Idan Kaya Ya Gaji Gammo Ma Ya Gaji 4 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Fareesa Category :  Romance

Chapter   2 / 28

3K to 6K   out of 83.6K words

Nasan ma nesa ba kusa ba in dai binciken asalina za'ayi ni dashi babu dacewar haWuwarmu, gashi daga tsatson malamai yake shima gashi Wan dangi. Ina tsoron amsarshi daga baya mu rabu in shiga damuwa ni ba ishasshiyar lafiya ba.
"Kina tunani ko? Ai ba dole sai yanzu zaki bani amsa ba zan baki lokaci har zuwa ki koma Najeriya kiyi shawara da Alhaji Baba da ?an uwanki abinda kika yanke a zuchiyarki sai ki sanar dani karki damu. Kuma kada ki zurfafa tunani da damun kanki.
Amman kada kiyi hukunci cikin gaggawa akwai yiyuwar ki haihu akwai yiyuwar baza ki haihu dani ba to kinga yana da kyau ki nemi zaSin Allah. Nima zan nemi zaSin Allah muyi istikara."
Kallonshi nayi na rasa tacewa sabida ha?i?a naji tausayinshi sosai da sosai, kuma ni tuni na amince dashi Haihuwa ni bazai zama matsala a wajena ba sam.
To shikenan Ubangiji Allah ya zaSa mana abinda yake mafi alkhairi."
Murmusawa yayi ya ?ura mun idanunshi masu kaifi yana mun kallon so dan yayi farin ciki sosai da furucina. Nima wallahi yayi mun ai dole ma yayi mun ni Win banza.
?urama junanmu idanu muka yi ga iska dake kaWa fulawowin lambun suna sakar mana ?amshi mai daWi sai yanayin ya zama na musamman lokaci guda wani irin sanyi ya soma busowa sai lumshe idanunmu muke yi.
Isowar uzairu zuchiyata ne ya katse mana daddaWan yanayin da muka tsinci kanmu aciki.
"Alhaji ina ganin muje ko magriba ta kusa"
Agogonshi ya kalla yace.
"To shikenan muje ma samu masallaci a hanya sai muyi Sallah. Amman ita gimbiya ba zata samu sallah ba.
Abinda zamu yi mu jira muyi sallah kawai in yaso sai mu fita kawai. "
Yanayi yana kallona. Ni dai ina cikin wani irin sabon yanayin da ban taSa shiga irinshi ba. Ga wani irin mugun sanyi da yake ta ratsani har kaWawa hanjin cikina suke yi,. Uzairu zuchiyata Baban ?arya rigarshi babu hannu amman ko a jikinshi sai dai duk tsigar jikinshi ta tashi ina kallonshi. "
Ciki na tashi na shiga ni da Felisha. Su Uzairu zuchiyata muka barsu zasu yi Sallah a cikin lambun.
Bayan na idar da sallah nayi gurum inata tunani ni dai tsorona guda Wayane kada mu soma daga ?arshe mu rabu.
Kai ina wannan ma yaudarar kaine lolo wannan ba kalarki bane gaskiya kada ki yaudari kanki.
Ajjiyar zuciya na sauke hawaye suka zubo mun. Wato kamun kai a rayuwa akwai daWi kaico da irin yadda muka tsinci kanmu. Ubangiji Allah ka kawo mana Wauki ka kawo mana hanyar shiriya ta inda zato bai zata ba.
Shigowar Felisha ya katsemun tunanina. Tana murmushi ta mi?o mun ?atuwar jaket fara mai gashi a wuyan irin na ( mage, kuliya, ?ar mussa)
Ina murmushi nima na amsa na zura na ?ara fesa turare ta ja hannuna muka fito.
A mota muka tarar dasu Uzairu Zuchiyata su suka zauna a gaba mu kuma muna baya lokaci zuwa lokaci muna haWa idanu mu sakarma juna murmushi na musamman.
Wannan daren ya kasance daga cikin dararen da suka tsaya mun a raina gaya.
Munyi yawo sosai a wannan birni mune gidan cin abinci mune siyayyar kayan sakawa da kayan ciye ciye dai. Shima Alhaji Zaidu a nan yayi ma iyalinshi tsaraba mai yawan gaske, nima haka yace in Wauki duk abinda nake so.
Da ?yar dai aka rabu har bakin hotel Winshi muka je muka saukeshi mu kai sallama da godiya muka nufi gida.
A cikin kwana bakwai Winnan sau uku muka haWu da Alhaji Zaidu, waya kuwa kullum sai ya kirani mun fi sama da awa guda muna hira duk da bai kasance mai yawan magana ba, amman yafi so dai ni ya tursasani in bashi labari.
Ranar da muka cika kwana bakwai a ranar jirginmu ya tashi zuwa Najeriya. Felisha da iyayenta har filin jirgi suka rakomu munyi rabuwa ta mutunci sosai. A cikin jirgi kuwa kujerar can bayana sosai Alhaji Zaidu ya zauna. Uzairu zuchiyata kuma kujerarshi a jere take da tawa. Idanuna na lumshe sai nake jin wani iri wanda ina kyautata zaton bazai wuce sabida Rabuwa da Alhaji Zaidu bane. A wannan kwana bakwai mun yi wata iriyar sha?uwa ta ban mamaki. Kuma na sake karantarshi sosai Wabi'unshi da irin yadda yake lallaSani abun yana yi mun daWi.
Haka muka kwana a jirgi washegari da misalin ?arfe goman safe sai gamu jirgi ya diremu a najeriya.
Ina tafe daga ni sai akwatin kayanmu. Uzairu zuchiyata da Alhaji Zaidu suna ta faman jan akwatunan namu kiyy_kiyy gaskiya mun lodo tsaraba sosai. Muna fitowa dan zuwa inda zamu samu tasi muka hango Maigogul tare da wani hamsha?in mai kuWi suna tsaye a gaban wata farar mota.
"Lolo ga Maigogul can yana ta washe bakinshi"
Cewar Uzairu zuchiyata. Saida gabana ya faWi dan tsorona Allah tsorona kada maigogul yaje yaita sakin layi a gaban Alhaji Zaidu.
?arasowarmu ke da wuya maigogul yace.
"Ka ganta Alhaji Maina Waya kenan tamkar ya dubu lolo ikon Allah. Mai sunan ummana kenan. "
Ni dai sai nayi turus nama rasa abun cewa.
"Ahh Alhaji ashe kuma zamu sake haWuwa, ahh ko kaima can canada Win kaje ne? "
Maigogul ke tambayar Alhaji wanda sai yanzu ya ?araso hannunsu na cikin na juna Alhaji Zaidu yace.
"Ai kuwa Alhaji can muka je. Harma naje can inda ita Shalelen taka suka sauka mun gaggaisa. Mun sameku lafiya? "
A cikin ladabi sosai yake maganar Maigogul kuwa sai rawar kai da Sarin zance yake yi.
"Ab kace kaga surukar tawa ma kenan? Allahu akbar amman naji daWi sosai. A wanne hotel kake a nan Lagos Win ko dai a yau zaka wuce arewa? "
Ya tambayeshi kafin ya bashi amsa yace.
"Lolo gafa Alhaji nawa da nake faWa miki. To shine da muka yi magana yace bari ya bar duk abinda yake yi mu tawo mu tarbeki kinga kwa Wan zanta ma hahaha"
Ya ?arashe yana dariya.
Alhaji Zaidu na kalla, shima ni yake kallo yayi mun ?ur ?ila yana son jin abinda zance ne.
"Masha Allah tabarakalla. Kai yanzu Maigogul kana da ?a kamar wannan shine ko hirar ba'a taSa yi mun ba duk surutunnan naka"
Uzairu zuchiyata na kalla. Yayi saurin cewa.
"Maigogul muje masauki wallahi yinwa nake ji sosai a jirgi muka kwana duk munyi tulus. Alhaji a wanne hotel zaka sauka?"
?ur nayi mishi da idanu ina son in karanci yanayinshi. Fara'ar fuskarshi dai ta ragu sosai.
Yana kallona ya faWa ma Maigogul hotel Win da yake sauka, ya sake lumshe idanunshi kafin yace.
"Kufa Shalele? "
Na Wago muka haWa idanu sai lokacin naga asalin yadda ya canja.
"Muma can Win muka nufa yanzu abinda za'ayi mu shiga mota Alhaji sai mu je dukka kawai"
FaWin maigogul. Kai Alhaji Zaidu ya girgiza yace.
"A_a Alhaji Baba ai abokina yana hanya zai tawo ya Waukeni kuma ma gidanshi zan soma sauka. Nagode sosai"
"To to shikenan. Zan kiraka a waya in mun nutsa dukkanmu in ka shigo hotel Win mayi magana kuma munfa gode Alhaji Babba. "
Maigogul ya shiga yi mishi fadanci. Ni sabida tsabaragen haushi harna shige motar da shi wannan mai ?aton cikin ya nuna mun. Ta gilashi naga Alhaji Zaidu ya ciro kuWin amurka ya dun?ulawa Maigogul a hannu.
Take hawaye ya zubo mun shar _shar.
Shigowarsu motar baisa na goge hawayena ba.
Ta gaban Alhaji Zaidu muka wuce idanu muka haWa dashi ya Wan sakar mun murmushinshi na kamilallun dattijai.
"Toh fa Alhaji Babba sai fa mun haWu akwai wata haja da zan tallata maka ne"
Rass gabana ya yanke ya faWi.
Shikenan maigogul zai tallatama Alhaji Zaidu sana'arshi sabida gani yake yi kowa watsattsene.
Muryar wannan Alhajin ce ta katsemun tunanina".

[10/4, 10:29 PM] +234 810 593 2041: IDAN KAYA YA GAJI...
GAMMO MA YA GAJI
LITTAFI NA HU?U
SHAFI NA BIYU




Maigogul inaga bari mu kaisu wajen cin abinci su ci su ?oshi tukunna. Amman lolo me kika ce.?"
?an murmushi nayi nace.
Naga Hotel Winma abincinsu yana da kyau ai gara muje can Win kawai."
Maigogul yayi dariya yace.
"Hakane Lolo suma abincinsu ?arshene. Uzairu zuchiyata ince dai kayo mun tsarabar abinda na bayar sallahu, kema Lolo ince dai kin siyo mun wani abun dai ko? "
"Ai dole Maigogul nayo ma kowa tsaraba. Taka tsarabar data Rakiya ma ta dabance"
Baki maigogul ya washe yana ta dariyar jin daWi. Ni wallahi tausayi ma ya bani
Oh shi maigogul babu abunda ya dameshi shi dai burinshi kawai ya samu abinda yake so.
Da waWannan tunane tunanen muka isa Hotel Win. Ni dai tunda aka nuna mun Wakinmu nayi shigewata dan mun gaji sosai.
BanWaki na faWa nayi wanka na Wauro alwala dan azahar tayi. Ina fitowa na buWe akwatina na zaro goduwar riga na zura, mayafin rigar na zaro sai katin Alhaji Zaidu ya faWo. ?auka nayi nabi numbobin da kallo na sake adanawa a cikin akwatin. Wayar da ya siyamun sabuwa na ciro na jona a chaji kana na tada kabbarar sallah. Ina zaune akan sallaya ina adda'ar Allah ya zaSa mun mafi alkhairi a cikin waWannan maneman nawa biyu. Duk da a zahirance Alhaji Zaidu yafi nagarta sai dai sanin baWini sai Allah masanin komai.
Amman ni dai hankalina yafi nutsuwa da Alhaji Zaidu. Na jiyo an danna ?ararrawar Wakin. A hankali na mi?e na je na buWe ?ofar wata ma'aikaciyace Wauke da abinci a tire ta diremun a ?aramin teburin Wakin ta fita.
Farfesun kaza ne sai shayi mai zafi. A tsanake na cinye shayinma na shanye shi tas nayi kwanciyata domin in huce gajiya.
Bacci nayi mai daWi cike da mafarkan Alhaji Zaidu. Ko dana farka naga ashe mafarki nayi ba zahiri bane sai kawai nayi murmushi tare da furta.
Allah yasa abinda na gani ya tabbata a gaske in dai kaine mafi Alkhairi"
Mi?ewa nayi na Wauro alwala dan ?arfe fa biyar lallai kuwa nayi bacci sosai. Kafin in kai ga soma sallah naji ?ararrawar Wakin tayi ?ara ashe Maigogul ne.
"Lolo bacci kike yi ne haka wai? "
E yanzu na tashi zanyi Sallah kenan.
"To kinsan fa jirgin ?arfe bakwai zamu hau mu koma gida ko? Ba kwana zamu yi ba. To Alhaji yana son ku Wan fita yace dani zai miki siyayya kuma yana so ku samu keSewa dashi sabida ku zanta.
Lolo dan Allah ki daure dai ki amsheshi zaki huta a gidanshi matanshi suna fantamawa wallahi gasar zuwa umara da Dubai kawai akeyi a gidanshi kafin Wayar Allah yayi mata rasuwa Wayar kuma sata ta kuntuka da dalolin amurka shine ya saketa.
Ungo wannan kwallin ki goga in zaku fita kada ki kuskure ki ambaci sunanshi in zaki shafa sunanshi Bilya muna kiranshi Bili maina sunane da ake kiranshi na gidansu. "
Hannu nasa na karSi kwallin.
Maigogul dan Allah wacce haja zaka tallatama wannan Alhajin da kace ne? "
Kallona yayi sai yayi murmushi.
"Lolo ki kwantar da hankalinki babu abinda na tallata mishi. Ba sana'ata na tallata mishi ba. Wasu motoci na tallata mishi sabida ?ulla ala?ar arziki. Shine yake sanarmun ashe shima yana da gonar motoci ashe hamsha?in mai kuWin gaskene. Yazo ai munfi awa guda muna hira. Ni lolo dama zaice yana sonki mana da mun caSa amman nasan ina bazai ce ba. Dan hamsha?ine sosai fa na fahimci haka a Wan bayanin da yayi mun.
Amman har hirarki nayi mishi wallahi na cusaki da dabars "
Me kace mishi to a kaina? "
"Me kuwa na sake jaddada mishi ke bazawarace mana da yawan yaranki, sai son taimakon ?an uwanki da kike dashi. Lolo na faWa mishi hakanne wala Allah ko zaiji wani abu a kanki. Ina sonki dai da arziki dan nasan kece zaki shiga cikin arziki mu kuma mu shiga cikin alkhairi dumu dumu. "
Dariya muka yi a tare daidai lokacin Alhaji Zaidu yazo wucewa. Muka haWa idanu haka siddan nake jin kunyarshi harma nake ganin tamkar na aikata mishi wani gagarumin laifi. Kuma ace ankai awa guda da Maigogul ana hira shikenan ai Maigogul ya kama tuSe mun zani nasan tas.
"Alhaji Baba kana ji da wannan shalele taka ni abun har burgeni yake yi"
Ya faWa a ladabce yana Wan murmushin da a ?asanshi akwai magana.
Ai firit maigogul ya juyo yana washe bakinshi.
"Ai wannan itace duniyata ita da Wan uwanta Uzairu zuchiyata. Yarane masu son iyayensu da tausayin kowa Alhaji. To ina dai sake lallashinta ne kan sha'anin zawarci kasan na faWa maka iddar bata daWe da gamawa ba. To ita tsoronta waye zai tausaya mata.....
Ni dai illahirin kunya bata barni na tsaya na gama jin abinda Maigogul zaice mishi ba.
Ya suka ?are ban sani ba. Kwallin daya bani na ajjiye a kan gado na tada kabbarar sallah.
Na Wan jima ina nazari har saida Uzairu zuchiyata aka aikoshi wai in fito Alhaji Bilya yana ?asa a mota yana jirana.
A yadda nake haka na fice sai kwalli dana zizara dan gudun kada Maigogul ya gane na?i saka kwallin daya bani.
Bani da burin kowa ya soni, ko in jawo hankalin wani ta hanyar asiri. Na fiso so yayi aiki da kanshi.
Kuma a cikin su biyunnan wallahi duk wanda ya nuna da gaske yake yi zan aureshi in sha Allah. Alhaji Zaidu ma nasan zuwa yanzu ya tsinke da lamarinmu.
Ficewa nayi sannu kan hankali na sauka ?asa har zuwa wajen mota.
Alhaji Bilya da kanshi ya buWe mun gidan gaba na zauna ya ja muka lula munyi tafiya mai nisa ba tare da yace dani kanzil ba. Nima bance ci kanka ba sai can dai ya Wan dubeni kaWan tare da washe bakinshi.
"Ai Sabuwa ban taSa sanin Maigogul yana da ?a tsaleliya irinki ba wallahi ai da tuni na lallaSo. Duk da dai ya faWa mun auren naki bai jima da ?arewa ba kuma a kotu ma aka raba auren. "
Wani ?ududune ya tokare mun ma?oshina jin abinda yace. Shi dai maigogul yafi sha'awar yaita bayani. Yanzu ina shi ina bama Alhaji Bilya labarin yadda aurena ya mutu domin Allah fa?
Nasanma ya riga da yasan komai ma. ?an murmushi nayi nace.
Kasan komai kamawa take yi yanzu gashi data kama mun haWu"
Dariya yayi yace.
"Hakane Sabuwa. Ai gaskiya inna sameki na rufe ?ofa da kyau. Wannan ke ai duk wata semina dake za'aje su Hajiya sai dai suyi ha?uri kawai tunda babu ?asar da basu zagayaba adai ?asashen da nake hulWa dasu. Wani sa'inma nakan rasa mai mun rakiya dake duk suna kasuwancinsu a lokacin muna tare. To ita Wayar rasuwa tayi. ?ayar kuma da mun rabu amman Allah cikin ikonshi an mayar da auren sai dai bata tare ba.
Ke in munyi auren me kike so ki ri?a da zaki juya taro ya dawo sisi? "
Idanuna na lumshe a hankali na buWe sai nace.
To wannan maganar ai inaga a barta har sai zuwa in anyi auren a tattauna. Kenan yanzu matarka Waya ko? "
"?warai kuwa matana Waya yarana ashirin cib kuma duk suna raye. Amman kada fa ki damu a gidana hatta gadon da kika kwanta masu aikine zasu gyara miki. Kar kizo kiji tsoron shiga dan kinji tulin yara ai gaskiya ne ko? "
Murmushin dole nayi kawai
Nasan a cikin raina Alhaji Bilya yayi ma ?o?ari da har yaji yana son aurena a irin rayuwata dai. Kuma nasan in baisan labarin rabin rayuwata ba. Tofa yasan kwata in dai Maigogul ne.
Haka dai na sake mukaita hira har muka iso wani ?aton kanti dake ?unshe da komai.
Da kanshi ya buWe mun murfin mota na fito. Ya tusani gaba muka shiga kantin ga ciki a gaba him.
Mata da maza anata kai kawo na siyayya a kantin kowa ka gani da kwando a hannunshi.
Wani layin turaruka da mayamayai da sabulai ya soma kaini.
A dai ta?aice yayi mun siyayya mai yawa danma ina no?ewane shi ba haka gogan naku ya so ba.
Mun dai tattauna babu laifi kafin muka dawo Hotel. Saida muka isa filin jirgi muke jin cewar jirgi sai gobe bakwai na safe zai tashi sakamakon babu jirgi a ?asa. Haka muka kuma dawowa Hotel
Da daddare ina kwance ga sabuwar wayata ga katin da Alhaj??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????i Zaidu ya bani.
Ina kwafe number wani shashe na zuchiyata yana nuna mun kada fa ace nayi azarSaSi da yawa tunda shima yana da lambata amman bai kira ba.
Wani shashen kuma yana jana da in kira.
Take nabi shashen da hankalina yafi raja'a a kai na danna kira tare da karawa a kunnena ina kuma dafe da ?irjina.
Wayar kamar dai zata tsinke sai kuma aka Waga.
Da kuma naji muryarshi ya ratsa dodon kunnena saina kasa sarrafa harshena yana sallama amman da ?yar na iya amsawa.
Sautin murmushinshi da ajjiyar zuchiyarshi suka sake sani faWuwar gaba.
"Shalele kin kuwa kirani a daidai. Dan Wazu kasa mallakar kaina nayi har da zanje in tambayi Uzairu lambarki sabida na rasa lambar taki a wayata. to kunyar Alhaji Baba ce tasa har naje ?ofar Wakin na juyo na dawo nawa Wakin.
Yanzunma a kwance nake zuchiyata nata ?ara burun?asamun ke.
Murmushi nayi mishi mai sanyi tare da cewa.
Allah sarki nima ina kwance ne shiru shine nace dai bari in taSoka to gashi ka sake samu lambar wayata"
Murmushi yayi yace dani.
"Kin kuwa kyauta sosai yanzu zan saka ma lambar sabon suna. In kuka koma gida yaushe ni za'a bani damar zuwa inji amsata kar daga kallon ruwa kwaWo yayi mun ?asa. Naga wani Alhajin nason ya kasani a hannun Shalele. Duk da a jikina nake jin shalele dai tawa ce"
Mun jima muna hirarmu ta mutunci da dattijantaka da natija.
Ni na zaci saurayi da budurwa, ko ince ma'abota soyayya dole sai sunyi batsa shine soyayya ashe sam ba hakan bane.
Duk samarina in banda Madubala in sun kirani a waya maganganune na tayar da hankula kawai muke aikema juna, sai yau da naji wani sabin abun
Daga ?arshe mukaima juna sallama.
Zukatanmu suka kwana a cike da farin ciki. Ni dai a ranar nayi mafarkai da yawa daga wannan mafarkin in Sulla wancan sai dai kash ba irin mafarkan da in aka wayi gari zaka iya tunasu turyan _turyan bane sai dai ka tsinci na tsinta.
Da sassafe muka wuce Airport da ni?i ni?in kayayyakin tsarabarmu.
?arfe bakwai

2 / 28