Idan Kaya Ya Gaji Gammo Ma Ya Gaji 4 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Fareesa Category :  Romance

Chapter   8 / 28

21K to 24K   out of 83.6K words

har gaba da abada a Wakinki kafeki ma ni zanyi gaskiya. Kinga yanzu haka gidanmu yace zai rushe yayi mana sabo. Lolo abun ?arin farin ciki dani dake ya biya mana umara zan rakaki muje mu ro?i Allah akan lafiyarki, ki kuma ro?i Allah akan yasa mutuwace zata raba aurenan.
Batun rushe gida da zuwa Umara ko Rakiya bata sani ba Aminina kaWai na faWama dalili shine a gidanshi zamu zauna kafin a gama ginin namu gidan. Yace kuma kada a takura miki a barki da kanki ki faWi lokacin da zaki tare a Wakinki a tsanake. Lolona nasan ai ba zaki bani kunya ba ko Lolo?"
Idanuna na lumshe wasu hawayen farin ciki cakuWe dana fargaba suka shiga gangaromun
Har cikin raina naji sanyi sosai. Kuma ina jin tsoro shima fal raina.
"Lolo kaddai bakya sonshi ne kike kuka? Ke da zaki yi farin ciki Allah ya zaSeki ya baki miji irin Alhaji Zaid babban mutumne fa a ?asarnan mai arziki kuma sananne. Nayi imani zai ri?eki da kyau. Duba yadda ya sauya miki rayuwa cikin ?an?anin lokaci. Ki dena kuka kada Allah yayi fishi ya karSe ni'imar daya baki. Ga ?an uwanki suna neman ko kamar tsohon fa?irin mijinki na dane basu samu ba. Ke Allah yayi gaba dake kuka kuma ai ya ?are ki dubi abinda Allah yayi mana ta sanadiyyarki fa Lolo"
Sai naga Maigogul na share hawayenshi da bayan hannunshi, take zuchiyata ta karye. Wato Allah ya jarabceni da son mahaifina sosai, duk yadda yakennan inason kayana a haka sosai.
Hakane Maigogul nagode ma Allah sosai. Kuma nayi farin ciki gaya Ubangiji Allah yasa hakan shine mafi alkhairi a garemu baki Waya
Nayi farin ciki daya biya mana umara tare muje mu ro?i Allah tare. "
Dariya muka yi. Zukatanmu cike da farin ciki marar misaltuwa ga hawaye tab guraben idanuwanmu
Wannan ranar tana Waya daga cikin muhimman ranaku marasa goguwa a cikin zuchiyata.
Lokaci Waya nauyin da kaina da zuchiyata yayi sai ya yaye baki Waya na shiga wani irin shau?i kawai ni kaWai inna tuno fuskar Alhaji Zaidu da kalamanshi sai in sauke ajjiyar zuchiya.
Kunji fa wata ?udurar Allah ina masu ganin bazan samu kamilin namiji ba sai ballazi irina?
To shi Allah babu ruwanshi
Soyayya kuma gaskiya ce. Tunda ana iya wanke karuwa tas a aura, ko a wanke kirista a aura balle ni tubabbiya mai cike da nadamar rayuwar dana gudanar a baya.
Haka muka wuni a asibiti, rabi ina bacci rabi idanuna a buWe.
Labarin zuwana umara da ginin da Alhaji Zaidu zaiyi mana ya karaWe gidanmu banda ma?ota Maigogul yace kada labarin auren da labarin komai ya fita waje. Amman nasan Hauwa zaiyi wuya ta iya kame bakinta ta dai ce zata kame.
Rakiya jin zamu je umara ta shiga fishi tana cewa ya dai tabbata Maigogul nake nuna ma tsantsar ?auna shi yasa na zaSi muje tare banda ita.
Uzairu zuchiyata yai ta mata dariya kawai yana cewa.
"Rakiya ai zaki Canada meye ma na Waga hankali tunda ya iya biya musu wallahi in kina da rabon zuwa zaki je ne, ko ni sai in biya miki gaba"
"Ai shikenan Uzairu zuchiyata gata ga Maigogul na Wauki idanu na zura musu zai bata kunyane in batai da gaske ba ma sai ya lalata mata auren zai huta. To kuma shi tarewar sai yaushe zaki tare tunda an riga da an Waura auren? "
To inaso muyi magana ni dashi tukunna inji yadda yake so sai in gani Rakiya"
Kai ta gyaWa tace.
"Ai shikenan. Wannan Alhaji ya taimakemu sosai gida shekara da shekaru babu sauyi kinga lokaci guda mun tattare komatsenmu za'a rushe gidan.
Wai kinga yadda akaita fitowa a layi ana tambayarmu ko lafiya gidan muka siyarne.
Hauwa ce ma take tankasu ni ko suna kan kwashe kayanma Maigogul yace in tawo wajenki."
Uzairu zuchiyata yace.
"Ni fa a wannan safgar ni aka taimaka Allah yasa yayi mana gidan sama wallahi da mun huta ma baki Waya"
Murmushi kawai nayi.
Sallamar su Mardiyya ce ta katsemun murmushina idanu biyu muka haWa da Babangida da ya kafe ni da idanu.
Da gudu malama tazo ta faWa jikina.
"Ummi yaya jikinki? "
Da sau?i malama ya kuke ya makaranta? "
Gaisuwar da Babangida ke ma Rakiya yasa dole na Wago uhm jama'a Babangida harda rusunawa fa in da ranka kasha kallo.
Rakiya da Fara'a ta amsa tana ri?e da hannun AWWa'u.
Mardiyya ta ?araso ta ajjiye abincin duk yaran suka matso muka gaisa.
"Sabuwa yaya jikin naki? "
Na jiyo amon muryar Babangida. Ya cika turare ya wani ci uban ado kamar zashi gidan biki.
Da sau?i nagode"
Na faWa kadaran kadahan tare da kwanciya na lumshe idanuna.
"Ummi ga abinci faten tsaki muka kawo miki in zuba miki? "
A_a mardiyya nagode bakina babu daWi ku ajjiye ?ila su Uzairu zuchiyata zasu sha. "
"Ke kawo nan ki gani in zuba. Babangida Bismillah ka zauna ga waje"
Cewar Uzairu zuchiyata dake dambe da kular fate.
Bayan ya zaunane yake cewa.
"Rakiya dama nayi niyyar zan samu maigogul in sanar mishi an kawo sadakin Mardiyya nera dubu Wari da hamsin"
Mardiyya tayi maza ta sauke kanta tana wasa da yatsunta, Uzairu zuchiyata ya duma mata dundun wasa su Aminu sunata mata dariya.
Rakiya ta kuwa washe baki.
"Kai masha Allah wannan labarin yayi daWi Allah ya sanya alkhairi. Dashi Sauban Winne? "
"Eh da shine Malam dai ya matsa bikin ma bazai daWe ba kamar dai yadda ya faWa."
Yawun ba?in ciki na haWiye wallahi Allah Waya kenan da badan Baba Malam ba banga uban da ya isa yasa ayi wannan haWin ba.
Babu komai zan Wauki ido in zuba, sai dai fa bazan taSa bari Wiyata tayi boranci ba.
A zuchiyata nake wannan maganar na?i fur in buWe idanuna dan bana ma son sake ganin Babangida har ?arshen rayuwata ma.
"Rakiya ta samu gurbin karatu ma Jami'a zata soma zuwa" Cewar Aminu
Nan sukaita murnarsu. Uzairu zuchiyata yace.
"Ai lokacin da muka shirin tafiya Canada ni da lolo mun kira ita mardiyya lokacin ma muna Airport akan suyi mana adda'a, naso ma in da kananan lokacin kaima muce kayi mana adda'a" Ya ?arashe yana ?ar dariya.
"Canada kuka je babu labari, ke mardiyya shine baki faWa mun ba? "
Babangida yayi maganar muryarshi har tana Wan Sari ko na meye oho, nasan Uzairu zuchiyata ya faWa mishi ne danya kunnashi, ya kuma sani sarai ?an gidanmu bama ?arya gaskiya duk Wacinta ita muke faWa. Ni dai har suka tafi ina haWiWiye ba?in ciki.
Suna fita na Sude idanuna na dubi Uzairu zuchiyata sai fate yake ta sha baya ko magana ga faten yaji tanta?washi sai mai?o yake yi harda yajin daddawa da man shanu a ciki. Idanu ya kashe mun, murmushi kawai nayi mishi"
"Lolo girma ya hauki dole. Wannan yarinya biki ya gabato damma Allah ya taimakeki yanzu mai dashi kike aure zaki fitar da Wiyarki kunya"
Uhm ita ta kunya take. Ni kuma ta makomar auren kawai nake yi Sa'a bata da daWi kamar kashi"


KANO:.
Alhaji Zaidu yana tafe a mota yana waya da amininshi Alhaji Rabi'u suna batu akan auren nashi.
"Amman tunda ka biya ma amaryar umara mai zai hana kawai ka bata kuWin lefen su wuce ko Dubai ne su haWo lefensu ko mai kake tunani in yaso sai ka haWasu da mutuminka Rasheed.
Ko Hajiya ce zata haWa mata kamar dai ko yaushe? "
Alhaji Zaidu yace.
"To ka kawo shawara abinda za'ayi zamu tattauna da amaryar muji yaya take so. Hajiya ma sai in saka mata kuWinta kawai a asusun bankinta kaga shikenan."
"To tsare_tsaren yadda za'a gudanar da shagulgulan bikin fa? "
Dariya Alhaji Zaidu yayi tare da cewa.
"Mu ba yara ba ai ina ganin Dina kawai zamu haWa ranar da Amarya ta tare aci asha a watse shikenan ai. Amman kada kayi hirarnan da Hajiya Mariya kasan dai mata sarai basu da sirri kuma wannan ba maganar wasa bace"
Dariya suka saka tasu ta manya da haka sukai sallama da juna.
Cikin hukuncin Ubangiji Alhaji Zaidu ya isa Kano cikin aminci.
Yana isa ?ofar gidanshi ya matsa ?ararrawar motar maigadinshi ya le?o yana ganin motarshi ya wangale mishi get ya shiga a hankali.
A tsakar gidan ya ga motar Hajara ?anwarshi mai bi mishi.
"Malam Bala yaya gida ya iyalan kuma? "
Malam Bala maigadin gidan Alhaji Zaidu ne sun shafe fin shekaru ashirin yana musu gadi
Tare yake zama da iyalinshi a wajen adana ba?i (BQ)
"Iyali sun tafi ?auye bikin ?ar ?anwar ita Gaji akeyi shine ta tafi tun jiya. Yaya jikin Hajiya ashe bata ji daWi ba? "
"Wallahi kuwa Malam Bala. Allah ya dawo dasu lafiya ni bari in shiga ciki sai na fito Sallah"
Malam Bala yayi mishi godiya ya koma Wakin gadinshi.
A tsanake cikin kamala ya shiga katafaren falon mai sha?e dam da kayan ?awa, ga wani irin turaren wuta na busa ?amshi a falon Ac kuwa tsabar sanyi kamar hunturu.
Babu kowa a falon sai tv a kunne da jakar Hajara a kan kujera da mayafinta.
Falon Hajiya ya nufa kai tsaye, nanma basa ciki a Wakin baccinta ya samesu Hajara na haWa mata Shayi ga aminanta biyu suna kan gadon itama tana gadon ta jingina kanta da fuskar gadon
Sallamarshi yasa ta lumshe idanunta ta buWesu a hankali a kanshi. Murmushi ya sakar mata, itama murmushin tayi mishi.
?awayenta duk suka mayar da mayafansu jikinsu Hajara ta mi?a mata shayin.
"Yaya Zaidu sannu da dawowa ashe zamu haWu?"
Hannu ya mi?a mata suka gaisa haka suka saba a gidansu.
"Mutanen Rano me zan samu ne Hajara sai kyau kike sake yi Abdulmalik yana ?o?ari da cinki sosai"
Dariya suka yi harda ?awayen Hajiya, ita ko Hajiya mijinta kawai take kallo damuwace linkib a fuskarta.
Gaggaisawa akayi cikin girmamawa duk suka zame suka basu waje.
Malum malum Win jikinshi ya ajjiye a kujera ya zauna a gefen gadon ya mi?o mata hannayenshi dukka biyun ta tawo, tana saka kanta a ?irjinshi ta sau kuka.
Ita mace fa bata tsufa da soyayya da shagwaSa sai idan itace taso mayar da kanta baya
Mrs bukhari

To ni kam na gudu>?:?>?:?>?:?>?:?
[10/4, 10:29 PM] +234 810 593 2041: MRS BUKHARI
7


Bayanta yake bubbugawa cikin sigar rarrashi. A kunnenta kuma yana raWa mata.
"Kiyi ha?uri ba gani a kusa dake ba. Ina tare dake har abada. FaWamun Menene ya hautsina mun ke? "
?agota yayi yana share mata hawaye tare da bata duk hankalinshi dan jin menene kokenta.
"Ba na sanar maka zamu je yima Hajiya Baturiya dannar ?irji ba? "
Kai ya gyaWa mata halamun yaji.
Taci gaba da cewa.
"Munje anata sha'anin biki sai Matar Ibrahim suka iso mutan Abuja.
Shine fa Hajiya Baturiya daga tambayar Matar Ibrahim Hafsa da muka je bikinta shine take cewa ai ta tafi london haihuwa su irin haihuwane kab danginsu in aka yima mace aure da Wanta take shekara "
Hawayene suka gangaro a kuncinta. Hannayenta ya ri?o yayi jigum yana nazari, ina kuma sai kuka marar sauti take yi zuchiyarta nayi mata ba?i"
"Wato ita dai Yaya Dubu bata kama girmanta ita duk sha'anin da zata zo in dai zaku haWu sai ta saka mun ke kuka?
Ke kuma kin kasa cire maganar haihuwa a ranki kika sani ko ba alkhairi bane haihuwar a garemu ba shi yasa Allah bai bamu ba. Bayan ke ba wasu matan sun shigo basu haihun ba? ko dai kina nadamar kasancewa tare dani ne sabida nakasun rashin haihuwata, ko kina ganin akwai wani hakkinki dana tauye miki? "
Da sauri ta Wago ?ur taga shima ita yake kallo.
"Har gaba da abada bazan taSa ?osawa dakai ba. Kada ka mance a shekaru biyar na aurenmu kayi mun tayin saki, a shekaru goma ma kayi mun tayi, muka shekara sha biyar shima kai mun tayi, mun shekara sha bakwai shima haka kamun tayin sakin yanzunma da muka riga muka manyanta tayi sakin zaka yi mun? .
Zaid har abada ni Winnan taka ce rayuwata a gidanka zata ?are kaine ma?abulina. Dangane da hakki wallahi ni gani nake yi babu yakai. Ka bani duk wata dama, ga soyayya, ga tarairaya danginka ma sai dai ince Alhamdullilah baka tauye mun komai ba"
Rungumeta yayi tsam yana sauke numfashi sun jima sosai a cikin wani yanayi.
Yaita rarrashin matarshi har saida ya kore mata damuwarta ta mance da komai.
"Hajiya kin mance dasu Hajiya Kulu. Nima kin mance baki ce a bani abinci ba."
"To ai Royal ganinka ya mantar dani komai.
Kaje kayi wanka zan kawo maka abincin da kaina."
Fita yayi yana murmushi tare da girgiza kanshi.
Babban falon gidan ya tsara ya hau ?afar bene da zata sadashi da sama.
"Yaya inaso zamu yi magana fa? "
Cewar Hajara. Bai juyo ba yace.
"In Hajiya zata hauro sai ku hawo tare Hajara.
Nasan ai jarinki ne zaki ce yayi ?asa bazai wuce haka ba. Gaye yaushe zai bar Hajara ta tara dukiya, haka ma cin abinci ai bazai barki ki tara kuWi ba. ( a daidai nan ina da tsokaci a page Win jiya akwai inda na rubuta Abdulmalik yana ?o?ari da cinki, to dake maganace mai harshen damo wasu sun Wauki Wayan Sangaren, wasu kuma sun Waukeshi a yadda na rubuta. Yana nufin yana ?o?ari wajen ciyar da'ita Hajara mai cin abinci ce sosai dan Allah ayi mun afuwa Subhanallah haka nake nufi)
Dariya tayi dan tasan a gidansu Yayanta yafi kowa saninta.
Ai kuwa da Hajiya ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?zata hauro tare suka hauro Hajara na ri?e da tiren abincin wan nata, a gabanshi ta dire yana zaune yana amsa waya. Saida ya kammala kana ya dubi Hajiya yace.
"To Yaya jikin naki ince dai yayi sau?i tunda gani ko? "
"Da sau?i kasu kusan hamsin ya tafi"
Murmushi suka yi su biyun. Hajiya na shirin mi?ewa dan ta basu waje yace.
"Yi zamanki jarine ta karyo shine ta dawo. Gara dai ki zauna ko zaki ?ara mata haske kan yadda ake tattala uwar kuWi a sake haSakata da ribar da aka samu. Yarinyarnan na kasa gane kasuwancinta Abdulmalik yana ?o?ari"
Dariya suka yi dukkansu ya Wauki kuWi masu kauri ya bata, Hajiya ma ta ?ara mata da nata. Alhaji Zaidu mutumne mai ?o?ari sosai, yana da son mutane da yawan alkheri in ana ganin kamar yawan Alkherinshi yayi yawa sai yace to wa yake dashi da zaici gado bare ace zai musu tanadi ai gara ya nemi lahirarshi.



SABUWA:.
Ina bacci bayan na idar da sallar isha wayata ta shiga tsuwa.
Rakiya ce ta tasheni ta mika mun wayar Alhaji Zaidu ke kirana.
Gabana saida naji ya Wan faWi a sanyaye na kara wayar a kunnena.
"Barka da dare Shalele amaryar Zaidul'abidin, da fatan jikinki da sau?i ko? "
Idanuna na lumshe ina jina wani iri dani wani bawai nake ji wallahi.
Lafiya lau kaje gida lafiya? "
Ajjiyar zuchiya ya sauke kafin yace dani.
"Lafiya lau na je gida. Sai dai babu nutsuwa sam tare dani. Na tafi na barki a cikin halin jinya, duk da gobe nake son zan dawo har sai an sallameki tukunna"
Idanu na zare nace.
Haba dai ai ba sai ka dawo ba. Kayi zamanka nagode sosai "
Shiru ne ya ratsa wayar ni dai bansan ta ina zan soma mishi godiya bane shi yasa nayi shiru.
Shi kuma ashe hawa da saukar numfashina yake saurare sai can yace.
"Kinyi shiru na zaci zaki tambayeni me yasa na aureki ba tare dana nemi izininki ba. Duk da dai kinsan abinda ke raina a game dake"
Daddagewa nayi nace.
Ni kuma nayi shiru ne ina jiran ka tambayeni gaskiyar abinda wannan matar tazo tana faWi, da kuma tambaya akan ahalina"
"A_a wannan ai sabgar kishinku ne na mata Shalele ina ni ina shiga wannan maganar. Batun tuntuSar ahali kuma ai mun riga mun haye wannan siraWin uhm?
Da fatan dai kin amince dani a matsayin miji ko? "
Munfashi na ja na sauke kana nace.
To ai babu macen da ba zata amince dakai ba.
Babu abinda zance dakai sai dai ince Allah ya bamu zaman lafiya Worarre sannan Allah yasa in haifa maka masu kama dakai"
Murmushi yayi yace.
"Ameen matata naji daWin wannan shinfiWar taki.
Sai dai kuma kash ni nafi son in samu masu kama dake, ko masu kama da Alhaji Baba dan ya fiku kyau nesa ba kusa ba"
Murmushi kawai nayi ina tuno fuskar Maigogul.
Shiru ya kuma ratsa wayar nina katse shirun ta hanyar cewa.
Naji labarin ka biya mana umara, kuma kasa su tashi zaka rushe mana gidan ayi sabon gini.
Sannan nagode da Wawainiyarka
Ubangiji Allah ne kaWai zai iya biy....
Kukane yaci ?arfina na kasa ?arashe maganar.
Rakiya ta zubo mun harara.
"A_a Shalelena banda kuka wannan ai yima kaine iyayenki ai nawa ne. Ni ba dan sabida ke nayi ba sabida Allah nayi.
Ke da baki da lafiya kina kuka"
Shiru nayi kawai.
"Shikenan yanzu ki kwanta kiyi baccinki zan shigo gobe da yamma in duba jikin naki, ki kula mun da kanki ko?
Illahirin kunya da mamaki tasa harna kashe wayar ko tari na kasa yi.
Ina sauke wayar Maigogul da Cicib da Labbai suna shigowa ga kulolin abinci a hannun Labbai.
"Lolona ke da wa kike waya? "
Maigogul ya ?araso ya zauna a bakin gadon.
Alhaji Zaidu ne ya kirani. Shine nake mishi godiyar abinda yayi."
"Allah sarki Lolona na fiki farin cikin samun wannan hamsha?in mijin. Amman fa tsugunne bata ?areba kinsan ba lallai abokiyar zamanki ta soki ba. Dole zan warware buzu in Wanyi abinda zan iya tawa gudunmawar kenan. Ko ba haka ba Rakiya? "
"Sosai kuwa kayi daidai hakan yayi irin waWannan masu arzikin matansu kishi dasu babu kyau ai"
Cicib ne ya ?araso bakin gadon da nake har da dafa mun kai.
"?annan ya jikin naki, ya muka ji da abun arziki kuma? "
Lafiya lau jikin da sau?i"
"Kai ba dole jiki yayi sau?i ba. Matar mai kuWi ce, ga zuwa umara na jiranta. Allah kaWai yasan ?asashe nawa zata taka haihuwa tayi mun rana ni maigogul"
Tsaki Rakiya tayi, Labbai tayi jigum, inta kalli maigogul sai ta kalli masoyin nata Cicib.
Maigogul da kanshi ya zubo mun faten tsaki yaji kifi da tanta?washi.
"Gashi ki sha ni da kaina nayi miki maza matar manya ki sha"
KarSa nayi ina sha yana bani labarai na takaici dana dariya dukka dai yaita hilatata na ko sha faten dayawa.
"To Rakiya mu kam ki taso muje

8 / 28