Idan Kaya Ya Gaji Gammo Ma Ya Gaji 4 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Fareesa Category :  Romance

Chapter   15 / 28

42K to 45K   out of 83.6K words

da'ita. Sama baya iya tsinana komai sai ni na cire kuWi na sai mata kayan abinci na sai mata kayan shayi. Ranar suna yaro yaci sunan Maigogul aka mishi inkiya da Abbati. Ragon suna mai Wari mai Wari biyu haka aka harhaWa na cika aka siyo ?aton rago
Ga dangin Rita sai da suka ciko bus dan masifa wai sunzo suna. Sun dai kawo mana tsarabar dankali da risga, ni ban taSa ganin risga ba sai wannan lokacin gashi da daWi musamman in yaji ?uli_ ?uli.
Allah ya tainakemu duk wannan sha'ani Maigogul baya gidan sun tafi biki Lagos shi da Cicib.
Suna dai an Wanyi hayaniya gaskiya har ma?ota amman batai yawa ba ?urar ta lafa akan hanjin rago akayi rikicin.
Su mardiyya da yaran su Rahama, Adama duk sun zo suna, ganin Hakane Labbai itama tace dole yaranta suzo sunan. Ai kuwa taima Aisha kuWin mota taje ta kawo yaran suka shiga cikin ?an uwa sukaita nishaWi. Matar isuhu da iyalinshi ma sunzo suna, harda Baba ma ?anwar Rakiya tazo wannan suna, sabida dama Rakiya ta labarta mata mun sake gida gashi zamu je umara dalilin da yasa tayi amfani da hakan kenan tazo. Baku tambayi labarin Laraba ba.
Hmmm Laraba dai tayi aure ta auri wani mahauci bata daWe ba kishiyoyi suka sakata gaba auren ya mutu daga haka ta tattare kayanta ta koma ?auye da zuwanta bata daWe ba tayi wani auren abunta.
Anyi suna da kwana biyu muka wuce Kano ni da Maigogul da Uzairu zuchiyata daya nace saiya mana Rakiya.
Hotel Babba Alhaji Zaidu ya sauke mu sai nan nan yake yi da Maigogul, shi kuwa Maigogul tsabaragen farin ciki bakinshi ya?i rufuwa.
Da daddare ina kan sallaya dana tawo da'ita a jaka naji an ?wan?wasa ?ofar Wakin nawa.
Ina buWewa naga Alhaji Zaidu Wauke da basket na abinci guda biyu.
Murmushi yayi mun ya mu?o mun Waya.
"Ga namu bari in kaima su Alhaji Baba nasu sai inzo. Anan wajenki fa yau zan kwana"
Ai sai naji ?ar faWuwar gaba domin har ga Allah nasan bazai kwana mu wanye lami lafiya ba, ni kuma nafi son in gyara jikina sosai tukunna.
Komawa ciki nayi jikina a mugun sanyaye na zauna a ?asan kafet ban jima da zama ba ya turo ?ofar ya shigo, ya saka key ya kulle gabana nata faWuwa.
Malum_malum Win jikinshi da ?ar cikin ya cire ya bar wandon shaddar da farar singileti. Zama yayi yana fuskantata yana murmushi.
"Zuba mana abincin Shalele yau ni da kaina ma zan baki abincin domin kada ki gaji uhm"
Jiki a kasale na zuba mana lafiyayyen tuwon shinkafa miyar taushe taji naman kan rago harda manshanu a miyar.
Cokali ya saka ya gutsuro tuwon ya nufo bakina dashi. A hankali na buWe bakin nawa ya saka mun.
Taunawa nake yi a tsanake. Babu yabo babu fallasa miyar tafi kyau a ido fiye da a baki gaskiyar magana. Amman ba za'ace babu daWi ba.
Ya dinga ciyar dani ina amshewa saida na ?oshi sannan ya mi?o mun cokalin yace.
"A rama ma kura aniyarta., dan nima bai kamata in wahala ba ko uhm Shalelena? "
Ina dariya na soma bashi abincin a baki. Cikin dabara nace.
Wannan girkin Hajiyane? "
GyaWa mun kai yayi saida ya cinye tuwon bakinshi kana yace.
"Girkin Hajiyane Shalelena"
Masha Allah abinci yayi daWi. Ai na Wauka matan manya basa girki sai dai ?an aiki su dinga yi musu, har da gyaran Wakin miji ma haka"
"Kinyi gaskiya Hajiya bata girki sai dai tana da ?ar aikinta wacce ta yadda da'ita itace mai yin girkin gidan baki Waya, kuma ko mata dana aura a baya duk itace dai take girkin ranar girkin mace itace zata faWa mata abinda za'a girka har ta fita girki kinji yadda tsarin gidan yake."
Kai na jinjina ina mamakin mata da samun waje. Abincin cikinku ku biyu da mijinki shine abinda sai ?ar aiki ta girka miki? Ina laifin tayi wasu aikace_aikacen ke kiyi girkin, kwanciyar aure shine kaWai aikin da kika yadda naki ne ko?
Hmmm
Murmushi nayi nace
Allah sarki. Abincin yayi daWi sai dai Hajiya bata san mu ka kawo ma abincin ba ko tunda dai bata san da zamana ba"
Ruwa ya tsiyaya ya sha kafin yace.
"Bata san da zamanki ba tukunna lokaci zaiyi halinshi tunda kafin ki tare dole zata san da zamanki. Abinci kuma bata tuhumeni ina zan kai ba, nima kuma nasan ba zata tuhuman ba, na barota tana ta lissafin kuWi.
Kinsan menene Shalelena? "
Girgiza kaina nayi.
"Ina sonki sosai fiye da yadda kike tunani ki dage sosai ki ro?a mana Allah dangane da zaman aurenmu. Bacci mai munshari ba naki bane umara kika je ki ro?i Allah ya sanya albarka, kwanciyar hankali, da fahimtar juna a tsakaninmu. Jibi zan biyo bayanku, har Dubai Winma dani za'aje Hajiya itama zata je umara to tare zamu je, sai dai ba zamu dawo tare ba sai in Waukeku muje Dubai. Nayi hakanne dan in baki dama ki zaSi duk abinda yayi miki.
Familina babban familine ba'a rabasu da sha'ani biki ko suna gashi anayin taro sau biyu a shekara a Rano. Bana so kowa ya raina mun mata ko ya raina daga inda kika fito, kema bana so kice zaki raina kanki Shalele uhm. Sannan ki sai kaya masu tsada sosai matata bata Waura ?aramin zani bata saka ?aramin takalmi, kada ki damu da kuWin akwai iya adadin kuWin dana ware miki na lefenki duka nake son ki kashe kita mun kwalliya ni kuma ina morewa.
Sannan zan ba Alhaji Baba kuWin kayan Wakinki ya sai miki komai in a Dubai Win kike so sai a siya a Wauro a jirgin kaya, in kuma na nan gida Najeriya kike so shikenan. Bana so da wasa a raina mun ke. Yadda kowa zata nuna isarta kema ki nuna taki isar kema matace kamar kowa"
To shikenan nagode sosai Allah ya saka da Alkhairi Allah ya ?ara buWi Ubangiji Allah ya barmu tare har abada. Allah yasa in zama uwar ?a?anka, batun kayan Waki bama saina siya a Dubai ba wallahi na gida Najeriya ma ya isa nagode sosai."
Jawoni yayi na faWo ?irjinshi muka zuba ma juna idanu sai rarrabe idanunshi yake yi a kaina.
"Shalele kina sani a cikin wani irin yanayi na musamman in ina tare dake sosai. Wannan tariyar na mata tanadi mai yawan gaske kema ki shirya kinji ko uhm?"
A wannan daren mun daWe sosai a cikin wani keSaSSen yanayi, ni dai inata fargaban babban, shima sai bai nema ba, nutsuwa kawai ya samar ma kanshi yaimun raWa a kunnena.
"Wancan akan gadona zai kasance ba a Wakin otel ba Shalelena. Ai wannan ranar ta musamman ce ba zanyi wasa da'ita haka ba. Nutsuwa na samar ma kaina ?walelen yayi mun yawa kyakkyawata uhm"
Mi?ewa yayi ya kintsa na rakashi ni da Uzairu zuchiyata har bakin mota muka saka mishi basket a mota.
Washegari da misalin huWun yamma jirginmu ya Waga zuwa ?asa mai tsarki.
Ina zaune a kusa da wata Hajiya a shekaru ba zata wuce Sa'a ba. Tun zamanmu dake kujerarmu tana kusa da tasu Maigogul sai naga tana ta satan kallonshi haka. Da dai abun ya isheta sai ta juyo tace.
"Mahaifinki ne wancan bawan Allahn da naga yana ta tattalinki, ko kuwa dai mijinki ne? "
Murmushi nayi nace.
Mahaifinane"
Sai ta murmusa itama gata ?ar gaye sosai sai ?amshi take yi hannunta da ?afarta sun sha ?unshi yayi mata kyau sosai. Ga zobunan zinarai data jera a hannun hagunta har guda uku, su kansu awarwaron hannunta kamar na zinare ne gaskiya dan gyansu ya kai.
Dana Wago sai inga Maigogul dai take kallo abun almara.
Bamu muka iso Saudiyya ba sai misalin ?arfe Wayan Ware. Amman sabida kyau da hasken daya mamaye ko'ina da kai kawon jama'a yasa mutum zaiji kamar ba dare ba. Muna sauka jirgin ?an wata ?asar ya sauka shima. Munyi munti talatin a Airport kafin muka fito wannan Hajiyar tana biye dani, harma ta taimaka mun da ri?on jakata.
Tunda muka sauka wallahi Allah naji na canja wani irin sanyi na shigata takota ina.
Maigogul na kalla naga sai sharce hawaye yake yi kuka na tunkuWo mishi. Nayi imanin kukan tsoron Allah ne. Ga mutane da yawa sunata hawaye ni kaina fuskata sharkab da hawaye. Gaskiya ana zuwa umara sosai babu laifi.
Hotel Winmu muna daga Waki muna kallon harami.
Allah mai iko kunga ?udurar Allah ko?
Maigogul na shiga Wakinshi zazzaSin tsoron Allah ya rabkeshi ?a?as.


Gidan Babangida:.
Kwanan ?ar Shuwa biyu a Abuja cib. Saida aka kaita wajen shugabar ?ungiya suka amfana da juna. Harma aka saka sunanta a tafiya yawon buWe idanu da za'ayi a cikin sabuwar shekarar da za'a shiga.
Ta ?udure a ranta wallahi ko da figi da yagi ne sai tayi wannan tafiyar ko me Babangida zaiyi sai dai yayi a yanzu ji take yi babu wanda ya isa rabata da su Sameerah.
Tana zaune a motar Sameerah tayi shiru tana tunanin Babangida daya bi ya kanainaye zuchiyarta tana kokonton kamar cusa mata soyayyarshi akayi ta ?arfi da yaji. Wayarta ce sa?o ya shigo ta yi saurin dubawa a tunaninta Babangida ne sai taga ba?uwar lamba.
"Baby Aisha Zarah ce shugaba. Na kwaceki daga hannun Sameerah wannan kayanane kinyi mun sosai, taraiyarmu tayi mun daWi. Ya zama sirri Baby zan baki duk abinda kike so, kiyi tunani ita kanta Samerah a ?ar?ashina take.
Love you"
Abinda sa?on ya ?unsa kenan. ?ar shuwa bata fice cikin mamakin hakan ba ta jiyo muryar Sameerah.
"Baby wai tunanin me kike yi ne ko dodon naki bai Wauki wayar bane har yanzu? "
Ajjiyar zuchiya ta sauke tace.
"Wallahi ya?i Wagawa sam. Yana da zafin kishine matsalarshi kenan. Baki ji yadda yake faWa a waya ba jiya wallahi kamar zai zazzageni haka yake mun magana. Na mishi sa?o ma ina hanya wallahi ya?i Waga dai wayar"
Murmushi Sameerah tayi mata cikin salon mantar da'ita zancan Babangida tace.
"Kada kiyi wasa da sharaWin ?ungiya. Ke yanzu ba jigari_jigarin mace bace. Sannan ki ri?e mun al?awarina kada ki samu wasu iyayen gidan a group, gaskiya ni ba'a haka dani ina da kishi zan iya komai akan Babyna wallahi bani da daWi "
Da haka dai sukaita hirarsu ?arfe uku na yamma suka iso garin dutse a ?ofar layinsu ?ar Shuwa Sameerah ta ajjiyeta.
?ar Shuwa bata shiga gida ba saida ta tsaya a bakin layin nasu tayi cefanenta na kayan miya harda kaza ta siya a shago.
Tana shiga matan gida sukaita mata sannu da zuwa sannu da zuwa ita kuma sai baki take washewa.
"Sannu da dawowa Maman Faty kawo akwatin in shigar miki dashi"
Cewar Rahama kenan.
A taSe tace"
"Basshi kafin a kaini gaba ai kinga hankalinta yananan"
Da Sumy take wacce take ?ofar Wakinta ta baza lesuka da takalma na siyarwa mata nata zaSa.
?akinta ta buWe ta shiga tana ta haki.
Saida ta huta tayi azahar da la'asar tayo wanka ta fito Kitchen ta Waura sanwa sai ga Jamee dasu Fati sun turo ?ofa sun shigo.
"Kin dawo ashe? Yanzu muka dawo ai dasu Fati sun rakani wajen Kulu"
"Nadawo in faWa miki tafiya tayi kyau sosai na samo alkhairi akwai labari ke dai bari in nitsa tukunna zaki ji labari gobe. Ina zuwa bari in kawo miki taki tsarabar"
Mi?ewa ?ar shuwa tayi ta shiga ciki ta zaro takalmin da aka raba musu a wajen taro ita nata yayi mata kaWan ta mi?a ma Jami.
"Gashi tsarabarki kenan"
KarSa tayi baki a yashe tai godiya nan ta lalace sukaita hirarsu ?ar Shuwa nata girkinta zuxhiyarta cike da tunanin Babangida a Wakin wa yake ma ita wallahi bata sani ba.
"Wai kuwa kinsan Ramatu babu komai yanzu a cikin Wakinta sai katifa katifarma a wajen dillaliya ta siya? "
Baki ?ar shuwa ta buWe nan Jami ta bata labarin dambarwar da akayi ?ar shuwa taita farin ciki da jin daWi.
Ko da Babangida ya dawo yaga ?ofarta a buWe bai nemeta ba itace ta wanke jikinta ta nufi Wakin Ramatu ta sameshi ta gaisheahi yana zaune yana cin shinkafa da miya da dafeffen ?wai. ?akin babu komai sai kafet dai a malale ko labule Babu zannuwan gado Ramatu ta saka ta kare tagoginta dama gulmar da ?ar shuwa ta shigo yi kenan
"Lafiya sai yanzu kika so dawowa? Daga yanzu sha'ani ya wuce na gari to banaso a sake kawoshi gabana ma yin hakan zaisa koma wacece ta fuskanci matsala. Ni dai na faWa muku kenan wallahi bazan iya ba"
"Ayi ha?uri Jannaty shi zumunci.... "
"Kiyi mun shiru kinji ko? Ba faWi in faWa nake bu?ata ba"
Fuu ya shige uwar Waki ya barsu nan.
?ar Shuwa bata mi?e ba suka jiyo Sallamar Sumy a bakin ?ofa. Tare suka shigo ita da Adeza ?ar uwarta matar Mustapha ta Wan ciki a jikinta. Sai lokacin ?ar shuwa ta ?arema Sumy kallo tsab itama ashe cikine a jikinta ?arami sosai.
"Ramatu Baban Amir yana ciki abokinshi na waje yana son magana dashi? "
"E bari a kirawo shi"
Mi?ewar da zata yi sai Babangida ya fito yayi waje.
"A kaine Mustapha da madam shine babu ko waya?"
To bari a fito mana da tabarma, su matan a barsu a ciki. Ramatu kiba yara tabarma su kawo"
Ramatu tayi sauri taba Yusuf tabarma ya fitarma da su Babangida, harda abinci da ruwan sha.
Adeza ta zauna suna gaisawa da ?ar shuwa, itama Sumy tana zaune duk a ?asa tace.
"Ashe kin dawo"
"Uhm"
Iyakar abinda tace kenan. Ramatu ta kawo abinci ta ajjiye ma Adeza, hirar dai jefi jefi akeyi sai kawai Sumy suka sake yare ita da Adeza sukaita yara yaren ibura. ?ar shuwa ta taSe bakinta ta hararesu kawai. Gashi babu damar ta fita ace ta wula?anta matar Mustapha.


Babangida:.
Bayan sun zauna sun gaisa.
"Ga abinci kaci Mustapha in zaka iya ci. Duk da a cikin damuwa na ganka"
"Hmmm Babangida ga Adeeza nan na kawota gobe zata kama hanyar garinsu akwatinta yana mota ni da kake ganina na saketa saki Waya
Wallahi bazan iyaba masifar yau daban ta gobe daban fa."
"Ashsha Mustapha kayi kuskure kuma ni a so samuna dan Allah ka daure ka dawo da Adeeza Wakinta ka Wauki mataki. Kuma in matakin ya?i Waukuwa ka Wauka wannan sakamakone muke karSa sabida mu kanmu babu irin tozarci da wula?anta mata da bamu yi ba. Ni Hameeda ce ta matsa kullum kuka da magiya akan in dawo da'ita kullum sai ta turo mun sa?o. tunda na rabu da'ita wallahi tace mutumin arziki bai sake zuwa wajenta ba da iskanci ake zuwa mata. Yana Waya daga cikin matsalolin da zawarawanmu na ?asar hausa suke fuskanta. Allah kada kasa ?a?anmu su WanWana iriyar azaba da tozarcin da mu muka ma mata, Allah ka tsayar da sakamakon a iya kanmu Allah mun tuba. Mustapha kaji tsoron Allah girma fa ya kamamu ya kamata mu watsar da komai a tuba kuma. Club Winnan ka dena zuwa ka tuba ga Allah"
Mustapha jikinshi yayi sanyi ya san Babangida ne kaWai yake iya tsage mishi gaskiya duk Wacinta sai kuma mahaifinshi. Ga babban yaronshi ya afka shaye_shaye neman matanma uwar tace yana taSawa bai tashi ankara ba sai da komai ya lalace sakamakon ri?on sakainar kashi da yayi ma ahalin nashi kaico.
"Ai na dena kulobin tuni Babangida dake ka jima baka ziyarci majalisarmu bane shi yasa. Na riga na tuba kuma nayi ma Allah al?awarin bazan sake ba."
Haka Mustapha ya tusa Adeeza a gaba suka koma gida.
Washegari da daddare ?ar Shuwa na zaune sai ga kiran waya daga mahaifiyarta.
"Ke Aisha wata Sabuwa wani babban al'amari ya faru fa. Bana sanar dake su Maigogul sun bar unguwarnan ba anata raWe raWin sun siyar da gidanne ba? "
?ar Shuwa da gabanta ya tsinke tace.
"E Mama yanzun wani abune ya faru kuma"
"Hmmm gidan anata gyara ana mishi kwaskwarima in faWa miki har da tsayin katanga ake ?ara musu. To yau sai ga Hauwa ta le?o unguwar shine take faWa mun mummunan labari wai Sabuwa ashe tayi aure? "
Baki ?ar Shuwa ta washe wani farin ciki ya lulluSeta.
"Mama ai aurenta shine kwanciyar hankalina"
"Inji uban wa kinsan yanzu Sabuwa da Maigogul suna umara, sannan daga can Dubai zasu wuce acan zasu haWo lefe. Ga gidan sama ya siya musu shi mijin sun bar unguwar, nasu gidan ana gyarashi zasu zuba haya. A yadda Hauwa take labarta mun tace babban mutum ne wanda ya fito daga babban gida gidan malumta sanannu"
Ai ba shiri ?ar Shuwa ta mi?e ta shige uwar Wakinta ta shiga zirga zirga ita kaWai sun jima sunata waya da Mama kafin daga bisani ta kashe wayar ta shiga kaikawo idanunta duk sun rufe tsabaragen ba?ar hassada dake damunta.
Kuka ta fashe dashi tayi tayi ta ?oshi ta dawo ta zauna shirum.
"Umara harda Maigogul sannan lefe a Dubai. Kenan Sabuwa kuma fina tayi? Ina inna yadda Allah ya tsine mun saina sakarma Sabuwa Sera a yayi duk inda dangin mijinta suke saina nemo su na sanar musu wacece Sabuwa. Dan nasan zaiyi wuya susan wacece ita"
Babangida ne ya kira sunanta da ?arfi. Tana Wagowa suka haWa idanu.
"Abincinki ya gama babbakewa kina Waki ke kaWai kina surutan banza da wofi lafiyarki ?alau kuwa? "
Murmushin mugunta tayi tace.
"Ashe Sabuwa tayi aure. Mijin ma ya biya musu umara ita da Maigogul yanzu haka suna can"
Dummm _dummm zuchiyarshi ta buga ?irjinshi ya wani yi jijjiga ta ciki.
Take yawu ya sar?eshi ya shiga tari kamar zai mutu.
Da sauri ta kawo mishi ruwa ya zauna akan gadonta ya sha. Ita kuma ta tafi ta sauke girki ta dawo.
"Ke a ina kika ji tayi auren harma tana umara? "
Dariya tayi yadda taji muryarshi ta koma.
"Labarin duniya baya Suya duk da Soye abun suke yi. Amman ya fito fili dan ance auren ma ya jima gaskiya. Ya sake musu gida tsohon gidansu kuma ya Waura Gaza akan aikin gidan. Ance ma daga Umarar dubai suka nufa acan zata haWa lefe"
Kai Babangida ya ri?e yanajin duniya na jijjigashi tana watangaririya da rayuwarshi abu kamar wasa wallahi da ?yar Babangida ya fita ya koma Wakin Ramatu. Bacci ya ?aurace ma idanunshi duniyarshi ta tsaya cak.
Wasane gaskene kafin gari ya waye Babangida baya ko iya Waga hannunshi, baya kuma gane waye

15 / 28