Idan Kaya Ya Gaji Gammo Ma Ya Gaji 4 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Fareesa Category :  Romance

Chapter   23 / 28

66K to 69K   out of 83.6K words

ya tarbesu harda zubewa a ?asa domin kwasar gaisuwa.
Maigogul ya ri?o hannunshi ya Wagashi.
"Ba girmanka bane Alhaji.
A dai mi?a hannu a gaggaisa. Ai da kaina dai nace bari muzo. Abokaina sun matsa sabida kasan sana'ar bata fiye son ana nisa ba in ba dai kasuwancin ne ya kawo tafiyar ba"
"Allah Sarki. Nima dama yanzu nake shirin inje Win in sameku. Ayi ha?uri na Sata lokaci"
Cicib yace.
"Babu komai Alhaji wallahi, ai mu bamu da sanya gamu mun tattako mu kam"
Ni dai dasu Adama muna tsaye. Su kuma Maigogul sun zazzauna haka duk muka gaggaisa. Maigogul ya kalleni yace.
"Lolona to yaya. Kinga dai wannan al?aryar duka taki ce ke kaWai Allahu Akbar. Allah dai yayi albarka ya baku zaman lafiya. Allah yasa a aikin hajji zamu yi babbar sallah tare dani dake da sirikina"
Sai ya sake washe baki. Abokanshi suka bishi da Ameen harda Uzairu zuchiyata.
"Adama a kawo ruwa da Wan abun motsa baki mana kunzo duk kun tsattsaya a kanmu"
Juyawa Adama da Labbai suka yi.
Shi kuma Alhaji Zaidu da jin haka yace yana zuwa.
Ai kuwa yana fita na kirawo Maigogul gefe.
Yaci ado ya sake saka alkyabba ba?a amman bayyi rawani ba. Ko ina ya samu wannan salon oho gashi shigar ta amsheshi.
Kaifa kace ka dena Maigogul sai kaita maganar kawalci bayan kamun al?awarin ka dena. Sannan dan Allah maigogul me yasa zaku zo yanzu fa yake shirin zuwa wajenku. Kazo kace a kawo abinci, ga aikin Hajji ka ro?a. Maigogul ina tsoron kada ya gaji da halinmu fa ya koroni ko kuma ya juya mun baya"...
Bub ya buge bakina irin na inyi shiru ba mai cutarwa ba.
"To kiyi ha?uri kinga wallahi ni nayi tunanin daWi zaki ji ganin ubanki da abokanshi. To lolo ki dai yi ha?uri ko? Sai in kiyaye gaba. Ki dena wannan koke_koken ai gidannan kinsan Allah kin shigo kenan lolo babu rabuwa sai dai....
Dawowar Alhaji da Hajiya, da ?annenshi biyu tafe da manyan kuloline yasa maigogul ya koma ya zauna ni kuma ina gefe, Hauwa ma fitowarta kenan da tana ciki.
Gaggaisawa akayi Hajiya harda tsugunnawa.
"Ah dan mahammada rasulillahi tashi dan Allah Hajiya. Ba sai kin tsugunna ba. "
Cewar Maigogul fuskarshi Wauke da dariya.
Mi?ewa tayi tana murmushi.
Mi?o mun ledojin hannunta tayi na amsa tace nasu Mardiyyane suka dai yima su Maigogul sallama suka fita.
Alhaji yaso ya tafi Maigogul yace sai dai yazo yaci abinci.
Zanyi magana Alhaji Zaidu ya dubeni ya lumshe idanunshi halamun in bari.
Dole na koma sama.
"Lolo ba zaki zo muci tare ba? "
Ni na ?oshi"
Na faWa ba tare dana juyo ba
Tsabar haushi.
A Wakina na tadda su Adama harda Hauwa dasu Baba Laraba suna maganar. Ni ko dan ba?in ciki kuka na fashe dashi.
"Kima dena Sata hawayenki in dai ubanki ne baki ga komai ba. Bare yanzu shima aure yake yi a Kano yadda aka auroki haka aka auroshi. Billahillazi bai yi komai ba saiya turguWe miki auren tukunna hankalinshi zai kwanta. Ya kwaso ?an iskan abokai sun baza riguna zasu zo suyi bara ?ar nasu ta samu gidan hutu. "
"Hauwa ya isa haka mana kina Waga murya. Mu dai dake komai namu babu sirri. In sha Allah ba zamu ga haka ba"
Cewar Rahama da ranta ya gama kaiwa ?arshe da Saci.
Baba laraba tace.
"Allah ya kyauta. Mu kam yanzu zamu soma shirin tafiya. Tun asussubar fari kayi nayi take ta kirana ko lafiya oho. Lolo mun kaima kishiyarki cincin Winta dangin mijinki ma akwai babbarsu a mata na dan?a mata da, uwargida na bata na ango nace ta ajjiye mishi. Ni da Adama dake mu muka kai ta bamu turamen zani biyu da dubu ashirin ashirin. Allah ya baku zaman lafiya amman kishiyarki dai mutum ce gaskiya hannunta a sake yake."
Ni dai sai binsu da ido kawai nake yi.
Nan suka ci gaba da shirye_shiryensu.
Uzairu zuchiyane ya hauro ya kirawomu wai su Maigogul zasu tafi.
KuWi na Webo na fita.
A hannun maigogul na ba da rabi. Ragowar na dam?a ma Cicib shi da su kawu Isuhu.
"To shikenan Lolo Hajiya ma ta aiko mun da shadda harda kuWin Winki kin ganta."
Ko magana banyi mishi ba"
"Zan rakasu su zasu wuce Dutse yau. Ala bashi gobe sai in kawo ita Iyali tazo ta kuma ganin waje."
"A_a Maigogul ai zata zo ma da kanta zasu yi waya tafa san gidan ita ta kawo mu muma"
Cewar Rahama. Yana dariya yace.
"Hakane hum Hakane to babu damuwa mun tafi Lolo. Ke kuma Hauwa sai kuma na dawo Dutse wajenku"
Murmushi Alhaji Zaidu yayi kawai.
Ni kuwa kamar me haka nake ji.
Sai da aka rabu dasu lafiya kana na samu nutsuwa.
Su Adama sha Waya suka tarkace yanasu _yanasu suka kama hanya.
Saida suka gyara mun waje tsab.
Ina hawa Sarayina na sake buga wanka na sakko falo.
Dangin miji suka ce Salamu Alaikum
Ai nan muka wuni akayi kaca kaca da gidan baki Waya akaci abinci duk aka tattaka shinkafa a kafet aka zubar da ruwa abubuwan kamar ma da gayya suke yinshi.
Sukaita hirar zumunci ni dai suna sakani ciki sai dai nai murmushi haka, suna da fara'a sosai sai haba_haba suke yi dani. Ga ilimi a cikin maganganunsu magana Waya biyu ta ukun larabci zaku ji anyi.
Basu suka watse ba sai magriba da suka ci abincin dare.
Nan ni kuma na shiga gyare_gyaren Sarayina gashi babu mataimaki. Ga kwanukan abinci da suka ci komai a wajen suka bar mun fa.
Ina gama kintsa wajen na banka turarukan wuta a gidan na Mrs BUKHARI gidan ?amshi cikin ?an?anin lokaci gida ya kaure da ?amshi mai sanya nutsuwa turarukanta suna da ?arfi da mugun kama waje sosai gaskiya.
Na zaSi rigar baccin da zanyi amfani da'ita na Waura akan kabbasa na zuba turaren kaya bayan na feshe jikin kayan baccin da kabbasiyya turaren fesawa kafin turara kaya, na bisu da turaren mai?o shima da ake WiWWigawa a jikin kaya kafin a Waura akan turaren kayan.
Na jawo ?ofar na sakko saida na game wanke_wankennan tas bani na gama ba sai wajejen taran dare.
A gurguje nayo wanka na saka doguwar rigar yadi mai laushi nabi ko wacce kusurwa a jikina da humrar Mrs BUKHARI. Na shafe marata da humrar matan aure. Jigidata wacce take a tsume cikin turare na ciro na Waura itama daga wajen Mrs BUKHARI Winne wannan mata ?arshece ni wallahi burgeni take yi sosai gata da lafazi.
Na sauko na zauna ina ?arema falona kallo ina jin wani farin ciki na ziyartata marar misaltuwa. Sai kawai naji an buWe ?ofa kuma da Wan mabuWi tabbas nasan Alhaji ne.
Ai kuwa ilai shine saye da jallabiya mai ruwan toka kanshi da hula. Amman sai naga babu nutsuwa tattare dashi.
"Shalelena aimun Afuwa Hajiyace babu lafiya kuma ciwo sosai shine zan kaita asibiti nace bari in sanar dake"
Subhanallah meya sameta Alhaji? "
"To shine sai munje tukunna. Ba jimawa zamu yi ba in sha Allah. Ga Wan mabuWin turakata ki haura kije ki jirani acan"
Amsa nayi a sanyaye.
Allah ya bata lafiya sai kun dawo. Dan Allah kayi mata sannu."
Fuskata ya shafa kawai ya fita.
Ta taga na le?a naga shigarshi cikin mota da ma fitarsu daga gidan.
Ajjiyar zuchiya na sauke kawai.
Kitchen na shiga ashe ba'a Waura silindar gas ba. Sai buta na jona na dafa shayi naci cincin da nakiya na ?oshi.
Banje turakarba sai kawai na saka kayan baccina na kashe komai na haye gado.
Sai naji ina kewar gida. Wallahi da kawai na tuno da rigimar gidanmu da sababbin rigingimun Rakiya data buWe sai nayi dariya.
Adama na tsinci kaina da kira. Ai kuwa ashe ita firgitata nayi.
"Lolo ince dai lafiya ko? "
Dariya nayi nace
Ah lafiya lau. Hajiyace ba lafiya Alhaji yaje kaita asibiti shine nace bari in kiraki inji kun koma gida lafiya? "
"Hmm lafiya lau Lolo. Nima jibi sai Malam madori kuma Rahama da Baba Laraba zasu kaini."
To Allah ya kaimu. Zamu yi magana zuwa gobe da safe zan kiraki mu gaggaisa duka harda su Rakiya"
Sai ta kece da dariya tace.
"Rakiya daru. Ai Wazu ta kira Maigogul a waya matarshi ta Wauka Rakiya ta dinga narko ashar baki ji ba.
Har kuka fa saida tayi wallahi, sabida Hajiya data Wauka sai tace wai Honey bacci yake yi sai dai Rakiya ta kuma kira. Kai kishi masifane musamman irin nasu Rakiya"
Nan suka shiga bani labari da Rahama.
Daga ?arshe dai mukai sallama na ajjiye wayata.
Saida na duba agogo sai naga sha biyun darene ashe. Lallai munsha hira da ?an gida.
Gashi har lokacin Alhaji Zaidu bai kirani ba. Inason kira ina fargaban kada suga kamar na matsune in soma kwana turaka wallahi shine dalilina da yasa ban kira ba.
Ina wannan tunanin sai ga kiranshi kuwa Wan halak.
?agawa nayi da sallama ya amsa mun muryarshi a tausashe.
"Kinganmu a asibiti jikin Hajiya yayi tsanani ciwonta ne kamar ya tashi sai dai ki taya ta da adda'a, ciwon inya tashi muna shan wuya Shalelena Sannan bazan dawo ba Shalelena bazai yiwu in baro yayarki a gadon asibiti in dawo gida ba uhm. Amman ina mai baki ha?uri zuwa gobe dai da safe zan shigo gidan kinji? "
A sanyaye nace.
Bai kamata ba kam lafiya ai itace komai. Wallahi babu komai Allah ya bata lafiya"
Ajjiyar zuchiya ya sauke yace.
"Wallahi inason wannan sanyin naki yana sake narkani cikin soyayyarki. Gaki da sau?in kai uhm.
Ki kwanta kiyi baccinki da safe angonki zai zo inda kike in sha Allah. Ki kwana kina mafarkin Zaid Winki.
Ina sonki Amaryar Zaidul'abideen muah."
Murmushin jin daWi nayi mishi mukai sallama na kwanta. Murmushi kawai nayi wanda ni kaWai nasan dalilin murmushin
Dama ga gajiyar biki gata aikin gyaran gida ai sai bacci.
Wani sassanyan lafiyayyen bacci nayi zuchiyata sawai da'ita gwanin daWi wallahi.
Bani na farka ba fa sai shidan safe na makara. Shima kiran Maigogul ne ya tasheni"
Kunga Maigogul zai soma ko?

Me kuke tunani game da Hajiya ne, ga ciwo ya tashi har an bata gado
Ku faWi ra'ayoyinku
Mrs BUKHARI
[10/4, 10:29 PM] +234 810 593 2041: https://chat.whatsapp.com/I7uDGV8V2DQDVS5RHRi0St

https://wa.me/message/QBXV2PDE2Y3CI1

Kina neman inda zaki samu ingantattun kayan gwanjo wato thrifts ma yaran ki kwantar da hankalin ki yar uwa oumokasha thrifts store ta kawo muku kala kala kaya na fita kunya akan farashi mai sauki tun daka kan overalls jumpsuits bodysuit bibs jeans tops blouses da sauran kaya na kece raini from 0 to 15 years
Muna garin abuja koh kaduna
Muna tura kaya ko wani gari da yarda Allah quality da sauki shine taken mu

MRS BUKHARI
19




GIDAN B HOUSE:.

"Nace lafiya ya ina miki karatu bakya mayar da hankalinki ne. Zaki ajjiye wayar ko saina farfasa wayar? Haba ki bani hadda aya biyu kin kasa ina ?ara miki kin kasa mayar da hankalinki.
Bari kiji Aisha ba wai tubana zaisa matana su samu lasisin rainani bane wallahi babu wacce ta'isa. Na lura abun naku ya wuce gona da iri fa, wannan wanne irin buyagine hiye"
Cike da faWa yake magana dan tura ta kaishi bango akan sha'anin gidanshi ko wacce ranar girkinta da gwaramar da zai shiga ya tarar Hameeda ce kaWai yaga kamar a kintse ta dawo zawarcine ko menene dai ta ladabtu ba irin Hameedar daya sani da bace.
"Kayi ha?uri Jannaty kaga kayane nake son sara na sai da gold Wina shine matar take tutturomun da'ita muke magana amman kayi ha?uri."
"Matsalolinki da yawa. Ga yawon ma?ota kinga wallahi bazan Wauki duk wannan abun ba. Sannan bazan hanaki kasuwanci ba tabbas da gwal Winki na auroki amman ki sani bafa zaki fake da kasuwanci ki Sige da yawo ko nemo rikicin kuWin mutane ba. Sannan gargaWi nagaba shine.
Wallahi Allah Wayane duk ranar dana sake shigowa Wakinki na tarar da matan ma?ota a kan gadona ke a cikin Wakin baccinnan to komai zai iya faruwa su kansu matan inaga saina kulle Wakin nayi musu duka. Sabida na lura so kike ki turani baki san waye Babangida kacigari bane labarina kike ji"
Yana gama faWar haka ya mi?e ya fita waje kawai ya samu dakali ya zauna badan komai ba sai dan ya huce ko zai samu sau?in zuchiya.
Sai da zuchiyarshi ta sauka ya shiga Wakin tana ganinshi ta sauke waya a kunnenta.
Gadan_ gadan ya nufo ta tare da fisge wayar yadda ta nuna halamun rashin gaskiya data ganshi sai yake zargin ko da namiji take waya.
Zarah yaga an rubuta duk da haka sai yake ganin ai gidogace irin nashi na da. Sau nawa_ nawa yake sama macce sunan maza.
Danna kiran Zarah yayi tare da saka wayar a buWe tana ta ruri kamar zata tsinke sai Zarah ta Waga da murya tattausa tace.
"Ba mai gidan bane ya dawo ba? Kije ki bashi hadda kada ki kuma laifi"
Ajjiyar zuchiya Babangida ya sauke tare da datse wayarshi. Yana jin kamar yayi ma mai muryar farin sani.
"Wato wannan abinda ya faru har kin kira ?awarki kina fesa mata ko? Ya ilahi ina zan saka raina?"
Wayarta ya tsilla kan kujera yayi shigewarshi ciki ya kwanta yanata sa?e_sa?e ita kuma madigar a kan kujera ta mimmi?e abunta ta?i shiga Wakin tunda tasan tana shiga zai hayeta.
Washegari ko data gaisheshi ?in amsawa yayi, ta bashi abinci ya?i ci. Da zai fita ya ajjiye mata kuWin cefane yayi tafiyarshi ya barta a tsaye tana hararar bayanshi. Da Sumy suka haWa idanu itama da hararar ta bita harma da daWi da tsaki.
"Aikin banza da wofi.
Tayi komawarta Waki rai a jagule tanata tunanin Sabuwa da Sabuwar rayuwar data shiga.


GIDAN MALAM:.
Da yamma lis sai ga su Mardiyya sun dawo. Malam na zaune dasu Adda'u a ?ofar gida sai ga su.
" Mardiyya kune a tafe har an gama bikin kenan. ?arama an dawo ko? "
"Malam kenan kana waje ka tusa jikoki a gaba anata lele. Allah yayi dawowarmu. Sai da ma muka huta a can gidansu Sabuwan kafin muka tawo dake mota har tsakar gidansu ta shiga damu"
"To madallah sannu da zumunci. Ita kuma Allah ya basu zaman lafiya. Mardiyya Saratu kuje ku huta"
Malama ?arama tace.
"Akwai cincin naka da Sabuwan ta bayar a kawo maka na ajjiye maka a turaka, da shadda"
Murmusawa yayi yace.
"To shikenan saina shigo Win. Ai da bakya gidan babu daWi har duhu yayi mun, su Aminu ke Webe mun kewa"
Murmushi tayi irin na matan da masu tsantsar ado da kunya wacce tazo har a al'adar malam bahaushe. Wanda a yanzu mata an zama fitsararru da sunan wayewa.
Mi?ewa suka yi yuu suka bisu dukka ciki.
Murmushi Malam ya bita dashi kawai.
Da daddare sai ko ga Babangida yazo wajen su Mardiyya. Malam ya bashi dama ya shige
Suna zaune a Wakinsu Mardiyya sun buWe cincin dasu atampa da shadda ga kuWi sunata zuba surutu ya shigo.
Kayan yake ta kallo su kuma baki a haWe suke mai sannu da zuwa har dai ya nemi waje ya zauna.
Nan Malama ta shiga zubo mishi surutun biki da irin kyan gidan umminsu. Babangida sai haWiWiyar yawu yake yi.
"Baba kaga duka wannan sabon Babanmu ne ya bamu. Kuma yasa munyi mishi karatu ni da Adda. Baba dan Allah zan...
" A_a uwata kina tare dani ba zaki je ko'ina ba. Malam bazai bari ba in yaji ciwonshi zai tashi. Kina so ciwonshi ya tashi ne? "
Tayi saurin girgiza kai.
"To in bakya so kar kice komai. Nima bazan so ba"
Aminu yace.
"Amman Baba zaka dinga kaimu wajen Ummi? "
Ai sai ya Waure fuska tamau. Me ya tuna kuma sai yayi murmushi yace da Mardiyya.
"Kin bata sa?on nawa? "
Mardiyya ta Wago tace.
"E Baba na bata. Amman dai a jaka ta saka"
Shiru yayi yana nazari.
"Bata buWe ba kenan har kuka tawo kawai a jaka ta jefa? "
"E Baba a jakar hannunta ta jefa, to kuma muna isa Kano wajen Dina muka wuce"
Baki ya buWe tare da jinjina kai yace.
"Au har Dina ma akayi kenan? Ai shikenan Sabuwa"
Cincin ta ?ulla mishi mai yawa ta ?irgo kuWi daga cikin kuWin da Alhaji Zaidu ya basu ta haWa da cincin Win.
"Baba gashi. Dan Allah kada ka?i karSa ni Wiyarka ni na baka"
Cikin jin kunyar Mardiyya ya karSa hannunshi na rawa yau shine ri?e da cincin Win bikin Sabuwa da wani ?ato? "
Ai saiya mi?e ya fice kamar kububuwa.
Ko da ya fito malam baya ?ofar gidan mashin Winshi ya hau ya fice da sauri.
Har zai wuce tsohuwar majalisarsu sai dai ya dakata wallahi ko gidan baya son zuwa sam.
A hankali ya isa tare da zama ya buWe misu waWannan kayan fulawa.
Suna ci anata gulma da musu.
Shi kuma bidiyon raya sunnah tsakanin Sabuwa da mijinta sai hasko mai yake yi harda yadda Sabuwa take karya wuya zuwa gefe saida ya hango.
Da mugun zafi ya Waga shayin gahawa ya WaWWake zafin na ?ona ma?ogoronshi da ?irjinshi har zuwa cikinshi.
Idanu ya lumshe kawai ya kwace sigari a hannun Gaddafi ya soma zu?a.
Har ya kusan shanyewa zuchiyarshi ta daka mishi tsawa tare da hasko mishi kuskuren daya tabka.
Zuchiya tana magana da mamallakinta kamar yadda ?awa ke magana da ?awa. Wani sa'inma zuciya tana iya rabuwa ta zama kashi kashi tare da yin maganganu mabanbamta a lokaci guda.
Mi?ama Gaddafi sigarin yayi ya dafe kanshi kawai idanunshi a rufe.
"Babangida kacigari duniya ta Wau zafi mata sai caja mana kai suke yi. Dama ance wanda baiji bari ba zaiji hoho.
Kaganni wallahi ban?i mu kwana a majalisarnan ba sabida tsabaragen yadda bana ?aunar in shiga gida ko da kuwa da wasa ne. Duk Wakin daka shiga kamar jira dama take yi. Sai kaji an soma kawo maka ?ara, ko ka shiga kaji suna zage_zage. Inma ka saki mace dole wata zaka Wakko. Ni mata ma duka sun ficemun a kayi na"
Musa yace.
"Kunga ga Ladidi zata wuce uwar gantali yau tadawo ma da wuri"
Idanu Babangida ya buWe a hankali ya dubi Musa. Hankalinsu duka yana kan Ladidi har da masu lashe bakunansu.
Idanu ya sake lumshewa yana jin zuchiyarshi na yi mishi tururi.
Ada yafi kowa son Ladidi tazo wucewa ya more kallon sifikun zamanta.
Shi dake ma ya fisu neman zunubin har fata yai tayi mijin Ladidi ya

23 / 28