Idan Kaya Ya Gaji Gammo Ma Ya Gaji 4 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Fareesa Category :  Romance

Chapter   21 / 28

60K to 63K   out of 83.6K words

ta kawosu sai kuma abokan kasuwancin Kayi nayi suma sunzo sun mata kara sosai a wannan karon.
Wajajen azahar sai ga Malama ?arama da su mardiyya suma sunzo. Mardiyya da malama harda kayansu kala bibbiyu a leda suka zo. Aminu da AWWa'u kuma sunce a wajen su Rakiya zasu zauna har su Adda su dawo.
Har Wakin Rakiya nabi malama ?arama na tsugunna aka gaisa. Ta mi?o mun kuWi masu yawa tace malam ne yace a kawo mini agen
Wannan kuma nata ne kulace mai kulu mai kyau sosai.
Godiya nayi mata sosai na fito
Nan Mardiyya ta mi?amun ambulon a manne fari wai gashi inji Babansu. KarSa kawai nayi na cusa a jakata tare da kuWin da Baba malam ya bani.
Da misalin ?arfe uku dangin ango da dandazon masu Waukar amarya suka zo a cikin zu?a zu?an motoci.
Ni dai jikina har rawa yake yi Malama ?arama ta dan?ani a hannun wata Dattijuwa. Fuskata a rufe kamar sabon aure jikina kuwa sai rawa yake yi zazzaSine sosai wallahi a jikina.
Da bismillah na fito daga samanmu ina ri?e gam da hannun Maigogul muna ta ratse mata aka sakani a cikin mota ni da Rahama da Madamcy. Maigogul nake ta kallo shima idonshi a kaina ga Rakiya a gefenshi.
Maigogul kace tare zamu tafi dan Allah ni ka shigo mu tafi tare"
Sai na saki kuka. Rakiya tace.
"Dake ku abun kunya gaba kuke bashi ba baya ba ai dole kice yazo mitsiyaciya. Maza dai yaje ya kaso miki auren kinga ai sai ku tare a gidan Amaryar tashi tare tunda Uzairu zuchiyatama yace can zai koma. Wawuyar banza in banda hauka ina aka taSa hakan? Ai ko kawoki cikin mota da yayi yana ratso mata kaWai abun kunyane."
Nan Rakiya ta shiga kumfar baki. Maigogul yayi ?ur yana kallona idanshi fal da hawaye, kawai saiya faWa gaban mota yana goge idanshi. Rakiya ta zagayo tace.
"Ai ko dai wallahi anji kunya raka Amarya da ubanta ko da yake ga can abokin sheWanancin naka Cicib ma ganin shigarka mota shima ya shige daga can sai ka zauna a wajen Amaryarka mu kuma sai mun ganka sallamemme"
Allah ya so mu direban motar tamu baya ciki da a gabanshi za'ayi wannan aikin. Sai daga baya ya shigo. Duk da Maigogul bai sake kallon Rakiya ba.
Rahama ta fita su dasu Sadiya suka shiga tantance waWanda za'aje dasu.
Motoci biyar kawai aka cika ragowar a haka suka koma cikin gomboi muka tafi.
Mai mota ya sake mana wa?ar ranar murna gimbiya tahau dokin girma muiyo murna zamu tafi mu kaita Wakin aure.
Wannan wa?ar ko yau aka fileyin Winta ina tuno wannan ranar a ?wa?walwata.
Sai hawaye nake zubarwa duk na Sata fuskata da hawaye. Gashi nayi kyau kayan da Alhaji Zaidu ya zaSamun su na saka da setin gwal Wina na akwati, takalmi da jakan ma abun kallone.
"Lolo jikinki yayi zafi sosai. Ya kamata ci cire wannan tsoron dan Allah ki bari ayi a gama komai lafiya. Ke dai kiyi ta adda'a kawai. Naga Malama ?arama itama ta shiga mota ashe da'ita za'aje.
Ragowar kayayyakin da kika samu an Wura a buhu mun tawo dasu. Akwatunanki kuma naga mota daban akayi musu Sadiya ce ta shiga gaban motar su gidanki zasu wuce kai tsaye."
Kai kawai na gyaWa mata ina jin wayata na rauji amman wallahi na kasa cirowa a jakata sai Rahama ce ta zaro mun tare da Wagawa ta bani.
Ga wayar a kunnena ina jiyo sautin amon muryarshi
Wallahi na kasa magana ni kaWai nasan halin da nake ciki wallahi na tsorata da yawa kuma gani nake aurenma kamar zaman bazai yiwu ba.
Rahama ce ta zare wayar a kunnena ni kuwa na saki kuka kawai. Maigogul yau baya magana sai girgiza kai yake yi sabida shima kamar fa kukan yake yi.
"Alhaji Zaidu Rahamace Lolo dai ta kasa magana sai dai ?ila zuwa anjima"
Ta cikin wayar yace.
"Yaya Rahama dama ke kuna Dutse tare kenan, Su Yaya Labbaine suke Kano kenan? "
"E sune muna mota zuwa Rano da Amarya.
" To shikenan Ubangiji Allah ya tsare muku hanya. A kula mun da'ita sosai a tabbatar taci abinci in kuka isa Rano. Na dan?a miki ragamar kulamun da Shalelena Yaya Rahama"
Dariya tayi tace.
"In sha Allahu kuwa. To shikenan sai mun iso Kano nagode"
Ta kashe wayar ta dan?amun kenan sa?o ya shigo kamar haka"
"Shalelen mijinta nasan dai wannan kukan na farin cikine bana ba?in ciki ko nadamar aurena bane. Kukane na farin ciki da murnar shiga wata sabuwar duniyar soyayya. Shalelena gidana cike yake tab da soyayya na tanadar miki abubuwa da dama na soyayya wanda ba sai gobe ba ayau zaki soma gani.
Mijinki mai Wokinki a ko da yaushe Zaidul abeedin
Murmushi nayi tare da sauke ajjiyar zuchiya sassanya sai naji na samu ?warin guiwa sosai
Allah cikin ikonshi da amincewarshi sai gamu a Rano da yamma lis mune tafe_ tafe har ?ofar katafaren famili house Winsu Alhaji Zaidu wanda yake Wauke da gini irinna sarauta da ganin ginin kasan irin gidajen gaggan masu kuWin da Winnanne.
A hankali na fito daga mota Malama ?arama da Rahama suna ri?e dani, Madamcy na ri?e da jakata haWe da wayata.
Maigogul yana cikin mota su basu sakkoba ma.
Ina cikin mayafi ina ?irga zauruka saida muka shiga zauruka goma sha biyu kafin muka shigo ainihin gidan.
An yi ma gidan ginin zamani sosai ta ciki. Ha?i?a daga waje in kaga gidan ba zaka taSa tsammanin haka zaka shigo ka tadda cikin ba.
Masha Allah Al'umma dai kuwa akwaita cikin wannan gida. Muna shigowa aka soma yiriririr.
Nan wata farar Dattijuwa tace.
"A wuce dasu shiyyar Goggo Amfana maza Mariya. "
Kafin mu kai ga bin Mariya su Hajiya Balaraba dasu Hauwa suka iso suma sai muka Wunguma du tare zuwa Sarayin Goggo da akace.
Tsofaffine a falon kusan su bakwai wannan na wane waccan a tsufa. Haka na gurfana gabansu kaina a ?asa bana ko iya Wagoshi sai dai kama muryoyi kawai nake yi.
Gaisuwace ta wakana kusan na minti biyar abunka da gidan Malunta wannan Tsohuwa mai suna Goggo amfana ita ta buWe taro da adda'a adda'a ta larabci zuryan tare da yin sallama duk muka amsa kafin ta soma da cewa.
"To Sabuwa muna farin ciki sosai da shigowarki cikin wannan zuriya tamu mai Wumbun tarihi da daraja. Mu nan da kike ganinmu daga iyayenki sai kishiyoyinki anan wanda da sannu zaki gane matsayin kowa tunda ana yin taro sau biyu a shekara. Sannan ko biki ko suna ?wai da ?war?wata ake taruwa ayi, in abun kukane haka za'a haWu a jajanta ma juna.
To kin shigo gidan yawa dole kiyi ha?uri da abubbuwa da zaki ji zaki kuma gani ko ba gaskiya ba? Kisa a ranki zaman mijinki kike yi ba zaman burge kowa ba. Amman ki rungumi dangin mijinki ki ba kowa matsayi daidai dashi. Wanda yace yanayi maraba, wanda yace bayayi umma ta gaida Aisha. Ba za'ace duk wannan taron kowa ya soki ba, kuma ke kanki ba zaki iya son kowa ba.
Uwargidanki ba mace bace mai matsala ba mun shaida tunda ta zauna zaman mutunci ba da kishiya Waya ba bada kishiya biyu ba mun shaida wannan. Ki yi ?o?ari kibi layinta a zauna lafiya.
Mijinku kune masu kwantar mishi da hankali a duk lokacin da wata damuwa ta dameshi, to hakan baya samuwa sai kun haWe kawunanku"
Haka sukaita yi wannan ta zu?a ta cika taba wannan ta guntsa sukaita mun nasihohi masu ratsa jiki. A maganganunsu wallahi na tsinci abubbuwa da yawa kuma na yaba ma waWannan tsofaffin gaya.
Cikinsu ko wacce kuWi ta bani sai Goggo Amfana data Wakko Wan kunne da sar?a na azurfa dahuwar da masu kauri sosai.
"Wannan ki ri?eshi da kyau. Tarihine mai tsawo inata Soyonshi Allah yasa rabonki ne haka kurum naji ina sonki fiye da ragowar matan da Zaidu ya aura. ?ila rabonshi na jikinki ne" Nan akaita Allah yasa Allah yasa.
Nan kuma suka ?are da koke koke dai da tuno mahaifan Zaidu da suka rasu.
Daga ?arayin Goggo Amfana an kaini shiyya shiyya takwas da nata tara kenan. Ba fa ?arewa suka yi ba dattijan gidanne suka shigo suna faWan a sake mu hakanan dare yayi mu kama hanya.
Wallahi duk shiyyar da muka shiga kuzo kuga abun alkhairi zumunci garesu sosai. Daga masu kuWi sai masu bani turaren wuta, sai masu bani turmin zani, masu bani takalmi nayi harda wacce ta bani ?atoton zanin gado Wan madina fari sol babban gaske.
Sai da mukai Isha muka ci tuwo kana aka sallamemu. Ni dai naji an sakani a mota Adama da Sadiya suka biyoni.
Sai taran dare muka iso gidan Alhaji Zaidu, Anan Maigogul mukai sallama na rungumeshi inata kuka yana rarrashina, Hajiya Balarabace ta janyeni. Na gaji iyakar ?arshe bana sha'awar komai sai in yi wanka in haWiyi maganin zazzaSi in kwanta kawai. Nasan hakan bazai samu ba tunda akwai dina
Amman ina ana shigo dani Hajiya Balaraba da Hauwa, da Malama ?arama da Baba Laraba suka nufi Sarayin uwargida dani. Sha?e da mutane Sarayin sai tashin hayaniya kawai kake ji.
Waje aka bamu muka zauna nima ina daga kan kujera a cikin mayafina.
"Wacece Uwargidan a cikinku ne bayin Allah. Gara muyi a gurguje mu samu muje mu kwanta mun shawo hanya"
Cewar Hauwa dan da muka shigo madadin su mayar da hankalinsu garemu sai suka ci gaba da hayaniyarsu.
Wata matace ta shigo ?amshin turarenta ya daki hancina ga ?aran takalminta mai tsini.
"Ah marabanku Amaryata ta iso ashe. Ai Hajiya Balaraba da kun wuce da'ita Sarayinta ta watsa ruwa taci abinci ga Dina da aka shirya Alhaji yace daga Rano kuke ma ?an zuwa dina duk suna can nima ku nake jira"
"Ai babu komai dama gaisawa muka kawota kuyi a baki girmanki ko? "
"Ahh babu komai wannan al'adar bana fiye sonta Amaryata a barta ta huta ta samu ta shirya awa Waya gareta kawai"
Matsowa tayi kusa dani ta shiga mayafin da nake ciki a hankali na Wago muka haWa idanu tubarkallah masha Allah itama tana da kyanta daidai misali wallahi yabon gwani ya zama dole. A yadda nayi tunaninta ba'a haka na ganta ba. Na zaci ?atotuwace ashe bata da irin wannan ?ibar ta Hajiyoyi ta dai kai Rahama jiki kamar dai ni da rabi da kwatana bata ?arasa biyuna ba. Nayi zaton farace sai naga ba?ace irin ba?innan na ba?a?en fata mazauna Amurka ( blacks American) Amman gaskiya ba yabon kaiba na fita kyau sosai. Tayi ado da gwala gwalai, ta zuba kayan kuWi sosai a jikinta. Tayi tsam da muka haWa idanu amman bansan menene daliliba dan ta kalleni ta maya harda mamaki akan fuskarta.
Sai kuma ta saki guda tare da dun?ulamun kuWi rafa uku tace.
"Amarya ta ?ara a kuWin li?i Allah ya bamu zaman lafiya yasa kin shigo kenan sai dai ki birneshi ko ya birneki ya kaWe fitina a tsakanin mu. Hajiya Balaraba a kaita Sarayinta. Za'a biyoku da abinci yanzu.
Alhaji ma ya shigo yafi a ?irga yana dakon zuwanku baku zo ba"
A dadda?ile take magana irin na madiga Winnan kun gane mata masu cikar iko.
Ni dai godiya muka yi muka wuce Sarayina.
Saida aka zaunar dani a bakin gado na sauke ajjiyar zuchiya tare da buWe fuskata na sarara.
"Sabuwa lallai Allah yana sonki irin wannan gida ko a mafarki ban taSa tunanin Aure zai iya kawo Waya daga cikinmu ba wallahi, sai gashi ke Allah ya zaSa ya kawoki. Gashi kishiyarki gaskiya halamunta ya nuna bata da wani matsala kema mun sanki sarai zamanku zaiyi kyau.
Kije ki watsa ruwa kizo ga doguwar rigar bacci ki saka Kafin a kawo miki kayanki"
KuWin da Hajiya ta bani na mi?ama Labbai.
Ki adanamun da wannan sar?ar da kudaWennan dana samu. "
Ina faWin haka na faWa banWaki dana saki ruwan zafi daidai_ daidai a jikina na duSe idanuna a cikin ruwan naga kyan banWakin sai kawai naji ina zubar hawaye.
Cikin ?udurar Allah harna gama wankan hawaye bai rabu da idanuna ba.
Ina fitowa na samu su Adama na cin abinci a tire ga kaji guda guda ko yankawa ba'ai ba kai da ?afa da kayan ciki kawai aka cire. Duk sun sake kaya sun saka ankon farin lace dake fararene sai suka fito kamar matan wasu hamsha?an Labbai har ha?orin makka na bogi naga ta saka, ga wata sar?a barawon zinari da duk suka saka.
Doguwar rigar baccin da Adama ta ciremun na akwati na zura kafin kayan nawa na dina su iso Alhajine ya kai Winkin. Nayi zaman dirshan na shafe jikina da Kulaccham ta jiki na wajen MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI kulaccham ce wacce take gyara jiki tasa laushi da she?in fata, bugu da ?ari ?amshi ya zauna daram a fata, gata Wauke da sirri mai girma.
Ina gama shafe jikina da man na bi jikina da humrori masu dogon tarihi na shafe jikina.
"Lolo waWannan kayan ?amshin na gaske ne nima zaki sanmun inje in ci amarci dashi wallahi naga Amaryar Maigogul tayo miki kayansu show glass guda muka je ?orayi gidan wata Farar Hajiya mai fara'a da sanin darajar mutane Hajiya Zainab sunanta Zee musa collection. Naga tana siyar da kaya ita kanta Hajiya zainab Win da dama, su kayan jinjiraye, atampopi, kayan Kitchen ke komai ma siyarwa take yi gaskiya."
Murmushi nayi nace.
Hajiya Labbai Amaryar cicib ohh duniya juyi juyi wai yau ke Cicib ya aura. Dan Allah daren farko yaya kuka yi ne? "
Adama harda ?warewa tsabar na bata dariya. Ita kanta Labbai Win har ?asa ta kwanta dan mugunta.
"Kinsan Allah banma taSa samun wani Wa namiji a kab mazajen dana aura a baya irinshi ba. Gaskiya uwargida take ta zage_zage. Daudunma yace mun zai dena tunda bana so. Yace tunda Maigogul ya dawo daga Umara yake ta faWa mishi ya sauke Daudu su fuskanci gaskiya da gaskiya. Kunga kuwa ai akwai damshin nasara ko? Ku dai ta taya ni da adda'a kawai amman fa naga waje wallahi, in dai mu'amalar Aurene to an rufe ?ofa kawai yasan takan mace."
Ai kuwa sai ga wayarshi ta shigo.
Ai saina shiga salati ita kuwa a guje tayi waje Adama tace.
"Ba gara Labbai ba. Nifa inna tuno zan koma malam Madori sai inji gabana ya faWi. Sabuwa Alhaji wani irin ?azamin mutumne sannan ranar kwanana baya Waga ?afa sannan salamatu kwanta kawai ya iya. Ga ba?ar wahalar gidan abun duk ya fice mun a raina. Amman haka damun koma Dutse nima zan tarkata in koma"
Tausayin ?an uwana ya kamani sosai.
Sallama muka jiyo a bakin ?ofa nayi saurin saka mayafina a ka na rufe fuskata.
Ashe Hajiya ce tana sanye cikin wani leshi mai manyan huda ja mai bala'in kyau kai da gani kasan da tsada. Takalmin ?afarta ba?ine mai tsinin gaske sai adon gwalagwalai da tayi su zobuna kawai saida tasa takwas wallahi kuma duk zinarine kwalliya irin dai ta alfahari. Ta sha ba?in goggoro tayi kyau.
"Amarya mai maganar siga. Da fatan kinci abinci dai ko? "
A_a fitowata daga wanka kenan yanzu zanci"
"Allah sarki. To dama Alhaji ne yake son ganinki yana waje yana jiran in kawoki. Kinsan fa bai fiye jin kunya akan abinda yake so ba"
Ta ?arashe da dariya. Mamakinta nake ji shin bata kishine irin na mata ita? Allah mai iko.
Ledar kayan dina ta mi?o mun Adama ta karSa.
"Bari in jiraki a falo in kin kammala sai mu tafi ko?
To nagode sosai"
Doguwar rigar wani irin leshi ne ko net ne ni wallahi nama kasa tantancewa tsabar kyau mai ruwan tokane kalanshi turarre, sai ba?in takalmi da goggoro ba?i a naWenshi yake sakawa kawai zanyi.
A cikin takalmin muka ga wata sar?a babba da Wankunne harda warwaro da zobe. Kuma wallahi gwalne Wanye ma kuwa.
Cire ta wuyana nayi na adana na saka wannan warwaron wacce na cire da zoben sai ban cire ba na ?ara na sabuwar sar?ar a hannun dama nasa zoben daidai hannuna kuwa warwaronne ma sukaimun yawa amman Adama tace in saka a haka.
A gurguje Sadiya tazo taimun kwalliya na fito shar dani goggoronne dai ya?i shiga kaina sam yayi mun kaWan.
Sadiya yi mun Wauri mai kyau kawai da Wankwalin kayana kinga har goma saura fa"
Ai kuwa Wauri ta buga mun gashina ya fito ya kwanta a tsintsiyar wuyana nayi kyau na musamman.
Fitowa muka yi tare Hajiya dake zaune a falo ta ?uramun idanu har muka sakko.
"Goggoronne bakya so baki saka ba? "
E ban fiye son goggoro bane shi yasa nace aimun Wauri kawai da Wankwalina."
Baki ta Wan taSe ina lure da'ita.
Wucewa muka yi ina jiyo muryoyin su Baba Laraba dasu Hauwa a Wakin dake ?asa sunata hirarsu.
Muna fitowa muka samu Alhaji Zaidu a tsaye ya sha malum malum ta waganbari mai ruwan toka anyi mishi ba?in surfani a rigar irinna sarakai, ga hularshi Zanna Bukar asalin babbar kunsun akwai Zanna Habu akwai Zanna Bukar =?? ?afarshi saye da ba?in takalmi mai rufaffen gaba.
Murmushi mai taushin gaske ya sakarmun tare da cewa.
"Wata barakallahu ahsanin khalikin."
Iyakar abinda yace dani kenan. Hajiya tayi dariya tace.
"Alhaji Manya to muje ko, kuyi gaba zan Wakko jakata"
"A_a mu na dai jiranki kije ki Wakko mu tafi uwargidan Alhaji Zaidu"
Dariyar manyan basawa tayi dan saida ta kaurara muryarta.
Tana wucewa Alhaji Zaidu ya jawoni ya shiga shinshinar ?amshina. Cikin wata muryar magagin ?auna yace.
"Zaki soma shiga turaka Shalelena yau. Zan jiraki komai dare ha?urin nawa ya ?are wannan ?amshi ya susutani"
Jin takun Hajiyane yasa na zame jikina da ?yar.
"Amman kamar zazzaSine naji a jikinki ai ko. Subhanallahi da kin sanar dani ai bama zamu je Dinar ba. No muje in baki magani kisha ki kwanta kawai"
Hajiya ce tace.
"Haba Baban Soyayya a daure dai. Anyo gayya gari _gari abokanka da matansu duk suna can suna jira kuma ace amarya da kanta bata samu Halartar wannan taron ba.
Muje akwai maganin warware gajiya a jakata sai in bata tasha a mota gabaki Waya Dinar ta awa biyu ce. KuWin da aka kashe ai bana wasa bane ko? "
Murmushi nayi nace.
Zan iya ma Hajiya dana sha magani in sha Allah zan warware"
"Yauwa ?anwata

21 / 28