Idan Kaya Ya Gaji Gammo Ma Ya Gaji 4 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Fareesa Category :  Romance

Chapter   5 / 28

12K to 15K   out of 83.6K words

ihu da tafi take wannan maganar abinda ya soma jawo hankalin su Rakiya kenan.
Sai ga Maigogul da Rakiya sun fito.
Dariya Gaza yayi tare jijjiga kai ya fisge hannunshi da Alhaji Zaidu ya ri?e ya zaro wu?a yaima wu?ar tsirara.
"Kutumar dumama yihuhu saini Gaza uban maza wuya a gida wuya a mararraba wuya a tafa wuya a dawo. Harmu za'a faWama iskanci mu da gidan Wan kande gidane a wajenmu. Kaga Malam kamar yadda ake yanka rago zan yanka matarnan. Ni da maza ma in suka ganni aron na kare suke yi bare mata. Ita kanta lolon zata iya farWeta balle ni Gaza kaji fa cika bakin da take yi"
Wannan ihu da kirarin da Gaza yake yi ya jawo hankalin munafukan unguwarmu har su Adama suma suka fiffito.
Alhaji Zaidu ya ri?e hannu Gaza kam suka shiga kici_ kici.
Maigogul kuwa hannu ya dun?ule ya zuba ma Matar Khalid dundu ba baya. Yana ta Wuma zagi.
Ban ankaraba naga Labbai a ruwan cikin Matar Khalid ta kaita har ?asa, Adama mai fama da hannu ma harda ita.
Gaza na tsaye Alhaji Zaidu na tausarshi bamu yi aune ba Magazin ya yanki matar Khalid a gefen kunne. Maigogul da Rakiya ne suka cabke mishi ?ugu.
"Rahine ku ?addamar mata"
Gaza ya ba karnukanshi umarni wallahi da ?yar Labbai ta rabata dasu Rahine ta faWa mota da mugun gudu ai da baya ta bar unguwar dan masifa har titi su Rahine suka rakata.
Da gudu na gangara kamar mahaukaciya na shige gidanmu a tsakar Wakinmu na faWi na sake sakin rushin kuka mai ciwo take na soma ganin duhu duhu babu zato babu tsammani numfashi ya katse.


"Ohh ni Maigogul Alhaji Zaidu kaine ashe kazo kazo ka tarar da rikici. Ke Rakiya ku shige ciki maza. Gaza mayar mai da wu?a gara da Allah yasa Alhaji Zaidu ya hanaka da yanzu wata maganar akeyi ba wannan ba. Kaida yaushe _yaushe ka fito daga yari kaima magazin ya kuma isa haka tunda dai ta tafi "
Wu?arshi ya mayar cikin gidanta ya dubi Maigogul yace.
"Allah taci sa'a ba a cake nake ba kuma ai baka ga yau ?an mutunci nake ji ba. Amman Allah eh da yanzu jini na kwarara anan mu za aima iskanci. Lolo fa tazo ta sha?e tana eh magana akan ?azamin mijinta wallahi taci sa'a macece da ace mijin nata ne da yanzu yana mace anan wajen."
Alhaji Zaidu wani jiri ne yaji yana Wibarshi tsabar kiWima da mamaki. Rakiya tace.
"Aikin banza ?ila matar Khalid Win lolo ce tazo za tai mana rashin hankali bata san gidan... "
Adama ta janye Rakiya suka shige ciki. Layuza ta taSe bakinta tace.
"Su lolo anji kunya matar farka har gida"
Da sauri Alhaji Zaidu ya dubeta cikin razana.
Maigogul ne yayi mata da?uwa ya cire takalmin ?afarshi zai jefeta dashi tayi ciki a guje.
"Labbai shige maza ki kirawo Lolo tazo"
A sanyaye labbai ta amsa ta gangara.
Maigogul yace.
"Alhaji ina zuwa bara in shiga ciki in saka a shinfiWa tabarma"
Yayi yin?urin zai haneshi Maigogul ya shige a guje yana saSa malum_malum. Da idanu cike da maWaukakin mamakin daya gigita tunaninshi ya buka kanshi yabi maigogul da idanu.
Maigogul kafin ya ?arasa shiga ya hau kwaWama Rakiya kira a gigice ya shiga gidan.
"Rakiya shinfiWa mana tabarma a ?ofar Waki Alhaji Zaidu zai shigo saurayin Lolo"
Baki Rakiya ta washe
"Au yanzu dama wannan mutumin mai haiba wajen lolo yazo? Uhm hiye babu shakka kaga yarinyar da aka haifa tsiya na bacci. Ai sai dai a shimfiWa mishi a ciki. Akwai ?an hana ruwa gudu duk gasu suje ma su soma farautarshi"
Hauwa tayi shewa tace..
"Rakiya kenan ke dai baki da aiki sai takale_ takale magana na zame miki ?arfen ?afa wallahi a gidannan kina da aure har kina kallon wani namijin kina ganin haibarshi"
"La'ilahaillahhau yanzu Rakiya biye mata zaki yi ba?o na waje? To shikenan kuci gaba"
Rakiya tayi dariya tace.
"Kaina bisa wuya Darling maigogul"
Dariya dukka suka kwashe dashi Maigogul yana dariya ya nunata da manuniya yace.
"Makirar mace kai Rakiya sai dai a barki"
Da sauri ya fice Adama ta shiga suka kakkawar da kaya aka shinfiWa tabarma harda feffesa turaren Maigogul a Wakin.
Maigogul ya fita ya tadda Alhaji Zaidu ?i?am a wajen daya barshi ya shiga dogon tunani da nazari mai zurfin daya wuce gaban misalin da al?alami zai iya rubutawa"
"Mu shiga daga ciki. Unguwar cike take tab da munafukai kaga ai sai zuruftu suke yi"
Ajjiyar zuchiya yayi kawai yayi ?undunbala yabi Maigogul izuwa ciki.
Yayi mamakin ganin gidan da irin kwaraSewarshi yanzu dama su Sabuwa da Uzairu zuchiyata duk wannan gayun nasu gidansu kenan.
Bai gama rabe Wayan biyu ba suka ?arasa ?ofar Wakin Rakiya yana saka ?afarshi Waya Labbai ta shigo a guje tana faWin
"Shikenan Lolo ta mutu shikenan Adama kuzo ku taimaka mun"
A guje Maigogul ya nufi hanyar fita yama mance Alhaji Zaidu na bakin ?ofar sai ji yayi ya rungumeshi.
Da sauri suka fito a gidan dukka gidan harda su Hauwa da Layuza.
Alhaji Zaidu shine har tsakar Wakin su Lolo tana kwance shame_ shame bata san wainar da ake toyawa ba.
"Alhaji Baba a Wakkota mu kaita asibiti"
Maigogul da Labbai ne suka sureta aka fito da'ita.
Shi Alhaji ya rigasu fita ya je ya Wakko mota aka shinfiWata a bayan mota. Maigogul yayi carab ya shige gaban mota.
"Labbai shiga muje maza ku Rakiya ku tafi gida babu komai Uzairu zuchiyata ma ya shige muje"
Labbai da Uzairu zuchiyata suka shige baya fuuu suka fice a layin a guje.
Gaza na ?arasowa inda su Rakiya suke Rakiya na kuka tace.
"Gaza Lolo dai ta bar duniyar shikenan hankalin kowa ya kwanta"
"Ahh ban gane ba wani abunne ya eh faru bayan na tafi ne. Ke madamcy shafa mun mana"
Madamcy ta faWa mishi yadda duk akayi.
"Rakiya Hauwa muje gida kunga eh jama'a sun soma taruwa zo muje"
Hannun Rakiya ya ri?e suka shiga gida.
"Bari a kira Labbai duk ma inda aka kaisu saita faWa mana Rakiya sai in kai ki.
Shi Uzairu zuchiyata dan abu ta kazanshi ai da shi ya zauna ke kika je.
Rakiya Uzairu zuchiyata anya ba mata maza bane kuwa? Naga abun nashi yayi yawa"
Rakiya ta sake fashewa da kuka.
Dariya Gaza yayi.
"Tabbb Rakiya eh ashe wai kina sonmu? Ni wallahi na Wauka ke da tsoho bakwa ko son ganinmu maganar fa gaskiya ku kuka lalata komai.
Ni wallahi eh har cewa nayi zan tambayeki anya kuma kinji zafin na?uda da zaki haifemu kuwa? "
Adama tace.
"Gaza gidanku meye haka? "
Dariya ya tuntsire dashi yayi ihu.
"Adama Adama matar dakacin ?auye ?onanniyar amarya. Ke wai kinga idon kishiyarki lokacin da nake kuikuya mata kuwa"
Hauwa tace.
"Ohh ni Hauwa Allah wadaran naka ya lalace gida sai kace gidan magajiyar karuwai"
Gaza ya harareta ya doka tsaki.
Wayarshi ya ciro ya kira Labbai akan in suka isa asibitin ta sanar mishi sunan asibitin.
Zama yayi a turmi yana shafa Rahine ga ?aton cikinta haihuwa ko yau ko gobe.
Rakiya kuma tayi shiru tana ta tunani.
Adama ma a zaune take ga ?una a hannu.
Suna isa asibitin Labbai ta labarta musu asibitin.
"Rakiya shirya ki Wan canja kaya muje. Adama ara mata takalmin ?afarki muje"
Adama ta cire takalminta tasa silifas Win fata na Uzairu zuchiyata.
"Amman Gaza wannan rigar farautan ni kam daka cireta dan Allah kasa wasu kayan. "
"Tabb wallahi bazan cire ba ina laifin kice in ajjiye makaman jikina dai tunda asibiti zanje"
Yana muzurai ya ciccire komai madamcy ta karSa.
Rakiya na fitowa Sama ya shigo gidan babu ko sallama du?un du?un dashi.
"Gaza muje maza kaji"
Cewar Rakiya kenan.
"Rakiya sai kun dawo to. Amman zuwa anjima in gado aka bata zan daure in yo girki in kawo, in kuma su Aisha sun dawo sai su kawo"
"A_a ke da eh kike fama da ?una tunda dai lolo ce eh ki ba Madamcy kayan girkin tayi. Inma gadonne ni zanzo in karSa musu abincin. Rakiya mu sakata"
Ficewarsu suka yi Adama da Sama suka bi bayansu da kallo.


Asibiti:.
Asibitin kuWi mai tsada Alhaji Zaidu ya tambayi Maigogul sabida so yake a ba Sabuwa kulawa ta musamman. Suna shiga aka amsheta cikin gaggawa Alhaji Zaidu da Uzairu zuchiyata suka nufi bakin taga inda za'a yanka muku kati. Maigogul da Labbai kuma suna ?ofar Wakin da aka shiga da lolo Labbai tayi tagumi kawai Maigogul kuma ?o?arin kiran Cicib yake yi a waya ya sanar mishi halin da Lolo take ciki.
"Helo Cicib ka gammu a asibitin kuWinnan da Alhaji Baraya ya taSa kwanciya Wiyarka lolo babu lafiya"
Cicib daga cikin wayar yace.
"Ma'aikin Allah na madina ni Cicib to banci ta zama ba kaga yanzu na ajjiye ha?ar?arina a gado zan kwanta kenan. ?iyarka Shafa auren nata ya mutu tana tsakar gida da uwar tata suna mayar da zance kasansu da rakin tsiya ganinan kaji"
Da haka sukai sallama Maigogul ya ajjiye wayar.
Uzairu zuchiyata da Alhaji Zaidu tare sukaita kai kawo har Waki yasa aka sake ma lolo aka maidata nata ita kaWai.
Dr ne ya nemi ganinsu tare suka shiga da Maigogul suka zauna.
"Jininta ne ya hau sosai gaskiya nayi mamaki da Sarin jikinta bai shanye ba tunda kunce kamar faWuwa tayi. Tana cikin damuwa mai tsananin gaske. Baba dama kunsan tana Wauke da waWannan manyan cutukan masu ruguza mutum hawan jini da cutar damuwa?"
Alhaji Zaidu ya ja numfashi yana jin tausayin rayuwar Sabuwa na tsirga mishi tako ta ina.
"Dafta mun dai san tana fama da hawan jinin tun tana gidan uban ?a?anta dan ta taSa yin wani ciwo da har saida muka zaci duniyar zata bari. To shi cutar damuwanne da kace ni wallahi bansan damuwa cuta bace wallahi ssbida ka ganni bana shiga damuwa kwata_kwata haka Allah ya yoni.
Dr yayi rubuce_rubuce kafin yace.
"Bata da aure kenan yanzu Baba? "
Maigogul harda share ?wallar makirci.
"Bata da aure yanzu. Burinta bai wuce ta samu miji nagari ta aura ko Allah zaisa ta samu nutsuwa ba. Dafta rayuwarce sai adda'a yayyenta duk zawarawane haka ?annenta ma. To ita mai saka damuwowin kowa a ranta ne, ga rashin miji na damunta sosai"
Da rishin kuka Maigogul ya gama maganar. Alhaji Zaidu yace.
"Alhaji Baba ka dena kukan in dai miji Sabuwa take nema tasamu a shirye nake da in aureta"
Ai sai sabon kuka Dafta da Alhaji Zaidu suka taru sukaita rarrashin Maigogul. Shi kuma sai godiya yake yi ma Alhaji Zaidu.
"Babu ai komai Alhaji Baba. Dr yanzu amman ya yanayin jikin nata yake? "
"To jikinta yayi tsanani akwai bu?atar a kula da'ita sosai. Sannan tana bu?atar terafis gaskiya a cikin depretion take sosai. In sha Allah zamu kula da'ita yadda ya dace sannan dan Allah banda zuruftun mutane, ko kuma mata su taru aita magana a kanta hutu take bu?ata in sha Allah jinin zai sauka. "
Dr ya jima sosai yana musu bayani daga ?arshe sukai mishi godiya Maigogul ya ri?o hannun Alhaji Zaidu suka fito. Suna shawo kwana Cicib na shawowa shima yana tafe salab_salab kamar ?wai ya fashe mishi a ciki yau dai jallabiyar ce kaWai a jikinshi babu Wankwali a kanshi.
"Yauwa Alhaji kaga wannan shine Cicib aminina kenan bashi da tamka. Cicib wannan sirikinka ne wanda zai auri Lolo"
Gaisuwa ce ta wanzu a tsakaninsu na minti biyu. Kafin Alhaji Zaidu yace yana zuwa zaiyi waya da ?anin mahaifinshi.
Gefe ya matsa can da nisa.
Maigogul ma ya ja cicib suna tafe yana labarta mishi abinda duk ya faru.
"Na taSaka da Alheri kishiya ta taSa kishiya da bakin wuta. Wallahi kada muyi sake wannan babban tajirin ya kuSuce mana. Wannan yarinyar in ka shiga ka fita ta shiga wannan haula sai fa munfi uban kowa morewa. Maigogul kayan tsubbunka suna adane ko? To ga a inda zaiyi aiki nan. Kawai kaje ka soma aiki."
"Kai dai bari Lolo ta shiga gidan Alhaji Zaidu ?ila harkar kawalcimma dainata zamu yi ya sama mana abun yi mai kyau"
Dariya suka saka Cicib ya ja shi suka koma ?ofar Wakin da su Labbai suke. Gaza da Labbai da Uzairu zuchiyata suna zaune suna tattaunawa Rakiya na ciki su Cicib suka ?araso. Yana hango Labbai ya soma washe bakinshi.
"Maigogul anya ba Labbai zaka bani ba kuwa in aura? "
A kunne yayi ma aminin nashi raWa. Shima maigogul raWar yayi mishi.
"Gaka gata in kun daidaita ni menene nawa cicib. Kai da kasan kana sonta shine kayi ?umun baki? "
Le?owar Rakiya yasa suka juyo.
"Maigogul a kira likita sai sambatu lolo take ta faman yi fa"
Uzairu zuchiyata ne yaje ya kirawo ma'aikatan jinya suka shiga Wakin Rakiya kuma suka ce ta jira a waje.
Duk suna zazzaune anyi cirko cirko.
Alhaji Zaidu ne ya ?araso bai zauna ba yace.
"Alhaji Baba inaso mu gana dan Allah"
Da sauri Maigogul ya jawo hannun Cicib suka nemi keSaSSen waje suka keSe.
"Alhaji Baba muddin babu damuwa ni kuma zan auri Sabuwa a yau ba ma sai gobe ba. Zanso ta buWe idanunta ta ganni a matsayin mijinta wala Allah hakan ya rage mata nauyin raWaWin da zuchiyarta take Wamfare da'ita.
Sai dai yana da kyau ayi bincike a kaina tukunna. Ni ba sai nayi binciken komai ba. Akwai Aminin ?anin mahaifina a cikik jigawa in kun bada damar a Waura auren yau sai yanzu inyi waya su tawo ayi komai. A hankali lokacin data shirya saita tare"
Tabb faWin farin jiki da irin murnar da Maigogul da amininshi suka yi wallahi yafi ?arfin gaban a kwatanta ma mai karatu. Take suka amince da Waurin auren ayau Winnan.
"To shikenan zan kira yanzu in sanar musu su kamo hanya kawai"
Hannu yasa a ajjihu ya ciro kuWi mai kauri ya ba Maigogul yace ko zasu yi wani abun dashi.
Ya matsa gefe yaita waye_ waye.
Maigogul ya kirayi ?aninshi Isuhu ya shaida mishi halin da ake ciki. Sai dai anyi rashin sa'a baya gari ya dai ce daga baya iyali sa zo gida.
"Cicib to kaifa zaka karSi auren lolo a ?ofar gidanka ma za'a Waura auren munafukan layinmu babu abinda zssu sani sai in zata tare ananne zasu ga biki"
Cicib ya kwashe da dariya yace.
"Ai babu damuwa dama Sabuwa ai tamu ce. Kai yau muna cikin alkhairi dumu _dumu Maigogul komarmu ta kama babban kifi. Mu tafi a sanar dasu Rakiya halin da ake ciki sabida ai ya kamata ace anyi girki sabida ba?i shi tuwon girma miyarshi nama"
Rankayawa suka yi ?ofar Wakin da lolo take su Rakiya duk suna zaune Maigogul ya labarta musu abun alkhairin da suke ciki. Murna a wajen waWannan mutane bata faWuwa.
Nan da nan aka tashi Labbai da Uzairu zuchiyata zuwa kasuwa domin siyo abinda ya dace.
Nan da nan su labbai suka shiga waya dasu Adama da Rahama kafin kace me sai suka haWu a gidan Cicib suka haWu da iyalanshi suka shiga girkin abincin ba?i anayi ana shewa da farin ciki.
Ba?in dai sai daf magriba suka samu isowa,
A masallacin unguwarsu Cicib sukai sallah bayan an idar da sallah liman ya sanar da batun Waurin auren. Cikin ?an?anin lokaci aka Waura auren Lolo da Alhaji Zaidu bisa sadaki Wari biyu da hamsin
Tarewa ba yanzu ba sai an shirya.
Ba?i dai anyi juyin duniya akan su shiga cikin gida su ci abinci sun?i fur dole sai Rahama da Uzairu zuchiyata ne suka saka musu abincin a mota suka tafi dashi.
Alhaji Zaidu kuma ya ja su Maigogul ya mayar dasu asibiti, kafin su ?arasa asibitin saida ya biya ta shagon siyayya aka siya musu kayan tea manyan gwangwanaye. Ya ajjiyesu a asibiti har Wakin da Lolo take kwance ya shiga.
Rakiya na zaune tana cin abinci suka shigo.
"Sannunku da shigowa kaddai an Waura Maigogul? "
"Wallahi an Waura bamu da ranar da tafi wannan a wajenmu. Tashi maza ya zauna"
Rakiya ta yun?ura zata tashi yace.
"A_a Mama ki zauna ni yanzu zan tafi masaukina dama dai su Alhaji Baba na kawo. Allah ya bata lafiya"
Yana faWin haka ya saka kai ya fita.
Su Rakiya dai zukatansu sha?e da farin ciki da annashuwa. Sabida ma fitina maigogul cewa yayi a asibitin zai kwana hakan kuwa akayi.
Yana kan kujera yana shan tea mai kauri bayan ya raka abokinshi ya tafi yace da Rakiya.
"Cicib ma ya nuna mun yana sha'awar auren Labbai ni dai nace suje su sasanta"
Dariya Rakiya tasa harda hawaye tace.
"Ya ko ji kunya wallahi. Amman in taga ta karSeshi mu bamu da matsala sai duk a haWa da bikin Uzairu zuchiyata a game kawai.
Haka suka ci gaba da tattaunawa. Cike da farin ciki lolo bata san wacce wainar ake toyawa ba.
Kunji wata ?udurar Allah ko?
Allah shi ke yin komai a sanda yaso

(Aimun afuwa daya yanzu posting ya dawo 8 na dare in sha Allah nadena na safe)
Mrs BUKHARI

Masoyiya maidoki Allah ya baki lafiya yasa kaffarane.
Dan Allah ku taya ta adda'a Allah ya bata lafiya mai Worewa.
Aminiyatace masoyiyata ta ha?i?a wacce bata da tamka kamar cicib da Maigogul. Kamar iyabo da Tabalbalin=??
[10/4, 10:29 PM] +234 810 593 2041: IDAN KAYA YA GAJI...
GAMMO MA YA GAJI
LITTAFI NA HU?U
SHAFI NA BIYAR





GIDAN BABANGIDA:.


A hanzarce ta ?araso gabanta na wani irin bugawa.
"Gani ashe kadawo? "
"Na dawo ai tun yamma. Amman meye ya tsayar dake a waje har kika kai dare alhalin dokar gidannam kinsan magriba Ba zata ma ko wacce mace a waje ba. Meye ya tsayar dake sannan me ya samu wayarki da bakya Wagamun? "
Kanta ta sosa.
"Rashin abun hawane yasa ban dawo da wuri ba, ruwa kuma kaga yazo ya kece"
Murmushin takaici yayi kawai ya fice. Ajjiyar zuchiya ta sauke mai nauyi. Ha?i?a ba da ban ta jarabtu da son Babangida ba da a daidai wannan gaSar zata ajjiye auren. Amman ina tana fatan har a gidan aljanna ta tashi a ?ar?ashinshi balle tana jin yanzu itace uwargida a gidan na Babangida, kawai dai saita tashi tsaye ne sosai a kanshi wannan kullen ne kaWai ba zata iya lamunta ba sam.
Tana zaune a bakin gado tana shafa mai suna waya da Samira har ta gama shafa man taje Kitchen ta kunna gas suna wayar, har ruwan shayin data Waura ya tafasa wayar suke

5 / 28