gidan abokinshi Sagagi. Da mota dai ya fita"
Illahirin mamaki, lallai Uzairu zuchiyata ko kuma ince Uzzi ya cika tataccen baduniye.
Ina ganin Labbai na dariya.
Haka muka wuni a gidannan sai da mukai magriba muka ci abincin Maigogul kana mukai musu sallama Labbai tace gobe da safe zata shigo mun, nima nace dama akwai maganar da nake son mu tattauna da'ita mai mahimmanci sosai, sannan akwai sa?on Rakiya
Muna cikin mota hannunmu sar?e dana

27 / 28